Sunday 25 February 2018

CIKAKKEN TARIHIN DR. ZAKIR NAIK: ME YASA SUKE SON SU KASHE DR. ZAKIR NAIK? Waye wannan Dr Zakir Naik ɗin??

Tura Wannan Zuwa
Cikakken sunansa shine Zakir Abdulkareem Naik.

Biography of Dr. Zakir Naik

TAKAITACCEN TARIHIN RAYUWARSA


An haife shi a ranar 18 Oct. 1965 a birnin India
na Mumbai a Maharashtra.

Zakir ya hallaci makarantu da dama inda ya
samu shaidar zama likitan tiyata wato "Bachelor
of Medicine and Surgery".

Zakir Naik na tare da mai dakinsa Farhat Naik, da
kuma 'yaya biyu Fariq Naik da Rushdaa Naik.
Zakir Naik ya tsinci kansa cikin sahun masu
Da'awah a shekarar 1991, lokacin da Muslunci ya
tsinci kansa cikin tsangwama da muwiyacin hali
a
kasar India saboda gallazawar da masu addinin
Hindu kewa Muslunci da Musulmi.

Biography of Dr. Zakir Naik

Zakir ya tasirantu ne da salon da'awar sannanen
malam nan wato Sheikh Ahmad Deedat wanda
Zakir ya hadu dashi a shekarar 1987, kamar
yadda Naik na sheda a 2006, saboda tarin baiwa
ta ilimi da Allah yayiwa Zakir yasa Deedat da
kansa yake masa lakabi da "Deedat-Plus" wato
kamar kace, "Malam da rabin Malam".

Biography of Dr. Zakir Naik

RUGUZA MASALLACIN BABRI

A shekarar 1992 wani muhimmin al'amari ya
faru.

A ranar 6, ga watan Disamba, na shekarar 1992,
masu bin addinin Hindu kimanin 150,000 da
taimakon jam'iyun siyasa na India; Bharatya
Janata Party (BJP) da Vishva Hindu Parishad
(VHP) suka afkawa gami da rugurguza Masjid
(masallacin) Babri mai dadden tarihi a cikin garin
Ayodhya bayan haka suka ruguje masallatai
masu
yawa a yankin, masallacin Babri an gina shine
tun
qarni na 16 kimanin shekaru 500 da suka wuce.
Rushe masallacin ya jawo gagarumar riga wadda
tayi sanadiyar asarar dukiyoyi masu tarin yawa
da kuma mutuwar mutane fiye 2,000 wadanda
yawancinsu Musulmi ne.

Hakika wannan rigima ta kara jefa Musulman
India cikin halin ha'ula'i, zullumi da kaskanci,
suka zamo basu da wata ta cewa, Muslunci ya
zama abin zolaya gami da tsokana.
Ana cikin wannan hali ne, Allah yayi nufin dawo
da martabar Muslunci da Musulmi ta hannun
Sheikh Dr. Zakir Naik, kamar yadda Muhammad
Reyaz ya sheda.

Biography of Dr. Zakir Naik

DEBATES DINSA

Dr. Zakir ya fara mahawararsa (debate) ta farko
a 1994 kan wani littafi mai suna "Lajja" wanda
wata mashahuriyar mai aibata muslunci Taslima
Nasreen 'yar kasar Bangladesh ta wallafa.
Haka a shekarar 2000, Zakir yayi mahawara da
sanannen masanin kimiyar nan Dr. William
Campbell a birnin Chicago ta Amurika. Campbell
ya kwashe shekaru yana nazari kafin daga bisani
ya wallafa wani littafi da yace Qur'an yaci karo
da kimiyar zamani (modern science). Muhawarar
mai taken "The Qur'an and the Bible in the Light
of Science" ta daukaka Naik saboda yadda yayi
kaca-kaca da littafin da aka dau shekaru ana
wallafa shi da hujja cikin kankanin lokaci, hakan
yasa Zakir ya zama abin tsoro tsakanin masu
yiwa Muslunci zambo, kamar su Ali Sina wani
dan
asalin Iran mai tsananin adawa da Muslunci.

Zakir Naik wanda zaka iya kwatanta
kwakwalwarsa data "computer" saboda kaifin rike
abu, ya gudanar da lakcoci kusan 4000 a fadin
duniya baki daya wanda ya hada da zuwansa
Nigeria har sau biyu.

Biography of Dr. Zakir Naik

NASARORINSA

A bisa kokari irin nasa Zakir ya samar da:
i, tashoshin satellite na Peace TV English, Peace
TV Bangla, Peace TV Urdu da kuma Peace TV
Chinese. Tashoshin wadanda babu kamar su
wajen yada addini, kimanin mutane miliyan 150
ne suke iya kama Peace TV a kasashe fiye da
200.
Zakir Naik ya samar gami da jagorantar;
ii, "Islamic Research Foundation" (IRF) wato
cibiyar bincike ta addinin Muslunci, a karkashin
IRF aka samar da (IIS) wato "Islamic
International
School".
iii, Sai kuma (UIA) "United Islamic Aid" wadda
aikinta shine bada tallafin karatu ga nakasassu
da masu rauni.

Irin wannan nasarori da Zakir Naik ya samu, gami
da dawo da martabar Musulmai a India dama
duniya baki daya, sune suka tsone idanun
munafukai musamman masu son gani bayan
Muslunci, tako wace fuska.

Gazawar masu son ganin bayan Muslunci a
sakamakon Zakir, yasa suke kokarin ganin
bayansa, ta hanyar tsomashi cikin ayyukan
ta'addanci, zargin da ako yaushe yake musawa
Karku manta jam'iyar Bharatya Janata Party
(BJP) wacce ta taka rawa wajen gallazawa
Musulman India itace ke mulki yanzu. Kuma
Prime Minister na yanzu Narendra Modi babban
yaron Lal Krishna Advani ne, wanda ya jagoranci
ruguza masallatan Ayodhya a 1992. Saboda haka
babu mamaki cikin sabon salon rufe bakin
Musulmai ta hanyar gamawa da Zakir Naik a
farko.

Biography of Dr. Zakir Naik

MUSULMAI MASU ADAWA DASHI

Yawancin masu adawa Zakir Musulmai 'yan Shi'a
ne, suna zarginsa da rashin yin biyayya ga
dokokin zamantakewa na India daga cikinsu
akwai:
Kalbe Jawad Naqvi da kuma Yasoob Abbas dss.
Amma yawancin qungiyoyin musulmai na mara
masa baya kamar su: Sheikh Abdulkadir Jilani
Foundation, Darul Uloom da kuma All-India Sunni
Board.

Biography of Dr. Zakir Naik


BARAZANA GA RAYUWARSA

A ranar 13 ga watan Juli 2016 shugabar Vishva
Hindu Parishad (VHP) wato Sadhvi ya bada
sanarwar bada tukyici na dalar Amurika $78,000
ga duk wanda ya fillo kan Zakir Naik. Hakan yazo
kwana daya bayan wata kungiyar Shi'a maiwa
kanta laqbi da Hussaini Tigers. ta sanya ladan
$23,000 ga wanda ya kashe Zakir Naik.

Biography of Dr. Zakir Naik

DAUKAKARSA

Zakir ya sami zama mutum na 89 cikin mutane
100 dake da karfin fada aji a India kasar dake da
mutane fiye da biliyan daya da miliyan dari uku.
(1.3 bn) ya sake zama na 82 a shekarar 2010
kamar yadda The Indian Express ta sanar.

Yanzu haka yana gudun hijra a kasar da ba'a
gano ba.

Allah ya kareshi ya karowa Muslunci wadanda
suka fishi ameen.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com 

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki Mungode


TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user