Wednesday 4 October 2017

01. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN'UWANSA SHAMSUDDIN.

Tura Wannan Zuwa

Allah shi ne Sarki ma fi daukaka daga dukkan
Sarakuna, shi ne ma fi tsarki daga dukkan
abubuwa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga
Manzonsa, Annabi Muhammadu (S.A.W).

Ka sani, ya Sarkin Musulmi, a kasar Misira an yi
wani Sarki, ma'abucin adalci da kyautatawa.
Yana da Waziri mai hankali, mai rarrabe abubuwa
da dabaru, mai tarin ilimi da fasaha, sai dai ya
kasance tsoho ne, shekaru sun yawaita a kansa.

Wazirin nan yana da 'ya'ya biyu maza, kai ka ce
'yan tawaye ne. Ga su kyawawan gaske, babu
kamar su a duk fadin kasar. Sunan babban
Shamsuddin, sunan karamin kuwa Nuruddin.
Karamin, watau Nuruddin, ya zarce wansa ga
kyawo da cikkar halitta. Ya kasance a cikin
wancan zamanin babu tamkarsa ga kyawo.

Labarin kyawonsa ya watsu cikin manyan birane
da kauyuka. Mutane da dama sukan tafi tun
daga garinsu har zuwa Misira, domin ganin
kyawo irin na Nuruddin.

Kwanci tashi, ran nan sai Wazirin Misira ya
kwanta ya mutu. Sarki ya yi matukar bakin ciki a
kan mutuwar Wazirinsa. Sarki ya rungumi 'ya'yan
Waziri a jikinsa, ya ce, "Ku ne a matsayin ubanku
a wurina." Yara suka yi farin ciki. Aka yi zaman
makokin mahaifinsu aka gama.
Shamsuddin da kanensa Nuruddin suka zama su
ne a matsayin Waziri ga Sarkin Misira. Idan
wannan ya hau karagar mulki, bayan sati guda
sai ya sauka dan'uwansa ya hau. Sukan yi canji
duk ranar Jumu'a, idan kuma Sarki zai yi tafiya,
sai ya tafi da daya, ya bar daya yana mulkin gari.
Wata rana daga cikin ranaku, Sarki ya yi niyyar
tafiya wata kasa, aka yi gamo da katar, hukunci
ya fada za a tafi da babban ne, watau
Shamsuddin.

Daren da za su tafi, Shamsuddin ya kira dan
uwansa suka zauna suna hira. A cikin hirar tasu
Shamsuddin ya ce da dan'uwansa, "Na yi nufin
idan Allah ya maido mu gida lafiya daga tafiyar
da za mu yi gobe da Sarki, mu yi aure lokaci
guda, a cikin rana guda."
Nuruddin ya ce, "Kai ne babba, kuma kai ne a
matsayin ubana a halin yanzu. Ka aikata duk
yadda ka so, za ka same ni mai biyayya a gare
ka."
Shamsuddin ya ce, "Insha Allahu da zarar na
dawo, zan nema mana 'yan mata biyu, mu aure
su rana daya, mu shiga dakinsu dare daya, su
sami ciki lokaci daya, su haihu rana daya.
Matarka ta haifi da namiji, matata ta haifi 'ya
mace. Su tashi tare, su yi wasa tare, idan suka
isa aure mu aurar da su ga junansu, su zama
'yan bappanni."
Nuruddin ya ce, "Allah ya sa haka. To amma idan
haka ta tabbata, me za ka karba gun dana a
matsayin sadakin 'yarka?"
Shamsuddin ya ce, "A matsayin sadakin 'yata,
zan karba gun danka, dinari dubu uku, da gona
talatin, da gidaje uku."

Yayin da Nuruddin ya ji haka sai ya ce, "Haba!
Wane irin sadaki ne mai tsanani za ka dora wa
dana haka, ko ka manta cewa mu 'yan'uwan juna
ne, kuma Wazirai muke, matsayinmu daya. Ya
zamanto wajibinka ne ka aurar da 'yarka ga dana
kyauta, ba tare da karbar ko dirhami daga gare
shi ba. Ko ba ka san namiji ya fi mace daraja
ba?"
Shamsuddin ya harzuka da wannan zance na
kanensa, ya ce, "Babu shakka kai ba ka da
hankali, tun da ka ambata tarayyar Wazirtaka
tare da ni, kuma kana nufin danka ya fi 'yata
daraja ne? Ni fa na roki Sarki ya sa ka Waziri
tare da ni saboda tausayinka da nake ji, shi ne
yanzu har kake hada kanka da ni. Tun da har ka
fadi haka, to Wallahi ba ni aurar da 'yata ga
danka, ko da zai biya zinariyar da ta kai nauyin
'yar tawa a matsayin sadaki."
Yayin da Nuruddin ya ji zancen dan'uwansa, ya yi
fushi, ya ce, "Ni ma dana ba zai auri 'yarka ba,
ko da babu sauran mata a duniya sai ita kadai."

Shamsuddin ya ce, "Ni ma ban yarda 'yata ta
auri danka ba, ko da babu sauran maza a duniya
sai shi kadai. Amma yanzu na yi nufin tafiya,
waccan niyyar ta aurenmu lokaci daya na fasa
yin ta, Allah ya aikata yadda ya so."
A cikin wannan dare, Nuruddin da Shamsuddin ba
su kwana wuri daya ba kamar yadda suka saba,
kowa ya kwana daki dabam saboda bacin rai. Da
gari ya waye, Shamsuddin ya shirya domin tafiya
da Sarki, ya nemi dan'uwansa domin su yi
sallama amma bai gan shi ba. Don haka sai ya bi
Sarki suka tafi.

Ashe kuma tun da asuba Nuruddin ya riga
Shamsuddin tashi daga barci, ya shiga taska, ya
dauki jaka karama ya cika ta da dinari. Ya tuna
maganganun da dan'uwansa ya yi masa a daren
jiya, da kuma gorin Wazirantaka da ya yi masa.

Ya tuna wakar wani mawaki, in da yake cewa:
"Ka yi tafiya cikin duniya, za ka sami musayar
abin da ka rasa.
Ka kafu da kafafunka, farin ciki na ga wanda ya
dogara da kansa.
Ni na ga tsayuwar ruwa wuri daya tana gurbata
shi, ruwan da yake gudu shi yake tsarkaka.
Ba don farin wata yana fakuwa ba, da ba a dube
shi ba ranar tsayuwarsa.
Ba don zaki yakan rabu da surkuki ba, da bai
sami abin farauta ba.

Ba don kibiya takan rabu da baka ba, da ba ta
zama abin tsoro ba.

Komai kyawon sanda, idan tana jikin icce ba a
ganin kyawonta.
Zinariya tamkar kasa take, ba a ganin kyawonta
sai ta rabu da kasa.
Wanda ya zauna gida, ba ya daukaka har duniya
ta san da shi."

Bayan ya dauki abin da yake so ya dauka daga
cikin taska, ya umurci wani bawansa ya daura
masa sirdi ga wani farin dokinsa mai kiba, mai
gaggawar tafiya. Bawa ya daura wa doki sirdi da
likkafu kirar kasar Hindu. Ya shimfida shimfidar
Asbihaniya a kan sirdin. Bawa dai ya shirya doki
da kayan kawa masu tsadar gaske wadanda sai
sarakuna da attajirai ke yin amfani da su.
Da Nuruddin zai fita, ya ce wa bawan nan nasa,
"Ina so in fita zuwa bayan gari, zan tafi unguwar
Kalyubati in kwana uku. Kada kowa ya bi bayana,
ina da bacin rai tattare da ni, idan na sami
nutsuwa zan dawo."

Yayin nan ya yi gaggawa ya hau dokinsa, ya rike
wani abu kadan na guzuri a hannunsa, ya fita
daga Misira ba tare da ya san inda zai tafi ba.
Burinsa kawai ya yi nisa da kasarsu da kuma
dan'uwansa Shamsuddin, ya shiga duniya, duniya
ta gan shi, shi ma ya ga duniya.

***
Wannan shi ne farkon labarin mai cike da tu'ajibi
da mamaki da ban tausayi. Za mu ci gaba ranar
Litanin mai zuwa daidai wannan lokaci (karfe 8 -
9 PM), Insha Allah.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Waziri Aku

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: