Monday 25 September 2017

TSAMMANIN WARABBUKA

Tura Wannan Zuwa

Wata rana ina zaune a masallaci sai wani mutum
mabukaci ya zo yana neman sadaka. Na zaro
Naira goma daga cikin aljihuna na mika masa.
Ina ba shi sadakar nan sai wani mutum ya taba
ni ta baya, da na waiga sai na ga ya miko mini
Naira dubu biyu 2000. Na sa hannuwa bibbiyu da
sauri na kalmashe ina godiya.
Ganin na yi sadakar Naira goma ga shi ni kuma
nan take Allah ya tausaya mini, ya ninka mini
ninkin-ba-ninkin abin da na bayar. Don haka da
na amshi dubu biyun nan sai na kira wannan
mabukacin na sake mika masa dubu daya, shi
kuwa sai murna, baki har kunne, ya yi ta sanya
mini albarka kamar dansa.
A zuciyata kuma ina fatan wannan karon wani
Alhajin a masallacin ya ninka mini abin da na
bayar. Na yi ta zuba na-mujiya ina baza na-zomo
in ji inda za a yafuto ni a miko mini masu kauri.
Na ji shiru, wai Malam ya ci shirwa, babu wanda
ya ce mini ungo har aka fara watsewa daga
masallacin.
Sai ni ma na fito domin taya shanu ciri, jikina a
sanyaye ina karanta wasikar jaki, a cikin raina
kuma ina cewa, “Da ma rike dubu dayata na yi
tun da dai Allah ne ya kawo mini ita, amma ga
shi yanzu garin neman gira na rasa ido.”
Na fito daga cikin masallacin duk jikina ya yi
la’asar, ina tunanin wannan rashi da na yi, sai ga
mutumin nan da ya ba ni dubu biyu. Ya masto
kusa gare ni ya ce “Malam, dubu biyun nan da na
ba ka fa kudinka ne suka zubo daga cikin aljihu
yayin da kake ciro Naira goma.”

Nan take na dafe kai, sai gumi ya fara keto mini.
Wannan shi ake kira tsammanin warubbuka,
malam ya ki noma domin jiran zakka.

KOMAI ZA MU YI MU RIKA TSARKAKE ZUCIYA.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bukar Mada

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: