Saturday, 7 October 2017

Adul'aziz Sani Madakin Gini: WASIKAR JINI!!! Littafi Na Daya (1) Part B

Tura Wannan Zuwa

Aka baiwa wannan manzo na sarki Marwatu suka
kama hanya suka durfafi birnin Hirama.
Al'amarin waziri Ridwan bin Silhar kuwa lokacin
da fada ta watsa sai ya tafi izuwa gidansa cikin
tsananin farinciki tamkar an mallaka masa
duniyar gaba daya
nan take yasa aka shirya walima ta musamman
ya gaiyaci duk manyan abokansa na birnin da
kauye. Washe gari kuwa gidansa ya cika makil
ya batse da jama'a maza da mata,ba'a fara
walimar ba sai bayan anje fada an gama bikin
nadashi,babban abinda ya bakantawa waziri
Ridwan rai shine ba sarki ne ya nada masa
rawani ba na wazirci,Gimbiya Nauwara ce ta
wakilci sarki kuma tun a fada yaga komai ya
sauya na irin ikonsa da karfinsa akan harkokin
arziki na kasa.Hatta dukiyar da ake ajiyewa a
Baitul Mali a gabansa mai kula da dukiyar yazo
gaban gimbiya da lissafin komai kuma yayi bata
bayanin yadda ake sarrafa dukiyar bisa tsarin
tsohon galadima,koda ta fahimci cewa tsari ne
nason kai da son zuciya,domin akwai wadansu
kudade da suke shiga aljihun galadima a banza
maimakon su rinka zuwa hannun talakawa
mabukata,sai ta dubi ma'ajin baitul Malin
tace,yau zan canja tsarin komai na dukiyar dake
cikin baitul Mali kuma zan kirawoka na baka
komai a rubuce bisa yadda nakeson a rinka
tafiyar dashi.

Koda waziri yaji wannan jawabi na gimbiya sai
zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone
kuma yaji ya sake tsanar gimbiya fiye da ko
yaushe,ba komai ne ya janyo hakan ba face ya
san cewa da zarar gimbiya ta sauya tsarin komai
na
dukiyar baitul mali shike nan ya daina samun
kudade masu yawan gaske wadanda dasu ne
yake sharholiyarsa a garin yake yin duk abinda
yaso har ma ake shakkarsa.
.
Da farko attajiran garin sun dauke
cewa sarki Aiyuba ne yake baiwa dan uwansa
Ridwan kudade shi yasa yake tafiyar da rayuwar
mai
mugun tsada a gidansa da harkokinsa,amma a
yanzu da aka sauke shi daga matsayinsa na mai
kula da bailtu mali sai komai ya sauya ya kasa
cigaba da bushasha kamar yadda ya saba duk da
ci
gaba daya samu a majalisa ba baya ba.
Bayan an dawo daga fada an fara walima mutane
maza da mata,sarakai da attajirai,da masu fada
aji suna ta ciye ciye da shaye shaye a cikin
babban falon gidan Waziri Ridwan amma shi mai
gaiyatar babu shi a wajen sai matarsa Gimbiya
Ra'isa wacce itace take
karbar baki tana sawa ana kaisu inda ya kamata
su zauna,koda Ra'isa taga an shafe kusan rabin
sa'a da fara walimar amma mijinta bai gama
shirin ba ya fito daga cikin turakarsa sai ta tafi
izuwa turakar tasa da sauri.Tana shiga sai ta
iske shi a zaune bisa kujera
ya kifa kansa akan tebur yana ta sheshshekar
kuka,al'amarin daya dugunzuma hankalinta kenan
ta ruga gareshi ta dago da kansa suka dubi juna
tace,Haba yakai Abul Zainur yaya zaka zauna
anan kana kuka alhalin yau rana ce ta farin ciki
bisa babban mukamin daka samu,ga masoyanka
can fa
sun taru a falo ana tayaka murna.Koda jin
wannan batu sai waziri Ridwan ya kyalkyale da
mahaukaciyar dariya,al'amarin daya firgita Ra'isa
kenan ta danja da baya ta kura masa idanu
kawai.Take Ridwan ya tsuke bakinsa ga barin yin
dariyar ya dubeta cikin
yanayi na bakin ciki a lokacin da hawaye ya zubo
masa yace,Yake matata kiyi sani cewa dan
uwana
sarki Aiyuba ba matsayi ya kara mini ba tauyeni
yayi domin wannan kujera ta waziri daidai take
da ajiye ice ko dutse abinda bashi da rai wanda
bazai iyayin
ko motsin komai ba,kin sani cewa bani da wani
buri a wannan duniya face na zamo gagarumin
attajiri
wanda babu kamarsa a duniya a tarin dukiya
dajin dadin komai na barwa duniya abin tarihin da
baza'a
taba mancewa dashi ba.
A da nayi tunanin cewa da zarar dan uwana sarki
Aiyuba ya mutu zan cika wannan buri nawa
tunda ni kadai nake da gadon duk abinda ya
mallaka amma a yanzu daya sami haihuwa sai
dukkan burina ya ruguje tunda gimbiya Nauwara
zata gaje dukiyar ce wacce a halin yanzu babu
wani mahaluki a doron kasa daya mallaki a
dadinta.bani da ikon batar da gimbiya Nauwara
ko na kashe ta domin duk abinda zan aikata a
boye sai ya gani da karfin sihirinsa na tsafi.
Babban abin bakin cikina shine na fuskanci cewa
wannan matsayi
na galadima da sarki ya rabani dashi yafi
kowanne mukami daraja da muhimmanci akasar
hatta karagar sarki kuwa...
Dalilin da yasa na fada miki haka shine gaba
daya harkokin kudi na kasar yana cikin wannan
matsayi haka kuma galadima shine da jan
ragama ta zabin sarki kuma shine mai baiwa
sarki shawara akan harkokin mulki,kinga kenan ko
na hau kan karagar mulki gimbiya Nauwara ce
mai jagorantar mutane a fakaice idan tayi aure ta
sami haihuwar 'da
namiji,danta zai iya zama sarki kinga kenan a
karshe nida duk iyalina zamu tashi a tutar babu,ki
tuna cewa a yanzu danmu Yarima Zainur da
shekaru biyu kadai ya girmi Gimbiya
Nauwara,yaushe ne
shima zai girma kuma yaushe ne nima zan hau
karagar mulkin kasar nan har ya gajeni?
Koda Waziri Ridwan yazo nan a zancensa sai ya
fashe da kuka,al'amarin daya karya zuciyar
Ra'isa kenan taji ta kamu da tsananin tausayinsa
don haka sai ta rungumeshi ta shiga rarrashinsa
tana cewa,
Ka kwantar da hankalinka yakai Mijina kayi sani
cewa komai nisan jifa kasa zai fado tunda idan
babu
mutuwa ai akwai tsufa da cuta,da sannu lokaci
zaizo wanda sarki Aiyuba yanaji yana gani
daukakarsa ko ikonsa zasu dakushe kuma ko
yana so ko baya so dole ne ya mutu yabar
wannan karagar mulki da dukiya daya tara a
hannunka tunda dai yanzu ya fara
tsufa kuma 'yar nan tasa yarinya ce karama
kaine kadai shakikinsa idan bai danka amanarsa a
hannunka ba saidai ya barta a hannun bare
wanda zai sami banza ya kwashe tsuntsu daga
sama gasasshe.
Koda Ra'isa tazo nan a zancenta sai fuskar
Ridwan ta fadada da murmushi take yaji wani irin
farin ciki ya lullube shi,kawai sai ya dubi Ra'isa
cikin murya yana cewa yake matata hakika ba
karamin hangen nesa kikayi ba yanzu domin na
tsaya na yi nazari naga cewa duk abinda kika
fada gaskiya ne,kuma banga hanyar da sarki
Aiyuba zai iya tsallake duk wadannan abubuwa
da kika fada ba,koda jin haka sai duk su biyun
suka kyalkyale da dariyar mugunta sukayi ta
dariyar kamar bazasu daina ba.
.
YARIMA ZAINUR ya taso a cikin wani irin hali
wanda yasha bambam dana mahaifinsa waziri
Ridwan by M. Kabiru Muhammad domin shi ko
kadan bashi da son abin duniya kuma harkokin
sarauta ma basa gabansa, a rayuwarsa
babu abinda yakeso sama da farauta da kuma
jarumtaka bisa wannan dalili ne ya mannanewa
sarkin yakin birini wanda ake kira Haiman bin
Husein ya rinka bashi horon yaki kuma suka rinka
fita
farauta daji tare.
Saida takai cewa dare da rana Yarima Zainur na
tare da sarkin yaki Haiman,kai watarana ma a
gidan sarkin yaki yake kwana,da yake matar
sarkin yaki bata taba haihuwa ba sai taji ta
kaunaci yarima zainur tamkar dan data haifa a
cikinta,kuma ta rinka kyautata masa
ainun,Al'amarin
daya janyo Yarima Zainur ya shaku da Lahisa
kenan ainun da kuma mijinta Haiman har yaji yafi
kaunarsu a kan iyayensa,sabida ra'ayinsu yazo
daidai da irin nasa na rashin damuwa da duniya
sabanin iyayensa wanda babu abinda suke so
sama dasu tara dukiya mai yawan tsiya kuma su
shagala a cikin jin dadi suyi facala da
warwasawa. Hakance tasa Yarima Zainur yaji
yafison yayi rayuwarsa a gidan sarkin yaki
Haiman.Nan da nan kuwa Yarima Zainur ya taso
da hazaka a bangaren iya yaki da farauta har ya
zamana cewa shi kansa sarkin yaki yana
mamakin irin baiwar da Allah ya yiwa Zainur,
sadaukantaka
tun yana yaro karami da tsananin jure wahalar
karbar horo ko kuma wahalar daji ya shafe lokaci
mai
tsawo na jure gudu,yunwa da kishirwa gami da
taurin kai,kafewar zuciya da tsananin rashin
tsoro.
.
Lokacin da Yarima Zainur ya cika shekara goma
sha hudu sai ya fara yin abubuwan al'ajabi
wadanda sukasa nan danan labarinsa ya bazu
ko'ina a nahiyar domin a wannan lokaci ne ya
shiga wani daji dake yamma da birnin Lailatul
Hawas wanda a cikin sane wadansu arnan daji
suka kafa sansaninsu.Ance yawan arnan dajin
yakai miliyan uku da doriya,kuma sunfi shekara
dari da wani abu a wannan daji,amma babu wani
abu a wannan daji,amma babu wani sarki daya
taba tunanin ya murkushe su su zama bayinsa
ko kuma ya rinka karbar haraji a hannunsu,gashi
dai ana harkokon kasuwanci dasu na cinikayyar
fatun dabbobi da sauran kayayyaki amma kuma
babu wata
kyakyawar alaka a tsakaninsu da mutanen birnin
Lailatus Hurus walau ta aure ko ta zumunci haka
zalika duk mutumin daya sake ya shiga cikin
iyakarsu yayi farauta koya debo wani amfanin
gona kona daji to kuwa bazai fito a raye ba
saidai gawarsa ta dawo amma sai gashi Jarumi
Zainur ya karya wannan alkadari nasu.
Abinda ya faru ne a wata safiya sa'adda jarumi
Zainur ya shiga daji
domin yin farauta a wannan lokaci yana sanye da
wata tsangalalliyar rigar fata iya cibiyarsa mai
yankakken hannu,wandon jikinsa na fata ne dogo
kuma matsatstse,takalman dake kafarsa ma na
fata
ne masu madauri iya gwiwa yana ruke da wata
baka babba mai kyau da daraja kuma ya rataya
kuttun
kibiyoyo a bayansa.
A gefen cinyarsa ta hagu da dama akwai
wadansu gajerun adduna guda biyu a daure kuma
a cikin kufensu da yake Allah ya yiwa Yarima
Zainur kira mai kyau gashi dogo kuma mai
matsakaicin kaurin jiki ga tarin gwanji kuma a
murde
yake duk wanda ya ganshi a wannan lokaci sai
ya burgeshi kuma sai yayi masa kwarjini.Saida
yarima Zainur ya shafe kusan sa'a hudu a cikin
dajin yana farauta amma bai hadu da wata
dabbar kirki ba face kananun dabbobin daji kamar
zomaye da tsuntsaye,al'amarin daya bata masa
rai kenan domin a rayuwarsa babu abinda yakeso
idan ya shiga
farauta face ya hadu da babbar dabba irin su
zaki,kura,damisa da sauransu wadanda zai fafata
dasu ya murkushe su da karfin tsiya ya kashe
sannan ya murkushe su da karfin tsiya ya kashe
sannan ya fede su ya kwashe abubuwan dake da
amfani a jikinsu yakai su kasuwa ya siyar.Wani
lokacin kuma dabbar da ranta zai daureta ramau
ya sabota a kafadarsa ya shiga da ita cikin gari
saidai kaga jama'a nata binsa du....ana mamakin
irin
wannan tsananin jarumtaka tasa.
Sa'adda Yarima Zainur ya shafe kusan sa'a hudu
yana farauta ya
sami nasarar harbo wani tsuntsi daga sama koda
tsuntsun ya fado kasa matacce sai murna ta
kama
Zainur saboda dama a wannan lokaci ya fara jin
yunwa nan take Zainur ya fige tsuntsun tas
sannan
ya shiga hada wuta ya fara gashi,shi dai wannan
tsuntsun kato ne mai tsoka sosai,kuma namansa
yana da matukar dadi da tsada a kasuwa koda
tsuntsun ya fara gasuwa yana digar maiko sai
Yarima Zainur yaji alamin takun sawaye a
bayansa,cikin hanzari ya mike tsaye ya zare
addunansa guda biyu yana mai gyara tsayuwa dif
sai yaji shiru wato takun sawun ya dauke tamkar
daukewar ruwan sama.Zainur ya cigaba da
tsayuwa
a inda yake batare daya motsa ba,kwatsam sai
yaga wadansu arnan daji sama dasu dari bakwai
suna
fitowa gaba dayansu kawai sai babbansu wani
narkeken kato abin kwatance ya tunkari inda
wannan
tsuntsu na Zainur yake,kawai sai ya dauke
tsuntsun ya yagi cinya guda ya kuma ci,al'amarin
daya fusata yarima Zainur kenan ya dakawa
narkeken katon tsawa yace dashi ya aje masa
namansa kada ya
cinye.Koda jin haka sai katon ya dubi sauran yan
uwansa ya tuntsire da dariyar mugunta
maimakon ma ya ci gaba da cin naman tsuntsun
sai ya jefa
naman cikin wani bakin ruwan tabo ya tattakeshi
da kafafunsa kuma ya cigaba da kyalkyalawa
Zainur dariyar mugunta.
A wannan lokaci ne fa jikin Yarima Zainur ya
kama tsuma kamar maijin sanyi zuciyarsa kuwa
ta kara tafarfasa kamar zata kone,kwatsam ba
zato ba tsammani sai arnan dajin sukaga Zainur
ya daka tsalle sama daga inda yake tsaye tamkar
an cilloshi daga cikin BAKA,kafin wani daga cikin
arnan dajin
yayi wani yunkuri tuni Zaiyanu yasa addarsa ya
sare wuyan wannan kato wanda ya bata masa
naman daya gasa,take kan katon yayi sama a
lokacin da jini
yayi feshi daga cikin dungulmin wuyan ya bata
wasu daga cikin yan uwansa.Koda ganin abinda
ya faru
sai ragowar arnan dajin suka afkawa yarima
Zainur gaba dayansu sukayi masa rundugu da
niyar suyi gutsun gutsun da sassan jikinsa.
Kaico tsautsayi ba'a sa masa rana kuma ita
masifa a kwance take duk wanda ya tsokanota
akansa takan kare,koda Yarima Zainur yaga
wadannan miyagun arnan daji masu naci kamar
suci babu sun afko masa gaba dayansu sai ya
durkushe kasa yayi wata irin
katantanwa yana mai zabtare musu kafafu a
lokaci guda kuma ya doki kasa da hannunsa
guda yayi
tsalle a sama kai kadan ya fafe cikin da yawansu
da addunansa biyu,sai gashi ya tarwatsa su da
karfin tsiya,ai kuwa sai ya sami dama ya rinka
kutsawa ta cikinsu yana sara da suka cikin wani
irin bakin zafin nama tamkar jikinsa bana jini da
tsoka bane,duk
inda yasa gabansa saidai kaga maza na zubewa
kasa kamar ana sassabe a gona.
Babu abinda zai baiwa mutum mamaki face
yadda Zainur ke sara ta gaba da baya kuma
sama da kasa kai kace iskace ke sarrafa
hannayensa ba wai shike sarrafa su ba da
kansa,nanfa arnan daji suka shiga uku suka rasa
yadda akayi wannan karamin yaro yake gasa
musu gyada a hannu.Saida aka shafe sa'a biyu
cif ana wannan bakin artabu Zainur yana
ragargazar arnan dajin amma an rasa mutum
daya dazai sami nasarar koda lakutar jikinsa,koda
arnan dajin sukaga irin mummunar barnar da
yarima Zainur yayi musu
domin ya kashe sama da kaso daya cikin kaso
ukunsu kuma ko alamar gajiya babu a tare dashi
sai suka fara cika wandunansu da iska suka juya
da baya da gudu izuwa cikin jeji domin su tserar
da rayuwarsu.Har Yarima Zainur ya fasa binsu
amma daya juya ya dubi inda aka jefa wannan
tsuntsu daya gasa cikin tabo aka tattakeshi sai
ransa ya baci ya falfala da gudu yabi bayan
arnan dajin duk wanda ya
riska saikaga yayi masa falan daya,
wohoho!ai koda arnan dajin suka waigo sukaga
Zainur ya taso su a gaba yana dadayi musu
barna sai suka kara ZAGE DAMTSEn gudun nasu
nanfa aka kasa uban tsere na GUDUN CETON
RAI!
sai gashi SA GUDU YA KORI KI GUDU,haka dai
akaci gaba da yin wannan tseren gudu baji ba
gani,abinda zai baka mamaki kuma ya baka
kunya shine wai yaro ne matashi dan shekaru
goma sha shi kadai ya koro karti majiyan karfi
sama dasu dari uku.Wannan karon dai da kyar
Zainur ya sami nasarar riskar mutum hudu ya
rafke har akayi gudu na tsawon sa'a guda
cur,kwatsam sai Yarima Zainur yaga gaba dayan
arnan dajin daya biyosu da gudu sun tsaya
cak,kuma sun juyo sun fuskance shi
suna haki ba tare da wata alama ta tsoro
ba,koda ganin haka sai shima ya tsaya cak a inda
yake saboda yasan cewa banza bata kai zomo
kasuwa kuma ruwa baya tsamin banza,adaidai
wannan lokaci
ne Zainur ya lura da cewa ai sun shigo cikin
yankin garin arnan dajin domin yana iya hango
gidajensu
tsilli tsilli a cikin dajin kuma yana iya hango
matayensu da 'ya'yansu da yayyansu suna
firfitowa daga cikin gidajen nasu daya bayan
daya tamkar daman sunsan da abinda yake
faruwa.Ko kuma abinda yake shirin faruwa,babu
zato babu tsammani sai Zainur yaji motsin wani
abu a samansa cikin iska
kamar kibiya aka harbo,kafin ya daga kansa
sama yaga ko meye tuni an doki kirjinsa.Saboda
karfin
dukan da akai masa shima saida yai sama kamar
majaujawa aka jujjuya sannan aka janye
shi.Bayansa ya maku da wata bishiya sannan ya
fado kasa a galabaice yana aman jini da tari. A
fusace Zainur ya daga kansa da zummar ganin
wanda yayi masa wannan duka,koda yayi arba da
wanda yai masa wannan dukan sai ya kidime
kuma ya kamu da tsananin mamaki.Ba wani
bane face kyakyawar yarinya wacce batafi
shekara tara a duniya ba.Tana
sanye da sutura irin ta wannan arnan dajin,amma
a kanta akwai hular sarauta ta zinare kuma
gadon bayanta ta rataya wata sharbebiyar takobi.
Kawai sai Zainur yaga yarinyar tana kallonsa
cikin murmushi
kuma tana yafito shi da hannun cikin nuna
alamun cewa ya taho suyi yaki.Cikin tsananin
fushi da kunar rai Zainur ya mike tsaye zumbur
yana ware hannunsa biyu masu rike da adduna
kuma jini na zuba daga jikin addunan.Bai jira
wata wata ba ya ruga da gudu izuwa wajen
yarinyar yana mai
kwarara uban ihu gami da daga addunan nashi
sama cikin mugun nufi.Koda ganin haka sai
itama yarinyar ta zaro sharbebiyar takobinta daga
cikin kufenta ta falfalo da gudu ta nufi wajen da
yake.Kodaya rage baifi taku uku su hadu dashi
ba sai ta daka wani
uban tsalle sama takai masa wawan sara a
kai.Cikin zafin nama Zainur yai amfani da dukan
karfinsa da zummar kare saran data kai masa
amma duk da
haka bai samu nasarar kare saran data kai masa
ba saida saran nata ya zabtare wani bari na
bakin
gashin kansa.A haka ta shallake shi ta dirga a
bayanshi bata gama dirga ba tasa kafa ta baya
ta
daki gadon bayansa.Zainur ya tafi ya fadi a kasa
har saida bakinsa ya fashe jini yana zuba,amma
sai yai
zumbur ya tashi yana gyara jikinsa ya kuma
gyara tsayuwarsa.
A wannan lokacin yarinyar ta kuma
kyalkyalewa da dariya shi kuma sai ransa ya
kuma baci saboda ganin gashin kasan iska tana
daukarshi
tana yawo dashi,yakai hannunsa ya shafa
lebensa yaga jini yake zuba.Hakan yasa ya
yunkura
zai taso mata,ganin haka yasa ta dakatar dashi
ta kalle shi cikin murmushi da kallon raini tace
masa....
.
Zan dakata anan sai ALLAH yakaimu 7:30pm ko
8:00pm a gogon Nigeria da Niger Cameroo,Chad
daga me debemuku kewa akullum Dako yaushe
M. Kabiru Muhammad 07068335066,090
20924676 mkm4676@gmail.com, mkabiru4676@
yahoo.com
.
Dalilin dayasa bankawo muku labarin Mazan Jiya
saboda kunce kun karanta bakwa bukata, amma
yanzu zanji daga bakinku idan kunaso se naci
gaba dayi?????
.
Sannan kuma abinda yasa banayin littafin
wasikar jini da sauran hikayoyi irin su Hikayar
Dan Dako da 'yan Mata,Hikayar Mutum da Aljan
da sauransu saboda na lura kamar duk bakwa
bukata dalili saboda bakwason yin Like dayawa
tareda Comment me yawan gaske hakan zaisa
nasan kunason nadinga kawo mukusu a kullum
don haka duk wanda yakeso yadaure yadinga
Like/Comment/Share karkuyi la'akari da cewa
wasu sunyi a'a kawai kayi naka saboda nakowa
daban ban bukatar sisi a hannunka sai dai Like/
Comment/Share Always...
.
Aha muje zuwa....
.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com
.
Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©M. Kabiru Muhammad

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: