Tuesday, 26 September 2017

WASIKAR JINI!! . Littafi na Daya (1) . Part A

Tura Wannan Zuwa

A wani zamani can baya mai tsawo daya shude a
cikin daular kasashen larabawa anyi wani
shararren
sarki mai suna Aiyuba Ibinin Silhar.Masana
hasashe da masu bincike na wannan zamani sun
tabbatar
dacewa babu wani sarki a duniya kaf wanda
yakai sarki Aiyuba tarin dukiya da kuma karfin
sihirin
tsafi,saidai kash,ko kadan bai kasance sadauki
ba ko jarumi mai karfin damtse da iya yaki,amma
saboda wannan dukiya daya tara da kuma karfin
sihirin tsafi sai ya zamo dodo ga dukkan
sarakunan dake nahiyar ya zamana cewa duk
tsoronsa sukeji.Komai yawan dakarun yakin sarki
da kuma jarumtakarsu indai sukace zasu yaki
sarki Aiyuba saidai su sha
kashi.Sarki Aiyuba yana da matar aure guda daya
rak mai suna Hufaira wacce sukayi auren saurayi
da budurwa tun kafin ya zamo sarki wato ya gaji
karagar mulki a wajen mahaifinsa kuma kafin ya
tara dukiya taban al'ajabi.Allah bai bawa sarki
Aiyuba haihuwa ba saida ya shekara daya akan
karagar
mulki a sannan idanunsa suka bude akan fadada
harkokinsa na kasuwanci izuwa ko ina a cikin
duniya,ya zamana cewa duk bangaren da mutum
yaje a duniya walau kasar larabawa,turawa da
bakaken fara da kuma bangaren kasar Hindu da
birnin Sin sai yaga gonaki,gidaje,da rumfuna Na
kasuwa anan na sarki Aiyuba Ibn Silhar.Kuma
gaba dayan fatakensa suna amfani da wani
hatimi guda
daya mai taswirar rakumi da takobi a jikin
kowacce irin haja tasa sai kaga wannan hatimi.
Dukkanin yaransa masu sarrafa duniya suna
tsananin tsoronsa
kuma suna adana masa dukiyar domin idan ka
kuskura kaci amanarsa tofa ka rinka ganin
masifu kenan iri iri na cututtuka masu
azaba,kuma ka rinka
shiga bala'i iri iri kenan har sai kazo gabansa ka
kawo wannan dukiya kuma ka tuba sannan zaka
samu kanka.
Wani babban hali na kirki a tare da
sarki Aiyuba shine ko kadan baya wasa da hakkin
yaransa yana biyansu ladan aikinsu kamar yadda
ya kamata,kuma indai ka shekara guda kana yi
masa bauta kaima ka fita daga sahun talakawa
saidai a
saka ka a sahun attajirai.
.
A shekarar farko daya hau karagar mulki ne
Matarsa Hufaira ta haifar masa 'ya mace
kyakkyawa ta gaban kwatance mai
sunaNuwaira,koda yake sarki Aiyuba yaso ace
'da namiji ya samu domin ya gaje shi amma duk
da haka saida yayi farin ciki ainun kuma saida
aka shafe kwana saba'in kullum sai anyi walimar
ta farin cikin samun
wannan 'ya.Attajiran sarakai da matsafa saida
sukazo daga kowanne bangare na duniya suka
halacci wannan biki na murnar haihuwar gimbiya
Nuwaira.Batun maroka kuwa duk wanda ya sami
damar shiga gidan sarautar sarki Aiyuba kakarsa
ta yanke saka domin shi da talauci sunyi hannun
riga.Da yawan marokan haukacewa sukayi
saboda ganin irin tsananin dukiyar da suka samu
wacce bama suba hatta jikokinsu da tattaba
kunnensu sai sunci albarkaci,wasu kuwa kuka
suka kamayi domin basu san ta yadda zasu iya
diban dukiyar ba su tafi
da ita,bisa dole komai hadamar maroki yabar
wata dukiya ya kwashi iya wadda ya iya diba.Yan
fashi kuwa dake kan hanyoyin zuwa birnin
Lailatun Harus wato birnin sarki Aiyuba basu taba
samun ganima ba a rayuwarsu irin ta shekarar da
aka haifi Gimbiya
Nuwaira,wasu ma da yawansu sanadin daina yin
fashin su kenan.
Bayan an kwana saba'in ana walimar murnar
haihuwar ta gimbiya Nuwaira sai baki suka watse
suka koma izuwa kasashensu,a lokacin ne fa
labarin Gimbiya Nuwaira dana mahaifinta ya sake
yaduwa da fantsama a ko'ina cikin
duniya,sunayensu ya zamo abin kwantace,daukak
arsu ta shafe duk wani mai sharafi a zamanin.
.
Wani babban abin mamaki da yake daurewa
mutane kai dangane da sarki Aiyuba shine babu
wanda yasan a inda yake tara dukiyarsa ko
yake boyeta,
Amma duk sa'adda yaso yayi amfani da dinare
ko lu'u lu'u ko makamancin su kawai zaice aje
guri kaza ne a dauko,ana zuwa kuwa za'a ga
dukiyar koda yawanta yakai cikin gari guda,kuma
koda an san cewa babu komai a wajen,mafi
yawan
wuraren dayake cewa aje a debo dukiyar ma
wulakantattun wurare ne marasa daraka inda
babu
tsaro kamar kududdufai ko inda ake tara shara.
Haka dai arzikin sarki Aiyuba yaci gaba da
habaka ya zamana cewa kullum a cikin gyara
birninsa yake da gine gine na kawa da kasaita
har saida takai cewa a duniya kaf babu wata
kasa data kai tasa
kyawu,tsaruwa da kawa,fadarsa kuwa aljanar
duniya ake kiranta domin komai na cikinta da lu'u
lu'u aka yishi.
Lokacin da gimbiya Nuwaira takai shekara
bakwai a duniya sai kyawunta ya ninka
nada,al'amarin da yasa iyayenta suka kara son ta
kenan ainun fiye da koyaushe.'Yayan masu fada
a ji
kuwa tun daga sannan suka fara kamun kafa ta
neman aurenta saboda matsayin ubanta da kuma
kyawunta,amma sai sarki Aiyuba yayi biris da
bukatarsu komai irin dangantakar dake
tsakaninsa
da iyayensu kuwa,wannan shine abu na farko
daya fara jefa hassada a zukatan sarakunan dake
nahiyar suka fara tsanar sarki Aiyuba.
A yamma da birnin Lailatul Harus wato birnin
sarki Aiyuba akwai wata kasa mai suna
Hirama,sarkin dake mulkin kasar Hirama ya
kasance gagarumin sadauki mayaki mai tarwatsa
maza a filin daga,ana kiransa da suna
Murwatu,shima matsapi ne na gaske,amma bai
kama farcen kafar sarki Aiyuba ba,domin ya taba
jarraba karfin tsafinsa akan na sarki Aiyuba yaji
ba dadi,harma saida ya durkusa bisa gwiwoyinsa
a gaban sarki Aiyuba ya nemi gafara don kada ya
rasa rayuwarsa.
Al'amarin ya faru ne a wata shekara da akayi fari
a kasar Hirama ya zamana cewa
yunwa,fatara da talauci ya addabi mutanen kasar
har takai cewa kananun yara da masu rauni suna
mutuwa.Lokacin da al'amarin yayi tsamari ainun
sai sarki Marwatu yasa aka rubuta wasika ya
tashi
manzo izuwa ga sarki Aiyuba a cikin wasi kar ya
nemi taimakon abinci mai yawa gami da aron
kudade masu yawa domin ya bunkasa harkar
noma a kasar tasa,dama babbar matsalar kasar
itace kasarsu bata da dadin noma sai masana
kasa sunzo sunyi mata aiki sannan kuma suna da
karancin
ruwa,dole ne a buda hanyoyin ruwa daga
kasashen ketare su shigo,kuma a nemi iri mai
kyau na
shuka.
Sarki Marwatu ya dauki alkawarin cewa bayan ya
shekara guda zai dawo da duk kudin da aka ara
masa kuma zai bayar da riba kaso guda cikin
uku.
Lokacin da wannan wasika ta riski sarki Aiyuba
yana zaune akan karagar Mulki a fadarsa ana
tafiyar
da harkokin mulki,ga Gimbiya Nauwara zaune a
cinyarsa kumaga fadawansa da sauran jama'ar
gari sun kewayeshi.
A tsakiyar fadar wadansu kyawawan 'yan mata
ne su bakwai suna ta tikar rawa anayi musu kida
don debe kewa.
A wannan lokacin sarki Aiyuba yana cikin nishadi
da walwala don daka dubeshi kasan cewa farin
ciki ya cika zuciyarsa.Bayan magatakarda ya
gama karanta wasikar sarki Marwatu sai sarki
Aiyuba ya tuntsire da dariya irin tasu ta sarakai
masu jin izza sannan ya dubi 'yarsa Gimbiya
Nauwara yace,'yata kinji
bukatar da sarki Marwatu yazo mini da ita,shin
kin amince na taimaka masa ko kuwa na rabu
dashi?
Kisani cewa duk wannan dukiya dana tara a
duniya badan kowa na tara taba sai domin
ki,kece kadai
kike da ikon fadin abinda za'ayi da ita.Koda
fadawan sarki Aiyuba da sauran jama'arsa sukaji
wannan
batu sai suka cika da mamaki sukayi zaton ma
ko sarki Aiyuba ya sami dan tabin kwakwalwa ne
domin basu ga dalilin da zaiyi wani abu da
dukiyarsa sai ya tambayi 'yarsa wacce ta
kasance yarinya karama 'yar shekara bakwai.A
lokacin da gimbiya taji tambayar da mahaifinta
yayi mata saita yi murmushi sannan ta
dubi sarki tace,yakai Abbana kayi sani cewa kana
daarzikin da zaka iya ciyar da gaba dayan
kasashen dake nahiyar nan tamu kuma ka
wadatar dasu da arzikin da zasu tsira daga
talauci to amma nafi so
kayi taimako a inda ya dace abinda nake nufi
shine wannan sarki Marwatu yana daga cikin
wannan
sarki Marwatu yana daga cikin irin sarakunan da
sukayi maka girman kai,
baya daga cikin sarakunan da suke zuwa
gaisheka duk shekara duk wani abu na farin ciki
idan ya sameka baya zuwa ya tayaka sai yanzu
da bukatarsa ta taso sannan zai nemi
taimakonka.By M. Kabiru Muhammad
To kasani cewa bazamuki taimakonsa ba,kasa
akai masa abinci mai yawan gaske kuma a bashi
kudade masu yawa wadanda zasu isheshi ya
gyara harkar noma amma bisa sharadin zai
biyaka kuma ya biya ka riba bayan cikar shekara
guda kamar yadda ya
sharadanta da kansa.In har ya karya wannan
alkawari to duk abinda ya biyo baya kada ya
zargo
kowa face kansa.
Baya ga wanann inaso ka gaya masa a cikin
amsar wasikarsa cewa kai mai arziki ne kuma
attajir uban sarakai inda ma ya nemi kyauta da
an bashi amma rashin biyayyarsa ce ta sanya a
bashi aro.
Koda Gimbiya Nauwara tazo nan a
zancentsa sai gaba dayan mutanen dake fadar
suka cika da tsananin mamaki bisa yadda akayi
Nauwara ta zamo yarinya mai kaifin hankali da
tunani haka, shi kuwa sarki Aiyuba sai ya kamu
da tsananin farin ciki ya dubi 'yan majalisa
yace,kunga wannan yarinyar dole ne ta kasance a
cikinku domin ko babu ni zata iya baku
shawarwari akan harkokin mulki wadanda zasu
amfane ku su amfani kasa gaba daya,kuma duk
abinda ya taso na kudi zata taimaka muku
dashi,saboda zata gaji duk dukiyarta bisa wannan
dalili daga yau dinnan na mika matsayin
Galadima a hannun Gimbiya Nauwara tunda shine
matsayi na kula da duk harkokin kasuwancinmu
da sarrafa kudaden kasa,koda jin wannan batu
sai idanun Galami suka zazzaro hankalinsa ya
dugunzuma kuma ransa ya baci.Ya dubi sarki
Aiyuba cikin alamun tsananin damuwa a lokacin
dayai sauri ya durkusa a gabansa zai fashe da
kuka yace,Haba yakai dan uwana ya za'ayi kace
gimbiya ce zata karbi matsayina alhalin
shekarunta basu kai ta ruke wannan mukamin ba
kuma idan ta karbi wannan
mukami ni kuma wane matsayi zan rike a wannan
majalisa ko kuwa so kake na karayin kasa ne?
Koda jin wannan batu sai sarki ya mike tsaye
daga kan karagarsa ta mulki ya sauko har kasa
inda galadima ke durkushe ya kama kafadunsa
ya tashe shi tsaye ya dubeshi cikin murmushi
yace,Yakai galadima kayi sani cewa har abada
bazan taba wulakantaka ko
kaskantar dakai ba saboda kaine kadai dan
uwana na jini daya rage a wannan duniya,a kan
wane dalili
zaka damu da mukami a cikin wannan fada
alhalin ko yanzu na fadi na mutu kaine zaka gaji
karagata,tunda babu yadda za'ayi gimbiya tayi
mulki bisa dokar wannan masarauta tamu?
Idan kana kwadayin dukiyar da take kai kawo ne
a ofishinka na
kasuwanci idan ka zama sarki komai na
hannunka,ka sani cewa gimbiya babbar
gudunmawa
zata bayar a gareka kuma da babban taimako na
kudi ko nawa ake bukata tunda arzikin da zan
barmata ya ninka duk arzikin dake cikin kasashen
nan na nahiyoyinmu sau goma,daga yau ka koma
matsayin wazirina tunda ka sani cewa tunda na
hau mulki kujerar wazirci babu kowa a kanta,koda
jin
wannan batu sai farin ciki ya lullube galadima ya
kama godiya kamar bazai daina ba,amma yana
hada idanu da gimbiya Nauwara sai ya murtuke
fuska kamar wanda aka aikowa da sakon
mutuwarsa,ita kuwa saita risina a gareshi kuma
ta tayashi murna bisa samun wannan sabon
mukami na waziri.
Nantake sarki Aiyuba yasa aka rubuta wasikar da
sarki Marwatu ya aiko da ita kuma akayi bayani a
cikinta kamar yadda Gimbiya Nauwara ta
bukata,daga nan
sai aka shirya buhunhunan abinci a kalla miliyan
uku bisa keken shanu da rakuma gami da
buhunhunan dinare duba arba'in bisa rakiyar
dakaru dubu dari aka baiwa manzo na sarki
Marwatu suka kama hanya suka durfafi birnin
Hirama..........
.
Dafatan littafin yayi.?
.
Kasancewar korape-korapen da najima ina samu
akan cewa ayi wani littapin yaki nikuma banida
lokaci daman kun sani, wannan dinma nayi
rubutun ne tun 2015 yana ajiye shiyasa nace to
ko akwai wanda basu karanta ba wasu kuma
zasu so sake karantawa...
.
Idan kanason cigaban labarin ka hanzarta yin
Like ko kayi Comment Inaso....
.
Ina patan zaku bani hadin kanku mu gudu tare
mu tsira tare.
.
Daga dan uwan ku kanin ku mai kaunar debe
muku kewa a koda yaushe M. Kabiru Muhammad
07068335066

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©M. Kabiru Muhammad

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: