Monday, 2 October 2017

KA KARANTA ANATSE 04

Tura Wannan Zuwa

Misali.

Wani malamin tauhidi ya kasance yana koyama
ya'ra AQIDA sai yariqa musu bayani akan kalmar
ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ
sai malamin yariqa yin bayani akan ma'anar da
kalmar taqunsah
sannan yakawo misalai na wasu daga cikin
kyawa'wan d'abi'un Manzon Allah s.a.w
da yadda Manzon Allah yariqa koyama sahabbai
aqidah har tauhidi yayi qarfi acikin zuciyar
Sahabbai r.d.a
sai wata rana wani yaro yazo da AKU yaba
wannan malamin kyautar akun domin malamin
yanason tsuntsa'ye da ma'guna
yau da gobe sai malamin yasa'ba da wannan aku
har takai yana zuwa da ita aji alokacin da yake
koyarwa
yau da gobe sai wannan aku ta haddace kalmar
ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ
sai tariqa furta kalmar alokaci zuwa lokaci
wata rana sai d'aliban suka wuce wannan malami
sai sukaga yana yin ha'waye sai suka
tamabayeshi dalilin hawayen sai yace: ayau 1
daga cikin ma'gunan da nake kiwo tazo
takashemin AKU
sai sukace yanzu wannan ne yasaka hawaye?
in kanaso sai mukawo maka wacce tafi tadah
sai malamin yace:ina yin hawa'ye ne saboda
lokacin da ma'gen tazo zata kashe akun
sai akun tariqa ihu alha'li adah mafi yawan
abinda akun ke furta'wa shine kalmar
ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ
amma sai ga'shi lokacin da tazo mutuwa sai ta
manta wannan kalmar sai tariqa ihu kawai
haka ta'faru ne saboda akun tariqe kalmar ne da
harshenta
amma kwata kwata babu kalmar acikin zuciyarta
sannan malamin yacigaba da cewa ina'jin tsoron
inzama kamar wannan akun
arayuwar mu muna yawaita furta kalmar
ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ
amma mun manta'wa da ita acikin zuka'tanmu
sai way'annan d'aliban suka fara hawaye saboda
rashin cikkiyar kalmar
ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ
acikin zukatansu
WANNAN KENAN
aha'lin yanzu Abu mafi muhimmanci da yakamata
muyi shine mutsaya muduba cikin zuciyarmu shin
munsan ma'anar kalmar
LA'ILAHA ILLALLAH
Shin muncika haqqoqin da wannan kalmar ta
qunsa?
INA ROQON ALLAH S.W.T da YA TASHEMU
ACIKIN WAY'ANDA SUKARIQE KALMAR
ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﺤﻤﺪ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺹ
DA GASKE ACIKIN ZUKA'TANSU,

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By © Rayuwa A Musulinci.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: