Thursday 14 September 2017

1. YAWON DUNIYAR HAJJI BABA Na James Morier Abubakar Tunau Ya Fansar Da Shi

Tura Wannan Zuwa

GABATARWA
Kamar yadda mu ke fada kullum, littafi shi ne
abokin hirar mai ilmi. To, yau kuma ga shi
malamai sun sami abokin hira wanda zai kayatad
da su cikin hirarsu. Wannan littafi na Yawon
Duniyar Hajji Baba, shahararre ne, domin yanzu
da buga shi da harshen Turanci ya fi shekara
dari da talatin. Ganin yadda duniya ke ta koda
shi, shi ya sa muka buga shi, cikin harshen nan
namu. Da can an taba jera labarunsa bi da bi a
cikin Gaskiya, to, amma da ya ke a warwatse ne
ya ke ba safai za ka sami wanda ya yi kokarin
tara shi sosai daki daki ba. Sai muka yi sa'a
Alhaji Abubakar Tunau ya tara guntayen labarun
nan har ya maishe su kamar littafi, saboda haka
muka fanshi nasa, muka buga shi ya zama littafi
domin jama'a kowa da kowa ya iya samunsa ya
saya.
Wanda ya fara rubuta labarin nan a cikin harshen
Turanci, shi ne Mr. James Morier, wanda a
lokacin nan yana wakiltar Sarkin Ingila a fadar
Sarkin Farisa a Tehran. Ya tsara labarin nan na
Hajji Baba kamar shi Hajji Baba din ne da kansa
ya ke bayar da labarin kansa, da kansa. Bismilla,
Malam.
BABI NA 1
Haihuwata Da Shigata Makaranta
UBANA sunansa Hassan, yana kuwa daya daga
cikin wanzamai wadanda suka shahara a Isfahan.
Yana da shekara goma sha bakwai ya auri wata
'yar wani dan kasuwa wanda ya ke
makwabcinsa. To, Allah bai nufi matarsa da
haihuwa ba, don haka bai kula da ita ba. Amma
gwanintarsa ta wanzanci, musamman tsakanin
’yan kasuwa, ta sa bayan shekara ashirin ya sake
auren wata yarinya ’yar wani mai arziki. Bai sha
wata wahala game da auren nan ba, domin ya
saba da mai arzikin, kuma shi ya ke yi masa
aski.
Bayan da ya yi wannan aure na biyu, sai ya
shirya ya ziyarci kabarin Husaini a Kerbelah, don
ya gudu daga kishin matan nan tasa ta fari. Shi
ke nan ya dauki matarsa ta biyu suka tafi. A kan
hanya Allah ya ba ta cikina, ta haife ni. Tun kafin
wannan tafiya sunan da a ke kiran ubana, shi ne
Hassan Wanzan, amma tuna da ya dawo sai aka
kankare sunan nan Wanzami. Ni kuma aka yi mini
Iakabi da sunan Alhaji. Da wannan suna aka fi
sanina duk cikin zamana na duniya.
Lokacin da ubana ya yi wannan tafiya, ya bar
aikinsa a hannun mataimakinsa. To, da
dawowarsa sai ya koma ga aikinsa haikan. Ganin
kwazonsa ga aikinsa sai hankalin malamai har da
na 'yan kasuwa ya koma gare shi. Ni kuma tun
da ubana yana sona da wanzanci ne, bai yarda
karatuna ya wuce na salla ba. Amma na yi sa’a
akwai wani malami wanda ya ke da makaranta a
jikin masallaci. Ubana kuwa ya kan yi wa
malamin nan aski ko wane mako sadaka. Shi
malamin ya kan biya ladan askin nan da koya
mini karatu da rubutu. Na kuwa ci gaba kwarai
da gaske, don cikin shekara biyu na iya karanta
Alkur'ani, na kuma fara rubutu yadda za a iya
karantawa. Duk sa'ad da ban tafi makaranta ba,
sai in tafi dakin aski in rika koyo. ln kuma akwai
mutane masu son aski da yawa, a kan yardam
mini in gwada akawunan masu kora alfadarai da
rakuma. A wani lokaci kuwa su kan biya kudi
masu yawa.
Lokacin da na cika shekara goma sha shida, yana
da wuya a bambance ko ni cikakken wanzami ne,
ko cikakken almajiri. A wajen aski, da gyara
kunne da gyara gemu na zama shahararre.
Wadansu dabarun ma da na ke da su ba wanda
ya san su sai ni kadai.
A wajen ilmi kuma hakika kam na gode wa
Malamina, don na sami isasshen sani na
mawaka. Sanin nan ya sa na ke iya magana mai
dadi, har ina kawo nassi. Har wa yau kuma
wannan, game da muryata mai kyau, ya sa duk
wadanda na ke yi musu aiki suka danke ni kamar
abokinsu. Kai, a takaice na zama mai farin jini
tsakanin masu arziki.
Dakin aski na ubana yana kusa da wani gida na
saukar baki ne. Dakin bakin nan shi ne mafi
girma a birnin, sa’an nan kuma shi ne mutane da
yawa suka fi shigarsa. Baki da dama, har ma da
’yan gari da masu ciniki, cikinsa su kan shiga. To,
irin wadannan a wani lokaci su kan biya kudin
aski fiye da yadda aka kayyade, don suna ganin
wasannin ban dariya da na ke yi musu. Har ma
daya daga cikinsu, wani dan kasuwa na kasar
Bagadaza, ya yi sha’awata kwarai da gaske, ya
ce zan rika yi masa aski kullum.
Dan kasuwan nan ya kan sa ni mu yi tadi cikin
harshen Santambul, don na iya dan kadan. Cikin
tade-tademmu ne fa ya fara ba ni labarin kyaun
birane da shi kansa ya ziyarta. Ai fa sai na ji ina
son yin tafiya. A lokacin nan kuwa yana son wani
mataimaki, don ya rika rubuta masa lissafe-
lissafen kudinsa. Da ya ke na iya rubutu, sai ya
neme ni don in yi masa aikin. Ni kuwa na yarda,
sa’an nan kuma nan da nan na fada wa ubana
irin niyyata. Ubana yana kishin rabuwa da ni, don
haka ya yi kokarin ya rinjaye ni, wai bai kamata
im bar baiwar da Allah ya ba ni in kama wata
dabam wadda ta ke mai hadari ba. Amma da ya
ga amfanin albishirin nan da dan kasuwan nan ya
yi mini, ya ga lalle mai yiwuwa ne ni kaina in
zama dan kasuwa nan gaba, sai ya daina yi mini
magana. Daga karshe ya sa mini albarka, ya
kawo dan akwatin sababbin asake ya ba ni
kyauta.
Uwata kuma ta yi bakin cikin rabuwa da ni, tana
fada mini irin hadarorin da ke kan hanya, amma
duk da haka hankalina bai fita daga wannan
tafiya wadda na sa raina ba. Ka san yadda
kaunar uwa ta ke ga danta, sai ta kawo jakar
biskit ta ba ni, ta kuma hada mini da wani
magani, wanda ta ce zai iya warkar mini da
ciwon kai da amosani. Ta kuma ce mini in zan
fita sai in fita daga gidan da baya, walau idanuna
suna duban cikin gida. Wai idan an yi haka sai a
dawo gida da murna.
To, shi maigidan nan nawa ana kiransa Usman
Aga. Ya shirya kome na tafiya zuwa Mashed.
Dalilin wannan tafiya, shi ne don ya sayi fatun
raguna irin na Bukhara ya kai su birnin
Santambul ya sayar. Maigidana gajere ne
kakkaura mai katon kai, hancinsa dogo, ga bakin
gemu. Duk wanda ya siffanta mutum mai
wannan bayani, to, tamkar ya ga maigidana ke
nan.
Ban da wannan shi Musulmi ne na kirki, mai
kokari wajen ibada. Amma fa burinsa shi ne
samun riba. Duk ran da zai kwanta barci, sai ya
tabbata ya ajiye kudinsa inda ba wani abin da zai
taba su. Ko da ya ke shi mai tsumulmula ne, duk
da haka yana taba dan nishadi. Ya kan sha taba
kullum, ya ci abinci mai yawa, ya sha giya a
boye. Domin shi da kansa ya sani in an ga
Musulmi ya sha giya ya zama mutumin banza.
A cikin shirin nan na tafiya maigidana ya sayi
wani alfadari kakkarfa, don hawansa. Ni kuma
aka ba ni doki wanda zai dauke ni, ya kuma dauki
wadansu kaya. Akwai kuma wani bawa mai yi
mana girki da ’yan aikace-aikace, da kuma wani
wanda ya ke dauke da akwatuna biyu na
maigidana. Ana gobe za mu tashi sai maigidana
Usman ya dauki kudi kamar £30 ya dinke su a
kokuwar hularsa, don ko da wani hadari zai faru
a kan hanya. Duk cikin 'yan tafyan nan ba wanda
ya sani sai ni da shi. Sauran kudinsa kuwa,
wadanda ya ke son ya yi saye-saye da su, ya
dinke su a cikin jakankunan fata, ya sa su can
karkashin akwatunansa.
Bayan da duk ayari ya gama taruwa, sai aka tarar
akwai alfadarai da dawaki guda dari biyar, da
rakuma metan, yawancinsu duk dauke su ke da
hajja wadda za a sayar a kasar Farisa. Ban da su
kuma akwai mutane dari da hamsin, daga 'yan
kasuwa sai barorinsu sai kuma madugai. Har wa
yau kuma akwai wadansu alhazai wadanda za su
je ziyara ga kabarin Imam Reza a Meshed.
Ko wane dayammu yana rike da makami.
Maigidana kuwa da ko ganin bindiga ba ya son
yi, kuma in ya ga takobi tsirararsa sai zuciyarsa
ta baci, yau shi ne da rataya katuwar bindiga da
takobi. A bel dinsa kuwa ya makala kananan
bindigogi biyu. Sauran jikinsa kuwa duk rufe ya
ke da su harsashi da sauran makamai. Ni ma
kaina tun daga kai har kafa makamai ne, amma
na fi maigidana da abu daya, shi ne ina rike da
wani katon mashi. Bawan da ke yi mana girke-
girke kuwa ya dauki wani karyayyen takobi da
wata bindiga mara kunama!
.
Zamu cigaba Insha ALLAH
.
.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba mungode Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
.
Source By ©Bukar Mada

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: