Wednesday, 21 May 2025

Kalaman Soyayya Masu Kara Dankon Soyayya Ga Budurwa

Tura Wannan Zuwa Ga

Ke ce mai sani murmushi a duk lokacin da na shiga duhun damuwa. Ke ce abar kulawa a lokacin da nake da rauni.


Kalaman Ƙara Danƙon Soyayya Ga Budurwa
Hoto: Freepik

Marubuci:- Hayat S.A Kwa


Zuciyata tana rawa da farin ciki a duk lokacin da na tuna ki.


Kin shige min zuciya, kin zauna canciki.


Na gode masoyiyata da kika kasance a kusa da ni.


Soyayyar ki tana ƙara min ƙarfin gwiwa kamar hasken safe.


Rayuwata ta yi armashi saboda ke.


Na zama mai sa’a da samun ki cikin rayuwata.


Ke ce babbar abokiyata kuma abar sona.


Ki sani cewa, cikin kowanne numfashi da nake shaƙa, ina jin ƙamshin soyayyarki.


Kin zama sashi na zuciya, rai da fata ta.


Ina ƙaunarki fiye da kalmomi, fiye da lokaci.


Zan ci gaba da ƙaunarki har abada, insha Allah.


Tabbas, ke kyauta ce daga Allah, mafi daraja.


Ina yi wa Allah godiya da Ya haɗa ni da ke, tamkar amsa ce ga addu’ata.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user