Tuesday 16 January 2018

Karanta Kaji Ma'aurata: Maganin karin karfin mazakuta

Tura Wannan Zuwa Ga

Gabatarwa

Assalamu'alaikum, kamar kullum yau ma barkan ku da war haka.
Yau darasin mu zamu yi shi ne a kan magungunan karfin mazakuta don amsa tambayar wani bawan Allah da yai mana mai suna "Danmusa". Wannan yasa muka ce to ya kamata muyi Wannan rubutu domin kowa ya amfani.

Yadda za'a kara karfin mazakuta
Wassu daga cikin mazaje Zaka same su da matsalar rashin karfin mazakuta ta dalilin sanyi ko wani abu daban.

To ina shaida wa duk mai wannan matsala daga yau ta kau, indai har kabi hanyoyin da za mu amfani, sa'annan muna shaida muka cewar in kuna tare da shafin Lafiyata to baku da matsala.

Ga yadda za'ai a magance kamar haka:

¶ Ka rika cin giginya
¶ Ka nemi gabaruwa ka daka ta, sai ka zuba garin a cikin ruwa ka na sha.

¶ Ka nemi danyar albasa sa'annan ka samo man zaitun ka soya albasar da shi, har sai albasar ta fara yin ja, sa'annan ka samo danyen kwai sai ka hada shi da garin habbatussauda ka gauraya su.

Daga nan sai ka juye wannan danyen kwai da aka hada da habbatussauda a cikin albasa da aka soya ta da man zaitun a sake soya wa, har sai ya kai dai-dai soyuwa, kada a barshi ya kone sai a sauke shi in yai sanyi ana cin sa.

Insha Allah wadannan sun isheka, indai kai wadannan abubuwa da muka zayyano to bazaka ka kara kokawa ba.

Wassalam. Daga karshe kada ku manta. Kuna yi mana  share tare da gayyato abokanku don su amfani suma.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: