Monday, 12 May 2025

Sakonnin Soyayya Na Lokacin Faduwar Rana

Tura Wannan Zuwa Ga

Murmushinki ya haskake ilahirin nahiyar dukkan jikina, ganinki yana bayyano da dukkan wani kuzari da shauƙina a kullum.


Sakonnin soyayya na lokacin faɗuwar rana
Hoto: Media bom

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR


Saƙon zuciya daga ɓangaren zuciya zuwa ga kyakkyawar sarauniya, kuma abun koyi ga dukkan sauran 'yammata.


Tsarin da na tsaro zuciyata shi ne na koya mata yadda za ta rayu da ke domin aminta da nagartarki da kuma ƙwarewarki wajen rarrashin abin da kike ƙauna.


Kin kasance wata alƙarya ta musamman wadda a cikinta ne nake wanzuwar kasancewa da shauƙi madawwami.


Tunanin zuciyata a kullum shi ne ki kusantu inda na kasance. Numfashina yana fita ne a cikin naki.


Son ki ya yi ado a cikin jikina, komai nake yi ina  kasantuwa ne a cikin yanayinki.


Kin zama ma'aunin da ke yawan  auna rayuwar jin daɗin da ke wanzuwa a tare da ni idan kina nan ni ma ina nan. 


Kin iya murmushin ɗaukar ruhin zuciya musamman lokacin da laɓɓan ki suka sha ado da kwalliyar jan baki.


Ni dai na san ina sonki. Kuma zuciyata ma tana sonki.


Ki taimake ni, ki agaji ruhina domin ki taya zuciyata sonki, da kuma taimaka mata wajen kulawa da ke.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user