Friday 1 December 2017

HANYOYIN MAGANCE YAUDARA A SOYAYYA TSAKANIN NAMIJI DA MACE

Tura Wannan Zuwa
Abun dai ruwan dare ne, ba ga mazan ko matan ba.

Kowane ɓangare na maza da mata suna taɓa
waccan halayya ta yaudara a soyayya kuma suna
fuskantar hakan daga abokan zamansu.

MARUBUCI: Abba Muhd ‘Dan-Hausa.

To amma shin wai mene ne yake kawo yaudara a
soyayya? Mece ce ma ma’anar kalmar yaudara?
Yaudara ita ce, hali na 6oye gaskiya da niyyar
cuta ko zambatar wani.

A lokuta da yawa maza su ke sakin jiki har mata
su yaudare su, ko kuma su mata suke
sakankancewa har maza su yaudare su a
soyayya. Ina ganin za ku yarda da ni idan na ce.

A dukkan lokacin da ka ji yaudara to da akwai
rashin so da tausayi.

MAZA:

A sau da yawan lokuta namiji kan makance a kan
soyayya har idanuwansa su rufe a kan haka, ya
gaza gane macen da ta ke son shi dan abun
hannunsa, ko ta ke kula shi kawai saboda rage
dare, ko dan wani abu da ta ke nema a wajensa,
ko macen da ta ke kula shi ba dan tana son shi
ba, sai dan kawai ya matsanta mata akan ta so
shi, da macen da ta ke son shi kawai dan tana
jin dad’in kalamansa ko jin dad’in hira da shi
amma ba dan tana son shi ba, har ta kai daga
baya da zarar ta samu wani da take so ko ta
gama cimma burinta a gare shi sai ta guje shi.
Sai ka ji daga bisani ana mayar da yawu kan
cewa ai wance ta yaudare ni, bayan kuma da ma
can babu son gaskiya a tsakani.

Domin gujewa fad’awa irin wannan halin, tun da
fari akwai bu’katar ka san wasu alamomi da
ganinsu zai tabbatar maka da cewa tabbas
wance tana sonka da gaskiya.

Amma duk da
haka sai ka yi taka-tsantsan.

MATA:

Ke ma akwai bu’katar dukkan wanda ya zo miki
da batun soyayya, ki tsaya ki nutsu ki tantance
masoyinki na gaskiya, domin gujewa fad’awa
tarkon samarin shaho (‘yan-yaudara)
Akwai wani zai zo ne yana son ki kawai dan ya yi
alfahari da cewa ke budurwarsa ce. Wani kuma
zai yi ‘ko’karin neman hanyar da zai bi ya
yaudare ki ne dan ya lalata miki rayuwa. Wani
zai zo wajenki dan ya rage dare ne kawai. 

Da sauransu

Da yawan ‘yan yaudara, za su iya kashe miki ko
nawa ne, har ma su yi wa waninki hidima, dan
bu’katarsu ta biya a kanki. Sun iya kalamai masu
dad’i amma na yaudara.

Maza ‘yan yaudara suna da wahalar ganewa a
wajen mata, wani zai iya zubar miki da hawaye,
wai dan duk ki yarda ya na son ki da gaskiya, zai
iya siyo miki duk abun da kike so, zai iya baki
duk abun da kika bu’kata daga wajensa
matu’katar bu’katarsa za ta biya a kanki.
Domin gujewa hakan ya kamata kike lura da irin
kalaman da yawanci ke futa daga bakinsu, kike
tace na gaskiya da kuma na ‘karya.

Karda SO ya
rufe miki ido ki gaza tabbatarwa da zuciyarki
wane yaudararki kawai yake son yi, bayan kin
gano hakan ko alamun hakan sun bayyana
‘karara a zahiri, saboda gudun yin da-na-sani
daga baya.

Wanka da gari dai ba ya maganin
yunwa.

Source: MURYAR HAUSA24
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user