Showing posts with label Kagaggun Labarai. Show all posts
Showing posts with label Kagaggun Labarai. Show all posts

Wednesday, 20 November 2024

Labarin Wani Uba Mai Hikima Da Yaron Sa A Kasuwa

Labarin Wani Uba Mai Hikima Da Yaron Sa A Kasuwa

Labarin wani mahaifi mai hikima da ya yi niyyar koyawa ɗan sa ilimin rayuwa. A wata ranar asabar da safe bayan karin kumallo, da yake ranar ba makaranta, sai uban ya umarci yaron da ya shirya su fita kasuwa tare, yaro ya yi ta murna domin abun da ya daɗe yana fata kenan.


Labarin Wani Uba Mai Hikima Da Yaron Sa A Kasuwa 
Hoto: Stocke cake

Marubuci:- Abdulfatah Yakubu


Haka suka wuni a kasuwa ana ta hadahadar kasuwanci, babban aikin da uban ya ba yaron shi ne ya zauna ya sa ido akan yadda komai yake gudana, dare ya yi suka dawo gida, washegarin lahadi ma suka koma.


Ranar litinin da safe yaro ya shirya zai tafi makarantar boko, uban ya kira shi ya ce "Yau lafiya ba ka zo ka karɓi kuɗin makaranta ba?" Yaron ya ce "Baba ka bar shi na gode, kuɗin da ka ba ni na abincin jiya ma sun wadatar".


Uban ya cika da mamakin yadda tunanin yaron sa ya sauya lokaci ɗaya, yaro ya ci gaba da cewa "Baba ban taɓa sanin haka kake shan wahala wajen inganta rayuwar mu ba, iya zaman mu a kasuwa na kwana biyun nan na fahimci cewa duk wahalar da kake yi, kana yi ne domin inganta rayuwar mu, a irin wannan yanayi idan ba mu tausaya maka ba wa za mu tausayawa?"


DARASI


1. Hikima da dabara su suke tarbiyya ba tada jijiyoyin wuya ba. Aiki ne muhimmi ga mai tarbiyya ya sa hikima da dabara wajen tarbiyyantar abun tarbiyyar sa. 


Masu hikima suka ce "Mutumin da ya san kansa cikin ruwan sanyi yake dafa ganda".


2. Mahaifan ka su ne ƙashin bayan nasarar ka, domin su ne kaɗai za su iya haƙura da jin daɗin rayuwar su domin inganta rayuwar ka da ta ƙannen ka.


3. Mafi girman sakamako ga wanda ya kyautata shi ne a kyautata masa, koda yanzu ba ka da halin taimakon iyayen ka, to ka sani za ka iya taimakon su ta hanyar rage musu nauye-nauyen ka.

Sunday, 17 November 2024

Labarin Wani Malami Da Yaro Mai Kaifin Basira

Labarin Wani Malami Da Yaro Mai Kaifin Basira

Wani malami yana koya wa wani yaro ɗan shekara 6 lissafi, malamin ya tambayi yaron, "Yanzu idan na ba ka goruba ɗaya, na ƙara maka ɗaya, na sake ƙara maka ɗaya, sun zama nawa?" 


Labarin Wani Malami Da Yaro Mai Kaifin Basira
Hoto: BradWynnyk/iStock photo

Marubuci:- Yahaya Bala


Kafin ƙiftawar ido, yaron ya ce, "Huɗu!" 


Da jin wannan amsa, sai malamin ya ɗan ɓata rai. Ta yaya kuma zai ce "huɗu", bayan amsar uku ce? Malamin ya sake cewa, "Ka saurare ni da kyau, ka ji. Tambaya ce mai sauƙi. Cewa na yi, idan na ba ka goruba ɗaya, na ƙara maka ɗaya, na sake ƙara maka ɗaya, sun zama nawa?".


Yaron ya yi amfani da yatsun hanunsa ya lissafa. Ya sake ba da amsa da, "Huɗu". 


Malam ya hasala tare da ƙura wa yaron ido cikin takaici.


Yaron a ransa ya ce, to yanzu wace amsa zan ba wa malam ya yarda har ya ji daɗi? Yaron ya sake cewa, "Huɗu". 


Ƙarshe dai malamin ya je ya nemo goruba har guda uku, ya kawo gaban yaron ya ajiye yana miƙa masa ɗaya bayan ɗaya yana ƙirgawa dalla-dalla har ya gama, sai ya sake ce wa malamin, "Huɗu kenan!" 


Malamin ya zare wa yaron ido ya ce, "Ha'a! Kai wane irin yaro ne? Ta yaya amsar ta zama huɗu?" 


Yaron ya firgita, cikin muryar tsoro ya ce, "Saboda ai ina da goruba ɗaya a cikin jakata. Idan na haɗa da waɗanda ka ban sun zama huɗu." 


Darasi


Idan wani ya ba ka amsa ko martani saɓanin abun da kake tsammani, to ba lallai ne ya zama kuskure ba. Wataƙila, ya fahimci abun da kai ba ka hango ba. Saboda haka, ka nemi ƙarin bayani domin a fitar da jaki daga duma.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum.

Thursday, 19 September 2024

Karanta Labarin Jaki Da Damisa Da Zaki

Karanta Labarin Jaki Da Damisa Da Zaki

Gardama ta murtuƙe tsakanin Jaki da Damisa har abin ya kai su ga ɓacin rai. Suka yanke shawarar su je gun Manyan Dawa ya raba musu wannan tankiya.


Labarin Jaki Da Damisa Da Zaki
Hoto: Success minded

MarubuciBukar Mada


Da isarsu sai Jaki ya ce wa Zaki, "Allah ya ba ka nasara don Allah ka raba mana wannan rigima. Na ce wa Damisa ciyawa shuɗiya ce, ita kuma ta dage da cewa koriya ce. A cikinmu wa yake da gaskiya."


Zaki ya dubi Jaki ya ce, "kai ke da gaskiya."


Jaki ya yi tsalle ya buga ƙafa ƙasa ya fashe da dariya, ya harari Damisa ya ce, "to, ga shi nan, ba ki san komai ba sai rigimar banza." Ya hura hanci, ya runtuma a guje cikin daji yana hargowa tare da harbin iska cikin farin ciki.


Bayan ya tafi sai Damisa ta dubi Zaki ta ce, "Allah ya taimake ka, ciyawa fa koriya ce ba shuɗiya ba."


Zaki ya ce, "i, na sani. Ciyawa koriya ce."


Damisa ta ce, "to me ya sa ka ba Jaki gaskiya?"


Zaki ya ce, "bai kamata ga irinki mai ilimi da kwarjini ki tsaya ɓata lokaci wajen gardama da Jaki, wanda bai san inda kansa ke ciwo ba, ga shi garin sakacinki yana shirin raina ki. Sau da yawa wasu kan dage da gardama, ko da kuwa sun san gaskiya, amma su rufe ido dole dai sai an yarda da abin da suka ce. Babban sakarci kuma shi ne nuna sani a inda jahilci ya yanke cibi."


Damisa ta tafi tana jinjina maganar Manyan Dawa. Ta ga kuma lalle abin da ya faɗa gaskiya ne, sakacinta ya sa Jaki ke son raina ta har yana yi mata dariya.


Sai bango ya tsage ƙadangare ke samun wurin shiga. Ba za ta sake yin sakaci kamar wanda ta yi ba, domin kuwa sakaci ne ya sa injin niƙa ya kwance wa turmi zani a kasuwa.

Tuesday, 27 August 2024

Karanta Gajeren Labari Mai Daɗi Na Wani Bera Da Tarko

Karanta Gajeren Labari Mai Daɗi Na Wani Bera Da Tarko

Daga cikin raminsa, ɗan ɓeran na kallon sa'adda maigida ke ta cuku-cukun haɗa masa tarko. Da ya gama sai ɓera ya fito ya nufi wajen zakara a firgice ya ce, "abokina ka taimake ni, an sa mini tarko a gidan nan."


Gajeren Labari Mai Daɗi Na Wani Bera Da Tarko
Hoto: Do with the flow


MarubuciBukar Mada


Zakara ya kaɗa fiffike yai shewa ya ce, "ina ruwan maza da wankan jego? Me ya sha mini kai da tarkon da aka sa maka, ɓarnarka ce ta jawo maka."


Ɓera ya wuce wurin zomo ransa a ɓace ya ce, "ɗan uwana ka taimake ni, an ɗana mini tarko a gidan nan."


Zomo ya harare shi ya ce, "wane ne ɗan uwan naka? Kai dai nemi su jaɓa da gafiya."


Ɓera ya ce, "ko da ba jinsinmu ɗaya ba, ai dukkanmu dabbobi ne, ya kamata mu haɗa kai mu tunkari matsalar da ta doso ɗaya daga cikinmu."


Zomo ya ce, "wuce ka ba ni wuri! Maganinka ke nan ai, ɓuruntunka ne ya jawo. Idan jifa ta wuce kaina, to ta faɗa kan kowa ma."


Cikin takaici ɓera ya nufi wajen rago ya ce masa, "ɗan uwa ka taimake ni, an haƙa mini tarko."


Rago ya yi dariya ya ce, "af, to me ya haɗa kifi da kaska kuma? Kai, ni raba ni da zancen kawai, in ka ƙi ko yanzu ina murje ka! Tafi ba ni wuri."


Ɗan ɓeran nan ya koma cikin raminsa cike da taikaicin yadda sauran dabbobi suka baɗa masa ƙasa a ido. 


Can cikin dare sai aka ji kararaf! Tarko ya kama. 


Ɗan maigidan ya zabura da sauri ya fita don ya cire gawar ɓera daga tarkon. Ashe maciji ne ya jefa wutsiyarsa ciki. Yaro na zuwa maciji ya sare shi, aka ɗauke shi kamar tsumma sai asibiti. Ɗan nan kuwa shi ke nan, ƙwallin ƙwal, ga uban.


Da safiya ta yi, maigida ya sa aka kama zakara aka yi wa yaro dabge/farfesu/dage-dage.


Bayan kwana biyu kuma aka yi farfesun zomo, aka kai wa yaro ya sha lagwada.


Da aka sallami yaro daga asibiti, saboda farin ciki, uban ya sa aka murƙushe rago aka yanka, aka yi abinci aka raba wa maƙota sadaka.


Duk wannan kicimilli da aka yi a gidan, ɗan ɓeran nan na cikin raminsa kwance yana kallon ikon Allah. Ya ce a ransa, 'da sun taimake ni mun kawar da tarkon, da abin da ya faru duka bai faru ba. Matsalar da ta doshi ɗaya, za ta iya game duka.'

Friday, 9 August 2024

Labarin Wani Sarki Mai Hikima Da Yara

Labarin Wani Sarki Mai Hikima Da Yara

Kasancewar bai taɓa haihuwa ba, Sarki ya sa aka tara masa yaran ƙauyen duka domin ya zaɓi ɗaya da zai riƙa idan ya girma ya gaje shi. Da ya yi musu jarabawa, sai yara goma suka yi nasara. Ya ce wa yaran nan, "zan yi muku jarabawar ƙarshe wanda duk Allah ya sa ya ci, shi ne sarki bayan raina."


Sarki Mai Hikima Da Yara
Hoto: Wvi


MarubuciBukar Mada


Aka kawo ƙwayoyin masara, Sarki ya ba kowane yaro ƙwaya ɗaya, ya ce su shuka a cikin ƙoƙo bayan sati biyu su kawo ya ga wanda ya fi kulawa da nasa. Yara duk suka ruga gida suka shuka masara, suka yi ta tarairayar ɗan tsiron da ya fito.


Audu ya yi baƙin ciki ƙwarai da tasa shukar ba ta fito ba. Sauran yara suka ba shi shawara, ya samu wata ƙwayar masarar ya shuka. Iyayensa suka hana shi, suka ce, "kul! kai dai tsare gaskiyarka."


Bayan mako biyu yara suka taru a fada. Sarki ya fito yana duba tsiron kowa. Kowane yaro ya tambaya, "wannan ita ce ƙwayar da na ba ka?" Sai yaro ya gyaɗa kai. Da ya zo gun Audu, sai ya ga ƙoƙonsa babu komai. Ya tambaye shi me ya faru da tasa ƙwayar?


Audu ya sunkuyar da kai ya ce, "na shuka kamar yadda ka ce ya Sarki, ga shi tsawon mako biyu ba ta fito ba."


Sarki ya kama hannun Audu, ya ja shi har gaban karagarsa, ya ce wa mutane, "Ku sani cewa ƙwayoyin masarar da na ba yaran nan dafaffiya ce, babu kuwa yadda za a yi dafaffiyar ƙwaya ta tsiro. Wannan yaro shi kaɗai ne wanda ya tsare gaskiya da amanar da na ba su. Don haka shi ne magajina ko bayan raina. Ba abin da aka fi so ga shugaba irin tsare gaskiya da riƙon amana."

Monday, 29 July 2024

Labarin Wani Dalibi Da Malamin Jami'a

Labarin Wani Dalibi Da Malamin Jami'a

Shekaru goma sha biyu da suka wuce, lokacin da sakamakon ƙarshe na kammala digirinmu zai fito, duka 'yan ajinmu sun saki karin cewa ni ne ɗalibi na farko a tarihin Tsangayar Nazarin Kimiyyar Kwamfuta da zai fita da sakamako mai daraja ta ɗaya. To, amma sai ga ni da sakamako mai daraja ta biyu.


Wani Dalibi Da Malamin Jami'a
Hoto: Study Pug


MarubuciBukar Mada


Ban yi mamaki ba, saboda na sani sarai Dakta Irukefe na nan tamke da bakansa, muddin iska na zagaya huhunsa ba zai taɓa bari na zama wani abu ba. Kamar yadda ya taɓa ce mini, "sai na ga tsiyar da za ka zama a cikin ilmin kwamfuta!" 


Ba kuwa komai ya sa yake gani na da baƙin fenti ba sai don wani ɗan gyara da na taɓa yi masa yayin da yake yi mana lacca cikin aji. Ashe bai ji daɗin gyaran ba, wai na tozarta shi. Hatta bautar ƙasa da zan yi, sai da ya yi kutunguilar da aka tura ni jihar da ba ita na so zuwa ba. 


A cikin satinmu na ƙarshe a sansanin horar da 'yan bautar ƙasa wani mutum ya zo da kwamfuta yana neman wanda zai gyara masa. Na karɓa na gyara masa nan take. Ya yi godiya, ya karɓi lambar wayata ya tafi.


Ashe mutumin nan yaron Sanata ne, maigidansa ne ya aiko shi da kwamfutar. Saboda jin daɗin gyaran da na yi masa sai ya sa aka tura ni ofishinsa don yin bautar ƙasa. Nan take ya ɗauke ni aiki a matsayin mataimakinsa na musamman, ya yanka mini albashi. Aka ba ni gida da motar da zan riƙa zaga gari.


Bayan mun kammala bautar ƙasa, sai Sanatan nan ya riƙe ni. Ya samar mini tallafin ƙaro karatu a Turai na yi digiri na biyu na kuma yi digirin digirgir a kan sha'anin kwamfuta. Cikin shekaru goma sha biyun nan sunana ya yi tambari a ciki da wajen ƙasar nan, ko'ina sai kirana ake yi ina ba da lacca. 


Wata rana na gama ba da lacca a wani gangamin masana kwamfuta na duniya a ƙasar Japan. Na sauko daga kan mumbari sai na hangi tsohon malamina, Dakta Irukefe, a cikin mahalarta taron. Na nufi wurinsa na gaisar da shi, amma ya nuna sam bai gane ni ba. Na tuna masa da kalaman da ya taɓa yi min na ce, "ni ne ɗalibin da ka taɓa cewa, 'sai na ga tsiyar da za ka zama a cikin ilmin kwamfuta.'" Ya cika da mamaki. 


Na ci gaba da cewa, "ina ba ka shawara Malam, ka zama mai ƙarfafa wa ɗalibai gwiwa, kada ka zama mai cutar da su, domin ba ka san abin da za su zama ba a gaba. Ka ga dai yadda Allah ya ɗaukaka ni, duniya gaba ɗaya an san da ni ta ɓangaren kwamfuta.


Sannan abin da ba ka sani ba, ni na biya kuɗin da aka ɗauki nauyin zuwanka wannan taro. Kuma zan ci gaba da biya maka duk shekara, domin nuna maka godiyata a kan ƙoƙarinka na tura ni bautar ƙasa jihar da ta zama silar wannan ci gaban nawa, kodayake ba da niyyar alheri ka yi ba, amma Allah ya mayar da shi alheri gare ni." 


Ban jira ya ce wani abu ba, na yi gaba abina, na bar shi nan tsaye yana nazarin maganata. Daga baya ya turo mini da saƙo yana ba ni haƙuri.


Don haka, ɗan uwana, kada ka kula da sharrin mai sharri, kai dai yi aiki tuƙuru domin ganin ka cim ma burinka, arzikin duk da Allah ya ƙaddara wa bawa, babu mai iya tare shi. Sara da sassaƙa ba su hana wa gamji toho.


Godiya ga DR. Auwal Aminu Gezawa da ya aiko mini da wannan labari da Turanci. Na taƙaita na kuma fassara shi.

Monday, 15 July 2024

Labarin Wani Mutum A Teku

Labarin Wani Mutum A Teku

Lokacin da jirgin fataken ya fashe a tsakiyar teku, sai Allah ya yi wa ɗaya daga cikinsu gyaɗar dogo, ya riƙi wani ɓalgace na jirgin, iska ya yi ta ingiza shi, har ya kai shi bakin gaɓar wani tsibiri. Falke ya yi godiya ga Allah da ya kuɓutar da shi daga halaka. 


Wani Mutum A Teku 
Hoto: Quora


MarubuciBukar Mada


Ya zauna a wannan wuri, kullum yana roƙon Allah ya koro wani jirgin da zai fitar da shi daga wannan tsibiri. Wasa-wasa dai ya share watanni da yawa, babu jirgi babu alamunsa. Ya haƙa 'yar bukka wadda yake kwana ciki, kullum kuma sai ya fita neman abinci. Wani lokaci ya farauto ƙananan dabbobi irinsu zomo, kurege da batsiya, wani lokaci kuma ya yi su, ya kama kifi. Yana nan haka har ya fara sabawa, kullum kuwa yana kan addu'ar Allah ya fitar da shi wannan tsibiri. Tun yana tsammani Allah zai karɓi addu'arsa, har ya fara ɗebe tsammani.


Ran nan ya dawo daga neman abinci, sai ya tarar da 'yar bukkarsa na ci da wuta bal bal bal, hayaƙi kuwa ya turniƙe ya yi sama. Duk 'yan tarkacen da ya tara ciki suka ƙone, ban da suturar jikinsa bai tsira da komai ba. Nan take sai ya harzuƙa, Shaiɗan ya shiga zuciyarsa ya fara yi masa kururuwa. 


Falke ya ɗaga kai sama yana faɗin, "Allah laifin me na yi maka? Wata da watanni ina roƙon ka fisshe ni daga wannan wuri, babu wanda ka turo domin ya taimake ni. Ga shi kuma yanzu duk ɗan abin da na tanada a wannan wuri ya ƙone." Ya durƙusa a kan gwiwowinsa yana mai baƙin ciki, gayar baƙin ciki.


Yana cikin wannan hali sai ya hango wani abu daga nesa a kan ruwa kamar jirgi. Ya murje idonsa ya sake murjewa, ya ƙura wa abun nan ido. Da ya matso kusa sai ya ga lalle dai jirgi ne har da mutane ciki. Nan take zuciyarsa ta yi fari, ya manta da halin da yake ciki.


Da masu jirgi suka iso wurin shi, suka tambaye shi labarinsa, ya kwashe duk ya gaya musu. Suka ɗauke shi suka juya. Bayan sun miƙa cikin teku sai ya tambaye su yadda aka yi suka san yana wurin. Sai shugabansu ya ce hayaƙi suka hango daga nesa yana tashi, sun kuwa san duk inda hayaƙi yake to akwai mutum a wurin.


Falke ya yi wa Allah godiya, ya kuma nemi gafararsa a kan izgilin da ya tashi yi da fari. Ashe Allah ya yi nufin kuɓutar da shi ne, shi ya sa 'yar bukkarsa ta kama da wuta, hayaƙin nan da ya tashi sama shi ya jawo hankalin masu jirgin da ke wucewa, suka zo suka cece shi.


Komai yana da dalili. Abin duk da Allah ya yi, yana da dalilin yin shi, sai dai mutum ya kasa fahimtar dalilin.

Thursday, 4 July 2024

Labarin Wani Maye Da Alkali

Labarin Wani Maye Da Alkali

Bayan dogon lokaci da Alƙalin ya kwashe yana rubutu a cikin ɗimemen littafin da ke gabansa, sai ya ɗago da kansa ya dubi dattijon da ke tsaye cikin akwatin tuhuma, ya ce masa, "Malam Kalla ka ji abin da Malam Tanimu yake tuhumarka da shi. Ka ce wai shi maye ne, wanda hakan ya jawo masa ɓacin suna da baƙin jini a cikin jama'a.


Labarin Wani Maye Da Alkali
Hoto: Vecteezy


MarubuciBukar Mada


Dattijon da ake tuhuma ya kalli alƙali, fuskarsa duk ta nashe da gumi kamar wanda ya haɗiye kunama da ranta. Da ma an ce mara gaskiya ko cikin ruwa ya yi jiɓi. Ya ce, "Iye, na'am! Allah gafarta Malam, Wallahi ni da wasa na ce masa maye, suɓul da baka ne kurum na yi. Kuma wannan 'yar magana da na faɗa a majalisa, tun da ba rariya na bi ina shela ba, ta yaya za ta yaɗu har ta ɓata masa suna? Da ma dai akwai azazza tsakaninmu, Allah ya taimake ka."


Alƙali ya ci gaba da rubutu a cikin littafin da ke gabansa. Bayan ya kammala rubuta abin da yake son rubutawa, ko kuskure ya yi a wajen rubutun nasa, sai ya yage takardar ya kekketa ta guntu-guntu. Ya ce wa mai ƙara da wanda ake ƙara su tafi sai gobe su dawo, zai yanke hukunci. Da za su fita sai ya kwashi guntayen takardun nan ya ba Malam Kalla ya ce masa ya watsar da su waje.


Washegari da suka dawo, sai Alƙali ya ce wa Malam Kalla, "Kafin na yanke hukunci, ina so ka fita yanzu ka tattaro mini guntayen takardun nan da na ba ka jiya na ce ka watsar. Kada ka baro guntu ko ɗaya, ka dawo mini da su duka."


Malam Kalla ya tafi, jim kaɗan sai ga shi ya dawo. Ya dubi Alƙali ya ce, "Allah gafarta Malam, ban ga takarda ko ɗaya ba, ina tsammanin iska ta kora su wani waje."


Alƙali ya ce masa, "to ka ga kamar yadda ka watsar da takardun nan wuri guda, amma iska ta kwashe su ta watsa su zuwa lungu da saƙo na garin nan, kuma ka kasa tattaro su. Haka maganar da ka faɗa a majalisa za ta yaɗu zuwa kowane saƙo da lungu na garin nan, kuma ba za ka iya bin kowa ka faɗa masa cewa abin da ka faɗa ƙarya ce ba. Don haka idan ana hira a majalisa, ko dai ka faɗi alheri ko ka ja bakinka ka yi shiru. Magana zarar bunu ce, idan ta fito ba ta komawa."


Alƙali ya buɗe littafi ya fara sabon rubutu, kafin ya yanke hukunci.

Sunday, 30 June 2024

Labarin Kwaɗo A Rami Mai Cike Da Darussa

Labarin Kwaɗo A Rami Mai Cike Da Darussa

Kwaɗi na cikin tafiya sai biyu daga cikinsu suka faɗa cikin wani rami mai zurfi. Da sauran suka leƙa suka ga irin zurfin da ramin yake da shi sai suka ce wa 'yan uwansu, "ku dangana kurum, babu yadda za a yi ku fito daga wannan rami."


Labarin Kwaɗo A Rami
Hoto: Nctbstudentbd


MarubuciBukar Mada


Kwaɗin nan ba su saurari shawarar 'yan uwansu ba, suka fara tsalle suna ƙoƙarin fitowa daga ramin. Duk da wannan ƙoƙari da suke yi, sai 'yan uwansu suka ci gaba da cewa, "da ma kun haƙura, kun daina wahalar da kanku, ba za ku iya fitowa daga ramin nan ba."


Ɗaya daga cikin kwaɗunan nan ya yarda da abin da 'yan uwansa suka ce, sai ya saduda ya daina ƙoƙarin fitowa. Ya cika cikinsa da iska fal, sa'annan ya fashe tus, ya mutu nan take. Shi kuwa ɗayan bai ko kula da abin da 'yan uwansa ke cewa ba, ya ƙara himma dai fiye da yadda yake yi da fari. Kwaɗi kuwa suka ci gaba da ce masa, "ka dangana kurum yadda ɗan uwanka ya dangana, ka mutu ka huta da wannan wahala."


Kwaɗo ya yi musu bakan, ya ci gaba da tsalle dai har Allah ya taimake shi ya fito waje. Da fitowarsa sai 'yan uwansa suka kewaye shi suka ce, "hala ba ka ji abin da muke faɗa ba ko?"


Kwaɗo ya ce, "na ji ku sarai, sai dai na toshe kunnuwana ne, na daina sauraren abin da kuke cewa, na ci gaba da yin abin da nake ganin shi ne daidai gare ni."


To, haka ma mutane suke, kamar kwaɗin nan biyu. Akwai wanda zai biye wa maganar mutane, har su kai ga sare masa gwiwa ya daina abin kirki da yake yi. Wani kuwa babu ruwansa da duk wani kwakwazo da mutane za su yi masa, sai ya toshe kunnuwansa ya durfafi abin da yake ganin shi ne daidai, har sai ya cimma nasara. 


Ku toshe kunnuwanku, ku yi abin da yake daidai ne gare ku. Kowa ya biye ta bado, sai ruwa ya cinye shi ga banza.


A yaɗa wannan labarin domin wasu ma su amfana ta hanyar yin share.

Saturday, 22 June 2024

Labarin Wani Mutum Da Giwaye

Labarin Wani Mutum Da Giwaye

Wani mutum ya zo wucewa ta inda ake ɗaure giwaye, sai ya lura da 'yar igiyar da aka ɗaure ƙafar kowace giwa ga turkenta, to ko jaki aka ɗaure da ita zai iya fizgewa ya kubce. Ya tsaya yana mamakin wautar masu kula da giwayen, domin ya san kowane lokaci za su iya tsinke igiyoyin.


Labarin Wani mutum da Giwaye
Hoto: Pinterest 


MarubuciBukar Mada


Yana nan tsaye yana wannan tunani, sai ga mai kula da su ya zo. Mutumin ya tambaye shi, "me ya sa kuke ɗaure giwaye da wannan 'yar igiyar, maimakon ku ɗaure su da sarƙa mai ƙarfi? Ba ku tsoron su kuɓce wata rana?"


Sai mai kula da giwayen ya yi dariya ya ce, "tun lokacin da giwayen suke ƙanana ake ɗaure su da waɗannan igiyoyin, tun a wancan lokacin kuwa sun gwada tsinka su, amma da yake ƙarfinsu bai kai ba, ba su iya tsinkawar ba, haka suka haƙura cikin tsammanin ba za su iya tsinka su ba. To har yanzu ma da suka girma, sun tafi a kan zaton ba za su iya tsinka igiyoyin ba, don haka ko ƙaƙarin jaraba tsinkawar ma ba su yi."


Mutumin ya bushe da dariya, ya tafi yana mamakin sakarci na waɗannan giwaye. Ga shi dai za su iya tsinke igiyoyin a kowane lokaci, amma zaton ba za su iya ba, ya hana su gwadawa. 


Kodayake wasu mutanen ma ai haka suke. Da zarar sun jaraba wani abu sau ɗaya sun kasa, to ba za su sake jaraba shi ba. Sun tafi bisa zaton wannan abu ya fi ƙarfinsu har abada. Alhali da za su sake jaraba abun, to da wataƙila su same shi cikin sauƙi. Kada mu yarda igiyar zato ta ɗaure mu, tamkar yadda ta ɗaure giwayen can.

Monday, 17 June 2024

Labari Mai Ratsa Zuciya Na Wani Ma'aikaci Da Maigadi

Labari Mai Ratsa Zuciya Na Wani Ma'aikaci Da Maigadi

Ko da ƙarfe huɗu na yamma ta buga sai duk ma'aikatan Gidan Kifin suka fara harhaɗa komatsansu suna ficewa, cikinsu kuwa har da ni. Bayan na ɗauki jakata na nufi ƙofar fita sai na tuna da wata ajiya da na yi a wani ɗaki. Na juya da sauri domin in ɗauko.


Labarin Ma'aikaci Da Maigadi
Hoto: Drew Binsky


MarubuciBukar Mada


Bayan na buɗe ɗakin na shiga, sai ƙofar ta koma ruf ta rufe kamar an tura ta. Ga shi kuma dole sai ta waje za a iya buɗe ta. Na bubbuga ƙofar ko Allah ya sa wani ya jiyo ni, amma shiru ban ji duddugen kowa ba. Mutane duk sun rigaya sun watse.


Ɗakin nan kuwa ɗakin ƙanƙara ne inda ake ajiye kifi. Nan take sanyi ya sallamo wa jikina, ya riƙa ratsa ƙashi da ɓargona. Na fara makyarkyata, haƙori na gamewa kaf, kaf, kaf. Na ci gaba dai da buga ƙofa, amma shiru babu wanda ya buɗe. 


Bayan kamar minti talatin sanyi ya fara cin ƙarfina, na fara fita daga cikin hayyacinna, gaɓoɓina suka fara sandarewa, na faɗi ƙasa rib, na miƙa wuya ga mutuwa. Ba zato ba tsammani sai na ji an bankaɗo ƙofa, an shigo da sauri an sungume ni an yi waje. Bayan na farfaɗo sai na ga ashe Maigadin ƙofar shigowa gidan ne. Na yi mamakin yadda aka yi ya san ina ciki. Da na murmure sai na tambaye shi, ya aka yi ya san ina cikin ɗakin?


Maigadi ya amsa mini cewa, "tsawon shekarun da na share ina aiki a wannan kamfani, ma'aikata kan shigo su fita kullum, to amma kowa ya zo sai ya shige abinsa, ba wanda ya damu da ya yi mini ko kallon arziki, balle ya yi mini magana, sai fa 'yan kaɗan kan kula ni. Kai kuwa kullum sai ka gaishe da ni idan za ka shiga ciki. Idan an tashi aiki, sai ka yi mini bankwana. To, yau da aka tashi aiki, na ga kowa ya fita daga gidan nan amma kai ban ga fitowar ka ba. Shi ne na shigo ina bi ɗaki ɗaki ina dubawa, sai ga shi Allah ya sa na tarar da kai."


Da na ji haka ban san sa'adda ƙwalla ta cika mini ido ba, na ma rasa kalaman da zan yi amfani da su wajen gode masa. Ashe 'yar gaisawar da muke yi kullum, wadda ni ban ɗauke ta wani abu ba, shi kuwa ashe da muhimmancin gaske ya ɗauke ta. Da ma Hausawa sun ce, shimfiɗar fuska ta fi shimfiɗar tabarma. Na gode wa Allah da ya kubutar da ni daga halaka, na kuma gode wa Maigadi.

Sunday, 16 June 2024

Labarin Soyayya Mafi Ban Tausayi

Labarin Soyayya Mafi Ban Tausayi

Jamila ta tsani kanta saboda kasancewar ta makauniya, ta tsani kowa ma in ban da saurayinta da take tsananin so, watau Anas, wanda koyaushe yana tare da ita.


Labarin Soyayya Mafi Ban Tausayi
Hoto: Medium 


MarubuciBukar Mada


Anas ba shi da burin da ya wuce ya auri Jamila. Ita kuma kullum ba ta da buri ko maganar da ta wuce, 'yanzu dai Allah ya buɗe mini idona, in ga yadda duniyar nan take, da na yi farin cikin da ban taɓa yi ba.'


Anas yakan ce, "ni kuwa ina tsoron idanunki su buɗe, ki ga yadda nake, ki fasa aure na." Takan amsa masa da cewa, "zan aure ka duk yadda kake, ya masoyina."


Ran nan sai ta samu kyautar idanu daga wani wuri, likitoci suka yi mata aiki cikin nasara, ganinta ya komo tangaram. Ta yi ta kallon abubuwan mamaki, sai dai babban abin da ya fi ba ta mamaki da kuma takaici shi ne da ta ga ashe surayinta ma makaho ne.


Da Anas ya tambaye ta maganar aure, sai ta buga kai ga ƙasa ta ce faufau ba ta auren makaho. Wannan abu ya ɓata masa rai har ya sa shi tattara 'yan komatsansa ya bar garin. Amma kafin ya tafi ya aika mata da takarda, a ciki ya rubuta: KI KULAR MINI DA IDANUNA. Ashe idanunsa ne ya sadaukar mata don kawai ya cika mata burinta na ganin duniya, sai dai ita kuma ta kasa cika masa nasa burin na auren ta. 


To, haka ne fa halin wasu 'yan siyasa yake. Talaka zai yi musu komai don cikar burinsu, su kuwa su kasa yi masa komai don cikar nasa burin. Allah ya ba mu shugabannin da za su iya cika mana burikanmu Amin.

Saturday, 8 June 2024

Labarin Wasu Abokai Mai Ratsa Zuciya Na Ban Tausayi

Labarin Wasu Abokai Mai Ratsa Zuciya Na Ban Tausayi

Na kira abokina Ahmad a waya, na faɗa masa gari fa ya ci wuta, an kwantar da mahaifiyata asibiti, kuma ba ni da ko ƙarfanfana, ko zan samu rancen kuɗi a wurinsa. Ya ce, "kada ka damu abokina, ka kira ni da yamma."


Labarin Tausayi Na Wasu Abokai
Hoto: Envato Elements


MarubuciBukar Mada


Almuru na yi na ƙwala masa kira, wayarsa a kashe. Na sake kira babu amsa. Na kira shi ya fi sau shurin masaƙi, amma wayarsa a rufe. Na fusata, na ce, 'ni Ahmad zai kashe wa waya, don na nemi kuɗi wurinsa? Da ni yake zancen!' 


Na fita neman inda zan samu rance. Na zagaya ko'ina ban samu ba. Da goshin Magariba na dawo asibitin shajaran majaran. In duba haka, sai na ga magani tirmis a kan gadon mahaifiyata dake barci.


Na tambayi ƙanina inda aka samu wannan. Ya ce, "abokinka ne Ahmad, da ya zo bai tarad da kai ba, ya karɓi takarda daga likita ya sayo duka maganin." Sai na ji jikina ya yi sanyi, kamar an jefi kaza da gishiri. Ban ko zauna ba, sai na nufi gidansu. Na same shi na ce, "don me ka kashe wayarka, ka kuwa san zan kira ka bayan La'asar ?"


Ya ce mini, "ka yi haƙuri Solomon, sayar da ita na yi domin na kawo maka kuɗin a saya wa inna magani."


Na kawar da kai, idanuna cike da ƙwalla. Na rasa kalaman da zan yi amfani da su wajen gode masa. Ga shi dai ba addininmu ɗaya ba, amma ya yi mini abin da ko wani ɗan uwana ba zai yi mini ba. Haƙiƙa abokin kuka ake gaya wa mutuwa!


Banbancin addini ba ya hana abota. Kada mu bari 'yan siyasa su yi amfani da addini su haɗa mu faɗa da juna!

Tuesday, 23 April 2024

Karanta Labarin Gaggawa Da Hakuri Da Lokaci

Karanta Labarin Gaggawa Da Hakuri Da Lokaci

Watarana, wasu matasa biyu Gaggawa da Hakuri suna tafe a cikin wani ƙungurmin daji mai suna Duniya, a ƙoƙarin su na neman wani lambu mai suna Nasara. Tare da su akwai wani yaro ɗan ƙarami, mai suna Lokaci, wanda yake yi musu rakiya.


LABARIN GAGGAWA DA HAKURI DA LOKACI
Hoto: PNGTREE


 

Marubuci: Muhammad Musa Yelwa


Su na tafe suka isa wani kwazazzabo mai yawan duwatsu, wanda kuma a wurin ne ɗan rakiyar tasu Lokaci ya yi tuntuɓe da dutse, ya faɗi! Kodayake, ya lallaɓa ya yi ƙarfin hali ya tashi, sai dai yanzu tafiyar tasa babu sauri, sakamakon jan-ƙafa da yake yi.


Su na cikin wannan hali ne kuma Gaggawa ya hango wancan lambu da suke ta faman nema. Don haka, nan take ya ruga a guje, ya nufi wurin.


Lokaci ya ƙwalla masa kira:

“Haba Gaggawa, ya za ka yi mana haka? Ka jira mu mu shiga tare mana.”


Gaggawa ya ci gaba da gudunsa, ba tare da ya ko waiwaya ba. Ganin haka, Haƙuri ma ya ƙara ɗaga murya, yana cewa: “Kai kuwa wanne irin ci-da-zuci kake haka? Ka tsaya mu mana.”.


Gaggawa ya juyo a fusace ya ce da shi: “Kai rufe min baki, ni ba ni da kai.”.


Lokaci ya juya ya dubi Haƙuri ya ce: “Ka ji fa, wai ba shi da kai. Yana nufin ya haukace ne?”.


Haƙuri ya ce: “A’a, yana nufin dai ba shi da kai ne, wataƙil.”


Lokaci ya gyaɗa kai, sannan ya ce: “To kai me ya hana ka ka bi shi?”


Haƙuri ya ce: “Ni ba na tashi ai.”


Lokaci ya ce: “Kana nufin ba ka da fuffuke kenan?’’


Ya ce: “Ina nufin ba na gaggawa.”


Lokaci ya ce: “To me ya sa?”


Ya ce: “Saboda ina sane da cewa, ko da na je zan taar da ƙofar lambun a rufe. Tun da dai babu wani abu da yake faruwa ba tare da lokaci ba. kuma ga ka a nan.” 


Lokaci ya yi murmushi, sannan ya ce: “Hakika ka yi kyan kai. Tabbas mabuɗin yana tare da ni, amma tun da ka yi haƙuri, karɓi mukullin daga yau na ba ka kyauta, ya zama naka.” 


Suna ƙarasawa bakin lambun kuwa, Haƙuri ya sa mabuɗi ya buɗe lambun Nasara, ya yi bankwana da lokaci ya shiga. Yana tunanin shin ko a ina Gaggawa ya maƙale!?”


Yayin da Lokaci ya juya don ci gaba da tafiya, sai ya hangi Gaggawa kwance magashiyyan a bayansa, yana numfarfashi, ashe zuwa ya yi ya riƙa bangazar ƙofar ba ta buɗe ba har sai da jikinsa ya yi la’asar (Sanyi). Can cikin wata murya mai raurawa, ya ce wa Lokaci: “Don Allah ko akwai wani mabuɗin ka taimaka ka ba ni, ni ma na shiga?”


Lokaci kuwa ya ce da shi: “Ai mabuɗin Nasara ɗaya ne, kuma tuni yana tare da Haƙuri. Da ka yi haƙurin jira na, da ka samu, amma da yake ba ka yi ba, ga shi nan har na riga na wuce. Kuma ni idan na wuce ba na dawowa baya.” .


Don ci gaba da samun ire-iren waɗannan, ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe.

Tuesday, 30 June 2020

YIN KISA AKAN SOYAYYA

YIN KISA AKAN SOYAYYA

Sun je kududdufi ne da nufin antayawa ciki don Sheƙe kansu sakamakon hana su auren juna da iyaye suka yi.

Wasan Barkwanci Ne Da Muka Ɗauka...


A yayin da suke shirin kammala addu'a kafin afkawa, sai ga wani saurayi daban ya sheƙo yana dakatar da Budurwar kada ta kashe kanta ya yarda zai aure ta.

Saurayin da suka taho tare da ya rage masa wasu 'yan mintuna ya sheƙa Lahira ya tsaya yana mamakin sabon saurayin da ya zo.

"Malam ya muna shirin kashe kanmu zaka zo ka hana ta?" Ya tambaya cikin mamaki.

"Ba ta faɗa maka ni wanene ba?"

"Waye shi?" Ya tambaye ta.

"Dama shi nake so zan aura shi kuma wata yake so ba ni ba, shi ya sa na so yin auren huce haushi da kai. Kai ma aka hana ka aure na, shine abin ya dame ni na shawarce ka mu kashe kanmu". Ta yi bayani.

"Yanzu ina matsayin kashe kan namu ya kwana?"

"Idan ka so kai ka iya mutuwar tunda ka rasa ni, amma ni ina ganin ba dai-dai ba ne na zaɓi a sanya min likkafani bayan ga rigar amarci".

Suka tafi tare da barin saurayi a bakin kogi yana saƙe-saƙen shin ya ɗauki shawararta na ya mutun ko yaya?

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tushe/Asali: www.muryarhausa24.com.ng

Sunday, 31 May 2020

Karanta Labari Mai Dadi Wanda Zai Canza Maka Rayuwa

Karanta Labari Mai Dadi Wanda Zai Canza Maka Rayuwa

Wasu tawagar kwaɗi sun tafi yawo sai biyu a cikinsu babu zato bare tsammanin suka faɗa wani dogon rami.

Yi Iya Ƙoƙarin Ka A Rayuwa

Marubuciya: Aisha Isah

Lokacin da sauran kwaɗi suka lura da haka kuma suka kalli dogon ramin sai suka ce "Ba zai yuwu ku iya fitowa ba, kar ma ku wahalar da kanku da tsalle, ku zauna kawai ku jira mutuwa!!".

Daya daga cikin su taji maganar ƴan uwanta ta zauna a ciki tana jiran mutuwa.

Ɗaya kuma tayita tsalle tana ƙoƙarin fita, suka ci-gaba dace mata bazaki iya fita ba kiyi haƙuri kawai kina wahalar dakanki ne.

Sai ko fit Allah yataimake ta tafito, lokacin data fito suka dinga mamaki suna ce mata, Yaya kika yi kika fito? Sai suka fahimci ashe kurma ce bataji kuma bata magana!!!

Lokacin da suke ihu suna faɗan kalamai na sanyaya mata gwuiwa, ita ta ɗauka kururuta ta sukayi suna yaba jarumtarta  wannan yaƙara mata ƙarfin gwuiwa harta iya fitowa.

DARASI

Bar maganganun mutane, ci-gaba kawai a rayuwa.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tushe/Asali: www.muryarhausa24.com.ng

Thursday, 16 January 2020

Karanta Hirar Masoya Tsakanin Saurayi da Budurwa

Karanta Hirar Masoya Tsakanin Saurayi da Budurwa

Budurwa: Baby kana sona kuwa?

Saurayi: Kwarai kuwa baby duk duniya ba wacce nake so kamar ke.

Hirar Masoya Tsakanin Saurayi da Budurwa

Marubuci: Jabir M. Hassan

Budurwa: Koda zan wanka maka mari mai zafi?

Saurayi: Ai ko abinda ya fi hakama ba zan damu ba.

Budurwa: Idan na mari ƙanwarka a gabanka fa ko yayanka?"

Saurayi: Idan kika mari ƙanwata haƙuri zan bata, ai ke yayarta ce dole tayi haƙuri, idan kika mari yayana haƙuri zan bashi, saboda ke ƙanwarsace ai, kuma akwai ƙuruciya a tattare dake, ko kuma na tsaya ya dakeni a maimakon ke ɗin.

Budurwa: To idan na mari mamarka fa?

Saurayi: Tasss! Tasss!! Tasss!!! ya wanketa da mari har sau uku.

Budurwa: Kan batasi! Ni zaka mara har sau uku daga na tambayeka?

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA ZAFAFAN SAKONNIN SOYAYYA GUDA 32 MASU RATSA ZUKATAN MASOYA MAZA DA MATA NA ZAMANI

Karanta Labarin Wata Kyakkyawar Budurwa da Samari Guda Biyu

KARANTA ALAMOMI 10 DAZAKA FAHIMCI MACE TANA SON KA

Saurayi a fusace  An mareki, ki ɗauki mataki dan ubanki, mari na farko danayi miki don kinyi tunanin zaki mari mamata ne, mari na biyu kuma don kin faɗa ne, na uku kuma gargaɗi ne don idan ma kikayi tunanin marin mamata sai na kakkaryaki wallahi, banza 'yar rainin hankali.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.



MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



Sunday, 5 January 2020

Karanta Kayataccen Labarin Wani Makaho Mai Kaifin Basira

Karanta Kayataccen Labarin Wani Makaho Mai Kaifin Basira

A Bobi akwai wani makaho wanda a ke kira Bakin Makaho. Dalilin da ya sa mutane ke kiransa haka, domin wayon da Allah ya zuba masa ne. Kullum in ya yiwo bara ba ya batad da kudin a wofi, sai ya sami wani wuri, ya yi ta tarawa har dai kudi suka yi yawa.

Labarin Wani Makaho

Marubuci: Bukar Mada

+2348021218337

Daga littafin Magana Jari Ce 2 wallafar
Alhaji Abubakar Imam

Ranar Jumma'a, da ya dawo sai ya kwaso kudinsa duka ya kidaya, sai ya ga har sun kai fam uku. Da ya ga sun yi yawa haka sai ya ji tsoron kada ya bar su a bukkarsa, wani ya zo ya sace. Saboda haka ya yi ta neman inda zai kai su, ya ga in ya ba wani ajiyarsa kuwa lalle za a zalunce shi.

Yana cikin tunanin yadda zai yi da su, sai ya tuna ba inda ya fi ya ajiye su sai a masallaci, don ya sani lalle ba barawon da zai yi tsammani akwai wani abu a masallaci ban da buzaye da gorunan alwalla.

Ya ga in ya tafi da azahar lalle ya sami wadansu suna salla, saboda haka ya bari sai da rana ta yi tsaka, sa'an nan ya dauki kudinsa ya sa aljihu, ya tasam ma masallaci.

Da ya isa bai zame ba sai gindin mumbari, ya tsaya tsit ko ya ji motsin wani ciki, bai ji ba. Sai ya ce a ransa, "Lalle ba kowa. Da ma me zai kawo mutum masallaci da rana tsaka haka?" Ya shafa, ya kwakwale ramin gindin mumbarin nan, ya zuba kudinsa, ya tafi, yana fadi a ransa, "In na dawo mumbarin nan shi ne shaidata, ba a dai motsashi."

Ashe duk abin da makahon ya aikata wani madinki na nan yana wuridi, yana kallonsa. Wucewar makahon ke da wuya, sai madinkin ya katse wuridi, ya ce, "Bukatata ta biya. Allah ya karbi rokona." Ya tashi ya tone ramin, ya kwashe kudi, ya yi tafiyarsa.

Kashegari wani attajiri ya fid da zakka, Bakin Makaho ya sami kamar sule biyar sadaka. Sai ya nufi masallaci da karamin dansa na ja masa gora, ya bar shi waje, shi kuwa ya shige, ya lalubi mumbari ya tona gindinsa ba kudi ba dalilinsu. Ya saurara ko ya ji motsin wani, bai ji ba. Sai ya rike baki ya yi salati, ya ce, "Ba kome, in dai kudin nan halalina ne, ai ba su bata."

Ya fito ya tarad da dansa, ya ce masa, "Kai, da mu ke zuwa nan ba ka lura da wani na dubammu yana dariya ba?"

Yaro ya ce, "Ba wanda na gani yana maka dariya, sai Sanda, madinkin nan da ba ya ba mu sadaka im mun je bara kasuwa. Nan wajen kofar gidan Sarki muka wuto shi. Da na waiwaya har gwalo ma na ga yana yi maka. Ina tsammani abokin wasanka ne, shi ya sa ban ce maka kome ba, don ka hana ni tsalma baki cikin sha'anin manya"

Makaho ya ce wa yaro, "To, kai ni wajensa."

Yaro ya'ce, "To." Ya ja goran ubansa har rumfar Sanda Madinki a kasuwa, suka tarar ya dawo daga yawo.

Ko da ganinsu sai Sanda ya ce, "Bakin Makaho, me ya kawo ka nan ne yau, ba kuma ma ran Jumma'a ba? Ku dai makafin nan kun dami mutane da bara."

Makaho ya yi dariya ya ce, "Kai Sanda, in da don kai kadai mu ke zuwa kasuwan nan, lalle da mun mutu da yunwa. To, yau ba bara na zo ba da karayarka, magana ce gare ni da kai, fito ka ji."

Sanda ya fito, suka koma wuri daya, Bakin Makaho ya ce, "Tun tuni na ke son ba ka shawara, na dakata tukun a kare rigimar zakka mu gani. Yau kudin da na ke tarawa na bara yanzu na ga sun yi dan yawa, saboda haka na ke so in ka yarda in ba ka su ka rika juyawa, kana sayen 'yan kayayyaki kana sayarwa, ka ga da ni da kai duk sai mu amfana. Yanzu dinki ba ya ciwuwa da damana, da ma ka bar shi sai kaka. Yau ma can inda na ke ajiya na tafi in kai wadansu 'yam fam guda da na samu wajen zakkar da attajirai suka fid da jiya, na tarar wurin da na ajiye kudin akwai mutane, saboda haka na bari sai rana ta take tsaka, sa'ad da kafa ta dauke na tafi in kai wadannan. Gobe kuma in na je, abin da na samu daga wadanda Sarki zai fitar, zan komo ma'ajina in dauki wadancan in gama, in kawo maka. Kai na ga kana iya rikon amana, shi ya sa na ba ka. Amma don Allah kada ka ci amanata. Ka san fa kowa ya ci amanar wani, Allah ya ci tasa."

Da Sanda Madinki ya ji haka sai ya yi murna a ransa, ya ce, "Subuhana lillahi, ai tsakanina da kai babu cin amana. Kai ne watakila ba ka sani ba, ai na ji labari da tsohona da tsohonka sa'ad da suna yara ba abin da ke raba su. To, gobe da azahar ina nan ina jiranka."

Bakin Makaho ya ce, "To, Allah ya kai mu." Sanda ya raka shi, suka yi sallama. Yaro ya ja goran ubansa, suka nufi gida.

Da wucewarsu sai Sanda ya yi wa makaho gwalo daga baya, ya ce a ransa. "Bari in je yanzu im mai da kudin nan fam uku a masallaci, don idan an jima, da rana tsaka Bakin Makaho ya kai fam gudan da ya ke fadi, ya tarad da wadannan can. Idan ya kai wadannan, watau sun cika fam hudu ke nan, da magariba sai in lababa in kwashe su duka, in zo in sayi turame in yi ta dinki. Kafin kaka kuwa ai lalle in sayi keke, in shiga cikin 'yan'uwana ina kece raini."

Nan da nan sai ya dauki kudin nan ya kidaya, ya ga ashe ma jiya har ya sai wa matansa zannuwa na sule goma daga ciki. Saboda haka ya tafi ya samo rancen sule goma ya gama, suka tashi fam uku daidai, ya kai inda ya tono su a masallaci, ya binne. Ya ce, "Ashe dai ba shakka abin da mutane ke fadi gaskiya ne, dare, daya Allah ya kan yi Bature. Dubi wannan baiwa da Ubangiji ya yi mini yau, in sami fam hudu ba saye ba sayarwa. Ya kama hanya ya tafi.

Da rana ta yi tsaka, Bakin Makaho ya komo masallaci ya tona mumbari sai ga kudinsa fam uku cur. Ya yi godiya ga Allah da ya nufa wannan dabara tasa ta fita. Ya kwashe ya koma gida.

Magariba na yi, Sanda shi ya riga Liman zuwa masallaci. Da aka yi salla aka kare, sai ya kama wuridin karya don mutane su watse su bar shi, shi kuwa ya tone kudin.

Da ya ga duk an fita, sai ya tashi ya nufi gindin mumbari, ya tona ya tona, bai ga kome ba. Sai duk ransa ya baci, ba don batan sule hamsin din nan ba, amma don sule goman nan da ya ranto ya cika. Da zai fita ya ce, "Kai, me ma zai bata mini rai ga wannan? Da ma na dauke su, zunubin da zan kwasa na wannan bawan Allah ai Ubangiji kadai ya san iyaka." Ya wuce yana tunanin abin da zai yi ya biya mutane sule goma dinsu.

Da gari ya waye ya yi ta jiran Bakin Makaho har azahar ta wuce, bai gan shi ba. Sai ya tashi ya bi shi gida, ya ce, "Na zo bisa ga maganar da muka kulla jiya ne, ka san ni ba na son in na ce i, in komo in ce a'a."

Bakin Makaho ya ce, "Ai ni ma yadda ka ke din nan haka na ke. Kudin na zamani ke da ban al'ajibi, in ka duba inda ka ajiye su, wata sa'a sai ka tarad da su sun tafi yawo. Da yanzu fa zan kai maka, sai na tarad da duk sun fita shan iska, ba ko daya,sai fa in sun dawo ka gan ni da su."

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA KAYATACCEN LABARIN ZAKI DA MUTUM

KARANTA KAYATACCEN LABARIN WATA MATA DA KWARTAYE BIYU

KARANTA KAYATACCIYAR HIKAYAR SHEHU JAHA "KARKA GASKATA SHI"

Da ya ji Bakin Makaho ya tasar wa yi masa ba'a sai ya yi fushi, ya haura takalmansa ya tafi yana cewa, "Mutanen duniya dai yanzu Turawa sun bata su da wayo, ko ina ka fito musu suna make suna kallonka."

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode





Sunday, 8 September 2019

KARANTA KAYATACCEN LABARIN WATA MATA DA KWARTAYE BIYU

KARANTA KAYATACCEN LABARIN WATA MATA DA KWARTAYE BIYU

Akwai wani mutum, daya daga cikin askarawan wani Sarki. Ya kasance yana soyayya da wata mace 'yar talaka.

Wata Mata da Kwartaye Biyu


Daga littafin LABARAN DARE DUBU DA DAYA

Fassarar

Ibrahim Malumfashi

Danladi Haruna

Bukar Mada

Wata rana sai ya aiki wani yaronsa domin ya kai mata sako a gidanta, kamar yadda yakan yi daga lokaci zuwa lokaci. Yayin da yaron nan ya kai wa matar sako sai ta yi ta tsokanarsa da wasanni na jan ra'ayi, ta rungume shi cikin kirjinta. Ba ta gushe ba tana jan hankalinsa har ta takalo masa da sha'awa, ta jefa shi bisa shimfida, suka rungume juna.

Suna cikin aikata masha'a sai ga askar din nan, ubangidan yaro, ya zo yana kwankwasa kofa. Nan da nan matar ta boye shi a cikin wani dan karamin daki. Ta je ta bude wa masoyinta kofa, ya shigo yana rataye da takobi, ya zauna bisa shimfida. Matar ta zo ta rungume shi tana sumbata, har dai suka kwanta bisa shimfida suna rungumar juna. Suna cikin wannan hali sai ga mijin matar ya dawo yana kwankwasa kofa. Askar ya tambaye ta, "Wane ne?"

Ta amsa masa, "Mijina ne."

"To, ina dabara?" Askar ya tambaya.

Matar ta ce, "Ka zare takobinka, ka yi ta nuna ni da shi kana zage-zage, ranka a bace. Da zarar mijina ya shigo sai ka fice daga dakin kana huci, kada ka ce masa uffan."

Askar ya aikata kamar yadda matar ta umurce shi, ya zare takobi yana ta zage-zage. Ta tashi da sauri ta bude wa mijinta kofa. yayin da mijin ya shigo sai askar ya mayar da takobinsa cikin kube, ya fita yana huci, mijin ya bi shi da kallo, baki wangame, har ya fice. Daga nan sai ya juya ya tambayi matarsa, "Me ya faru?"

Matar ta ce, "Kai dai bari mai gida, Wallahi na gode wa Allah da ka dawo cikin lokaci, ba don haka ba da an yi kwababba." Mijin ya yi tsaye dai yana sauraron ta. Ita kuma sai ta ci gaba da cewa, "Ka sani ya kai mai gida, yau ka kubutar da saurayi daga kisa. Ina zaune bakin kofar daki ina kadi sai ga wani saurayi ya shigo gidan nan da gudu, yana haki kamar ransa zai fita. Ya fadi gabana yana cewa in yi masa rai, ga askar nan daga cikin askarawan Sarki ya biyo shi da takobi tsirara zai kashe shi. Ni kuma sai na ji tausayinsa, na ja shi da sauri na kulle cikin dan karamin dakin nan namu. Ina boye shi sai ga askar ya fado cikin dakin, kamar wanda aka bankado, da takobi tsirara, yana cewa in fito masa da saurayin da na boye. Na ce masa ni ban ga wani saurayi ba, ya tsaya yana ta zage-zage, yana cewa lalle sai na fito masa da shi. Muna cikin wannan jayayya sai ga ka ka fado. Wallahi Allah ya kyauta al'amurra da ka dawo da wuri."

Mai gida ya rike baki cikin mamaki, ya ce wa matarsa, "Ai wannan ba karamin allheri kika aikata ba, Wallahi Allah kadai zai biya ki ladan wannan taimako da kika yi." Ya shiga inda saurayi yake boye ya ce masa, "Fito ka tafi."

LABARAI MASU ALAKA:

KARANTA KAYATACCEN LABARIN ZAKI DA MUTUM

KARANTA KAYATACCEN LABARIN WATA MARAINIYA DA DAN SARKI

KARANTA KAYATACCEN LABARIN WANI AKU DA MATAR UBANGIDANSA

Saurayi ya fito yana makyarkyata don tsoro. Mai gida ya ce, "Saki ranka, kada ka ji tsoron komai domin babu abin da zai same ka." Da wannan makirci matar nan ta fitar da kanta, ba tare da mijinta ya zarge ta ba. Haka kuma sauran kwartayen biyu ba su san abin da ya faru ba bayan fitarsu.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








Sunday, 4 August 2019

KARANTA KAYATACCEN LABARIN WANI AKU DA MATAR UBANGIDANSA

KARANTA KAYATACCEN LABARIN WANI AKU DA MATAR UBANGIDANSA

Wata rana wani tajiri za shi fatauci, sai ya bar matarsa a gida. Yana kuma da wani aku. Suna nan tare, sai matar ta rika fita yawo, don ta ga mijin ba ya nan. Barorin gida da suka ga abin ya dame su, ba su da damar su yi magana, kada matan nan ta sare su wajen mai gidan in ya komo. Saboda haka suka zura mata ido.

Aku


MarubuciBukar Mada

+2348021218337

Daga littafin MAGANA JARI CE 1 na
Alhaji Abubakar Imam

Ana nan ran nan sai mai gida ya dawo. Ka san al’amarin duniya ba shi boyuwa, sai wani ya tsegunta masa abin da matarsa ta yi ta aikatawa bayan ba shi nan. Da mai gidan nan ya ji haka, sai ya kira matar, ya same ta ya yi ta zagi. Ya dauki sanda kuma ya ba ta kashi.

Da matan nan ta ga haka sai ta yi yaji, aka komo da ita. Ta ce a ranta, “Ba wanda ya fadi abin nan sai aku.” Ka san mu, Allah ya ba ka nasara, bakin jini gare mu kwarai, tun ba game da mata ba. Suna cewa mun faye tsegumi.

Saboda haka, ta bari mai gida ya tafi kasuwa, sai ta kama aku, ta fige shi da rai, ta wurga shi waje ta taga, ta ce, “Daga gare ni ka bar tsegumi!” Allah ya sa aku bai mutu ba, ya tsallaka har ya kai wani hurumi ya sami kabari ya shige, ya yi ta jiyya.

Da mai gidan nan ya dawo, sai matar ta ce wai bayan fitarsa kadan kyanwa ta cinye aku. Ko da ya ji haka sai ya san karya ta ke yi, kashe shi ta yi, don tana tsammani shi ya gaya masa tana fita da ba shi nan. Saboda haka ya fusata kwarai da gaske, ya same ta da duka kamar ba zai bar ta da rai ba. Ya kore ta daga gidan, ta tafi wajen hurumin nan tana kuka.

Ashe aku na nan kusa da ita cikin wani kabari, yana ji. Sai ya ce mata, “Yi shiru, bari kuka, in Allah ya so kya koma dakinki. Amma akwai sharadi guda, sai ki je ki aske kanki sarai, sa’an nan ki dawo nan, gobe zan taimake ki ki koma.”

Matan nan ta duba, ba ta ga kowa ba. Abinka da mace, sai ta yi tsammanin wani matacce ne ke yi mata magana. Nan da nan ta tafi gidan iyayenta, ta sa aka aske mata kai kwal.

Da gari ya waye, maraice ya yi ta nuho wajen hurumi, kai na kalli sai ka ce na namiji. Da isowarta sai ta tafi wajen kabarin. Abinka da jahila, ta durkusa, ta ce, “Na asko.”

Sai aku ya ce, “To, kin san dalilin da ya sa na ce ki aske kanki, domin kin zalunci wani dan tsuntsu, kika tsarge shi a kan abin da bai ji ba bai gani ba, har kika fige shi da ransa, kika wurgo shi bayan gida. A wannan na yi miki sauki, na ce ki aske gashin kanki kawai, amma in kin kuskura kika sake yi wa wani tsuntsu haka, ki kuka da kanki. Amma akun nan da kika kashe zai komo duniya, yadda zan mai da ke dakinki, shi kuma zan mai da shi gare ki. To, ki lura da shi da kyau, ki sa mijinki ya ajiye yaro guda mai mai hankali wanda zai rika lura da shi, a rika ba shi ruwa da sukari. Kuma ki tsawata wa yara su bar kiransa aku kuturu.”

Matan nan ta kara dukawa, ta ce, “Na ji.” Da za ta tashi sai aku ya ce, “Da saura. Yau kin ga sha biyu ga watan Safar. To, ko wace shekara sha biyu ga watan Safar ki aske kanki, don ya rika tuna miki aku dai da ki ke ganinsa banza-banza ba banza ba ne. Amanar Allah ce ya sa hannunku ‘yan Adam, ya fi kyau kuwa ku lura da ita da kyau. Watan duk da ya zo ba ki aske kanki ba, yadda na gaya miki yanzu, ki tabbata ba ki shekara.

Shi ke nan, gobe kya koma in sha Allahu. Tafi gida abinki. Amma ki kiyaye gargadin nan da na yi miki, ki kuwa yi kirki, ki bi mijinki sau da hannu. Allah ya gama mu da alheri a Darassalamu!”

Mace ta koma gidansu. Aku ya tashi yana tsalle, har ya kai gidan tajirin nan, ya ce masa, “Ka san ni?”

Tajirin ya dubi aku ba gashi, ya ce, “Yaya zan yi in san ka, ban taba ganinka ba?”

Aku ya ce, “Ba ka taba ganina ba? Ai ni ne akunka wanda kyanwa ta cinye.”

Tajiri ya ce, “Tun da kyanwa ta cinye ka, yaya kuma aka fara har ka yi rai? Da ma dai ba kyanwa ta ci ka ba akwai yadda aka yi.”

Aku ya ce, “Daga cikin kyanwar aka nufa in fito, don in shaida maka duk abin da matarka ta fadi na batun kyanwa ta cinye ni gaskiya ne, kada ka zarge ta. Amma in kana sona, zan kara dakatawa kuma wurinka, in yi gashi in koma kamar da, har Allah ya kari kwanana gaba daya. Amma sai ka mai da matarka, ka yafe mata, ku yi zaman lafiya.”

Mai gida ya ce, “To.” Ya aika matar ta dawo, ya gafarta mata suka sake zamansu. Daga ran nan ta zama matar kirki, duk gari ba wadda a ke so sai ita a kan kirki.



LABARAI MASU ALAKA:

KARANTA LABARIN GOJE MAI DAWA KASHI NA DAYA

KARANTA LABARIN MALAM DUDU MAI-GANI-HAR-HANJI

KARANTA HIKAYAR WATA RANA A KASAR HAUSA KASHI NA DAYA

KARANTA KAYATACCEN LABARIN ZAKI DA MUTUM


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode