Friday 6 October 2017

Hikaya: 01 HIKAYAR MASUNCI DA IFRITU

Tura Wannan Zuwa

Allah shi ne Sarki mafi daukaka daga dukkan
sarakuna. Shi ne mafi tsarki daga dukkan
abubuwa. Tsira da aminci su tabbata ga
Manzonsa kuma Annabinsa, Muhammadu dan
Amina (SAW).

: Akwai wani mutum tsoho masunci, yana da mata
d'aya da 'ya'ya uku, ya kasance talaka ne, bai
ajiye abincin yau ba ballantana na gobe. Kullum
yakan je kogi ya kamo kifi ya kai kasuwa ya
sayar ya sayo abin da za su ci. Yana da wata
al'ada mai ban mamaki, duk lokacin da ya tafi su,
yakan jefa komarsa sau hud'u ne kawai, daga
nan sai ya nad'e ta ya tafi da kifin da ya kama
ya sayar, idan ma bai kama komai ba a jefawa
hud'un nan, to ba zai yi ta biyar ba, sai dai ya
koma gida haka nan, ranar su kwana da yunwa.
Wata rana ya fita da Azuhur zuwa ga yankin
bahar domin yin su, da ya isa ya shiga cikin ruwa
daga bakin gaba, ya jefa komarsa ciki, ya juya
ta, ya kuma juyawa, sa'annan ya jawo ta, ya ji ta
da nauyi, ya fitar da ita daga cikin ruwa. Ya juye
abin da ke ciki, bai ga komai ba face ciyawa. Ya
kakkab'e ta ya sake jefawa karo na biyu cikin
ruwa, jim kad'an ya jawo ta da kyar saboda
nauyi, har rigarsa ta bi ruwa. Koda ya juye abin
da komarsa ta d'ebo, bai ga komai na daga kifi
ba face mataccen jaki. Da ya ga haka ya yi
bak'in ciki, ya ce a ransa babu tsimi babu dabara
face daga Allah mai girma da d'aukaka, neman
wannan abinci nawa da ban al'ajabi yake, yayin
nan ya waka wad'annan baitoci:
"Ya mai bayarwa a cikin duhun dare,
Ba da dabara ko wayo ba,
Na dogara gare ka ya Razzak'u,
Kai ke azurta mu ba don k'ok'arinmu ba."
Bayan ya gama rera wannan wak'a, ya jefar da
mataccen jakin, ya wanke komarsa ya shanya ta,
ta sha iska, ya d'auke ta ya shiga cikin ruwa
sosai sannan ya jefa ta kashi na uku yana mai
cewa Bismillahi. Koma ta nutse cikin ruwa, ya
hak'ura har ta nutse sosai. Ya jirkita ta, sannan
ya fara jawo ta zuwa tudu, ya ji ta nannauya fiye
da jefawar farko da ta biyu, ya yi farin ciki domin
ya zaci kifi ne.
Koda ya juye abin da ke cikin koma, sai ya tarar
da karafuna da matattun tangaram da duwatsu
da yashi da laka, babu komai na daga kifi. Yayin
da ya ga haka ya yi bak'in ciki mai yawa, ya rera
wannan wak'ar:
"Ya rayuwar zamanina ki fahimta,
Idan ba ki fahimta ba ki yafe ni,
Har yanzu ba a ba ni rabona ba,
Har yanzu ba a yi hukunci a kaina ba,
Na fita bid'ar arzikina na ishe ya k'are,
Sau da yawa jahili yakan ga abin b'oye,
Sau da yawa ilimi kan b'ace wa Malami."
Masunci ya zubar da tarkacen da komarsa ta
kwaso, ya wanke ta, ya nemi gafara ga Allah
bisa wannan wak'a da ya yi. Da komar ta sha
iska ya d'auke ta ya shiga cikin ruwa, wannan
karon ya kutsa nesa cikin ruwa, ya d'aga kansa
sama ya ce, ya Ubangiji ka sani cewa ba ni jefa
komata fiye da sau hud'u a rana, na jefa sau uku
ban sami komai ba, Allah ga ta hud'u kuma ta
k'arshe zan jefa, ka nufe ni da samun abin da
zan ci, ni da iyalina. Ya ambaci sunan Allah, ya
jefa komarsa karo na hud'u.
Bayan ya dad'e yana juya ta, sai ya jawo ta
zuwa tudu, wannan karon ta fi koyaushe nauyi.
Da ya fito da ita da kyar, ya juye abin da ke ciki,
babu komai face yashi da wata yar batta
(kwalba) k'arama, ta farin k'arfe, girmanta bai
wuce a saka ta a cikin aljihu ba, an lik'e bakinta
da darma, an buga hatimin Annabi Sulaimanu a
saman murfin.
Yayin da masunci ya ga wannan batta, ya yi farin
ciki ya ce wannan na sayar da ita a kasuwar
farin karfe dinari goma, in sayi abin da za mu ci.
Ya sa hannu d'aya zai d'auki batta, ya ji ta da
nauyi, hannunsa d'aya ya kasa d'aukar ta. Ya yi
mamaki da wannan abu, ya ce babu makawa in
bude ta in ga abin da ke ciki, in zazzage shi cikin
jaka, sannan in sayar da battar a kasuwa. ya
zare wuk'a, ya b'amb'are murfin darma daga
batta, ya ajiye shi gefe a kan k'asa.
Ya girgiza batta domin ya ji abin da ke ciki ko
yana motsi, sai ya ga hayak'i na fitowa yana yin
sama. Masunci ya cika da mamaki, ya yi tsaye
yana kallon ikon Allah. Da hayak'i ya gama fita,
ya tattaru wuri d'aya a sama, sai ya juye ya
zama Ifiritu, kansa yana cikin gajimare,
k'afafunsa cikin k'asa. Girman kansa kamar d'aki,
bakinsa tamkar kogo, hak'oransa kamar duwatsu,
k'ofofin hancinsa tamkar ibirik', idanunsa ja wur
kamar garwashin wuta, damuttsan hannuwansa
kamar ginshik'i, k'afafunsa kuwa tamkar
bishiyoyin kuka. Wannan Ifiritu ya kasance mafi
daud'a da k'ura cikin halittu.
Yayin da masunci ya ga wannan irin halitta,
gab'ob'insa suka yi sanyi, yawun bakinsa ya
k'afe, ya kasa motsawa daga inda yake. Da Ifiritu
ya ga masunci sai ya ce, babu Sarki madawwami
sai Allah, na shaida Sulaimanu Annabin Allah ne
kuma Manzonsa. Ya Annabin Allah kada ka
kashe ni, na rantse da Allah ba ni koma sab'a wa
umurninka.
Muryar masunci na rawa don tsoro ya ce, "Ya kai
wannan maridi, kana tsammanin a gaban Annabi
Sulaimanu kake? Bayan ya rasu da shekara dubu
d'aya da d'ari takwas, ka sani yanzu muna
k'arshen zamani ne. Ka labarta mini wanene kai?
Menene sanadiyyar shigarka wannan batta?"
Koda Ifiritu ya ji zance masunci sai ya ce, "Babu
Sarki sai Allah, hak'ik'a ka faranta mini ciki ya
kai wannan dan Adam, da sannu zan saka maka
da abin da ka yi mini." Masunci ya fara murna ya
ce, "Da me za ka saka mini?" Aljani ya ce "Da
kashe ka a cikin wannan sa'a, muguwar kisa."
muyutumin yace " yanzu wannan shine abunda zakamini
albishir dashi, kuma menene nayi dazan
chanchanci kisa ? me nayi dazaka kasheni ? NI
da nataimaka maka nafito dakai daga cikin
wannan kogi, kuma naciroka daga cikin wannan
tulu natsirar dakai daga halaka wannan shine
sakamakona ?... sai aljani (almaridu) yacemasa :
kazabi kalar kisanda zanma saboda kana
batamini lokaci… sai mutumin yace : wani
zunubine na aikata da zaka sakamini da wannan
mumunan sakayya ? sai (Almaridu) yacemasa :
kafin inkasheka bari inbaka labarina tukuna… sai
maikamun kifin yacemasa : inasauraranka kuma
kataqai labarinnaka saboda yanzu zuciyata
tabuga…
sai aljani (almaridu) yace : kasani cewa : ni
nakasance dagacikin aljanu (ma’riqai) wato -
masu taurin kai - wadanda sukabijirewa umurnin
ALLAH da manzonsa kuma suka kafircewa
ALLAH.. kuma nasabawa annabi (sulaimana) dan
annabi (da’wuda) dani da aljani maisuna (sakhru)
To sai annabi (sulaimana) ya aikamini wazirinsa
maisuna (a’sifu dan barkhiya) yakamani adole
yakawoni wajan (annabi sulaimana) ya
tsayardani agabansa aqasqance.. da (annabi
sulaimana) yaganni sai yarazana yace : (A uzu
billahi) saboda munin halittata.. daganan sai
(annabi sulaimana) umurceni da inyi I’MANI da
ALLAH kuma inshiga qarqashin ikonsa, (wato –
inyiwa annabi sulaimana DA’A) To nikuma sai
nayi taurin kai naqi amincewa… To sai (annabi
sulaimana) yasa aka kawomasa wannan tulun
yasakani aciki yamanne bakin tulun, yabuga
tambarinsa da suna maigirma, sannan sai yasa
akajefani cikin (teku) kogi, nikuma sai nakasance
acikin kogin har tsawon shekara 100, sai nace -
acikin zuciyata - : duk wanda yazo yafitardani
daga cikin wannan kogin acikin shekaru 100 to
zan arzuqtashi har abada..
amma babu wanda
yazo yafitardani dagacikin wannan kogi, sai
nacigaba da zama aciki har nakai shekaru 200
bangusheba inaciki, to anan sai nace : duk
wanda yazo ya fitardani zan budemasa taskokin
duniya gabadaya.. amma babu wanda yafitar
dani, sai nacigaba dazama aciki har shekaru 400
suka shude bangusheba inaciki.. bayan haka sai
wasu shekaru 400 daban sukazo sukashude sai
nace : duk wanda ya fitardani a wannan lokacin
to zan biyamasa buqatu guda 3… amma babu
wanda yafitar dani daga cikin wannan teku.. To
daganan kawai sai nayi fishi mai tsanani nace : -
acikin zuciyata - duk wanda yazo a wannan
lokacin to zan yimasa mumunan kisa, kuma zan
bashi dama yazabi kalar kisanda zanmasa.. To
yau gashi kazo kafitar dani saboda haka zan
kasheka kamar yadda nayi alqawari..
da wannan maikamun kifin yaji wannan labari sai
yacemasa : to ai ni ALLAH baibani damarda zan
fitardakai daga wannan kogi ba sai a wannan
lokacin… saboda haka kayi hakuri kar kasheni
ALLAH zaimaka afuwa, idankuma ka kasheni to
ALLAH zaikawo wanda zai halakaka kaima..
amma sai (almaridu) yace karka batamini lokaci
kasheka babu makawa.. kawai kazabi kalar
kisanda zanmaka…
Da maikamun kifin yatabbatar cewa (almaridu)
zai halakashi, sai yaqara durqusawa yaroqeshi
yacemasa : kayimini afuwa saboda karamcin
tsirar dakai danayi.. sai (almaridu) yace : To ai
nima zan kashekane saboda tsirardani da
kayine… sai mutumin yacewa (almaridu) ya
dattijon aljanu shin zan maka alheri kaikuma
kasakamini da sharri ? sai (almaridu) yacemasa :
karkasa tsammanin zaka rayu inajiranka kazabi
kalar kinsanda zan maka ..
To anan sai mai kamun kafin yatseya yaiy tunani
- acikin zuciyarsa – yace : wannan aljanine, niku
DAN ADAM ne, kuma ALLAH yabani hankali
cikekke, saboda haka zanshirya wata dabara
saboda inhalaka wannan aljanin kafin ya
halakani.. bayan yagama tunaninsa sai yacewa
(almaridu) : shin bakagusheba har yanzu kanada
ra’ayin kasheni ? sai (almaridu) yace : e’h inakan
ra’ayina.. sai mutumin yace : dan darajar suna
maigirma wanda aka rubuta akan zoben (annabi
sulaimana) inason inyimaka wata tambaya kuma
inafata zakabani amsa daidai.. da (almaridu) yaji
an ambaci ( suna mai daraja ) sai yaji dadi ya
girgiza kanshi yace : kayi tambayarka kuma
kataqaita zan amsamaka.. sai mutumin yace :
taya ka kasance cikin wannan dan karamin tulu,
bayan kuma ko hannunkama bazai iya shiga cikin
wannan tulu ba ballema kafafunka ?.. yaya akayi
tulun ya daukeka ?... sai (aljani almaridu) yace :
shin baka yardabane daga cikin wannan tulu
nafito ? sai mutumin yace : bazan taba yardaba
sai nagani da idona quru quru..
MUHADU RANAR LARABA MISALIN 9 PM DONCI GABA INSHA ALLAHU01 HIKAYAR MASUNCI DA IFRITU

POSTED BY USEEY

sai gobe zamuci gaba in allah yakaimu
abunda nake bukata kawai shine hadin kanku

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Useey Media24

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: