Wednesday 4 October 2017

Magana Jari ce: ZAFIN NEMA BA YA KAWO SAMU

Tura Wannan Zuwa

Akwai wani mutum matsiyaci ne kwarai da
gaske, ba shi da kome sai gatari da jakuna biyu.

Sana'a tasa kullum sai ya tafi ya saro itace, ya
dora wa jakunansa, ya kai kasuwa ya sayar, su yi
awon abinci da za su ci ran nan. Allah ya yi
mutumin nan ba mai kasala ba ne ko kadan, rani
da damina, kome ruwa kome dari, bai taba
makarar tashi ba.

Shekararsa kamar bakwai ke nan yana itace, bai
taba fasawa ba, ko da rana daya. To, ce ma ya
fasa, me za su ci ran nan? Ga yara kanana. Da
'ya'yansa suka tasa suka shiga taimakonsa,
amma duk da tarin kokarin nan nasa bai kulla
kome ba, yana nan a matsiyacinsa.
Ran nan ya gaji, zuciyarsa ta baci, ya zauna shiru
ya rasa abin da ke masa dadi nan duniya. Ya ce,
"Kai na gaji da wahalar banza, mutum ya yi ta
wahala shekara da shekaru, amma duk da haka
bai kulla kome ba? Nan gaba in Allah ya yarda,
na bar sake tafiya jeji garin saran itace. Bari in
yi kwanciyata, idan da nufin nan gaba in yi arziki,
ina bisa gadona ya zo ya iske ni!"
Kashegari ya yi kwanciyarsa, har lokacin
tafiyarsa jeji ya yi, har ya wuce bai tashi ba.
Matarsa ta tashi ta gama dukan aike-aikenta na
gida, ba ta ji motsin maigida ya tashi ba, sai ta
shiga daki ta gani ko lafiya. Da ta shiga ta iske
shi ya mimmike a gado, ta ce masa, "Maigida,
maigida, yau lafiya? Ba ka ji gari ya dade da
wayewa ba? Ya kamata ka tashi hakanan mana,
ka tafi neman mana abin da za mu ci."

Shi kuwa maigidan ko ma ya ta da kai ya dube
ta, sai ya ce, "Haba uwargida, in tashi in yi miki
aikin me?"
Ta ce, "A'a! Yau ba za ka tafi jeji ba ne?"
Ya ce, "Ba zan tafi ba. Ina amfanin dukan
wahalan nan da na ke yi shekara da shekaru, tun
da ya ke zan fita tun da jijjifi in tafi jeji, duk da
haka da kyar zan sami abin da zan ciyad da ku?"
Ta ce, "To, maigida, haka Allah ya yiwo mu, sai
mun yi fata-fata sa'an nan mu samu. Kowa ka
gani nan duniya kuwa haka yake, ba wanda ke
kwance a gado. Yaya muka iya da rammu?"
Sai maigida ya ce, "Ni dai yanzu abin da zan
gaya miki na gaji da wahalar banza ta neman
arziki, idan da nufin in yi arziki a nan gaba, ya zo
har bisa gadona ya same ni, amma na daina
wahalar banza har abada."
Matar ta durkusa, ta ce, "Haba maigida, kada dai
tsiya ta sa ka haukace mana, duk duniyan nan
wa ka taba gani yana kwance arziki ya zo ya
same shi a bisa kan gadonsa, in ba ya tashi ya
nema ba? Tashi, saba gatarinka, fita da jakuna ka
tafi jeji, ka yi abin da ka saba yi. Ya kamata ka
gode wa Ubangiji Allah da ya ba ka karfi da
lafiya. Tashi! Yau ba mu da ko kwara a gidan
nan."
Mijin ya harare ta ya ce, "Ke, na ce miki ban
gode wa Allah ba ne? Ki rabu da ni, ko muna da
hatsi, ko ba mu da shi, ni ban kula ba. Hasali ma
dai tafi abinki, kada ki kara wahal da ranki a
banza, duk duniyan nan babu abin da zai sa in
koma saran itace."

Matarsa ta yi, ta yi da shi, amma duk a banza,
har ta gaji da 'yan surutanta, ta tashi. Ba ta dade
da tashi ba sai wani makwabcinsu wanda a ke
kira Sambo ya zo gidan ya yi sallama. Matar ta
fito, suka yi gaisuwa, ya ce mata ya zo ne ya
roki arziki wajen maigidanta ko ya yarda ya ba
shi aron jakunansa, yana da wani aiki ne, har shi
ma idan yana da zarafi yana so ya zo ya taimake
shi.

Sai matar ta shiga gida, ta shaida wa mijinta ana
sallama a kofar gida. Mijin ya waiwayo da hushi,
ya ce, "Na rigaya na gaya miki duk garin nan
babu wanda ya isa ya fito da ni daga kan gadon
nan. Ko wane ne ya ke son ganina ya shigo."

Sai matar ta koma ta shaida wa Sambo. Sambo
ya shigo, ya mayar wa maigida da jawabi kamar
yadda ya gaya wa matarsa. Amma maigidan ya
ce, "Wayyo, na rigaya na yi rantsuwa ba zan tashi
daga nan ba, babu kuwa abin da zai sa in sake
maganata."

Sambo ya ce, "To, in ba za ka ba, ka ba ni aron
jakunanka idan na komo na taimake ka da abin
sayen goro."

Maigida ya ce, "Haba, don wannan? Tafi da su,
sai ka komo."

Sai Sambo ya kama jakuna ya daura musu
mangala, ya fita. Ashe abin da ya sa ya ke
neman aron jakkai ke nan, ya gano wani wuri ne
inda barayi suka boye wadansu kudi gangariyarsu
cikin wani kogon dutse. Sambo yana tsammani
kudin Sarkin garin ne, don yau bai fi kwana uku
ba da wadansu barayi suka shiga taskarsa, suka
yi masa kat, ana kuwa tsakiyar nemansu ne a
lokacin nan. Saboda haka ya ke so ya kwashe
kudin gaba daya kafin a gane.

Da isarsa wurin sai ya yi ta dibar kudin yana
zubawa a mangala. Ya diba gwargwadon yadda
jakunan za su iya dauka. Ya sami wani tsumma
ya rufe da kyau yadda ba za a gane abin da ke
ciki ba, ya dauki wata 'yar hanya zai koma gida.
Yana cikin tafiya, kwaram sai ya hango wadansu
dogaran Sarki guda biyu. Abinka da mara
gaskiya, yana tsoron kada su gane abin da ya ke
ciki ya sani kuwa idan suka kama shi suka tafi
da shi wurin Sarki shari'arsa kashewa ce. Saboda
haka ya runtuma da gudu ya bar jakai. Su kuwa
suka kama hanya, da ma sun saba bi zuwa itace,
suka nufi gida, ba su zame ko ina ba sai a
turkensu.

A lokacin nan kuwa matar gidan na waje na
tsigar tafasa sai ta ga jakuna da kaya niki-niki,
da kyar su ke cira kafa. Ta sheka a guje tana
kiran mijinta ya fito, ga jakuna sun komo dauke
da wani abu mai nauyi.

Da maigida ya ji ta sha masa kai da kira ya ce,
"Haba, don Allah na ce kada ki dame ni. Sau
nawa zan gaya miki ba zan fito ba?"
Da dai ta ga mijinta ya ki tashi, sai ta tafi wajen
jakai ta buda mangalolin, sai ga karfe tsabarsu,
sulalla ja wur, sai daukan ido su ke. Da ganin
haka sai ta sake shekawa a guje wurin mijinta, ta
ce masa, "Don Allah ka fito maza. Ashe
gaskiyarka da ka ki tafiya itace yau, kana jiran
arziki ya zo maka har gado. Ga jakunanka sun
komo dauke da sulalla. Na rantse har da kabarin
tsohona, yau duk kasan nan babu wanda ya fi mu
arziki!"

Da dai gagon naka ya ji haka sai ya yi farat daga
kan gado, ya nufo waje da gudu zuwa wajen
turken jakuna. Matar ta kama masa, ya sassauke
mangalolin ya buda, sai hawaye don murna.
Da shi da matarsa suka kinkima suka je suka
dura cikin tukwane. Ya dubi matar, ya ce,
"Uwargida, yanzu kin ga abin da na gaya miki ya
zama gaskiya ba? Arziki abu ne mai wuyar kan
gado, muddin kai ke nemansa shi kuwa sai ya
dada guje maka, amma in ka guje shi, sai ya
neme ka har inda ka ke."
Matar ta ce, "Wallahi na dai yarda, gaskiyarka,
maigida."

Azahar ba ta yi ba sai ga Sambo ya biyo. Ya
tambayi mai gida kayan da jakunansa suka kawo.
Da mai gida ya gane kudin nan ba na Sambo ba
ne, shi ma lalle akwai yadda aka yi ya same su,
sai ya ce, "Allah ya ba ni ina kwance. Duk
duniyan nan kuwa ba mai karbarsu, in kana jin
wani abu yi kara."

Sambo ya san kudin Sarki ne, lalle in ya fadi aka
gane, kashe shi za a yi. Saboda haka ya ce, "Je
ka, na ji, Allah ne ya ba ka, amma kai kuma
yadda Allah ya ba ka, in kana kaunarsa ka
taimake ni."

Mai gida ya shiga ya kawo fam ashirin ya ba shi,
ya wuce yana cewa, "M, ka ga halin 'yan Adam,
basu ganin mutum ya yi abu, su ma sai sun yi
masa abu!"

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Waziri Aku tareda Bukar Mada

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: