Sunday 17 September 2017

2. YAWON DUNIYAR HAJJI BABA Na James Morier Abubakar Tunau Ya Fansar Da Shi

Tura Wannan Zuwa

Ko wane dayammu yana rike da makami.
Maigidana kuwa da ko ganin bindiga ba ya son
yi, kuma in ya ga takobi tsirararsa sai zuciyarsa
ta baci, yau shi ne da rataya katuwar bindiga da
takobi. A bel dinsa kuwa ya makala kananan
bindigogi biyu. Sauran jikinsa kuwa duk rufe ya
ke da su harsashi da sauran makamai. Ni ma
kaina tun daga kai har kafa makamai ne, amma
na fi maigidana da abu daya, shi ne ina rike da
wani katon mashi. Bawan da ke yi mana girke-
girke kuwa ya dauki wani karyayyen takobi da
wata bindiga mara kunama!
Kashegari da asuba madugai suka yi ta ihu suna
buga ganguna, lokacin tafiya ya yi. A wannan
tafiya ne muka saba da mutanen da da ba mu
san su ba. Haba, wannan tafiya ta faranta mini
rai da gaske. Don murna da doki sai ka ga na
tsikari dokina ya yi gaba, sa’an nan in dawo
baya. Ashe maigidana ba ya son haka. Ya kwabe
ni wai in ina yin haka dokin ba zai iya karasa
tafiyar ba. Ga. mu nan muna tafiya har muka ci
zango guda zuwa Tehran, ba abin da ya auku
gare mu.
A Tehran muka ya da zango, muka yi kwana
goma, don dabbobimmu su hutu, don kuma mu
kara samun wadansu mutane mu yi kauri. Mun
san a kan hanya za mu hadu da hadari, domin a
lokacin nan wata kabila ta 'yam fashi tana yaki
da Sarkin Farisa, an kuwa ji labarin sun rufe
hanya. Domin bai dade ba da suka auku wa wani
ayari, suka kwace kayansu, sa'an nan suka kama
su duka suka sa su bauta. Sabodu wannan hadari
da ke gabammu kowa sai ya shiga tsoron
karasawa Meshed, musamman maigidana. Amma
labarin da ya ji na fatun raguna suna kudi a
birnin Santanbul ya sa yu manta da mutuwa, ya
dada niyya, bai yarda wani abu ya tsorata shi ba.
Ashe tun kafin mu iso Tehran wani mai lura da
alhazan da za su hajji ya tara mutane, don an ji
labairin muna zuwa. Da zuwammu sai ya fada
mana wai shi da mutanensa da dama sun shirya
su tara tafiya da mu. Ya kuma ce ya kamata lalle
mu yarda mu karbe su, don irin hadarin da ya ke
gaba. Mutumin nan sananne ne a tsakanin
hanyar Tehran da ta Meshed, har ya yi suna a
kan wani abin dariya da ya yi. Wata rana ne ya
iske wani dam fashi matacce, sai ya sa takobi
ya sare kan, ya yi ta kirari wai ya yi jaruntaka !
A hankali ya rinjayi maigidana ya yarda ya bi shi.
Bayan da muka shiga masallaci ranar Jumma'a,
sai muka dunguma wani kauye wanda a ke kira
Shahabul Azim, inda za mu kwana mu yi
sanimako.
BABI NA 2
Na Shiga Bauta
KASHEGARI muka fara tafiya a hankali. Ba a
maganar kome sai ta kabilan nan ta ’yam fashi.
Maigidana kuwa sai kuri ya ke yi, yana fadin abin
da zai yi ko da za a auka mana. Im mutum ya ji
abin da ya ke fada sai ya yi zaton duk cikin
zamansa na duniya bai yi kome ba sai yaki da
kisa. Akwai kuma abu daya da maigidana Usman
Aga ya ke kuri da shi, wai shi ma yana cikin
masu bin Halifa Umar ne. Su ma 'yam fashin nan
da danginsu Turkawa Halifa Umar din su ke bi. A
gare su launi tsanwa launi ne mai tsarki. Suboda
haka Usman Aga ya sami rawani tsanwa ya nada,
watau dabararsa ko da 'yam fashin za su auka
mana, shi ba za su kashe shi ba, sai su san
dan’uwunsu ne.
Mun yi kwanaki muna tafiya a cikin halin haka,
sai mai lura da alhazan nan ya ce mana mun
kusa inda ’yam fashin su ke. Don haka ya
kamata mu yi cincirindo wuri daya mu yi tafiya
tare. Mu kuma shirya sosai ko da za su auka
mana. Abin da maigidana ya fara yi, shi ne ya
daure bindigarsa, da takobinsa, da kananan
bindigoginsa a kan wani alfadari. Ya lullube
jikinsa da alkyabbarsa, ya murtuke fuska tasa, ya
kama tasbaha yana addu’a. Shi kuma mai lura da
alhazan ya rataya layoyinsa na kau da bara, wai
muddin suna tare da shi, ba kuwa kibiyar dam
fashin da za ta same shi.
Kwaram, sai muka ji karar bindiga, sa’an nan
muka ji wani irin ihu mai rarrawad da jiki. Sai ga
mu cif a tsaye tattare wuri daya, kamar ’ya’yan
kaji sun tsinkayo shaho! Da muka hango 'yam
fashin sun yiwo kammu, wadansu daga cikimmu
suka ranta cikin na kare, wadansu kuwa har da
maigidana suka dimauce, suka kasa gudu, sai
cewa su ke yi, “Ya Allah, ya Imam, ya Annabi,
yau mun lalace, yau za mu mutu, yau mun
mutu !" ’Yam fashin nan kuwa sai zubo kibau su
ke kamar ruwa. Malamin nan kuwa da ya ke
wannan ba bakon abu ne gare shi ba, ya gudu, ba
mu kara ganinsa ba, ko mu ji labarinsa. Da
zuwan ’yam fashin nan sai suka tasam ma duba
kaya, ko da ma ga su nan a warwatse ko ina.
Maigidana da tsoro ya cika shi, ya shiga tsakanin
wadansu manyan kaya ya boye, amma ina! Sai
da wani katon dam fashi ya sakuto shi. A da ya
tsammaci kaya ne, ya juya shi sai ga kafafuwa
da hannaye. Wohoho, maigidana ya yi ta kiran
sunan Halifa Umar, wai ko dam fashin nan ya bar
shi, abu dai ya ki. Dam fashin nan ya cire duk
kayansa ya bar shi daga shi sai 'yar ciki sai
kuwa rawaninsa, don darajar launinsa tsanwa.
Sa'an nan maigidana yana gani dam fashin nan
ya sa tufafinsa. Ni kuwa nawa tufafin da ba su
cika kyau ba aka bar mini abina. Amma abin da
ya fi sa mini farin ciki duka, shi ne ba wanda ya
dauki akwatin asakena. Bayan da ’yam fashin nan
suka kare bincike-binciken kaya, sai kuma suka
shiga raba mu, mu ne ganima da aka samu. Aka
rufe mana idanu, ko wane dayammu aka aza shi
bisa doki, muka kuwa dinga tafiya hakanan. Sai
da dare aka sauke mu a kogon dutse, muka huta.
Kashegari aka bude idanummu don mu ga gari.
Sai ga mu a wadansu hanyoyi wadanda ba
mahalukin da ya sani sai fa su 'yam fashi. Shi ke
nan muka sake tafiya, sai ga mu a wani makeken
fili cikin duwatsu. Filin nan don girmansa muka
zaci ko shi nc karshen duniya! A nan wurin muka
ga dakunan 'yam fashin ga su nan birjik, ga kuwa
garkunan tumaki ba iyaka.
Sa'ad da aka zo raba mu tsakanin wadannan
’yam fashi, sai ni da maigidana muka yi sa’a, aka
sa mu a hannun wanda ya sakuto maigidana
daga cikin kaya. Ana kiransa Alhasan Sultan. Sai
muka ga ashe shi babba ne kwarai da gaske a
wannan wuri, don yawancin dakunan nan da na
ba ku labari duk nasa ne, ga garkunan shanu har
iyakacin da idonka zai iya gani maka. Wadannan
gidaje nasa suna kan iyakar wani katon kogi ne,
ga filin kiwo nan ya mike kamar ba shi da iyaka.
Sauran ’yan’uwammu kuwa abokan shan
wahalarmu aka kai su can da nisa, aka rarraba
su ga sauran ’yam fashi wadanda su ke wurin.
Da zuwammu wannan wuri sai duk aka tsaya ana
kallommu, wanda ya kawo mu kuma aka yi ta yi
masa maraba da ihu. Ashe a lokacin da a ke
wannan wadansu manya-manyan karnuka sun
gane mu baki ne, saboda haka suka yi ta yi
mana haushi, suka taso kammu kamar za su
yayyage mu. Maigidana kuwa da ya ke da rawani
mai launi tsanwa aka fara ganin girmansa. Da
uwargidan Alhasan Sultan ta ga rawanin nan, ta
yi sha’awarsa, ta ce kuwa lalle sai a ba ta. Ai
dole aka cire aka ba ta, aka bar maigidana da
hular da ya dinke kudinsa ciki. Af, ashe wata
mata kuma ta ga hulan nan, ta yi sha’awa tata,
ta ce wannan zai yi kyau a sa cikin sirdin
rakuminta, don sirdin ba ya da taushi. Saboda
haka aka ba ta ta jefa a sauran kayan rakumin.
Ba kokarin da maigidana bai yi ba don a bar
masa, amma ina! A maimako aka ba shi wata
tsohuwar hula wadda aka yi da fatar rago. Hular
ma ba tasu ba ce, ta wani mutum ne wanda suka
kamo har ya gaji da azaba da bacin rai ya mutu.
...
Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, da karfe
tara na dare (9:00PM), in sha Allah.
Allah ya kai mu.
.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum farin cikin Ku shine Farn Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
.
Source By ©Bukar Mada

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: