Monday 11 September 2017

LABARI NA KASHI NA DAYA

Tura Wannan Zuwa

Zaune nake a wajen da nake siyar da fetir, gari
yaci wuta babu ciniki, wayata dake aljihuna
nazaro nahau facebook online budewarsa keda
wuya sainaga message inbox guda 10, 3 maza 7
mata, sai
notification guda 50, friend request guda 20 a
Hankali nakebawa kowa Hakkinsa,
!
Banyi Auneba Sai ganin wata mota baka Element
2017. Glass dintama bakakene baka hangen
waye a ciki, can sainaji Anyi Hon,
Abokina Al Amin Danshehi dake kusadani Yace
wannan mai motar badakai yakeba,? Nace AA
meye Hadin biri da Gada.
!
Sautin Hon Yasake cikamin Kunne, lokacin da zan
sake dago kaina daga bawa frnds dina na fcbk
Hakkinsu, sainaga Glass Din motar
yana sauka Alamar dai sunada abincewa, lokacin
da glass din yagama sauka wow! Mezan gani.
!
Wasu Yammata ne tsala-tsala guda 2 farare tas
dogayen Riguna ne a jikinsu ruwan Hanta, yayin
da fuskokinsu suke dauke da wani
Bakin Glass ko wacce tayi Kyau sosai Bansan
lokacinda wayata tafadi daga Hannunaba.
!
Can sai suke tambayar waye mai fetir din nan,
Abokina Al Amin Danshehi Yanunani yace gashi
nan, tace malam kaine mai fetir
din nan cikin rawar jiki nace mata eh nine, tace
bissmilla.
!
Nazagaya bangaren da take tuki nace Hajiya
barka da zuwa Galan nawa za'abayar? Murmushi
tayi ba fetir zan siyaba akwai maganar
datakawoni nakeso muyi dakai.
!
Ta bude murfin gefe tace bismilla shigo ko! Yake
nayi haba Ranki yadade, waneni da hawa wannan
motar dubenifa kiga yanda nake.... Shiru Dakatar
dani tayi kashigo nace Saina Kalli Abokina
AlAmin Danshehi, shima sai ya yadaga min kai
alamar kawai nashiga.
!
Haka nacire takalmana nashiga ita kanta yarinyar
saida nabata dariya wajen shiga motar, sbd kana
gani kasan ba'asababa, sai take cewa Qawarta
wadda suke tare da tacewa Abokina Yajiremin
yanzu zamu dawo, Danshehi Ya Amsa to Hajiya.
!
Tuni tawani finciki motar nan muna dan yin
tafiya kadan sai naga taja birki ta tsaya, gabana
yakara faduwa Hankalina yatashi,
rawar sanyi nafarayi sakamakon ehsy din dake
fita daga motar.
!
Kyakkyawar Yarinyar da take Jan motar tafara
tambayata kamar haka: shin kaine mamu mai
fetir Rijiyarlemo tsallaken yamma
layin banki ko? Ba Amsa wani gumi yaketomin
duk da ehsy din yake tashi a cikin motar mamaki
nayi to ya akai tasan sunana?.
!
Tasaki wani mayen murmushi tace malam
Hafeez inkeya mamu mai fetir kwantar da
hankalinka basaceka zanyiba, sai a lokacin
nayi magana "Dama kin sannine?.
!
Kyakkyawan murmushin da yake kara mata kyau
tasakeyi, mai fetir kenan kana mamaki ko? Tace
dani
nikuma nace mata eh dole nayi mamaki kuwa.
!
Tace Nidai Sunana Hafsat amma Anfi sanina da
Khairat kamar kaima yanda akafi saninka da
mamu mai fetir, tace tunda na farajin sunanka a
gidan Radio Arewa lokacin da kake aiko da
sakonka ta whatapp, nafara
bibiyar Al'amuranka, sannan nasameka a shafin
sadar warka na facebook.
!
Tunda naturo maka frnd request kakarba bamu
taba yin maganaba amma kuma inatare dakai duk
lkcin da nahau online, Yanzuma da kaganni
abinne yakici yaki
cinyewa shiyasa nayo takanas ta
unguwarmu domin nazo na bayyana maka abinda
yake faruwa.
!
Hafsat taci gaba bayani, Hafeez Sonka nakeyi
kuma so marar musaltuwa, kullin dadyna da
momyta sunkasa gane kaina, kuma gashi tun
2010 nakammala Dgree dina a Jamiar Bayero,
dadyna yace nafito masa da wanda zan Aure
kafin 2018 kokuma yabani wanda yayi niyya,
kullin cewa dadyna nakeyi inada
saurayi, yanzu haka maganar da ake ciki cewa
yayi nafada maka kazo yana son ganinka.
!
Hafeez Ina sonka fiye da Yanda uwa takeson
Danta, Hafeez Ina Kaunarka fiye da Yanda maijin
Kishirwa Yake neman ruwa a sahara, Hafeez
Idan basameka a mijin Aureba, zanrasa rayuwata.
!
Dakata! Dakata!! Na daga mata Hannu kema
kinsan Abinda bazai yuwubane kike fada, kema
kinsan a gidanku baza'a bari ki Auri
talaka irinaba, wanda 500 take masa wahala.
!
Hafsat tayi murmushi tace Hafeez
Amincewarka kawai nake bukata Yanzuma zamu
tafi dakai wajen dadyna, kagaisheshi, nace AA
bazai yuwuba, nan tatakura sai
munje, nace to indai kinaso muje sai munkoma
wajen fetir dina mun taho tare da Abokina
AlAmin Danshehi.
!
Hafsat tace indai wannan ne bamatsala haka
muka dawo baya zuwa wajen fetir dina
mukatarar dashi yayi dame-dame da bakin
mai Abinka da wanda ba har kar saba wai wanine
yazo siyan fetir da bakin mai yabata jikinsa.
!
Nace Abokina Danshehi mukwashe kayan nan a
mayar dasu shago, Danshehi yace me
yafaru nace wai gidansu zamuje sona takeyi.
Danshehi yayi dariya yabani Hannn muka tafa.
!
Mungama kwashe kayan muka shiga mota nida
Hafsat muna gaba Abokona Danshehi da Qawar
Hafsat suma suna Baya can saina
fuskanta Hafsat tana satar kallona idan nayi
kokari gane saita basar.
!
Haka Hafsat taci gaba ta tafiya damu a mota
babu inda ta ja birki sai Nasarawa G.R.A wani
Katon Gate ne cikin Hanzari mai gadi
yabude kofa ta tausa Hancin motar nan cikin
harabar gidan.
!
Gefe daya cikin wata rumfa-rumfa ta faka motar
kawarta ce tayi ma jagaba zuwa ciki wani fallo a
akayi mana masauki..
.
Zamu cigaba Insha ALLAH
.
.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address dinba mungode
.
Source by Hafeez R/lemo

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: