Amintaccen abin alfarmar rubuta saƙona yana neman izinin zama dirshan wajen gabatar da rubutattun saƙonnin da ke cikin zuciyata. Kyakkyawar rana da lokacin da na samu sun wadaci zuciyata wajen wakitar gangar jikina domin isar da saƙon gaisuwar aminci a gare ki. Barka da sabon wata.
Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR
Zan so a ce na zo inda kike domin na ba ki kulawa ta musamman, sai dai zan wakilta alƙalamin rubutuna domin ya iso da saƙona kafin na samu damar isowa zuwa ga babban birnin da kike sarauta. Barka da sabon wata
Abin da ke ƙaruwa a cikin raina bai yi ƙasa da ƙaruwar yawan tunanin abar sona ba, komai salon yadda nake rayuwa, sai na dinga jiyo sautin ki, koda a cikin baccina nake jin daɗi. Barka da sabon wata
Murmushi kika iya cikin tsayuwar ƙwarewar girman daraja, kin saci zuciyata da kalamanki, zuciyata ba ta yi, babu ke. Barka da sabon wata
Ina son ki, cikin so wanda doguwar tafiyar hakan, ta sa nake miki ƙauna kullum, kalamanki su ne abokan hira ta. Barka da sabon wata
Ni fa a son ki ban yi niyyar wani hutu ba, komai girman huɗubar mahassada a kanmu, ba zai girgiza zuciyata daga ƙarƙashin inuwar son ki ba. Barka da sabon wata
Alƙalamin rubutun zuciyata yana farawa cikin farkon abin da faruwar hakan ke faruwa wajen isar da saƙon so zuwa ga gimbiyar mata. Barka da sabon wata

