Thursday 23 November 2017

11. YAWON DUNIYAR HAJJI BABA Na James Morier Abubakar Tunau Ya Fansar Da Shi

Tura Wannan Zuwa

Da farko da na fara, abin bai yi kyau ba ko kadan. lm masu jin labarin nawa sun ji, sai kowa ya tashi ya tafi abinsa, ba mai ba ni ko da anini.

A hankali dai na fara koyon dabara. In na fara ba da labari mai dadi, na matso kusa da karshe, sai in tsaya in dubi mutanen in ce musu in za su ba ni kudi to, zan karasa musu labarin. Ka san in labari mai dadi ne kowa yana so ya ji yadda ya kare.

Da na fara yin haka, haba, na yi ta samun kudi. Da haka dai na fara samun abin kaina. In na ga kamar mutanen sun fara gajiya da ni da labaraina, sai in tafi wata kasar in ci gaba.”

BABI NA 7

Zamba Ba Ta Ci, Na Yi Wa Meshed Adabo
BAYAN da kowane sufi ya kare ba da nasa labari, na yi musu godiya saboda hirar da muka yi, da abin da na koya gare su. Daga nan na yi niyyar in yi iyakar kokarina in koyi dukan abin da zan iya samu daga wurinsu, don ni ma in zama sufi, ko da watakila wani abu zai tsare ni daga aikin da na ke yi yanzu. Sufi Sefer ya koya mini dabaru da yawa wadanda suka sa mutane suna ganinsa da daraja. Sufi na biyu ya koya mini rubuta laya.

Na ukun kuma ya koya mini wadansu labarai, ya ba ni aron littattafansa, ya koya mini dokokin da zam bi mutane su yi ta ciro kudi daga aljifansu suna ba ni, ba tare da sun sani ba. Har yanzu dai ina nan ina tallar tabata. Kai, sai in ce ma ba taba na ke sayarwa ba, kashin dabbobi da ciyayi da busassun ganyaye ne kawai.

Wata rana da yamma lokacin da a ke watsewa daga kasuwa sai wata tsohuwar mace tankwararriya cikin tsumma ta zo wurina, ta ce in shirya mata taba ta sha.

Duk fuskarta a rufe ta ke, ba ta ce kome ba fiye da im ba ta taba kawai. Na ba ta taba wadda ta fi sauran rashin kyau. Da ta kai bakinta sai ta fara zubad da yau, ta yi tari tana maganganu. Ba zato ba tsammani sai ga katti shida sun zo sun kama ni, suka ka da ni a kasa.

Ka da ni ke da wuya, sai tsohuwan nan ta buds idonta. Kana tsammani me na gani? Dan Sanda !
Ya ce, “Yau na kama ka, kai lalataccen mutumin Isfahan.

Ka bi mutanen Meshed duka ka cika su da dafi. Bulalar da za a yi maka sai ta yi daidai da kudin da ka karba.” Daga nan ya ce wa mutanensa su kawo turu. Suka kawo, aka daure ni a jiki, aka yi ta tsala mini bulala. Ba irin kukan da ban yi ba da rokon gafara. Amma ina ! Sai ji ka ke tsal tsal tsal.

Ni kuwa ina ta zagin taba, ina cewa har abada na bar shanta. Duk da haka dai sai bulala a ke ta zabga mini. Na yi yaushi kamar ba ni da rai.

Can da na farfado, sai na gan ni a gefen hanya, keyata tana jingine ga bango. Mutane sun kewaye ni, ba wanda ya ke jin tausayina. Kayan tallata kuma aka kwashe daga ni sai azabar da na ke sha. Da kyar na rarrafa na kai gida, ko da ma ba nisa daga inda na ke.

Bayan da na yi kwana daya da azabar ciwo, kafafuna sun kumbure sun fita daga kamanninsu, sai wani sufi ya ziyarce ni. Ashe shi da kansa ma an taba yi masa hakanan, saboda haka ya san maganin da zai warkad da ni. Ya kawo ya ba ni. Cikin ’yan kwanaki kadan na warware sarai.

Ina nan na shiga tunanin barin Mashed, don na ga ba ni da sa'a a wannan gari. Da farko dai ga shi an yi wa bayana rauni, ga shi kuma yanzu an yi mini bulala. Na tone kudina da na binne a kusurwar dakina, na ce da zarar na ga wani ayari mai zuwa Tehran zan tara hanya da su.

Na fadawa abokan nan nawa nufina, Suka kuwa yi murna. Sufi Sefer ya ce tun da ya ke mutanen Meshed suna neman hanyar da za su halaka ni, ya kamata im bar musu garinsu, in tafi wani wurin inda zan nemi abinci. Suka yarda kuma in shiga tufafi irin na sufi. Shi ke nan na nufi kasuwa na sayo hula da tasbaha da fatar akuya. Sufi Sefer kuma ya ce shi ma zai bi ni.

Lokacin da mu ke binciken ayari mai zuwa Tehran sai Allah ya yi mini gamo da katar da abokin nan nawa Ali Katir. Shi ma zuwansa ke nan Meshed, wani dan kasuwa yana tsada da shi ya daukam masa fatun rakuma irin na Bokhara ya kai masa birnin Santambul.

Da ganina ya yi murna, ya kunna lofensa ya ce mu sha tare. Na fada masa labarin duk abin da ya auku gare ni tun rabuwana da shi, shi kuma ya gaya mini nasa. Ya ce da ya bar Meshed sai ya doshi Isfahan dauke da azurfa da fatun raguna.

Allah dai ya fisshe shi lafiya, bai gamu da ’yam fashi ba, har ya isa Isfahan. Wai har yanzu labarin ’yam fashin nan yana nan kamar jiya aka yi. Duk mutanen garin sun gaskata wai ’yam fashin nan sun zo cikin kungiya ne, wai yawansu ya kai dubu, sa’an nan kuwa an tayar musu haikan. (Ka ji Karya). Wani ma wai shi Hassan, wanzami, ya ce shi da hannunsa ya yi wa wani shugabansu mugun rauni, da kyar ma ya tsira. (Ka ji wata karyar).

Labarin kokawar da muka yi da ubana ban fada wa kowa ba. Don haka da Ali Katir ya ke ba ni labarin abin da mutanen Isfahan su ke cewa, ban yarda na nuna alama na san wani abu a kai ba. In na ga kamar fuskata za ta bashe ni, sai in hura masa hayakin taba a ido don kada ya ga fuskata. Da ya kare ba ni labarin, sai ya ce ya yarda ni da Sufi Sefer mu bi shi har zuwa Tehran. Im mun gaji zai yardam mana mu hau alfadaransa.

Bayan mun kintsa kome sai muka kama hanyar zuwa Tehran. Da muka fita kofar gari, na daga hulata, na ce da ma Allah ya sauko wa garin da bala’i. Dalili kuwa, shi ne don muguntar da mutanen garin suka yi mini. Sufi Sefer shi ma ya goyi bayana. Na ce masa ai shi in ya ga dama yana iya tsayawa a garin. Ya ce allambaran ba zai tsaya ba, don tun da ya ke Sallar Azumi ta kusa ya sani mutane za su kura masa ido, su ga abin da zai yi. Ya ce shi ba zai iya yin azumi ba, ba zai iya barin shan taba ba, don kamar yadda ka san mutum ba zai iya barin shakar iska ba, haka. shi ma ba zai bar taba ba. Kuma giya kamar ruwa ne gare shi, ba zai iya bari ba. Ya ce gara dai ya bar garin don ya yi nishadinsa.

Ga mu nan har muka iso Semnan ba abin da ya faru, Bayan da muka kwana biyu a nan sai na yi giggiwar in taya Ali Katir lodin alfadaransa. Ai kuwa sai ciwcn bayana ya sake dawowa. Ciwon ya tsananta kwarai ya zama dole a bar ni a baya. Na kuwa yi niyyar in zauna har sai na warke. Sauran suka tafi. Sai na sami wuri a bayan gari na shimfiɗa fatar akuyata, na kwanta. To, ga al’ada, in sufi ya zo wani gari sai ya hura kaho, don a san yana nan. Don haka na dauki kaho na yi ta hurawa, “Hak! Hu! Allahu Akbar!” Na yi ta yin haka da karfi yadda za a iya ji.

Nan da nan na ga mata da yawa sun zo wurina. Na rubuta musu layoyi suna biyana, daga mai ba ni ’ya ’yan itace sai madara, sai zuma da sauran tarkace. Da na ji bayana ya tsananta da ciwo sai na tambaya ko akwai wani wanda ya san aikin Likita a Semnan. Aka ce akwai wani gwanin kaho da cire hakori da dori.

Akwai kuma wani wanda ya kware ga cucecucen dawaki, har ma yana gwadawa a jikin mutum. Akwai kuma wata tsohuwa wadda aka ce tana da maganin kome.

Ko wannensu ya ziyarce ni dai dai. Dukansu suka ce sai a yi mini lalas. Aka zabi Likitan dawakin nan ya yi mini, don ya rigaya ya saba. Likitan nan ya kawo garwashi da zugazugai da karfe, ya hura wuta, ya sa karfen ya yi ja wur. Aka kwantad da ni rub da ciki aka sa mini jan karfen nan.

Mutanen da key kewaye suna cewa, “Allah ya ba da sauki.” A wurare 13 aka yi mini lalas. Haba, da farko dai na yi ta maza, ko motsi ban yi ba. Amma daga baya abin ya wuce na dauriya, na yi ta tsala ihu da koke-koke. Ko kulawa Likitan bai yi ba, sai da ya gama. Na yi kwanaki da dama ina fama da azabar ciwo, amma daga baya na warke sarai, karfina ya dawo kamar da.

Bayan wannan na yi niyyar in karasa tafiyata zuwa Tehran. Amma kafin in tashi na yi shawarar im ba mutanen garin wani labari, don su sani ni sufi ne sosai. Shi ke nan na tafi kasuwa na yi yekuwa, mutane jingim suka taru suka kewaye ni.

Ina wurin ne ma wani labari game da wani wanzami a Bagadaza ya fado mini zuciya.

Na gyara murya, na daga idanuna sama na ce :

Za mu ci gaba ranar Asabar mai zuwa, da karfe tara na dare (9:00PM), in sha Allah.

Allah ya kai mu

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Bukar Mada

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: