Wednesday 4 October 2017

TUSHEN HAUSAWA: NAZARI KAN ASALIN HAUSA

Tura Wannan Zuwa

Kashi na uku

Farfesa Umar El zakzaky Al Bahaushe yace"
kwayoyin halittar Fir'auna Seti, wannan daya
yayyanka yahudawan zamaninsa, da kuma na
magajinsa Fira'una Remesis II, wanda yayi
zamani da Annabi Musa A.S sunyi
kamanceceniya da kwayoyin halittar mutanen
kano na yau, musamman ma nacikin kwaryar
badala."

Sai dai Farfesa Muzzah Jibrin, Farfesa
Abdullahi Elkanawy da wasu masana da dama
sunyi watsi da wannan bincike. Ga abinda ya
fito daga makalar masanan kamar yadda suka
gabatar a wani taro daya gudana a Arewa
House dake kaduna:

Kuskure ne a hada asalin wancan Fir'aunan da
kano tunda Gawar Mornoptah, dan Fir'auna
Remeses II, fir'aunan da aka halakar a ambaliyar
ruwa yayin da yake bin sawun Annabi Musa A.S
don ya halaka shi, wadda Masani Loret ya gano
a shekarar 1898 a tsohon birnin Thebes ta nuna
cewar kwayoyin halittar ta sunfi kamanceceniya
dana mutanen egypt ne ba mutanen kano ba".

A wani kaulin kuma, masanan sunyi hasashen
cewa kwayoyin halittar mutanen zariya dana
kabilar Gwari da Igala suma sunyi
kamanceceniya da juna, wanda hakan na nuni
da cewar kodai kabilun asalinsu a zariya suke da
zama, ko kuma al'ummar kabilun ne suka kafa
garin na zaria lokaci mai tsawo daya shige, don
haka yanuwan juna ne kenan. Muna kuma iya
cewa daga jikin mutum guda kabilun suka fita.

Amma maganar su da sukace sun auna wasu
ɓuraguzai na kasusuwan mutanen dake kwance
a wasu makabartu a kano, har kuma sun gano
cewar mafi yawan kwayoyin halittar mutanen
kano yafi nuni dana Sharifai, kamar akwai siyasa
a ciki.

Tabbas, tarihi ya nuna cewar a wajajen karni
na goma sha uku, wangarawa karkashin Sheik
Abdurrahman Zaiti tare da wasu malamai
kimanin arbain irinsu Modibbo sheshe,
Mandawari, Limamin Madatai, Limamin Jujin
'yan labo sunzo kano har ma suka kawo
musulunci garin. Lokacin Sarkin Kano Yaji dan
Tsamiya ke bisa gadon sarauta.
Sai kuma a karni na goma sha biyar zamanin
Sarkin Kano Rumfa Akace wani balarabe masani
mai suna Imam Maghili ya ziyarci kano shima da
wasu jama'a tasa. Daga baya ma ance yabar
wasu daga zuriyarsa anan kano, wadanda su
ake kira Sharifai zuwa yanzu.
Marubuci, marigayi Maje Ahmad Gwangwazo
ya kawo wata muhimmiyar gaba a shafi na 22
na littafinsa mai suna Wangarawa Sun iso Kano,
inda yake cewa "Sheik Abdullahi Ilorin ya nuna
cewar tun a karni na goma sha ɗaya wangarawa
suka fara bazuwa suna yaɗa musulumci a afirka
ta yamma. Yace su wangarawa kasarsu ta farko
misira(Egypt). Yace asalin mazaunan kabilar
Sundiata da asalin kabilar Kakan Mansa Musa
da asalin kabilar Songhai irinsu Askiya
Muhammad kenam, tarihi ya nuna duk a misira
suke kafin su iso Mali, inda mafi yawan masu
tarihi ke cewa daga Mali wangarawa sukazo,
amma Mali din
ma zuwa sukayi".

Sai dai, koda auratayya ta wanzu tsakanin
wangarawa da larabawan da suka sauka a kano
da kanawa bakaken fata na lokacin, da wuya
ace an samu kwayoyin halitta sunyi irin wannan
mamakon rinjayar. Domin kuwa kano tun asali
garin bakaken fata ne ba farare ba, ba kuma a
taɓa samun cewar an maye mutanen kano da
wasu mutanen ba, don haka faɗin cewar
kwayoyin halittar kanawa ya nuna su sharifai ne
ba lalle ya zamo ya inganta ba.
Amma tana iya yiwuwa, anyi rashin sa'a,
ɓuraguzan da aka samu a makabartun waɗanda
akayi wannan gwajin dasu (sample) na
Wangarawa da larabawan ne dana zuriyarsu
wadanda watakila sun cakuɗu da bakaken fata,
don haka binciken bai iya bada labarin ɗaukacin
mutanen kano ba, tunda dokar irin wannan
binciken ta nuna cewa wajibi ne abubuwan da
za'ayi bincike akansa su zamo suna wakiltar
ɗaukacin abinda ake magana akansa.

Wani abin lura ma anan shine shigar siyasar
addini acikin dukkan binciken.

Munji bincike na farko ya nuna cewar Fir'aunan
daya kashe jarirai ɗan kano ne, don haka wasu
ke ganin hakan kamar kaskanci ne ga kanawa,
shiyasa sukuma suka wanke kanawa da cewar
asalinsu sharifai (jikokin fiyayyen halitta) ne..

A hakika dai, bamu da karan nunawa ga
waɗancan Malumma masu girma, amma wajibin
mune mu karɓi gaskiya komai ɗacinta dangane
da asalin mu. Maganar addini ba zata sa mu
ɓoye asalin muba, tunda da ayyukan mu akace
za'ay mana hisabi bada asalin muba. Rashin
ingancin binciken na farko shine kurum hujjar da
zatasa muki aminta dashi amma ba laifiɓ da
firaunan ya aikata ba.

Akwai binciken masana dake cewa Kwayoyin
halittun Firauna Remesis II yafi kamanceceniya
da kwayoyin halittun mutanen Afirka ta tsakiya a
ma'auni na farko, daga nan sai mutanen kasar
south Africa a ma'auni na biyu, sannan mutanen
Afirka ta yamma inda hausawa suke a ma'auni
na uku. Wanda hakan ke nuna alakar hausawa
da wancan firauna tayi tazara da shekaru masu
nisan gaske... (Watakila sai kowacce kabila
daga cikin biyun ta tike da Annabi Nuhu ko
Annabi Adamu za'a ɗiga aya)

Sai dai kuma, akwai tsohon zance dake nuna
kwararowar misirawa izuwa yankin afirka ta
yamma a tsahon zamani daya shuɗe. Watakila
tun zamanin Annabi Musa A.S hakan ta faru, ko
kuma wani lokaci kafin haka, domin kuwa
labarin baka yana nuna cewar garin Auyo dake
jihar jigawa ya kafu tun kafin Haihuwar Annabi
Musa A.S, sai dai kuma karancin tarihin da
muke dashi akan kabilar Auyokawa da akace
sune suka kafa garin ke hanamu gane alaka ta
jini ko ta sadarwa da wayewa a tsakanin mutan
garin da kuma misira tun a wancan tsohon
zamani.

Da alama dai, Magana mafi inganci bisa
kwayoyin halittar hausawa shine wanda wasu
gungun masana suka gudanar akan hausawa
mazauna sudan.

Da fari, Binciken ya nuna cewar kashi arbain
na kwayoyin halittun hausawa dake zaune a
sudan sunyi dai-dai dana kabilun sudan ɗin.
(Hassan et al 2008)

Akwai kuma makamancin binciken daya nuna
cewa kwayoyin halittar Hausawa ya nuna cewa
su 'yanuwan juna ne da wasu kabilu masu
amfani da yaren Nilu mazauna Nigeria,
Cameroon, Central Chad da kuma kudancin
Sudan. (Toshkoff et al 2009).

Binciken ya nuna cewar asalin yaren hausa, da
yarukan waɗancan kabilu guda ɗaya ne saboda
alakar yarukan da aka gani suna dashi da juna.

Bakaken fatar chadi dana kamaru duk ana
tsammanin sun gangara yankin ne shekaru da
dama da suka gabata daga daular sudan.
Sukuwa mazauna sudan, duk da gaurayuwar
kwayoyin halittun larabawa dana sauran kabilu a
tattare dasu, an gamsu da cewa su jikokin
tsoffin bakaken fata ne na tsohuwar daular nan
ta 'Meroa' data shahara a duniya wadda ta
wanzu a sudan ɗin.

Ta haka, sai ake hasashen cewa kakannin
hausawa da kakannin sudawa da kakannin
wadancan kabilu mazauna cameroon da chadi
sun fito ne daga tsatson Uba daya, amma hijirar
data rinka aukuwa tsakankanin mutanen_da
shine sanadiyar rarrabuwarsu ta yadda yanzu
kowa yayi nesa da kowa. Hasashen kuma na
nuna cewar wannan rarrabuwa ta auku akalla da
shekaru dubu biyu baya zuwa sama, tayadda a
iya wancan lokacin ne kowacce kabila tayi
chakuduwa da sauran kabilu har kashi sittin na
kwayoyin halittar su ya sauya, kashi arbain ne
kadai zuwa yanzu bai jirwaya ba.

Babbar hujjar
hakan itace samuwar wasu kabilun daga jikin
waɗancan na ainihi, tayadda ansan ana ɗaukar
tsawon lokaci kafin faruwar hakan. Sai kuma
tsawon zamanin da daular bakaken fatar tayi a
raye har kuma ta rushe. Kamar abinda Marubuci
Morton H. Fried ya faɗa a littafinsa mai suna
'The Notion of the Tribe' cewar akwai kabilu na
ainihi (primary tribe), akwai kuma kabilu
samammu daga na ainihi (secondary tribe).

Don haka idan har kabilun yahudawa guda
goma sha biyu sun fita daga jikin Annabi Yakuba
A.s (Israel), to muna iya cewa kabilar Annabi
yakuba da yarensa shine kabila ta ainihi,
samammun kabilun kuwa sune waɗanda
'ya'yansa sha biyu da jikikinsa suka ɗauka
bayan rarrabuwarsu ga wajen zama
Kuma ana iya samun kabilu sama da ɗaya mai
amfani da yare ɗaya, amma dai anfi samun
kowacce ɗlkabila da irin nata yaren gami da
ɗabi'a wanda take samarwa kanta-da-kanta
gwargwadon wurin zamanta da aɓin bukatarta
da kuma abubuwa makusanta da take dasu.

Sannan tana iya yiwuwa ma, kafin Hausa ta
zama hausa, sai da wasu kabilu suka firfita
daga asalin kabilar ta ainihi. Tunda dai zamu
gamsu cewa hausa daga wata kabilar ta cire
kanta.

Kowa dai ya rike cewar Maguzawa sune
asalin hausawa, har ana kallon kalmar hausa a
matsayin bakuwa. Don haka yadda akayi
hasashen alaka ta jini tsakanin kabilun
maguzawa, Gwandara, Ngizzim da kuma Bole
shima abin nazari ne wajen gane asalin uban
jinsi wanda hausawa suka fito daga gareshi,
tunda masana sun nuna cewar kwayoyin halittu
gami da yaruka duk sunyi kaman-ce-ceniya da
juna.

A Littafin tarihin Gwandara da Dr. Silvestri O.
Ayihai ya wallafa mai suna 'The History of
Gwandara towns and villages' ya nuna cewar sai
da kabilar Gwandara ta jima tana zagaye-zagaye
daga nan zuwa can, suna Farauta karkashin
jagorancin shugabansu mai suna Dan Baba
sannan suka riski wani waje mai suna Kupai
sannan suka fara zama. Daga nan ne sannu a
hankali suka samar da masarautar su gagaruma.
Mu kuwa anan kasar hausa, an samu labarin
baka cewar asalin Gwandara hausawa ne da
suke zaune a kano, wai lokacin da Musulunci
yazo sukace sam Gwanda (suyi) rawa da (suyi)
Sallah, don haka suka bar kano zuwa wani
wajen da zama.

To idan ma wannan labarin na Gwanda-rawa-
da sallah bai inganta ba, wancan binciken na
kwayoyin halitta ya isa ya nuna mana cewar
zamani mai tsawo daya gabata kabilun biyu sun
zauna da juna a matsayin yanuwan juna.

Kabilar Ngezim kuwa ance sune asalin
wadanda suka soma zama a tsohon birnin
Ngazargamu na daular Kanem. Suma dai ance
sun warwatsu a wannan yanki da hausawa suka
mamaye ayau, amma dai yankunan Yobe, Borno
da Jigawa nan ne tsohon wurin zamansu.
Haka ma kabilar Bole, wadda akace suma
mafarauta ne waɗanda suka mamaye yankunan
Bauchi, Gombe, Yobe da kuma Jos. Zuwa yanzu
ana ganin kamar sun saki al'adunsu da yarensu
sun ɗauki na hausawa.

Su kuwa maguzawa ance manoma ne, amma
tana iya yiwuwa sun jarraba noma ne sukaga
yagi farauta riba don haka suka yadda sana'ar
kakannin nasu.

To ai waɗanda suka fara zama a dutsen dala
na garin kano ma ance mafarauta ne.. Wai har
taron shiga farauta ma akeyi a bakin dutsen
lokaci zuwa lokaci, inda manyan mafarauta ke
zuwa daga sassa mabanbanta.. Kenan farauta
sana'ar kakannin waɗannan alummomin ne baki
ɗaya, don haka suka kasa sakinta, tayadda koda
sun zauna a wani wuri na wani lokaci sun
jarraba wani abin, da zarar sun tashi daga wurin
kanta suke sake komawa..

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By © Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
08060869978

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: