Thursday 5 October 2017

7. YAWON DUNIYAR HAJJI BABA Na James Morier Abubakar Tunau Ya Fansar Da Shi

Tura Wannan Zuwa

Ya tambaye su ina kudin da suka sace mini?
Suka ce ba su saci kome ba. Dan Sarkin ya ce a
tambaye su. Tun da aka fara koli koli da su, sai
suka ce suna nan. Suka kawo kudin, dan Sarkin
ya kirga ya daga tabarmarsa ya zuba, ya ce mini.
“Tashi an sallame ka.” Na tsaya ko zai miko mini
kudin amma ina! Da dai na ce ina kudina, shi ke
nan sai na ji an rufe ni da duka, aka ce mini
maza in tafi im ba ina so a yanke mini kunne ba!
Ka ji ikon Allah, ni da kudina wai har za a yanke
mini kunne!
Da na ga haka sai na nufi mai alfadarin nan. Na
gan shi bai yi ko mamakin wannan abin da ya
same ni ba. Ya ce, “To, wane abu kuma ka ke
zato? Ashe shi ba dan Sarki ba ne? Duk ran da
shi, ko wani mai iko, ya sami wani abu, kana
tsammani za su bayar da shi? Ai duk daya ne da
a ce alfadari ya mayad da ciyawar da ya rigaya
ya sa a baki."
Muna cikin tafiya har muka isa Meshed. Ashe ko
da ma an san dan Sarkin nan yana zuwa, mutane
jingim suka taru, Sojoji suka yi holi, aka yi masa
maraba. Na duba na ga, ga ni a garin da ban san
kowa ba, ba ni da aboki wanda zan nemi taimako
gare shi. Hasali ma ko da asake biyu ba ni da su!
Na tsaya na dubi irin abin da ke gare ni, na ga
ina da wajen £4, wadanda na sato a jakar kudin
nan da na sace a Isfahan, na dinke su a kokuwar
hulata. Ina kuma da kwat mai kauri, da ’yar ciki
ta fatar rago, da kwalashat, da wando daya, da
manyan takalma kafa daya. A da na ji dadi na
raba wa mai alfadarin nan ina samun abincin da
dan Sarkin nan kan ba shi ko wace rana, to, ga
shi yanzu an sallame shi duka da alfadarinsa. In
na ce zan zama wanzami ba wanda zai yarda in
taba masa kai, don an ce ni dam fashi ne. Ko da
a ce ma zan sayi asake, duk da haka ba ni da
isassun kudi wadanda zan gina dakin aski da su.
Da abu ya rikirkice mini sai na koma ga abokin
nan nawa mai alfadari. To, shi ya rigaya ya san
irin halin zaman Meshed, don haka ya ce ba aikin
da zai dace da ni sai dan ga ruwa. Ya ce mini,
“Ka ga kai yaro ne kana da Karfi, ga shi kana da
murya mai kyau wadda za ka iya jawo hankalin
mutane da ita su sha ruwanka. Alhazan da su
kan zo Meshed su yi ibada suna da yawa kwarai.
Tun da ya ke kuwa sadaka ce muhimmiyar aba
da su kan bayar don su sami tsira, su kan ba da
ita da yawa ga wanda ya yi musu fata ta gari. Ka
sayad da kowane digo na ruwanka cikin sunan
Imam Husaini. Kullum ka yi tallar ruwan kyauta,
amma ka lura kada ka zuba wa kowa sai ka rike
kudin a hannu. In wanda ya sayi ruwan wurinka
ya sha ya gama, ka ta da murya da karfi ka yi ta
kiran sunan Imam kana yabonsa yadda kowa zai
ji. A takaice dai, ka fadi kome da ka ke so a
gaban alhazai, ka tabbata kuwa za su gaskata
ka. Ni kaina na taba zama dan ga ruwa a nan
wurin, na san kome da kome na wannan sana’a.
Har na sami isassun kudin da na sayi alfadarai
hamsin, na zama mutumin kaina yadda ka ke
ganina a yanzu."
Shi ke nan na bi shawarar abokina. Nan da nan
na sayi salka da wani kwaf mai kyalkyali da ’yan
kudin da na ke da su. Na tafi na cika salkar da
ruwa, na bar ta ta tsotsi ruwa don sabuwa ce, na
sake cika ta na rataya abata a baya, na tafi inda
alhazai ke salla na yi ta tallar ruwana, kamar
yadda abokin nawa ya fada mini. Na wage baki
na yi ta yin abina, da ka gan ni ka ga tsohon dan
ga-ruwa.

Da zuwana sai na ga na fara jan hankulan sauran
'yan garuwan da ke wurin. Suka fa rufe ni da
tambayoyi, wai wa ya ba ni izni in yi cinikin
ruwa. Da muka tafi rafi tare kuma wajen dibar
ruwa, sai suna tonona fada, suna kokarin su
ingiza ni cikin rafi. Ni kuwa na dage. Da suka ga
dai ina da karfi da yawa ba za su iya cin zarafina
ba, sai kuma suka shiga habaici, suna zage zage.
Ashe ba su sani ba in dai a zagi ne ni ma wane
ne, na fa shige musu da zage zage. Da suka ga
ba gidan dadin suka tabo ba tilas suka yi shiru.
Daga baya dai na ga kamar an halitto ni ne in
zama dan ga-ruwa. Dalili kuwa ruwan nan na fari
da na debo a wani kazamin rafi, na zo na yi ta yi
masa kirari, ai fa kada ka so ka ji yawan kudin
da na samu tun da na fara ba da shi kyauta.
Kullum idanuna suna dubawa ko an yi bakin
alhazai, da zuwansu kuwa tun kafin su sauka
daga alfadaransu sai in nufe su, im ba su ruwa
kyauta su kashe kishirwa, in ce kuma ya kamata
su ba ni kudi masu yawa tun da ya ke sun tsira
daga miyagun mutanen nan ’yam fashi. Ba safai
su kan kyale ni ba, su kan ba ni kudi masu yawa.

Ana nan sai ranar tunawa da mutuwar Imam
Husaini ta matso. Na kuwa yi niyyar a wannan
rana in nuna lalle ni dan ga-ruwa ne, in yi
wasanni na nuna karfi don in yi suna, kuma in
sami riba. Shi wasan nan a gaban Sarkin garin a
kan yi. Na yi niyyar in sami wata katuwar salka in
cika ta da ruwa in hada ta da abubuwa masu
nauyi in dauke su baki daya.
Ina da wani makiyi dan ga-ruwa ne shi ma da ya
yi irin wannan wasa shekarar da ta wuce, amma
fa a wannan karon lalle abin da na yi niyyar yi ba
zai iya ba. Domin katuwar salkan nan da zan cika
da ruwa ba zai iya ko daga ta ba balle ya dauka.
Da ranar ta zo, Sarki ya fito fada ya zauna,
mutane suka taru jingim. Sai ga ni na zo daga ni
sai dan wando duk jikina rufe da jini, ina danke
da katuwar salka. Da na iso inda Sarkin ya ke sai
na yi ihu don ya san ina nan. Da ya gan ni sai ya
yi murna ya jefo mini kudin zinariya. Don murnar
samun wannan kudi sai na gayyaci wadansu yara
nan da ke kusa su hau bisa salkar, suka kuwa
hau. Haba, sai tafi raf raf raf jama’a ke yi mini
don murna. Na sake kiran wani yaro ya hau ashe
makiyin nan nawa yana kusa, sai ya yi wuf ya
hau salkar, wai ko ya ba ni kunya, amma ina! Na
daga shi tare da sauran yaran da ke kai. Tun da
aka fara yi mini tafi sai makiyin nan nawa ya fita
daga filin sumui sumui. Amma fa da aka tashi sai
na ji jikina duk ya yi tsami, bayana kuwa kamar
ya karye. Da na ga dai ba zai yiwu in sake sayad
da ruwa ba, sai na sayar da salkata, na hada
kudin da wadanda na samu na sayad da ruwa na
kuwa zama mai samu gwargwado. Na yi tunanin
in kai makiyin nan nawa kara, amma na ga ba
zan ci wata riba ba, sai na kyale. Abin haushi
kuma, shi ne abokin nan nawa mai alfadari ya
tafi Tehran, don haka na zama ni daya tal ba
aboki.

Za mu ci gaba ranar Asabar mai zuwa, da karfe
tara na dare (9:00PM), in sha Allah.
Allah ya kai mu.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bukar Mada

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: