Thursday 6 June 2019

ALLAHU AKBAR: KARANTA LABARI MAI SOSA ZUCIYAR DUK WANI MAI IMANI

Tura Wannan Zuwa
Anyi wani sarki ya kasance yana da bayi guda uku wadanda yafi ji dasu, wata rana sai yace musu su dauki buhu su tafi gidan gona su tsinko mishi kayan marmari.


Tuffa


Marubuci: Yusuf Æbdullâhi  Æ  Jibagâ



Sai kuwa kowa daga cikinsu ya dauki buhunsa suka shiga gidan gona, guda daga cikinsu sai ya fada a ranshi cewa sarki yafi son nunannu dan haka sai yacika buhunshi da kayan marmari nunannu.

Na biyun kuma ya cika nasa da ɗanyu waɗanda basu riga sun kosa ba.


Amma na ukun kuwa saboda shegantaka sai yacika buhunshi da ganyaye da ciyawa.


Kowa sai ya dauko nashi, gasu nan har wajen sarki, suka zube a gaban sarki koda sarki yaga abinda kowa ya debo....sai abin ya fusata shi yace ni zaku yiwa shakiyanci.


Nan take yasa aka daure su a kurkuku su duka ukun sannan kuma yace baza'a ba kowa abinci ba sai dai kowa yaci abinda ya debo.


Tofa shi wanda ya ɗebo nunannu yana ta murna, domin yasan cewa shi masu kyau ya ɗebo dan haka shi kam bashi da matsala....


Amma wanda ya debo ɗanyu da wanda ya debo ganyaye kuwa sai nadama suke, domin sun san cewa ba abun alkhairi suka debo ba.


DARASIN LABARIN DAI SHINE....


Duk abinda ka shuka shi zaka girba, ko alkhairi ko sharri, kamar yadda kaga misalin bayin nan guda uku to haka misalin rayuwar duniya take kowa yana aikata aikinsa wani na alkhairi wani kuwa na sharri.


Kurkukun nan kuwa misalin kabari kenan, duk abinda kazo dashi shi zaka tarar, in alkhairi ne to farin ciki ya same ka, in kuwa sharri kazo dashi bakin ciki ya same ka.


Ya Allah ka tsarkake zuciyar mu, don samun kyautatuwar ayyukanmu, sannan kuma kasa muje kabarinmu da ayyuka kyawawa domin tsira daga azabar kabari Amin.



Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode






TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user