Tuesday 22 September 2020

Karanta Zafafan Sakonnin Soyayya Masu Ratsa Zuciya

Tura Wannan Zuwa
MASARAUTA

Kin wadata zuciyata da farin ciki, kin haskaka rayuwata da haskenki, kulawarki a gare ni ta musamman ce, hakan ya sa nake jin kaina tamkar sarkin wata masarauta mafi girma da ƙarfin iko. Ina Son Ki.

Saƙonnin Soyayya

MarubuciAbba Muhammad Dan Hausa

KALMOMI

Ke ce kaddarar da na jima ina tsimayin tarar da ita a rayuwata, zan kasance a duk inda kike, zan tsaya a duk inda kika tsayar da ni. Ina son ki, adadin son da kalmomi ba zasu iya siffantawa ba.

TASIRI

Ina jin labarin soyayya ne a da, tamkar tatsuniya, amma a yanzu bayan na haɗu da ke, na gaskata soyayya wata aba ce wadda ke da tasirin sanya farin ciki a cikin zuciya. Ina fatan zaki kasance tare da ni, domin zama maganin damuwata na tsawon rayuwa? Ina Son Ki.

DAƊI

Koda a ce za ki sa wuta a jikina na babbake na zama toka, ba zan damu ba, matuƙar zaki ɗauke ni, ki kasance tare da ni a duk inda kike. Fatana mu kasance tare da juna a cikin wuya ko daɗi. Ina Son Ki.

LEMO

Son da nake yi miki, tamkar ruwan lemo ne da ke rufe a cikin kwalba, irin wanda babu irin sa ko makamancin sa a faɗin wannan duniyar. Ina fatan zaki karɓa domin jin irin ɗanɗanon da ke kunshe a cikinsa? Ina son ki.

AMINCI

Ina fatan Allah Ya bar mu tare, cikin aminci da kaunar juna.

WATA RANA

Tun ranar da na fara ganin ki, na ji a jikina, watarana hannuwanki zasu zamo masharin hawayena, kuma zasu kasance riƙe da ni na tsawon rayuwa, zuciyarki zata zamo makwancina na har abada. Na gode da irin kulawar da kike nuna min a kullum. Ina Son Ki Sosai.

MASOYI

Kin zamo cikin baitukan waƙar da zuciyata ke rerawa a kullum, waɗanda a dukkan lokacin da na ji su, na kan ji dukkan damuwata na gushewa. Tabbas ina jin na kamu da son ki ne..... kai babu ko shakka matsanancin son ki ya shiga zuciyata. Ina son ki ina kuma fatan zaki amince da ni a matsayin masoyi na hakika?

TUNANI

So tamkar wutar murhu ne da ke ci a cikin zuciyar masoya. Tini zuciyata ta babbake da son ki abar tinanina. Ina son ki, so mara misaltuwa.

RANA

Ba zan taɓa mantawa da wannan ranar ba, wadda dare ya yi na kasa bacci a cikinta, saboda tsabar tinaninki, wato ranar da na fara ganin ki. Na Yi Kewar Ki.

BAYAN RAINA

Idan har ba kya jin irin yadda nake ji a kan ki a yanzu, to tabbas na san zaki ji irin hakan bayan na mace.

AIKI

Babu wani sinadari da zai iya mayar da zuciya, ya haɗe ta guri guda, ta dawo da aiki kamar yadda take a da, bayan ta fashe ta tarwatse. A saboda haka nake roƙon, da ki kasance cikin ba wa zuciyata tsaro, karda ta yi fashewar da za a rasa ni gaba ɗaya. Ina Son Ki.

FARIN CIKI

Ke kaɗai ce nake gani kullum a cikin baccina, ke ce abar begena kuma ke ce wadda nake so, domin a gurin ki nake tsammanin samun farin cikin da nake fata. Ina Son Ki

LOKUTA

A wasu lokuta so yana zama wani abu mara tausayi ga duk wanda ya raɓe shi, ya raba mutum da duk abun da yake da shi na farin cikin rayuwa, amma ni na yi sa'a kuma na tsallake wa sharrinsa tunda na same ki.

MUHIMMANCI

A dukkan lokacin da tinaninki ya bujuro a cikin zuciyata, na kan tina irin yadda son ki ya zamo abu mai matuƙar muhimmanci a rayuwata. Ke ce wadda nake so, kuma nake fatan na rayu tare da ita, rayuwa ta har abada.

MA'ANA

Za ki fahimci ma'anar soyayya, da kuma irin muhimmancin girman son da nake nuna miki, a lokacin da aka ce na mutu ba na raye. Har Yanzu Ni Dai Ina Son Ki.

NUTSUWA

A kullum zuciyata kan nutsu ta yi tinani, domin tsara sakon da zan aikewa da abar tinanina a dare ko rana, domin ganin yalwatuwar murmushi a saman fuskarta. Ina fatan sakonnin nawa suna yin tasirin sanya ki farin ciki? Ina Son Ki

RABUWA

A dukkan lokacin da masoyi ya rabu da abar ƙaunarsa, ya kan tsinci kan sa cikin kaɗaici da damuwa na tsawon lokaci, ya kan tsinci kan sa cikin rashin yarda da gujewa amincewa sauran mata. Ki kasance tare da ni na tsawon rayuwa, karda ki bari zuciyata ta ɗanɗani raɗaɗin zafin rabuwa da abar so. Ina Son Ki

CIWO

So shi ne abu mafi tasirin warkar da kowane irin ciwo a cikin zuciya, kuma shi ke sanya mu jin kanmu a matsayin wasu mutane na musamman, a dukkan lokacin da muke tare. Na Yi Kewar Ki

TSANTSAR SO

Shigowar ki cikin rayuwata, gami da irin tsantsar son da kike nuna min, sun zama dalilan yin murmushina a kowane lokaci. Ba ni da wata da nake so sama da ke. Ke ce ƙarfina, ke ce karsashina. Ina Son Ki

DALILAI

Kowace soyayya da kake gani, tana samuwa ne a bisa wasu dalilai, saboda haka, ina son bayyana maka cewa, ina son ka ne saboda kai ne da ma wanda zuciyata ta daɗe tana jira. Ina tare da kai a duk inda na shiga. Ina Son Ka.

ZOBE

Matsayinka a gare ni, tamkar na wani dutse ne na musamman da yake jikin wani zobe, wanda ya kasance a dukkan lokacin da babu shi, zoben zai zamo mummuna mara daraja abar nunawa. Ka kasance tare da ni masoyina. Ina son ka, so mara misaltuwa.

RAYUWA TA

A lokacin da ka shigo cikin rayuwata, na ji tsoron kar ka raunata zuciyata, amma yanzu da na same ka, ina jin fargabar rasa ka. Ina fatan zuwan ranar da zan zamo mata a gare ka. Ina Son Ka.

YANAYI

Ina son kasancewa ne tare da wanda zai kasance cikin saka ni farin ciki, ya sa ni murmushi a lokacin da nake cikin damuwa, wanda zai kasance cikin so na a kowane irin yanayi. Na san babu wanda zai iya hakan sai kai, a saboda haka nake kara bayyana maka cewa, ina son ka.

NASARA

Ina fatan zuciyata da taka su narke su zama abu guda, har zuwa ƙarshen rayuwa. Zan kasance cikin yi maka addu'ar samun nasara a dukkan al'amuranka, kuma zan kasance cikin son ka har ƙarshen rayuwata.

MAFARKI

Kai ne ke bayyana kullum a cikin baccina, ta cikin mafarkin da nake fatan ya zamo gaskiya watarana. Ina son ka, irin son da ke kawar da zuciya daga yin tinanin kowa face naka.

KEWA

Na yi kewar ka sosai. Na kan yi tinanin lokacin da muke shafewa tare, mu yi raha tare da farin ciki a cikinsa. Wannan tunani ne na abun da ya faru tsakanina da kai a dangane da soyayyarmu, ko zai sa ka tino da ni. Na yi rashin ka a kusa da ni.

TARAIRAYA

Zan so mu kasance tare a matsayin miji da mata, ka tarairaye ni ka nuna min irin yadda kake ji na a cikin zuciyarka a zahiri. Ni wannan shi ne kaɗai abun da nake muradi. Ina Son Ka.

AURA

Idan har da a ce wasu zasu tambaye ni wanda nake fatan na aura, amsar ba zata wuce kai ba, domin kai ne wanda zuciya ke fatan ta kasance tare da shi har abada.

BAIWA

Wanda nake fatan na aura, mutum ne na musamman mai baiwa ta musamman a cikin dubunnan samari, shi ne wanda zan iya kasancewa tare da shi a cikin wuya ko daɗi, domin na san tinaninsa a kullum, bai wuce neman hanyar da zai inganta rayuwata ba. Ina Son Ka.

SAKO MAI MUHIMMANCI

Kana da damar tura wa abokiyar tsinkar furenka, amma ba a amince wani ya yi amfani da shi da niyyar yaudarar wata ruhi ba. Akwai mai ganin ka/ki a ko'ina wato Allah. A kiyaye haƙƙin mallaka, a guje wa satar fasaha.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user