Friday 18 October 2019

KARANTA YADDA LITTAFIN BIBLE YA TABBATAR DA ANNABTAR ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)

Tura Wannan Zuwa Ga
An shafe shekaru masu yawa kiristoci na yiwa littafinsu kwaskwarima, amma sun kasa cire ayoyin dake tabbatar da annabtar Manzonmu masoyinmu S.A.W cikin littafin nasu, amma baƙar ƙiyayya da hassada gami da son zuciya ke hanasu karban gaskiya, wannan ba abun mamaki bane dama Allah yayi alƙawarin cika wutar jahannama da mutane da Aljanu baki daya.


Injila (Bible)Marubuci: Aliyu Imam Indabawa

An sami ayoyi masu tarin yawa daga Bible wanda suke rushe maganganun kiristoci akan Manzon Allah S.A.W tare da tabbatar da gaskiyarshi ta annabta. Su dai kiristoci suna raya cewa babu wani Annabi da zai zo bayan Annabi Yesu wanda littafinsu bible ya ƙaryata hakan.

Misali kamar Deuteronomy 18:18 bible yace wai Allah yace"

18:18 I will raise them up a Prophet from among their brethren, like unto thee, and will put my words in his mouth; and he shall speak unto them all that I shall command him."

"Zan tayar musu da wani Annabi daga cikin ƴan uwansu, kamar kai.(Yesu) Zan saka kalmomina cikin bakinshi, sannan zai yi magana zuwa garesu ga duk abinda na umarce shi."

Wannan ayar tana nuna abubuwa guda biyu, abu na farko Yesu A.S Annabi ne ba Allah ko ɗan Allah ba kamar yadda kiristoci ke ikrari, abu na biyu tana nuna samun Annabi Muhammad bayan Annabi Yesu.

Hallau dai bible ya cigaba da cewa wai Allah yace"

18:20 But the prophet, which shall presume to speak a word in my name, which I have not commanded him to speak, or that shall speak in the name of other gods, even that prophet shall die."

"Amma Annabin da zai yi shigar burtu yana basaja yana magana da yawuna  bayan ban umarce shi ba, ko wanda zai fake da gumaka tofa lallai wannan annabin karyar sunanshi matacce"

Idan muka nazarci wannan ayar bible ya bamu labari duk wani annabin ƙarya bazai sami nasara ba, mutuwa zayyi, shi kuwa masoyinmu S.A.W be koma ga Ubangijinsa ba sai da addinin musulunci ya yaɗu a ban ƙasa. Wannan ke nuna Manzon Allah Annabin Gaskiya ne bana ƙarya ba.

Akwai wata shubuha da kiristoci ke amfani da ita wajen ɓatanci wa risalar Manzo S.A.W cewa wai tunda ake annabawa ƴan Isra'ila ake aikowa, me yasa Annabi Muhammad S.A.W zai zama Annabi bayan shi balarabe ne ɗan makka? Bible yayi kaca-kaca da wannan shubuha tasu, bari muje Matthew 21:43 muji abinda bible ya fada"

21:43 Therefore say I unto you, The kingdom of God shall be taken from you, and given to a nation bringing forth the fruits thereof."

Yesu ke cewa" Saboda haka ni ina faɗa muku za'a karbe sarautar Allah daga wajenku a baiwa wata ƙasa wacce zata baiwa duniya alkhairi mai yawa"

Ba wannan kaɗai ba an sami maganganu akan kasar makka da yawa cikin bible zanyi rubutu akan hakan zuwa gaba Inshallah.

har ila yau dai Cikin tabbatar da annabatar Manzo an samu a  gospel of John 14:16 Bible yace"

14:16 And I will pray the Father, and he shall give you another Comforter, that he may abide with you for ever.

Yesu ke cewa" Zan roƙi Allah ya aiko muku da wani mai taimakon (bayan ni) wanda zai kasance tare daku har abada"

Wannan ayar tana nuna Manzon Allah ne wannan mai taimako, domin addininshi ne zai kasance ga masu imani har zuwa tashin qiyama, babu wani manzo da zaizo bayanshi.

Sannan dai gospel of John 14:26 ta kara fassara wannan ayar ta sama cewa"

14:26 But the Comforter, which is the Holy Ghost, whom the Father will send in my name, he shall teach you all things, and bring all things to your remembrance, whatsoever I have said unto you."

"Amma shi wannan me taimako wanda yake rai mai tsarki da Allah zai aiko zai koya muku dukkan komai, kuma zai tunatar daku dukkan abubuwan dana faɗa muku"

Haka nan idan muka koma gospel of  John 16:7 zamu ga yadda Yesu AS kewa mutanenshi bayanin wannan me taimakon. Inda akace"

16:7 Nevertheless I tell you the truth; It is expedient for you that I go away: for if I go not away, the Comforter will not come unto you; but if I depart, I will send him unto you."

"Duk da haka ina faɗa muku gaskiya, zaifi muku alkhairi na tafi, don idan har ban tafi ba, bazai zo ba, amma idan raina ya tashi, zan aiko muku shi"

Sai ayar gaba ta ƙara bayyana ainihin wannan mutumi ba kowa bane sai Annabi Muhammad S.A.W bisa ga abinda da bible gospel of John 16:8 ya bada labari wannan mutumi zai aiwatar.

"16:8 And when he is come, he will reprove the world of sin, and of righteousness, and of judgment:"

"A loton da yazo zai tsawatarwa duniya game da aikata zunubi, zai tabbatar da adalci da hukunci."

Aya ta 12 zuwa ta 14 ta kara bayani kan zuwan wannan mutumi. Inda tace"

16:12 I have yet many things to say unto you, but ye cannot bear them now."

Yesu AS yace" Har yanzu inada abubuwan faɗi a gareku, sai dai ba zaku iya ɗaukansu a halin yanzu ba"

16:13 Howbeit when he, the Spirit of truth, is come, he will guide you into all truth: for he shall not speak of himself; but whatsoever he shall hear, that shall he speak: and he will shew you things to come.

"Koda yake lokacin da ruhin na gaskiya yazo zai shiryar daku zuwa gaskiya, bazai magana don kanshi ba, sai abinda aka mishi wahayi shi zai faɗa, zai sanar daku abubuwan da zasu faru a gaba."

Kunji bible ma yace Annabi baya furuci akan son zuciya sai abinda aka saukar masa. Sadakallahu azeem
 وما ينطق عن الهوى* إن هو إلا وهي يوحى.

Sai dai kash bayan zuwan wannan mutumi mai daraja da Annabi Yesu A.S ya sanar da mutanensa sai sukayi watsi da maganar Yesu.
Wannan yasa Allah ke cewa a suratul baqara"
ﻭﻟﻤﺎ ﺟﺎﺀﻫﻢ ﺭﺳﻮﻝ ﻣﻦ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﺼﺪﻕ ﻟﻤﺎ ﻣﻌﻬﻢ ﻧﺒﺬ ﻓﺮﻳﻖ ﻣﻦ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺃﻭﺗﻮﺍ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺍﺀ ﻇﻬﻮﺭﻫﻢ ﻛﺄﻧﻬﻢ ﻻ ﻳﻌﻠﻤﻮﻥ"

"A lokacin da Manzo daga Allah yazo musu yana mai gasgata abinda littafinsu wasun su sai sukai watsi da littafin Allah kamar basu sani ba"

Idan muka duba ƙissar da bible ya kawo ta Yahudawa da Annabi John (Yahaya) har suke tambayarshi ko shine wannan Manzon na ƙarshen zamani, gashi kamar yadda Bible ya kawo:"

1:19 And this is the record of John, when the Jews sent priests and Levites from Jerusalem to ask him, Who art thou?

Wannan shine tarihin Yahaya, a yayin da yahudawa suka aiki faada da kuma mutanen Hebrew daga Jerusalem su tambaye shi wane shi.

1:20 And he confessed, and denied not; but confessed, I am not the Christ.

"Ya fada musu gaskiya be musu jayyaya ba, yace bashi ne Yesu Almasihu ba."

1:21 And they asked him, What then? Art thou Elias? And he saith, I am not. Art thou that prophet? And he answered am not.

Suka tambaye shi ko kaine iliyasu? Yace a'a. Ko kaine wannan annabin ?  Yace a'a.

Babu wani Annabi da suka tambaya Sai Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam domin Yahudawa sun san da zuwanshi suka ƙi yarda dashi saboda son zuciya.

Yazo a bible Acts 3:22 an rawaito Annabi musa nayi wa mutanensa wasicin zuwan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam inda akace"

3:22 For Moses truly said unto the fathers, A prophet shall the Lord your God raise up unto you of your brethren, like unto me; him shall ye hear in all things whatsoever he shall say unto you."

"Hakika Annabi Musa ya faɗa Allah zai tasar muku da wani Annabi kamar yadda ya tasheni daga cikin ƴan uwanku, wajibi ne ku saurari duk abinda zai faɗa muku"

Idan muka koma Song of Solomon 5:9-16  an wassafa siffofin wannan me taimako wanda siffofin sukai dai-dai da siffofin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam.

Zan tsaya haka ba don hujja ta ƙare ba, amma hakika ina tausayawa kiristoci musamman ma'abota riko da addinin cikinsu, wallahi tallahi addininsu ba gaskiya bane, Yesu ba Allah bane, ba ɗan Allah bane. Annabi ne kamar Sauran annabawa duka bible ya tabbatar da wannan, haka nan Bible ya tabbatar da annabatar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam ya goyi bayan shari'arshi wannan yasa duk kiristan dake neman gaskiya indai zai karanta bible da idon basira zai musulunta insha Allah domin musulmai sune kan gaba wajen amfani da abinda bible ya faɗa.

Wajen muqabala da kirista kada ka wahalar da kanka wajen kawo masa hadisi ko aya, bible din da yayi imani dashi kaɗai ya isheka hujja. Bible Hujja ce a kansu ba a garesu ba. Sau tari idan ina karanta bible nakance a zuciyata babu wanda zai san bible yaci gaba da addinin kiristanci sai ɗan son zuciya ɓatacce, lallai akwai abin tausayi ga yawan kiristoci domin basu fahimci addinin ba, basa karanta bible balle su gane, yana da kyau musulmai mu tashi tsaye wajen karanta bible tare da tadabburin ayoyinshi domin ganin mun ceto wadan nan mutane daga halakar da suke ciki ta kafurci, wannan babban jihadi ne.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Dalilai 13 Da Suka Sa Na Musulunta- Inji Emmanuel Adebayo Dan Kwallon Kafa

SHIN KO KASAN ZA KA IYA SABAWA ALLAH AMMA DA SHARUDA GUDA BIYAR?

Karanta Yadda Za'a Tashi Al-Kiyama ta Hanyar Amfani da Hasken Rana tare da Ilimin dake Cikin Hasken Rana

Shin me kasani dangane da Takaitaccen Tarihin  Addinin Kirista? Shin me ne ne Alakar Addinin Kirista da Addinin Musulinci??

Kiristoci na ɗaukan Yahudawa ɓatattu kafurai saboda ƙin amincewa da Yesu da sukayi, amma su kuma kiristoci sunƙi amincewa da Annabin da littafinsu ya sanar dasu zuwansa, wannan ba komai bane sai ƙiyayya, zalunci da son zuciya.

"YA KU MA'ABOTA LITTAFI (KIRISTOCI/YAHUDAWA) KU ZO GA WANNAN KALMAR DA ZATA DAI-DAITA MU,  KADA MU BAUTAWA KOWA SAI ALLAH. KADA KU HAƊA KOWA DASHI. KADA SASHINKU YA RIƘI SASHI UBANGIJI. KU YARDA MUHAMMAD MANZON ALLAH NE, IDAN KUKA ƘI TO KU SHAIDA MU MUSULMAI NE."  -QUR'AN

Allah Ya shiryi masu rabon cikinsu.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user