Saturday 24 March 2018

Karanta Takaitaccen Tarihin Yaren Harshen Hausa ﻫَﻮُﺳَﺎ

Tura Wannan Zuwa
Kabilar Hausa dai, ƙabila ce dake zaune a arewa maso yammacin tarayyar
Nijeriya da kudu maso yammacin jamhuriyyar Nijar .

Tarihin Kabilar Hausa

Kabilace mai ɗimbin al'umma, amma kuma a al'adance mai mutuƙar haɗaka, akalla akwai sama da mutane miliyan tamanin da harshen yake asali gare su.

 A tarihance ƙabilar
Hausawa na tattare a salasalar birane.

Hausawa dai sun sami kafa daularsu ne tun daga shekarun 1300's, sa'adda suka sami nasarori da dauloli kamar su daular Mali, Songhai, Borno da kuma [ fulani ]. A wasu lokutan
Hausawa sun sami gagarumin ikon, mulki da haɗaka ta kau da baki 'yan neman ruwa da tsaki, da kuma neman angizo a cikinta da kuma harkallar bayi.

A farko-farkon shekaru na 1900's, a sa'adda kabilar Hausa ke yunkurin kawar da mulkin angizo na fulani, sai turawan mulkin mallaka na Birtaniya suka mamaye arewancin Nijeriya, da kuma kafa manufofin mulkin bayan gida,a bisa ƙarƙashin mulkin
birtaniya ,'yan mulkin mallaka sai suka marawa Fulani
baya na ci gaba da manufofin angizon siyasarsu, har yanzu dai mulkin gamin gambiza tsakanin Hausawa da [[ fulani ]] shi ne ya yi kane-kane a arewacin Nijeriya.
Wannan haɗakar gamin gambiza, an faro ta ne tun asali a matsayin [[fulani Fulani ]] su dare madafun ikon a tsararren tsarin siyasar arewa. Akasarin masu mulki na [[fulani Fulani ]] sun kasance yanzu, a al'adance Hausawa gwamitse.

Ko da yake, Hausawa na farko-farko maharba ne, amma zuwan addinin
Islama da kuma karɓansa da hannu bibbiyu ya sanya labari ya sha bambam. 

Ginshikokin al'adun
Hausawa na da mutukar jarumta, kwarewa da sanaiya fiye da sauran al'ummar dake kewayenta.

Sha'anin noma ita ce babbar sana'ar Hausawa inda Hausawa ke ma sana'ar noma kirari da cewa, na doke tsohon ciniki kowa yazo duniya kai ya tarar, akwai kuma wasu sana'o'in kamar su sha'anin jima watau harkar fatu, rini, saka da kira, fannonin dake mutukar samun cigaba a harkokin sana'o'in
hausawa . Hausawa dai sun jima da shahara wajen harkar fatauci kana kuma masu arziki na taka rawa a sha'anin yau da kullum, tare da masu mulki da masana. Harshen Hausa shi ne mafi girma da kuma mafi sanannen harshe a nahiyar Afirka .
Harshen
Hausa ya aro wasu kalmomi daga wasu harsuna musamman larabci kana kuma harshen na tafiya tare da yanayin mu na zamani bisa al'adar cudeni-na cudeka. Harshen Hausa dai ya zama harshen yau da kullum ga miliyoyin jama'a da ba Hausawa ba ne a nahiyar Afirka.

Bugu da ƙari, akwai cincirindon al'ummar Hausawa a manyan biranen yammacin Afirka da arewacinta da kuma yankunan cinikayyar al'ummar Hausawa da kuma yankunan da Hausawa suka jima suna bi a hanyar ta zuwa aikin hajji. Akwai kuma rubutattun adabi masu zurfi da kasidodi da kuma rubuce-rubuce a rubutun ajami da aka buga tun kafin zuwan turawa 'yan mulkin mallaka na birtaniyya.

Har ila yau, kuma wani tsarin rubutu a ajami da aka ƙirƙiro tun kafin zuwan turawa, da ba kasafai ake amfani da shi ba yanzu.

Ire Iren Yaren Hausa
Yaren Hausa yana da ire-ire da yawa.

Gabarcin Hausa su ne:-

1 - Kanawa
2 - Katagumawa
3 - Hadejawa

yammacin Hausa :-

1- Sakkwatawa
2- Katsinawa
3- Kurfayawa
4- Gobirawa
5- Adarawa
6- kabawa
7- Zanfarawa

Arewacin Hausa :-

1- Arewa
2- Arawa
Hausa ajami wanda suka fita daga ƙasashin Hausa suka shiga kasashin larabawa shekaru aru-aru :-
1- Sudan
2- Saudiyya
3- Libya
4- Aljeriya

Muhimmancin Yaren Hausa

Yaren hausa yare ne mai muhimmanci sosai a kimanin kasashe ashirin wurin aikin kasuwanci musamman ma a manyan biranen ƙasashen Afrika ta Yamma (Najeriya, Benin, Burkina Faso ,
Ghana , Nijer , da sauransu

HAUSA A FAGEN YADA LABARAI
GIDAGEN REDIYOYIN DA SUKE YADA SHIRYE-SHIRYE DA HARSHEN HAUSA DAGA KASASHEN WAJE :

NAHIYAR TURAI :

1- BBC Hausa. (Ingila)
2- RFI Hausa. (Faransa)
3- DW Hausa. (Jamus)
4- TRT Hausa. (Turkiyya). (www.trt.net.tr/hausa)

LATIN AMERIKA :

5- VOA Hausa. (Amerika)
NAHIYAR YURASIYA :
6- Sashen Hausa Radio Moscow. (Rasha)

NAHIYAR ASIYA :

7- CRI Hausa. (China)
8- IRIB Hausa, ko kuma : Hausa Radio Tehran. (Iran)

NAHIYAR AFRIKA :

9- Muryar Afirka Birnin Alkahira. (Misira)
10- Sashen Hausa Radiyon kasar (Libiya).
Idan ka san wasu gidajen rediyon, ka taimaka mana da sunayen su, da sunayen kasashen da suke.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki 

Mungode

Source: Wikipedia
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user