Friday 22 September 2017

3. YAWON DUNIYAR HAJJI BABA Na James Morier Abubakar Tunau Ya Fansar Da Shi

Tura Wannan Zuwa

Af, ashe wata mata kuma ta ga hulan nan, ta yi
sha’awa tata, ta ce wannan zai yi kyau a sa cikin
sirdin rakuminta, don sirdin ba ya da taushi.

Saboda haka aka ba ta ta jefa a sauran kayan
rakumin. Ba kokarin da maigidana bai yi ba don a
bar masa, amma ina! A maimako aka ba shi wata
tsohuwar hula wadda aka yi da fatar rago. Hular
ma ba tasu ba ce, ta wani mutum ne wanda suka
kamo har ya gaji da azaba da bacin rai ya mutu.

Da maigidana ya gaji hular marigayi, sai kuma ya
gaji aikinsa. Aikinsa shi ne ya kai rakuma kiwo a
bisa duwatsu. Ba su ji tsoron ba shi wannan aiki
ba, don sun ga yana da kiba, ba ya iya gudu. Ni
kuwa sai aka ki yarda im fita, aka ba ni wani aiki
a nan wurin.

Ana nan sai Sarkin nan ya shirya gagarumar dina,
don murnar wannan babbar nasara da aka kamo
mu. Ran nan an yi shagali. Wata katuwar tukunya
aka samu aka cika ta fal da shinkafa, sa’an nan
aka yanka raguna biyu aka gasa. Dinar ta rabu
gida biyu, da ta maza da ta mata. Su mazan duk
dangin Sarkin nan ne, galibinsu kuwa duk suna
cikin wadanda suka yi mana fashi. Bayan an kai
wa maza shinkafa da nama sun ci sun yi tatil, sai
a kai ragowar ga mata. Su kuma in sun ci sun
koshi, sai a ba yaran makiyaya. Su kuma in sun
ci iyakar cinsu sai a turo mana kasusuwa da sudi
a ba mu, mu da karnuka.

A lokacin da na kosa a kawo mana abin da za a
ba mu, don kuwa tun da aka kama mu ban ci
kome ba, sai wata mace ta yafuto ni a boye, ta
ce im boye a bayan daki. Ta kawo mini kwanon
shinkafa da ’yar wutsiyar rago, ta ce uwargida ce
ta ce a kawo mini, domin tana jin tausayina. Wai
kuma kada in karaya, amma in yi karfin hali.
Ajiyewarta ke da wuya sai ta juya da sauri ta
tafi, ko jiran in ce mata na gode. Nan da nan na
kawad da shinkafa.
Bayan da aka kare kome da kome, maza suka
koma wuri daya suna ta shan lofe, ana ba da
labarin yadda aka kamo mu. Mata kuma suka
ware wuri guda suna waka, suna buga ganguna.

Ni kuwa da maigidana muka koma gefe guda
muka yi zugum muna tunanin wannan abu da ya
auku gare mu. Amma ni ban cika damuwa ba
saboda alherin nan da uwargidan nan ta yi mini.
Na yi iyakar kokarina in tausasa ran maigidana,
amma abu ya ki. Na ce masa im Musulmi na kirki
ne, to, in ya shiga irin wannan hali na bacin rai
abin da ya kan ce shi ne “Allah mai jinkai ne."
Shi kuwa sai ya ce, “Kai da ba ka yi hasarar
kome ba ka ce ‘Allah mai jinkai’ mana. Ni kam a
yanzu an tsiyata ni har abada.” Duk abin da ya
ke bata masa rai, shi ne rashin samun riban nan
da ya yi zato zai samu. Ya zauna ya lissafe duk
abin da ya yi hasara, ko anini bai manta ba.
Kashegari Sarkin nan ya aika maigidana ya tafi
da rakuma hamsin can bisa tsaunuka su yi kiwo.
Ya ce masa muddin daya na bacewa, to, lalle
kunnuwansa da hancinsa su za su biya. Ko kuma
in daya ya mutu, lalle ya sani za a kara kudinsu
a bisa kudin fansarsa da Sarkin nan ke zaton zai
samu nan gaba. Da zai tafi, na nuna ina
kaunarsa, na yi masa aski a gaban jama’a duka.
Da fa mutane suka ga na iya aski, sai kowa ya yi
ta zuwa ina yi masa. Har Sarkin nan da kansa
murgujeje ya zo na yi masa. Ya ce tun da ya ke
bai taba ganin wanda ya iya aski kamata ba. Ya
ce kuma shi ba zai karbi kudin fansata ba, ko
nawa ne, amma zan zauna in zama masa
wanzami na kansa.
Da na ji haka, haba, malam, sai na durkusa na yi
godiya, sa'an nan na yi ta tunanin yadda zan
gudu da zarar na ga hanya, don na ga na sami
'yanci, ana kuma gaskata ni. Shi ke nan na fara
shige wa Sarkin nan jika, kuma ko da ya ke idon
kowa a kaina ya ke, duk da haka na shiga kulle-
kullen dabaru da zan gudu daga wannan bauta da
na shiga.
A cikin kulle-kullen dabarun da na ke yi na gudu,
abu gudu shi ne babba, watau in san hanyar da
na bi na sami kudin nan na maigidana, wadanda
ya dinke a hularsa. Na kuwa ce muku hular da
kudin ke ciki an jefa ta a wani daki na mace. To,
ba ni da damar zuwa wurin, don ba a yardam
mini ba. Kuma ko da ya ke na yi suna a tsakanin
jama’ar wurin, duk da haka ba zai yiwu matan
nan su kira ni in yi musu aski ba. Tsakanina da
su sai hange.

Ana nan kan haka sai ran nan uwargidan Sarki ta
aiko ko na iya yin kaho. Da jin haka sai na yi
hamdala, na ce muddin za a ba ni wuka, ni kuwa
zan iya. Domin na ga yin haka watakila zai sa in
sami abin nan da raina ya ke so. Aka kawo
wuka. Wani daga cikinsu wai shi malamin hisabi
ya ce taurarin da za su fito kashegari su suka
dace da yin kaho. Kashegarin aka kai ni dakin
mata, uwargidan tana zaune tim a kan tabarma
ta kosa in zo. Da zuwana na shiga shirye-shiryen
yin kaho, kuma na walkata ido a dakin ko na ga
hulan nan da na kosa in samu.
Da na kama hannunta na tattaba sai na ce lalle
jikinta ba kyau. Don haka tilas a samo kwano
wanda za a tare jinin, don in na gama in duba. A
nan fa aka yi ta. Ko wace mace aka ce ta kawo
kwano sai ta ki, ta ce tana son abinta, ba ta
yarda a zuba mata jini ciki ba. Aka bincika wurin
duka ko a sami abin zubawa, amma ba a samu
ba. Sai uwargidan ta aika wata ta kawo wani
tsohon kwaf na fata.

Da aka kawo sai na ce mata ai ba zai yi ba, don
yana da huji. Ni ne fa na yi hujin da wayo yadda
ba ta sani ba. Shi ke nan sai ta ce, "Ina hular
tsohon Sarkin nan?” Matar ta biyu ta ce, “Nawa
ne, ina so in sa wa sirdin rakumina.” Uwargidan
ta cika da hushi, ta ce, “Naki! Ba ni ce
sarauniyarku ba a nan ? Maza kawo shi.”
Matar ta ce, “Na ki." Nan take gardama ta
murtuke da ihe-ihe, ni kuwa duk tsoro ya cika ni
kada Alhassan Sultan ya ji ya zo ya kwace abin
da ya sa gardamar. Allah ya sa dai bai ji ba, sai
malumin hisabin nan ya zo ya raba gardama. Aka
kawo hular. Da dai uwargidan nan ta ga wuka, ga
idunu a kanta, sai tsoro ya kama ta ta ce ba ta
yuarda in yi kahon ba.
A’a, ga abin da na ke burin samu ya zo hannu,
amma matar nan tana hanyar da ba zan samu
ba. Saboda haka na matsa hannunta, na ce mata
ba wani amfani ta ki a yi mata kaho, don ita da
sauran matan duka sun sani yin wannan kaho
kaddara ce, ba kuwa dama ta ki abin da aka kafa
tun farkon duniya. Da jin haka sai ta yi Iikimo, ta
miko hannunta, na daba mata wuka, jinin ya taru.
Sai na ce a kai hular can da nisa, kada kowa ya
matsi wurin sai ni, don dukan abin da zai faru ga
matan ko alheri, ko mugunta, ya dangana ga abin
da ya faru ga jinin.

Da dare ya yi, kowa yana barci, na tashi na
lababa wurin, na yanke dinke-dinken, na kwashi
kudina £30 cif, na binne su a kusa da wurin,
hular kuma na binne. Kashegari na ce wa
uwargidan na ga kerkeci da yawa suna zagaya
wurin, don gudun kada wani abu mugu ya auku
ga jinin na binne hular da jinin duka. Ta kuwa yi
murna da na yi hakanan. Da za ta biya mini
ladan aikina sai ta gasa rago guda daya cif da
hannunta, ta dafa shinkafa ta aiko mini game da
kwanon madara.

Da kudin nan suka zo hannuna sai na shiga
tunanin maigidana na farko. Ga shi can yana
shan wahala cikin duwatsu, ni kuwa ga ni zaune
cikin daula. Na yi tunanin im mayar masa da
kudinsa, amma daga baya na shashantad da
tunanin. Na ce wa kaina, “Da ba domin
gwanintata ba da wadannan kudi sun bi ruwa ke
nan har abada. Don haka ba mai su sai ni. Ko da
a ce ma ya same su, ba za su yi masa wani
amfani ba a irin halin da ya ke ciki, za ma a
kwace a wurinsa. Saboda haka ya fi kyau in rike
yanzu. Hasali ma dai kaddara ce ta sa ya yi
hasararsu, ni kuma na same su.” Na dai rike
abina.

Na ce uwargidan Sarki ta aiko mini da rago
gasasshe. Daga ciki na yi kokarin in aika wa da
maigidan nan nawa na fari da rabi. Na sami wani
yaron makiyaya wanda zai tafi can dutse, na ba
shi ya kai masa. Yaron ya yi alkawarin ba zai ci
a hanya ba. Shi ke nan ya kama hanya ya tafi.
Ya ketare kogi ke nan sai na hango shi ya kai
naman bakinsa. Na kuwa tabbata kafin ya bace
wa idona sai da ya cinye duka. Ga shi kuwa ba
abin im bi shi ba, nisan da ke tsakanimmu ya yi
yawa. Dole na hakura, na dauki dutse na jefe shi,
na zuba masa bakaken maganganu, amma ba
wanda ya kai gare shi.

Za mu ci gaba ranar Asabar mai zuwa, da karfe
tara na dare (9:00PM), in sha Allah.
Allah ya kai mu.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum farin cikin Ku shine Farn Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
.
Source By ©Bukar Mada

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: