Monday 25 September 2017

Ba Mu Daga Cikin Matattu

Tura Wannan Zuwa

A wani kauye ne wasu yara guda biyu suka saci
mangoro a cikin buhu. Sai suka tsaya shawarar
inda za su tafi su raba ba tare da kowa ya gansu
ba. Sai daya ya bayar da shawarar a tafi
makabarta.
Bayan sun isa makabarta dauke da mangoron
nan, a kofar shiga sai mangoro biyu ya fado daga
cikin buhun, amma saboda suna sauri kada a
gansu sai suka bar su nan suka wuce cikin
makabartar da sauran mangoron.
Su na shiga sai suka zube mangoron a kasa suka
fara rabawa, babban ne ya ke rabo, sai ya dauki
mangoro daya ya aza a gabanshi ya ce, “Ni daya”
sai kuma ya dauki daya ya aza a gaban karamin
ya ce, “Kai daya.”
Haka suka ci gaba da rabonsu. Can sai ga wani
mashayi ya fito daga cikin daji wajen shaye
shayensa, yana zuwa dai dai kofar makabarta sai
ya ji wata yar karamar murya kamar ta yara ana
cewa, “Kai daya, ni daya,” kuma anci gaba da
maimaitawa. Sai kawai ya garzaya da sauri sai
gidan limamin kauyen.
Yana zuwa ya same shi kofar gida yana shirin yin
alwalar magariba. Ya ce, Allah gafarta malam,
yau wani bakon al’amari ke faruwa a makabartar
can. Na ji ana rabon matattu. Sai liman ya ce mu
je in gani.
Su na zuwa, sai suka labe a bakin kofar
makabartar, sai suka ji ana cewa, “Kai daya, ni
daya, kai daya, ni daya…” Can sai suka ji ance,
“To kai ga yawan naka nan, ni ga yawan nawa
nan.” Can kuma sai suka ji an kara cewa, “To
wadan can biyun na bakin kofar shigowa fa?” sai
suka ji daya ya ce, “To mu je a dauko su mana.”
Haba! Ai liman da mashayin nan na jin haka, sai
suka ari takalmin kare, su na fadin ai mu ba mu
mutu ba, ba mu daga cikin matattu, tsammani
suke yi da su ake, ba su san cewa yaran nan
mangoron su biyu da suka fadi bakin kofa suke
nufi ba.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By © Abubakar Yusuf Mada

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: