Thursday 1 March 2018

Karanta Kaji: Ko me Yasa Mansura Isah ta Zabi Aure akan Yin Films?

Tura Wannan Zuwa
Hajiya Mansurah Isah, fitacciya ce a fagen finafinan Hausa kafin ta yi bankwana ta shige dakin aure.
Tana daya daga cikin matan da aurensu ya dore a cikin mata ‘yan fim da suka yi aure. Wannan ya sa Adon Gari ya yi tattaki na musamman zuwa wurin Mansurah Isah domin jin yadda take gudanar da rayuwarta a gidan aure bayan ta bar fagen fim. Kodayake ta ce ba ta bari ba, har yanzu akwai wasu abubuwa na fim da take yi.
Hakazalika ta bayyana yadda ‘yan gulma suka so su kashe mata aure tun tana amarya a gidan Angonta, Alhaji Sani Musa Danja.
Haka nan, ta shimfida wa mata marasa sana’a kyakkyawar turbar da za su bi domin gyara yanayin jindadin rayuwarsu ko da ta Allah za ta kasance idan maigida ya riga uwargida rasuwa.
Wannan da sauran tsaraba duk suna kunshe a cikin tattaunawar kamar haka:
Zai yi wahala a ambaci sunanki mutane ba su fahimci wace ce ake nufi ba, amma duk da haka ki fara fada wa masu karatu cikakken sunanki tare da bayyana salsalarki da kuma takaitaccen tarihin rayuwarki… .
Assalamu alaikum. Sunana Mansurah Isah wacce aka fi sani da ‘Mansy’, (sunan da aka sanni da shi a makaranta ke nan). Sunana Mansurah Isah kamar yadda galibi kuka sani, mahaifina marigayi Alhaji Isah Naira da Kobo. Ya rasu shekara 4 zuwa 5 da suka wuce.
Sunan mahaifiyata Hajiya Halima Abdulwahab, mu tara (9) mahaifiyata ta Haifa. Ni ce `yar auta. Biyu a ciki sun rasu (Alhaji Isiyaku Baba Lipsy da Hajiya Maimuna Iya Akwara). Sun rasu sun bar yara 10. Mu bakwai muke da rai yanzu (Hajiya Kuburah, Hajiya Mai Jidda, Abdulrafi’u, Hajiya Razika, Jibril GG Power, Muhammad Rabi’u Amage, sai ni yar auta Mansurah Isah, (a gidanmu auta ake kira na).
Na fara makarantar furamare a Samadi, sai wata rana direba bai zo ya dauke ni ba, sai na fito daga makaranta na bata, shi ne aka cire ni daga makarantar aka mai da ni ta kusa da gida a ‘Children Day Nursery and Primary School’.  Daga nan na je kawai Kwaleji ‘yan mata na yi aji 1 da 2, daga nan sai aka mai da ni ‘Kings College Normans Land’ na yi aji 3. Daga nan na je ‘Face Staff School’ na yi aji 4 zuwa 6. Daga nan na fara zuwa koyan haddar Kur’ani a ‘BUK tsohon mazauni, da yake na yi sauka ta farko a Makarantar ‘Nurudeen Society’ da ke Sabon Gari. Daga nan na fara ‘Diploma’ a BUK ,ina karanta tsarin Manhajar makarantu daga nan na fara digiri a jami’ar Abuja inda na karanta Kimiyar siyasa. Na kammala karatun a halin yanzu, ina kokarin fara digiri na biyu insha Allahu.
Yanzu kina karatu ne ko kina aiki ko kuma kin ci gaba da harkar fim din ne bayan aurenki?
Shekarata uku a fagen Fim na yi aure, na auri wani shahararren jarumi, Sani Musa Danja. Shekara 10 a gidan miji ina da yara hudu 4 (Khadija, Khalifa, Sultan and Sudais Sani Danja). A rayuwar aure akwai kalubale, sai dai addua’ar dangi da sauran jama’a tare da soyayya da aminci da tsakaninku su ke ba ka kwaringuiwa. Na zama abin kwatance ce, domin ina tallafa wa al’umma a halin yanzu, sannan ina jin dadi yadda nake yi saboda na yi Imani da hakan shi ne ribar rayuwa.
Malama Mansura Sani Danja ko za ki fada mana yadda kike iya tafiyar da harkar gidauniyarki da kula da iyali a lokaci guda?
Ni na kafa ‘Gidauniyar Rayuwa A Yau’ kuma ni nake jagorantar ta. A wannan gidauniya muna taimaka wa marasa karfi da marayu da zawarawa. Idan muka hadu da matsalar da ta fi karfinmu mukan nemi taimako daga jama’a ta hanyar turawa a dandalin sadarwarmu. Ya zuwa yanzu muna samun taimako daga Rukunin Kamfanoni Dangote, suna ba mu sukari, gishiri, taliya muna raba wa zawarawa. Kana iya ganin hotuna da bidiyo a shafukanmu na ‘Instagram’ da ‘facebook’ ‘@today life Fuondation’.
Wasu mutane sukan kira mu su nuna goyon baya ga ayyukanmu kuma suna ba mu gudummawa, muna godiya kwarai. Kin san an ce duk abin da mutum yake yi a duniya in har yana da masu goyon bayanshi to inshaa Allahu zai yi nasara.
Alhamdu lillah ina da miji mai kyakkyawar fahimta wanda koda yaushe yake ba ni kwarin guiwa. Kodayaushe yakan ba ni shawarwari tare da nuna min irin alherin da ke tattare da abin da nake yi. Ni ko ina jin dadi hakan da yake man. Farkon aurenmu mutane sun yi kiraye kiraye da turo masa tes, cewa wai, ba zama zan yi ba. Amma yau da gobe ta karyata su, Bayan kaikomo na aurnenmu gashi har yanzu muna tare. Kuma ina kaunarsa. Wannan ya sa shi kuma kullum yake karfafa ni. Kuma wannan ne dalilin da ya sa gidauniyata take habaka cikin gaggawa.
Mu dawo fagen fim, shin kina da sha’awar komawa harkar fim, koda a matsayin Mai shiryawa ce?
Mai shiryawa ba matsala, ba wani abu mai wahala ba ne, kudinki ne zai yi aiki ba ke ba. Domin ko a yanzu ina rubuta ‘wasan’, ina fitarwa kuma ina ba da kayan kwalliya na fim. Yanzu haka ina neman shago da zan bude, insha Allahu in rika ba da kayan kwalliya na fim.
Mene ne dalilin da ya sa kika zabi aikin Tallafi akan aikin ofis alhalin kin yi karatu sosai?
Ba wani dalilin, aikin Tallafi ba zai taba aikin ofis ba. Ban zabi Tallafi a kan ofis ba, domin ko an ba ni albashi a kan taimako yake karewa. Daya na da bukatar dayan.
A karshe muna so ki yi kira ga mata marasa son tashi su nemi na kansu?
Duk macen da ta ki tashi ta nemi na kanta. To lallai tana cike da damuwa. Domin ba kasafai mu mata muke son tambayar namiji kudi ba. Shi kuma namiji ba kasaife yake son taimaka wa matarsa ba.
Musamman mazanmu na yanzu. Daga wani namijin ya ga matarsa ta fara samun kudi fiye da nashi. Sai su fara bakin ciki da yawan masifa a cikin gida. Dan haka za ku ga miji ya mutu ya bar matarsa da yara suna bara a kan titi, dan bai gina su ba kafin ya mutu.
Ba wanda ya san gawar fari. In mace ta nemi aikin to, za ta taimaka wa yaranta da gidanta za ta kula da dukiyar da kyau. Ko bayan ranka ba za su shiga wani yanayi.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu
Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Muryarhausa24.com don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum
An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri
Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke
KARIN BAYANI
Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@gmail.com mungode
Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki
daya Amin Summa Amin.
Source by  ©Hausaleadership
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user