Thursday 26 October 2017

9. YAWON DUNIYAR HAJJI BABA Na James Morier Abubakar Tunau Ya Fansar Da Shi

Tura Wannan Zuwa

“Ya ce mini in an sami wutsiyar zomo an sa ta
karkashin matashin kan yaro, nan da nan barci
zai zo masa.

In kuma an sami jininsa am ba doki,
to, dokin nan zai zama maguji kwarai. In an sami
idon kerkeci da kasusuwan yatsunsa an rataya
wa yaro, sai yaron ya zama jarumi. In an sami
kitsensa kuma an shafa wa mace, kaunarta ga
mijinta za ta bace. In kuma matsarmamansa aka
samu aka shafa wa mace, za ta yi ta haihuwa.

Amma abin da ya fi daraja duka, shi ne a sami
busasshiyar fatar kura mace a rataya. In an yi
haka, wanda ya ratayan nan zai yi farin jini ga
kowa. Ya dai yi ta yi mini maganganu irin
wadannan, ya nuna mini abubuwan da zan iya yi,
har daga karshe ya yi mini wata magana wadda
shi kansa ya san ba zan yarda da ita ba.

“Ya ce mini, ‘Sefer, ba ka san irin arzikin da ke
cikin bikan nan ba - ba ina nufin a yadda ya ke
da ran nan ba, amma in ya mutu. Da a ce
matacce ne, zan iya cire wadansu abubuwa daga
cikinsa wadanda zan yi layoyi da su, in sayad da
su da kudin gaske. Ya kamata ka sani, hantar
bika, tun ba irin wanda ka ke da shi din nan ba,
in an yi amfani da ita za ta dawo da kaunar wani
abin da a ke kauna a da ga mai ita.

ln ka sami
fatar kewayen hancinsa ka kewaye wuyanka da
shi, ba abin da zai same ka, in dai maganar dafi
ce. In kuma an kona bikan dungum aka dibi
tokarsa aka sha, sai mutum ya dauki halinsa
duka. watau wayo, da hikima da ikon kwaikwayo
na ko wane iri. Daga nan ya ce zai kashe bikan
nawa.

“Raina ya baci kwarai da wannan magana da ya
yi mini ta zai kashe bikana. Ga shi tun ina yaro
na ke tare da bikan nan, cikin murna da bacin rai
duk tare mu ke. In na ce zan kashe shi lalle na
tabbata kasaitaccen mugu. Da zan ki yarda,
amma da na ga fuskar sufin nan ta baci, na ji
tsoron kada ya gwada mini karfi ya kwace, sai na
yarda hakanan ba da zuciya daya ba.

“Daga nan muka ratse cikin daji muka isa ga
wani dutse, muka tattara itatuwa muka hura
wuta. Bayan wannan ya kashe bikan, ko addu’a
bai yi ba. Ya fede shi ya dauki hantar da fatar
hancinsa, ya jefa sauran gangar jikin cikin wuta.

Da bikan ya cinye kurmus, sai ya tara tokar a
hankali ya daure a mayaninsa. Shi ke nan muka
kama tafiyarmu.

“Da muka isa Isfahan na watsad da tufafina na
shiga irin na sufi, sa’an nan muka kama hanyar
zuwa Tehran. Da zuwammu wannan gari sai na
ga mutane da yawa suna ta zuwa wurinsa suna
bidar magani. Iyaye suka zo suna tambayarsa
maganin tsare 'ya'yansu daga kambun baka,
mata suna neman maganin da za su kashe kishin
mazajensu, jarumai suna tambayar layar yaya ka-
yi-ka fito, matan Sarki suna tambayar maganin
da hankalin Sarki zai koma kansu.

“Kai, ga su nan dai barkatai. Duk kuwa sufin nan
ya shirya su tun farko, don ya san haka zai auku.

Wata tsohuwa daga cikin matan Sarki ta sami
hantar bikana, wai in ta rataya Sarki zai fi ganin
darajarta, ya fi kaunarta. Wata kuma ta sami
tokar bikan, wai za ta yi farin jini ga Sarki. Wata
kuma ta sami mai, wai in ta shafa da kyau, in dai
ba dariya ta yi ba, lalle tamojin fuskarta zai bata,
fuskarta ta yi sumul! Ina ta taimakon sa
bayarwa, amma duk abin da ya samu, ko da
kuwa da bikana ya hada maganin, sai ya sa
aljihunsa, ko anini ba na gani."

BABI NA 6

Karshen Abin Da Su Sufi Sefer Suka Fada
MUN ZAGAYA kasashe da dama da Sufi Bideen
muna yi wa mutane tsubbu. A wani wuri a dauke
mu ana yi mana sujada kamar alloli, a wani wuri
kuwa sai a yi ta jifarmu. Duk tafiye-tafiyen nan
namu a kasa mu ke yinsu, don haka na sami
zarafin sanin cikin garuruwa dabam dabam.

“Daga Tehran muka tafi Birnin Santambul, daga
nan sai Aleppo, sai Alkahira. Daga nan muka tafi
Makka da Madina, muka shiga jirgi daga Jidda
muka sauka a Surat. Daga nan muka kama tafiya
a kasa zuwa Lahore da Kashmir a lndiya.

“A Kashmir muka so mu gwada wannan hanyar
zamba, amma sai muka ga mutanen garin idonsu
ya waye, ba su yarda da karairayi ba. Don haka
muka saci jiki muka gudu zuwa Herat. A nan
kam burimmu ya biya mana. Mutanen jahilai ne
na ainihi, kome muka ba su suna yarda da shi.

"A wannan gari ne fa sufin nan ya ke so ya fito
musu kamar shi Annabi ne. Ya tafi kan wani
dutse ya shiga bukka ya kulle kansa, ni kuwa ina
ta fada wa mutane wai ba ya cin kome sai dai
abin da aljannu ke kawo masa. Nan kuwa sai da
ya shirya abincinsa kaf kafin ya tafi.

“Ba a dade ba ya mutu a kan dutsen. Na bi
mutanen nan ina ce musu wai aljannu ne su ke
kishimmu saboda muna da irinsa a cikimmu, don
haka suka cika shi da abinci har ransa bai sami
wurin zama ba, don haka ya fito, iska kuwa ta
kora shi can sama ta biyar ! Na yi kokarin im
bayyana wa jama’ar garin wai iskan nan mai karfi
da ta kan zo kowace shekara sufin nan ke aiko
da ita don amfanin kansu. Amma tsofaffin wurin
da suka san irin wannan iska tun tuni ba su
yarda da ni ba. Duk da haka wannan bai rage
mana daraja da kwarjini ba.

“Da aka zo jana'izarsa, haba, kada ka so ka ga
yawan mutanen da suka taru. Har Sarkin Herat
Eshek Mirza da kansa ya shiga cikin masu
daukar amuku ! Bayan wannan, na zauna kadan
ina yi musu tsubbu, amma da na ga in na kara
dadewa za su gane, sai na gudu na tafi na zauna
a cikin wata kabila.

A nan ma wurin sun dauke ni
kamar Annabi."

Daga nan na ga Sufi Sefer ya dibiya hannunsa a
kan daya sufin ya ce mini, “Aboki, ka ga
dan’uwana nan a wannan lokaci zai iya tuna
dabarun da muka yi ta yi wa kabilan nan. Sun
gaskata za mu iya yin kome, in dai abin zai
amfane su. A takaice dai, na zama shahararre
tsakaninsu. Daga nan na zo Meshed na zauna.

Bai fi mako guda ba da muka yi wani abin al'ajibi
a nan. Wata yarinya ce makauniya muka sa ta
tana ganin gari. Don haka, yanzu a nan ana
girmama mu kwarai da gaske."

A nan Sufi Sefer ya kare Iabarinsa, ya ce kuma
dayan ya ci gaba da ba da nasa. Shi kuma ya
kama, ya ce, "Ubana shahararre ne game da
shari'a a Birnin Kom. Duk cikin Farisa ba a taba
wani wanda ya fi shi wajen rashin fashin yin
salla da azumi ba. A takaice dai, shi cikakken
Musulmi ne abin kwaikwayo. Yana da ’ya’ya da
yawa, dukammu kuwa an goye mu da tsananin
kiyaye addinimmu. Da muka ga an tsananta
mana sai muka yi dabarar kubcewa, muka shiga
shashanci.

Darajar mu wadda a ke ganimmu da
ita ta bata, aka kuwa ce mu ne cikakkun
makaryata da mazambata. Hasali ma a cikinsu ni
ne babba. Da na ga abin ya zama haka, sai na
zama sufi. Ga labarin yadda na yi farin jini a
cikin wannan hali.

(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi

bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada

Za mu ci gaba ranar Asabar mai zuwa, da karfe
tara na dare (9:00PM), in sha Allah.

Allah ya kai mu.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Bukar Mada

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: