Saturday, 29 June 2019

Wata Sabuwa: Ana Zargin Mawaki Nura M. Inuwa Dacin Hakkin Al'umma

Tura Wannan Zuwa
Fitaccen mawaki a masana'antar shirya fina-finan Hausa (KANNYWOOD) Nura M. Inuwa ana zargin sa da cin hakkin wasu mutane.
Nura M Inuwa ya wallafa wani bidiyo a shafin sa na sada zumunta, a cikin bidiyon mawakin ya mika godiyar sa ga ilahirin masoyan sa maza da mata a wasan Sallah da ya gabatar na karamar Sallah ga  masoyan sa.
Bayan wallafa wannan bidiyo ne sai wani mawaki mai tasowa Ali Prince Amir wanda yake da burin shahara yayi wa Nura M. Inuwa Raddi mai zafi.Ali Prince Amir yace "Ka dinga tinawa da mu ka karɓi hakkin mu amma kamar hakan bai dame ka ba".

Inda nan take  mawakin ya mayar masa da martani "Hakkin ka na karba mai naci maka? ".

Nura M. Inuwa ne yayi masa tambaya.
Ali Prince Amir ya kara da Cewa "Naji daɗin wannan tambayar, idan zaka tuna shekarun baya wasu marubuta sun zo wajen ka daga garin Gombe sun turo maka da scrift, ka karɓa kace zaka duba sannan ka ba Hajiya ta duba, tun daga wannan lokacin ka daina ɗaga wayar mu kuma ganin kayi hakan mu  haɗa akwai da babu mu kazo kano wajen ka akan hakan sai kace mana wai zaka neme mu , haka mu koma garin mu har yau abun yana kona mana rai ace wanda muka yarda dashi muna masoyan sa yayi mana haka."

A karshe Nura M. Inuwa ya saki bidiyo akan zargin da ake yi masa , bidiyon wanda ya dauki hankula a kafafen sada zumunta na yanar gizo.

Kalli Bidiyon Kai Tsaye...

A ciikin jawabin da Nura M. Inuwa ya yi a wannan bidiyon mai dan takaitaccen zango yayi Allah ya isa ga duk wanda yayi masa sharri.

Nura M. Inuwa yayi sharhi inda yace wa wani mabiyin sa wanda ya gasgata furucin mutumin dake zargin Nura M. Inuwa dacin Hakkin su Cewa "Bansan kaba ban kuma taɓa ganin kaba amma ina roƙon Allah ya tsai damu ranar  ƙiyama domin kaba da shaida akan abunda ka faɗa".
Wanda yake zargin Nura M. Inuwa dacin hakkin su a karshe yace "Nura ashe a masoyan naka akwai mahaukata bansani ba sai yau..".Kusan zamu iya Cewa "Wannan shine karo na farko da Duniya taji wani yayi wa mawakin zargi".

Kasancewar anyi masa Shaida wajen Hakuri da iya zama da Mutane.


Sharhi

Wasu daga cikin masoyan Nura M. Inuwa sun bashi hakuri akan ya daina kula irin wadannan mutanen.
Yayin da wasu kuma suka yi masa Shaidar mutumin kirki ne.Wasu daga cikin masoyan Nura M. Inuwa sun bashi shawara mai muhimmanci.

Sharhi

Harzuwa yanzu da wakilin Muryar Hausa24  yake haɗa wannan rahoto babu wani kwakkwaran dalili da kai tsaye za'a iya gasgata zargin da ake yiwa fitaccen mawakin.

KARANTA TAKAITACCEN TARIHIN NURA M. INUWA 

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user