Friday 22 September 2017

Ni fa har yanzu babu wanda ya dakatar da Ni daga Kannywood-Rahama Sadau

Tura Wannan Zuwa

Rahama Sadau. Da zarar an ambaci wannan
suna babu abin da zai fado ran mutane sai ce-
ce-ku-ce saboda kurar da mai sunan ta tayar a
shekarar 2016 lokacin da aka nuna ta a wani
bidiyon waka tana "rungumar" wani mawaki.

Wannan batu dai ya jawo hankalin duniya
musamman saboda caccakar da aka rika yi wa
jarumar ta fina-finan Kannywood, abin da ya kai
ga "korarta" daga yin fina-finan na Hausa.

Sai dai a zahiri Rahama Sadau, wacce ta soma
taka rawa a fina-finan Kannywood a shekarar
2013, mace ce mai kamar maza, kamar yadda a
duk lokacin da muka hadu take gaya min.

"Ni fa mace ce jaruma wadda idan na sa abu a
gaba sai na kammala shi domin babu abin da ke
dakatar da ni daga son cika burina".

Mene ne burinta?

A wata hira ta musamman da na yi da ita a
shekarar 2015, jarumar ta shaida min cewa
"babban burina shi ne na taka rawa a matsayin
jaruma a dukkan manyan bangarorin fina-finan da
ake yi a duniya: Hollywood, Bollyywood,
Kannywood da kuma Nollywood".

Ta kuma jaddada min shaukinta na cika wannan
buri nata a tattaunawar da muka yi a ranar
Alhamis din da ta gabata.

Tun da ta soma fitowa a fina-finan Kannywood
take hankoron baza komarta kuma tun ma kafin
a "kore" ta daga Kannywood ta soma fitowa a
fina-finan Nollywood da ake yi a kudancin
Najeriya.

Sai dai babu ko shakka hanawar da aka yi mata
fitowa a fina-finan Kannywood ta zamar mata
tamkar gobarar Titi a Jos.

Jim kadan bayan haka ne fitaccen mawakin nan
kuma jarumin fina-finan Hollywood Akon ya
gayyace ta birnin Los Angeles na Amurka domin
share mata hawaye.

A can ne kuma ta fito a wani fim din Hollywood
wanda shi Akon din ya bayar da umarnin
hadawa.

"Na ji dadin zuwa Amurka domin kuwa na koyi
abubuwa da dama a kan fina-finai.

Na yi fitowa
ta musamman a wani fim da Akon ya hada.

Yanzu kuma ina shirin fitowa a wasu fina-finan
na Hollywood. Hasalima jiya-jiyan nan wasu
Amurkawa suka zo nan Najeriya inda za mu ci
gaba da daukar wani fim", in ji tauraruwar.

'Babu wanda ya dakatar da ni'

Da yake Rahama Sadau na cikin jaruman da suka
fito a fim din na Rariya, na tambaye ta ko an
janye korar da aka yi mata daga Kannywood, sai
dai ta ce dama can ba a kore ta ba.

"Ni fa babu wanda ya kore ni daga Kannywood.

Har yanzun nan babu wanda ya aiko min da wata
takarda da ke nuna cewa an sallame ni daga
Kannywood.

An rage ganina a fina-finan ne saboda, kamar
yadda na gaya maka, ina fitowa a fina-finan
Nollywood da kuma gudanar da sauran al'amuran
rayuwata.

Amma yanzu zan koma yin fina-finan na Hausa
gadan-gadan musamman ganin irin nasarar da
fim dina na Rariya ya yi. Zan ci gaba da daukar
nauyin fim baya ga fitowa a ciki da zan ci gaba
da yi", in ji jarumar.

Na fahimci cewa akwai wata fahimtar juna a
tsakanin kungiyar MOPPAN da ke sa ido kan
masu shirya fina-finan Kannywood da Rahama
Sadau ta yadda za ta janye jikinta daga fitowa
daga fina-finan na Hausa, alabashi su kuma su
bar ta ta koma fita a fina-finan bayan wani
lokaci, musamman idan mutane suka soma
mantawa da abubuwan da suka faru.

Da na tambaye ta kan ko ta yi da-na-sanin fitowa
a bidiyon wakar da ya janyo ce-ce-ku-ce,
Rahama Sadau ta yi murmushi sannan ta ce "kar
ka manta na bai wa magoya bayana hakuri
saboda abin da ya faru. Amma daga haka ba zan
sake cewa komai ba".

Ganawa da Priyanka Chopra

Ita dai Rahama Sadau, wacce ke "jin" yaren
Hindu kamar Amitabh Bachchan, ta shaida min
cewa ta soma sha'awar fitowa a fina-finai ne
saboda kaunar da take yi wa fittacciyar jarumar
Bollywood, Priyanka Chopra.

"Tun ina karamar yarinya nake kallon fina-finan
India kuma su ne ma suka yi gagarumin tasiri a
rayuwata. Watakila hakan ba zai rasa nasaba da
son fina-finan na India da mahaifina ke yi ba: ya
je kasar India tun muna yara kuma shi ne ya
soma koya min Indiyanci. Amma a dukkan
jaruman fina-finan India babu wadda na fi kauna
kamar Priyanka Chopra: mace ce jaruma, hazika
kuma kuli-kuli ce mai sa gabanta inda take so,"
in ji jarumar.

Rahama Sadau ta ce takan yi wa Priyanka
Chopra magana a shafukan sada zumunta akai-
akai domin bayyana mata irin kaunar da take yi
mata.

"Karon farko da na yi mata magana a Twitter shi
ne a 2013, sai kuma a 2015 da kuma
shekaranjiya [Talata]. A karon farko ba ta ce min
komai ba; a karo na biyu kuma ta tambaye ni ni
wace ce sai na gaya mata cewa ni jarumar fina-
finan Hausa ce da ke matukar kaunarta.

Amma shekaranjiya da na yabi wani abu da ta
wallafa a Twitter sai kawai ta ce min ta gode
kuma tana fatan za mu hadu nan ba da dadewa
ba. Hakan ya sa na ji dadi sosai", a cewar
Sadau.

Yanzu dai jarumar ta ce ta samu hanyar ganawa
da tauraruwar da take kauna kuma "na daure
jakata ina jiran ranar da za ta ce min na hawo
jirgi mu hadu da ita a koina ne kuwa a duniya.

Wannan shi ne daya daga cikin manyan
burikana".

Rariya

Baya ga fitowa a fina-finan da take yi, jarumar ta
dauki nauyin hada fim na kanta a karon farko
mai suna Rariya.

Fim din, wanda ya hada fitattun jaruman
Kannywood irin su Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq,
Fati Washa da Maryam Booth, ya karbu sosai a
wurin masu kallo.

A cewar Rahama, "Na dauki nauyin fim dinne
domin na fadada ilimina a fannin fina-finai
sannan na samarwa matasa karin aikin yi. Fim
din yana magana ne kan irin sakacin da iyaye ke
yi na rashin kula da ya'yansu da ke karatun
jami'a.

Za ka ga mahaifi ya bar 'yarsa a jami'a ba tare
da yana sanya mata ido ba. Wani lokaci ma 'yar
ce ke ciyar da gidansu kuma babu wanda ke
tambayarta inda take samun kudi.

Yawanci za ka ga Alhazan birni da lakcarori sun
lalata 'yarka kafin ka ce kwabo. Kuma wannan
ya samo asali ne saboda rashin kulawar iyaye.

Shi ya sa na ga ya kamata a fadakar da su".

Wani abu kuma da fim din na Rariya ya fito da
shi, a cewar Rahama, shi ne irin kyashi da bakin
kishin da ke tsakanin mata 'yan jami'a ta yadda
wata za ta iya halaka wata idan ta ga ta fi ta
samun abun duniya.

Rahama Sadau za ta gana da Priyanka
Chopra ta India

Abin da ya fito fili game da rayuwar Rahama
Sadau shi ne, kamar yadda ta fada, ita mace ce
da ka iya shafe tsawon lokaci tana taka rawa a
fina-finai da ma sauran al'amuran rayuwa,
musamman ganin cewa baya ga fina-finan, tana
yin wasu harkoki na wayar da kan jama'a kamar
shirinta na kamfe a kan yaki da cutar daji da
kuma kasuwanci.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: