Monday 2 October 2017

Wata rana gari yayima wani gurgu da yake rayuwa a wani qauye zafi.

Tura Wannan Zuwa Ga

Babban abinda yasa rayuwarsa qunci kuwa shine
nakasar da yake da ita. Musamman idan zaiyi
tafiya zuwa wani qauye ko ka'suwa. Domin tafiya
tana mugun wahalar dashi.
Wata rana wannan gurgu yana tafiya akan
hanyarsa ta zuwa wani qauye. Sai yaga wani
maka'ho a zaune. a qasan wata bishiya. Sai
gurgun ya tambayi makahon ina zaka tafi?
Sai Makahon ya bada amsa. Sai gurgun yayi
murmushi. Yace: kaga nima cen zanje.
Sai makahon yaji da'd'i kasancewar ya samu
wanda zaiyi masa jagora.
Sai gurgun yacema makahon: kai nakasas_
shene. Nima nakasas_she ne. Don haka me zai
hana ka d'aurani akan kafad'arka. Tunda kai kana
iya tafiya. Ni kuma ina gani. Kaga sai in riqa
nuna maka hanya.
Nan take. Makahon ya amince. A haka suka tafi
qauyen.

Wannan shine had'uwarsu ta farko. Kuma tun
daga nan suka zama abokai saboda tasu tazo 1.
Sai ya zamana cewa kullum a tare suke zuwa
duk inda za suje.
Wata rana wannan makaho da gurgu. Sunzo suna
tafiya za suje kasuwa. Sai gurgun yace da
makahon tsaya
naga wata jaka. Sai makahon ya tsaya. Gurgun
ya sauka ya d'auko jakar ya bud'e. Sai yaga jakar
cike take da gwala'gwalai. Sai makahon yace:
meye a cikin jakar?
Sai gurgun yace: gwala'gwalai ne.
To. Masu binmu a shafin Rayuwa A Musulunci.
Anzo wajen.
Domin kuwa Makahon cewa yayi shine yafi
cancanta abarma jakar.
Domin da badan ya taimaka ya d'auko gurgun ba.
To gurgun bazai iya zuwa wajen akan lokaci ba.
Shi kuma gurgun yace: ai da badan ya gayama
makahon ba. To da makahon bazaiga jakar ba.
Ballantana ya d'auka. Kai koda qafar makahon ta
taka jakar bazai iya ga'ne cewa akwai wani abu
mai amfani a cikin jakar ba.
Wannan shine abinda ya janyo jayayya a tsakanin
way'annan abokai. Haka suka d'auki lokaci
sunata sa'insah. Har izuwa lokacin da wani
mutum yazo wucewa yaga zazzafar muhawarar
da sukeyi.
Nanfa mutumin ya tsaya yayi iya'kacin qoqarinsa
don ya sasantasu. Amma abin ya faskara. Don
haka sai mutumin yai tafiyarsa. Ya barsu anan
suna tabka sa'insa
suna cikin tabka muhawarar ne. Sai wani mutum
yazo wucewa yaji mujadalal da sukeyi
sai mutumin ya tambayesu: INA JAKAR GWALA_
GWALAN TAKE?
Sai suka nuna masa. Sai mutumin ya d'auki
yakar ya fita da gudu. Sannan yace: duk wanda
ya biyoshi ya kar6i jakar to jakar ta zama tasa.
Bayan mutumin ya gudu sai suka tabbatarma
kansu cewa LALLAI WASU ABUBUWA DA SUKE
DUNIYAR NAN MUTUM 1 BAZAI IYA
TINKARARSU BA. KUMA YACI NASARA BA.
DOLE WASU ABUBUWAN SAI ANNEMI
TAIMAKON WANI KO WASU SANNAN ZA A IYA
SAMUN NASARA HAR AKAI GA GACI. Ballantana
su da suke nakasassu.

NI ADMIN 9. NAKE ROQON ALLAH S.W.T DA YA
HA'DA KA'WUNAN MUSULMAN DUNIYA. Baki 1n
mu.
YA ALLAH KA TAIMAKI MUSULUNCI DA
MUSULMAI.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By © Rayuwa A Musulinci.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: