Sunday 1 October 2017

Magana Jari ce: LABARIN YUSHA’U NA-NARIMI DUTSE BA-KA- FARGABA

Tura Wannan Zuwa

Daga littafin Magana Jari Ce 2
Na Alhaji Abubakar Imam
(c) NNPC Nigeria

Da, an yi wani yaro wanda Allah ya nufa da wata
irin zuciya sai ka ce dutse, don rashin fargaba.
Saboda ganin haka sai ya rika alfahari, yana
cewa shi duk duniyan nan bai ga wani abin da zai
ba shi tsoro ba har ya kadu. ‘Yan’uwansa yara su
kan kulla abubuwa da yawa yadda za su sa ya
kadu, amma duk a banza. Saboda haka har suka
sa masa suna ‘Dutse.’ Da sun gan shi sai su rika
yi masa kirari suna cewa, “Yusha’u Na Narimi,
dutse-ba-ka-fargaba.”
Da kakansa ya ji haka, sai ya ce shi lalle sai ya
ba shi tsoro har ya kadu. Yusha’u kuwa duk bai
san abin da a ke ciki ba. Ran nan da tsakad dare
sai ya tafi hira wata unguwa, ya raba dare bai
dawo ba. Da kakan nan nasa ya ji haka sai ya
tashi, ya sami karare, ya daura wani mutum-
mutumi dogo, ya sa masa farar riga, shi kuma ya
sa wa kansa fara. Sai ya tashi ya dauki mutum
mutumin nan ya dora bisa kansa, ya tafi hanyar
da yaron nan zai biyo, ya make.
Can zuwa tsakad dare, duk ba wani mahaluki mai
motsi, sai ya ji yaron nan tafe yana waka. Da
jinsa sai ya fito daga inda ya ke boye, ya tasam
masa haikan. Da Yusha’u ya ga ya nufo shi sai
ya ce, “Kai tsololo, in aljani ne kai, lalle Allah bai
halicce ka da tsari ba, ga ka tsololo, amma dan
kai sai ka ce kodago. Ko kuwa fatalwa ce? In
kuwa fatalwa ce, na so in gan ta sa’ad da ta ke
da rai, Zotori!”
Kakansa dai bai ce uffan ba, ya dai nufo shi har
ya taka wa yaron nan kafa. Sai yaron ya tsaya,
ya ce, “A’a! Shakiyancin nan na aijannu da fatale
har ya kawo gare ni? Kai tsololo, mene ne na
taka ni? To, ko da ya ke tsawona bai kai in mare
ka ba, ai ka sha kulki!” Sai ya dunkula hannu, ya
kai wa kakan bugu tim!
Ya sake dagawa zai kara, sai kakan ya yad da
karan, ya ce, “Kai, kai, kai, ni ne kakanka Narimi,
kada k buge ni.”
Yaron ya yi murinushi ya ce, “Kaka, me ya sa ka
yi mini haka, ga shi har ka sa na buge ka?”
Narimi ya ce, “Mutane na ke ji suna cewa, wai ba
wani abin da za a yi maka har ka kadu, shi ya sa
na yi wannan dabara wai ko na sa ka ji tsoro.
Ashe dai gaskiyarsu. Gobe kuwa sai na tafi na
gaya wa Sarki jaruntakan nan taka.”
Yaro ya ce, “Shin kaka, mene ne tsoro ne? Ni ban
san abin da a ke kira hakanan ba. Ashe yanzu
nan duniya har akwai abin da zai sa in kadu?”
Kakan ya yi murmushi, ya koma gida.
Gari na wayewa sai kakan ya tafi ya gaya wa
Sarki, ya ce yana da jika wanda ba abin da za a
yi masa ya kadu. In Sarki yana so ya gani, ya
kirawo shi ya gwada shi. Fadawa suka ce, “Allah
ya ja zamaninka, wannan yaron ai sananne ne a
kan rashin tsoro, ai tun da ya ke babu abin da ya
taba sa shi ya kadu.”
Sarki ya ce, “To, madalla, gobe ku zo da shi mu
gani. Ai inda ba kasa a ke gardamar kokawa.”
Da gari ya waye kakan ya kira yaro, ya gaya
masa abin da suka yi da Sarki; Yaro ya ce, “To,
sai mu tafi, in shakka ya ke yi.”
Da aka yi sallar azahar, da yaro da kakansa suka
tafi gidan Sarki. Suka tarad da fada ta cika, kowa
na fadin albarkacin bakinsa. Suka fadi suka yi
gaisuwa. Dogarawa suka ce, “Sarki ya gaisheku.”
Sarki ya dube su, ya ce, “Kun taho?”
Kakan ya ce, “I, Allah ya ba ka nasara, ga
yaron.”
Sarki ya dubi jama’a ya ce, “Kun ga yaron da aka
ce bai tafa kaduwa ba don tsoro ina so in gwada
shi, amma ku shaida, in aljannu suka halaka shi,
ko kuwa suka zauta shi, kada a zarge ni. Zan sa
shi ya kwana cikin dakin gindin tsamiyan nan ta
gunki. In ya tashi lafiya gobe, ba a ii ya yi kuwwa
ba, ko wata firgita, zan ba shi ‘yata aure.”
Da kakan yaron nan ya ji haka sai idonsa suka yi
kwal-kwal. Fadawa kuma duk suka dube su, suka
yi dariya. Kowa ya san tsamiyan akan
kwankwamai. Nan ne kuwa fadar Sarkin aljannu.
In mutum ya bari magariba ta yi masa, ko kuwa
rana ta take yana kusa da wurin, sai wan, ba shi
ba. Wannan abu ba ko camfi ba ne, an ga haka
ba daya ba, ba biyu ba. Saboda yawan aljannu
har a ke kiranta “Mutuwa kusa.”
Da kakan yaro ya ii haka sai ya ce, “Ranka ya
dade in da wannan za a gwada shi, ba ya iyawa,
kwarinsa bai kai haka ba.”
Yusha’u ya yi wuf ya ce, “Me ya sa ka ce haka?
Cikin duniyan nan ashe har akwai wani abin da
zai sa in kadu ma, balle har a ce in yi ihu? Haba,
ranka ya dade, ko ba ka san labarina ba ne? Ni
ne fa Dutse Na Narimi ba ka fargaba. Allah ya
kai mu magariba.”

Kakansa ya yi, ya yi, ya hana shi, ya tsaya shi
sai ya kwana. Narimi ya gaji, ya ce, “Je ka, ai
mai rabon shan duka ba ya jin kwabo, sai ya
sha.” Suka sallami Sarki, suka tafi gida, duk
Narimi na zulumin abin, yana cewa, ‘‘Lalle baki
dai shi ke yanka wuya.”
Magariba na yi sai yaron nan ya dauki ‘yar
tabarmarsa, ya tafi gindin ‘tsamiyan nan, ya
shige dakin ya yi shimfida, ya kunna fitila, ya
kwanta, ya bar ta tana ci. Aka zo aka gaya wa
Sarki. Sai ya sa wadansu malamai su hudu, suka
sami wani wuri can nesa da gindin tsamiyar, suka
buya. Suka tsaya daidai da inda za su iya hangen
duhun yaron nan cikin daki don kada ya fito.
Yana nan kwance sai ya ga wani aljani ya keto
bangon dakin ya fito, duk tsawonsa bai fi kamu
guda ba. Amma kansa, duk inda tulu ya kai da
girma ya fi hakanan. Da fitowarsa sai ya zauna
gindin fitila tare da yaron, ya yi masa kuri da ido.
Sai Yusha’u ya ce masa, “Me ka ba ni ajiya ne.
har ka dame ni da kallo haka? Ko kuwa kana da
wani da ne kamata wanda ya bace?” Aijannin nan
dai bai ce masa uffan ba, sai lashe lashen
bakinsa ya ke yi. Yaro ya ce, “Kurwata kur, ka ci
kanka, ka sha bakin ruwa!” Aljanni dai bai ce
masa kome ba.
Suna nan zaune, sai ga cinyar mutum ta fado
kasa tim, har da jini. Yusha’u ya dubi cinyar, ya
ce, “Kai, mai wannan cinya lalle kafin ya mutu an
yi kato! Shinkici! Amma irin kattan nan galibi ba
su kan yi karfi ba. Bari in jinjina cinyar, in ji in da
alamar karfi.” Ya tashi ya ciccibi cinyan nan ya ji
ta sakwat, ba nauyi. Sai ya ce, “Allah wadai, yau
ga katon kwabo! Ashe duk katancin nan ta gina
ne ba ta shiga ba.” Sai ya yar da ita waraf, ya
koma kusa da gajeren nan na tsugune.
Ya zauna ke nan, kuma sai wata cinyar ta fadoo
kusa da ta fari. Kafin a yi haka kuma sai ga
hannuwa sun fado. Yaro dai bai ce kome ba sai
dariya ya ke yi musu. Can kuma sai ga gangar
jiki ta fado tirim. Ko wace gaba ta like ga
‘yar’uwarta, sai gamutum ya tashi ya nufo su,
amma ba kai. Yaron nan ya ce, “Kai, wannan
huhun ma ahu ya faye doki! Tsaya mana tukun
kanka ya fado sa’an nan ka zo, in hira za mu yi.”
Aijani dai bai ce kome ba, sai ya zo wurin
wancan dan gajeren nan da ya fara zuwa, ya
danne shi, ya kama hannunsa guda ya kakkarya
shi rugu-rugu, ya bar shi nan yana kuka. Ya
zabura zai gudu sai ga wadansu aijannu guda
biyar sun tsago kasa sun fito. Da ganin abin nan
da ya faru, sai suka yi cacukwi da wannan da ya
karye dan uwansu, suka ce, “A’a, a,a! Kai
Kururrumi, kai ka karye Dandagizge? Wallahi yau
in Sarkin Aijannu ya zo, bari ta kai, ko da
mutumin nan mai fitila da ke nan aka yi abin,
kashinsa ya bushe!”
Sai yaron nan ya ce, “Kai, in kuna shiriritarku ku
bar gamawa da ni, ka ji yan nema masu manyan
kunnuwa! Kashina ya bushe halama ni na kashe
shi.”
Kai, in gajarce muku labari dai, aljannun nan suka
yi ta ba yaron nan tsoro har gari ya waye, amma
Yusha’u bai razana ba, balle har ya kadu.
Da rana ta fito ya dauki ‘yar tabarmarsa, ya nufi
gidan Sarki, ya ce ya dawo. Mutane za su yi
musun bai kwana ba, sai malaman nan hudu
suka shaida ya kwana. Sarki ya rasa abin da ke
masa dadi, ga shi ya yi alkawari ba damar
warwarewa. Mutane suka yi ta mamakin yaron
nan, kakansa kuwa ya yi ta farin ciki da ya
kubuta.
Sarki ya tashi, ya shige gida duk rai a bace, ya
kira ‘yar da uwarta, ya gaya musu wannan
al’amari duka. Yarinyan nan ta ga ran iyayenta ya
baci, sai ta ce, Kada ku bata rayukanku a banza,
na ce ko kaduwa ce ya ce bai ga abin da zai sa
shi ya yi ba?”
Uban ya ce, “I, lalle ko gaskiyarsa, duk duniyan
nan kuwa babu.”
Yarinya ta ce, “To, na ce ko kun gama naku na
manya? Saura kuma mu mu yi kokarim mu na
yara, mu gani.”
Uban ya yi dariya ya ce, “Wane kokari gare ku na
yara ban da wauta?”
Yarinyar ta ce, “Ina so, in ka yarda, baba, ka je
yanzu cikin taro, ka ce ka ba shi ni, amma da
sharadi guda, shi ne daga yau har kafin rana wa
ta yau, in wani abu ya sa shi ya kadu, baiko ya
tashi”
Uwar ta yi dariya ta ce, wanda ya kwanta dakin
gunki bai ji tsoro ba, to me zai ba shi tsoro a
gidansa?”

Uban ya ce, ‘‘Bari in je in fadi, kada mu rage
mata hanzari.” Sai ya koma zaure ya fada wa
mutane haka, duk suka shaida. Yusha’u ya yi
dariya, ya sallami Sarki ya tafi gida, iyayensa
suka yi ta yi masa guda don murna. Yarinyan nan
kuwa ta san tun da ya kwana dakin gunki jiya,
lalle aljannu ba su bar shi ya runtsa ba, tun da
abin ya ke haka kuwa, daren yau lalle in ya fara
barci sai Allah. To, lokacin nan kuwa cikin
tsakiyar dari ne muku muku. Saboda haka da
asuba sai yarinya ta tashi ta fada wa ubanta, ta
sa ya aike aka tado Waziri da Alkali, da manyan
malaman gari guda hudu wadanda Sarki ya sa su
tsaron nan jiya da dare. Da suka taru, sai
yarinyar ta debo ruwa mai sanyi kwarai daga
wani sabon tulu, ta ba Sarkin Zagi ya dauka, duk
suka dunguma zuwa gidan.
Da suka isa kofar gida, ta ce kada kowa ya yi
magana, ko wani babban motsi. Ta sa aka tafi
sululu aka tado kakan yaron nan, ya fito waje ya
tarad da su, kowa dai ya zuba wa ‘yar yarinya ido
ya ga abin da za ta yi.

Sai ta ce kakan yaron ya shiga gaba ya nuna
musu dakin jikansa, amma fa ba a ce in ya je ya
ta da shi ba, ko motsi mai karfi ma kada kowa ya
yi.
Suka isa, ta tarad da dakin rufe da asabari, ta sa
hannu sannu a kan hankali ta cire, sai ga yaro
kwance tim, daga shi sai durwar bante, barci ya
sa har ya ture dan bargonsa bai sani ba. Sai ta
karbi ruwan nan ta shiga cikin dakin sadadaf,
saddaf, ta watsa masa a jiki. Ko da ruwan nan ya
zuba masa sai ya kadu, ya yi firgigi ya tathi, ya
ce, “Wai!” Duk mutanen nan suka yi tafi baki
daya, suka bushe da dariya, suka ce, “A’ ya kadu,
ya kadu!”
Da Yusha’u ya bude idonsa, yagane makirci ne
aka yi masa, sai kunya ta rufe shi.

Don gudun jin
kunya bai bari gari ya waye masa ba, sai da ya
gudu ya bar garin. Mutane suka yi ta mamakin
wannan fasaha ta ‘yar yarinya.
Da Sarki ya komo gida ya gaya wa uwar yarinyar
abin da ya faru, duk sai suka rungume ta don
murna. Da gari ya waye Sarki ya nemi yaro, aka
ce ai ya gudu. Sai ya sa mutane su bi shi. Kafin
azahar aka komo da shi. Sarki ya nada shi Sarkin
Yaki. Aka ba shi katon gida. Sarki ya aura masa
‘yam mata biyu daga cikin ‘ya’yan bayinsa: Da
ma abin da ya tsana ya ba shi ‘yar cikinsa, ga
shi talaka. Sarki kuma ya yi wa kakan yaron nan
kyauta mai yawa don jaruntakar jikansa. Suka yi
ta cin duniyarsu a tsanaki. Kullum idan Sarkin
Yaki ya tafi fada Sarki ya ce masa, “Yusha’u,
Sarkin Yaki, Na Narimi, dutse ba ka fargaba.” Shi
kuma sai ya ce, “Lalle ba na fargaba sai na ruwa,
Allah ya ba ka nasara.” Duk sai a yi ta dariya.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bukar Mada

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: