Monday, 2 October 2017

KA KARANTA ANATSE 06

Tura Wannan Zuwa

Misali.

[JIBRIL YA MUTU]

Wani babban malamin addinin kirista ya kasance
yana zuwa wajen wani tsohon mutum musulmi.
Aduk lokacin da wannan malamin kiristoci yazo
wajen wannan tsoho sai yace masa: KANA 6ATA
LOKACINKA DA KAKEYIN SALLAH HAR SAU 5.
Akullum. Kai kullum kaine a cikin tsayuwa da
rukuw'i. da sujjadah. Kuma kake kwa'she wata 1.
Kana yin azumi. Kuma kai ko na'man alade
baka'ci. A gaskiya kana quntatama rayuwarka.
Idan kanaso ka hutar da kanka kuma ka ku6uta.
To abu 1 ya kamata kayi. Shine ka amince cewa
Allah ya turo d'ansa guda d'aya da yake dashi
zuwa wannan duniya. Kuma d'an ya mutu saboda
zunuban da kake aikatawa.
Don haka kayi imani cewa Allah ya sauko cikin
wannan duniya kuma ya mutu saboda zunuban
da kake aikatawa. INDAI KAYI IMANI DA HAKA.
TO ALJANNAH ZAKA SHIGA A SAUQAQE.
::::::::::::::
kullum idan wannan fasto. Wato malamin
kiristoci. Yazo wajen wannan tsoho to abinda
yake maimaita masa kenan. Kuma kullum ne sai
wannan fasto yazo wajen tsohon.
By Rayuwa A Musulinci.
Shi kuma wannan tsoho akullum tinani yakeyi ta
wace hanya zan 6ullowa wannan fasto. Har in
samu nasa akansa?
Kawai sai tshohon ya gayama wani maqwacinsa
cewa inaso idan Allah yakaimu gobe. Kaga fasto
yazo wajena. Ya zauna tsawo minti 7. To kazo
kayi mini rad'ah akunne sannan kai tafiyarka.
Kashe gari bayan fasto yazo ya d'an huta. Sai
wannan mutumin yazo yayima tsohon rad'a a
kunne.
Ai kuwa anayi masa rad'a a kunne. Kawai sai ya
fashe da kuka. Yai ta yin kuka. Fasto ya
tambayeshi wai me aka gaya maka ne kake tayin
kuka haka?
Tsoho yace: zan gaya maka amma ba yanzu ba.
Domin labari ne na baqin ciki ya same ni.
Fasto yace: ka gaya mini. A yanzu mana. ka
kwantar da hankalinka kaimin bayani abinda ya
faru.
Tsoho yace: bazai yiwu in gaya maka ba. A
yanzu. Domin al'amarin babbane.
Haka tsohon yaci gaba da kukansa. Yai tayin
kuka da gaske.
Fasto yace: ka taimaka ka gaya mini wannan
labarin. Domin ka sani a cikin tinani. Kwata
kwata bana jin dad'i a yanzu. Ka taimaka ka
gaya mini.
Sai tsoho yace: labari ne na baqin ciki ya riske
ni. Cewa Mala'ika Jibril. Ya Mutu.
Nanfa fasto ya fashe da dariya. Sannan ya kalli
tsohon yace masa: ammah dai kai mugun dolo
ne. Waye ya gaya maka cewa ma'iku suna
mutuwa? In ban da kai dolo ne yaya za'a gaya
maka haka. Kuma ka yarda?
Sai tsohon yace: to idan ni na zama dole ne don
angaya mini cewa mala'ika ya mutu. Ni kuma na
yarda. To ina ga wanda akace masa Allah ya
mutu. Kuma ya yarda?
Nanfa fasto ya tsaya yayi tinani. Hardai ya
tabbatarma kansa cewa Mutuwa bata dace da
Allah s.w.t ba. Kuma wannan ya zama sana
diyyar Musuluntar sa.
Ni Admin 9. Ina roqon Allah s.w.t da ya d'aukaka
Musulinci. Da Musulmai. Aduk inda suke a
duniya.

Source By ©Rayuwa A Musulinci.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: