Thursday 5 October 2017

Takaitaccen Tarihi A shekara 90: Yadda Allah Ya albarkaci Sheikh Dahiru Bauchi

Tura Wannan Zuwa

A ranar Juma’ar da ta gabata ce
fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh
dahiru Usman Bauchi ya cika shekara 90 a duniya,
kuma ya jagorancin taron addu’o’in da aka saba yi
a farkon kowace shekarar Musulunci. Shehin
Malamin wanda ya yi aikin Hajji 48 da Umara 200,
jagora ne a darikar Tijjaniyya kuma Mataimakin
Shugaban Kwamitin Fatawa na Majalisar koli kan
Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, ya zanta
da manema labarai inda ya yi takaitaccen bayani
game da rayuwarsa:

Allah gafarta Malam mene ne takaitaccen tarihin
rayuwarka?

Assalamu alaikum wa rahammatullah. Tarihina
dai ni Bafulatani ne, dukanin kakannina hudu
Fulani ne, domin kowane mutum yana da kakanni
hudu ta wajen mahaifinsa biyu, ta wajen
mahaifiyarsa biyu. To ni dukanin kakannina
Fulani ne babu inda muka hadu da wata kabila ta
kowace fuska. Mu Fulanin Bauchi ne a lokacin da
Jihar Bauchi take hade da Jihar Gombe. Bayan
da aka raba Jihar Bauchi da Jihar Gombe, sai
muka zama mu Fulanin Jihar Bauchi ne, a lokaci
guda kuma Fulanin Jihar Gombe ne. Ta wajen
mahaifina ni Bafulatanin Jihar Bauchi ne, ta
wajen mahaifiyata ni Bafulatanin Nafada ne da
ke Jihar Gombe.

An haife ni ne a watan Janairun
1927 wanda ya yi daidai da watan Muharram
1346 Bayan Hijira a ranar Laraba.
Sunan mahaifina Alhaji Usman dan Alhaji Adamu,
shi mahaddacin Alkur’ani ne. Na rayu ne a
hanunsa shi ya koya mini karatu har na haddace
Alkur’ani a hannunsa. Sunan mahaifiyata Hajiya
Maryam. Bayan na haddace Alkur’ani a hannun
mahaifina ne ya tura ni duniya domin in je in
gyara tilawata ta Alkur’ani. Na shiga duniyar
Allah Ya taimake ni na gyara tilawar tawa,
lamarin da ya sanya wadansu kan ce mini Gwani
na Alkur’ani, wadansu mutanen kuwa kirana suke
yi da Gangaran a fagen haddar Alkur’ani. Bayan
nan sai mahaifina ya ce zai tura ni duniya in je in
sake nemo ilimi, daga nan aka turo ni nan Bauchi
domin neman ilimi. Na fara neman ilimi ban riga
na samu ilimin da yawa ba, sai Allah ya sa Failar
Shehu Ibrahim Kaulaha din nan ta bayyana.

Dama mahaifina dan Tijjaniyya ne Mukaddami ne
ta salsalar Umaru Futi, wato ta wajen
Muhammadu Ghali. Kuma shi mahaifina ne ya ba
ni darikar Tijjaniyya. Bayan da muka shiga Failar
Shehu Ibrahim, sai ya zama kowace harka tawa
sai ta hada da maganar Shehu Ibrahim.
Alhamdulillahi na samu rabo mai tarin yawa a
sha’aninsa, na soma yin tafsirin Alkur’ani ne a
wajajen 1950, sannan na yi aurena na farko a
1948. Cikin alherin da Allah Ya yi mini, ’ya’yana
tun suna kanana suke haddace kur’ani. Da farko
’ya’yana suna haddace kur’ani tun suna ’yan
shekara 11, aka dawo 10, aka zo 9 har ya
zamana cewa akwai ’ya’yana da suka haddace
kur’ani suna ’yan shekara bakwai-bakwai da
haihuwa. Ina da ’ya’yan da suka haddace
Alkur’ani guda 70, kuma mutum uku ne kawai
suka rasu daga cikinsu, wato Dokta Hadi da
Ahmad da kuma A’ishatu (Yalwa) wacce ta rasu
a hadarin mota a hanyar Yola amma sauran duk
suna raye yanzu haka.

Ta fuskar jikoki fa?

Alhamdulillahi, su ma suna da dama sosai. Ina da
jikoki mahaddata guda 120 wadannan sun
haddace Alkur’ani amma dukkansu suna da yawa
sosai.

Ta fuskar iyali fa ko Malam nada mata guda
nawa?

Matana hudu ne na kuma dade ina tare da mata
hudu din nan, wadansunsu sukan tsufa sai su yi
ritaya da kansu sai kuma na sake samun
wadansu matan. Matana hudu ne a halin yanzu.
Mutane na mamakin dimbin ilimin da Allah Ya
bai wa Malam ko akwai fannin da ya fi
kwarewa?

Na farko bangaren da na fi kwarewa sosai shi ne
Alkur’ani. Daga nan kuma sai bangaren tafsiri, a
nan malaman tafsiri sun ce lallai na iya tafsiri inji
su. Sai kuma bangaren Ma’arifa, ma’anar
Ma’arifa shi ne ilimin (gyaran) zuciya wanda ake
kiransa ilimin tarbiyya, a nan ma masu irin ilimi
kan ce ina da sani a fannin. Shehu Ibrahim ya ce
lallai na san wannan bangare. Sauran ilimomi ina
tattabawa, su Hadisi da Lugga da Li’irabi da
Tasrifi da Fikihu duk ina tattabawa.
Jama’a na mamaki idan aka yi wa Malam fatawa
sai ya hada da ba da misali maimakon gundarin
amsar, ko me ya sa Malam yake yin haka?

Wato shi buga misali wata runduna ce ta Allah
mai shigar da ilimi cikin kawunan mutane, idan
ka kawo amsar magana sai ka buga misalin da
za ta hau kan mutane domin fahimtar da su. Shi
buga misali yana jawo hankali a fahimci mene ne
aka fada. Misali na da matukar muhimmaci
wajen ba da amsa.

Ko Malam ya taba yin karatun boko?

(Dariya)…. Ai ko ABCD ban yi ba. Ni ban yi
karatun boko ba, ko ABCD ban je na koya ba.

Ga shi Malam bai yi karatun boko ba ga kuma
zamanin yau gwagwarmayar da boko ake hadawa
ta yaya Malam yake yi?

Eh to, da yake muna tare da masu bokon, masu
karatun na boko, wadansu ’ya’yanmu sun zama
daktoci ba daya ba, ba biyu ba. Don haka suna
dafawa wajen tafiyar da komai yadda ya dace.

Muna da masu karatun boko sosai a cikin
’ya’yana da almajiraina kuma muna tare da su, ta
haka muke gwagwarmayar rayuwar yau din.

Me Shehi ya fi sha’awa a rayuwarsa?

Abin da ya fi ba ni sha’awa, irin yadda na mayar
da kur’ani sa’anata da kuma yadda na rungumi
darikar Tijjaniyar nan ta zama rayuwata, kuma da
dukanin wani mutumin da yake dangantuwa da
son Annabi da son Allah ina sha’awar in sadu da
shi.

Me Shehi yake yi lokacin da yake hutawa baya
karatun Alkur’ani ?

Wai! A duk lokacin da nake hutu ina shagaltuwa
ne da karanta Salatul Fatihi da Tasbihi da
Istigfari da Salatin Annabi (SAW) da sauran
zikirori.

Wani irin abinci ne Malam ya fi sha’awa a
rayuwarsa?

(Cikin matukar dariya)… Abincin Hausawa da
Fulani su nake sha’awa, ina cin tuwon shinkafa,
ina cin shinkafar ita kanta. To amma yanzu a
halin da muke ciki na daina cin dawa da masara,
na kuma daina cin tuwon masara da tuwon gero
duk na daina cin su yanzu. Kuma babu wani
likitan da ya hana ni cin su hankalina ne kawai
ya ki su. Ka ga yanzu dai ina cin tuwon shinkafa
da ita shinkafar kanta. Masara, tuwon masara,
dawa, tuwon gero duk na yi ritaya da cin su a
halin yanzu ba na cin su bisa ra’ayin kaina.
Ga shi yau za a yi taron zikiri da addu’o’in zama
lafiya na sabuwar shekara kuma da safe Shehi
ya yi magana a kai ko me Shehi ya ce?

Alhamdulillahi yau za mu yi taro na Zikirin
Juma’a na wannan wata na farkon Shekarar
Musulunci. A Almuharram, Juma’ar Farko mukan
fara yi a nan Bauchi, Juma’a ta biyu mu yi a
wani waje da na uku Juma’ar karshe na hudu
kuma mu yi a Birnin Tarayya, Abuja.

Daga yau za
mu fara a nan Bauchi don Ubangiji Yana cewa:
“La’ilaha illahu babbar katangaTa ce duk wanda
ya shige ta ya huta da azabaTa.” Za mu gabatar
da wannan La’ilaha illallahu mu sa Najeriya a
cikin wannan babbar katanga Allah Ya kiyaye mu
Ya kiyaye mana kasarmu daga dukan fitina.

Kuma za mu fiskanci sabuwar shekara da
La’ilaha illallahu sannan mu roki Allah Ya yafe
mana zunuban da muka aikata a shekarar da ta
wuce, abubuwan da muka yi na lada kuma Allah
Ya karba. Sabuwar shekarar da muka shiga kuma
Allah Ya sa mun shige ta da alheri ta zama
shekarar alheri, shekarar zaman lafiya da
kwanciyar hankali.

A lokutan taron muna
gayyatar dukan Musulmi domin La’illaha illallahu
kayan dukan Musulmi ne mu zo mu yi zikiri tare
a ji jawabai kuma a roki Allah tare. Allah Ya ba
mu alheri Ya kiyaye sharri, fitintunun da suke
faruwa Allah Ya yi mana maganinsu, bala’o’i
duka Allah Ya kiyaye mana su.

Kamar bala’o’in
da muke fama da su na Boko Haram da satar
mutane a nemi kudi da satar dabbobi da dukan
bala’o’i Allah Ya yaye mana su, Allah Ya ba mu
lafiya da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Aminiya

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: