Wato shi fa talauci babban maƙiyi ne, babu wata soyayya tsakaninku. Idan tsautsayi ya sa har yanzu ba ku gama raba hanya da shi ba, ga wasu dabaru da za ka iya amfani da su domin ku yi hannun riga da shi.
Marubuci:- Abubakar Abba
Allah yake bayar da arziki, amma sai an yi aiki.
1. KAMA SANA’A MAI KAWO ARZIKI
Kowacce sana’a za ta iya bayar da arziki a wani zamanin, kuma ba lallai ba ne ta bayar a wani zamanin daban.
Yana da kyau ka tsaya ka duba wacce ce take bayar da arziki a zamanin da kake, ko kuma yaya za ka ingantata ta kawo arziki.
Arziki yana zuwa ne bayan an neme shi, ba’a yin arziki daga kwance.
2. KAMA ILIMI KAM-KAM
Duk yadda za’a zuga ka, kada ka yarda ka zauna ba ka da ilimin abin da kake yi.
Idan Leburanci kake, ka nemi ilimin inganta ta, idan kasuwanci kake, ka nemi ilimin gudanarwa, da bunƙasawa.
Babu wanda ya yi nasara tabbatacciya da jahilci.
3. KA YI NESA-NESA DA JAHILAI
Ko ka yarda ko kar ka yarda, mutanen da kake mu’amala da su yau da kullum suna da tasiri sosai wajen nasararka a rayuwa.
Jahilai har kullum lissafinsu ba na ci gaba ba ne, don ba su da masaniya akan me rayuwa take tafiya akai ba.
4. IDAN KA SAMU DAMA KA BAR UNGUWAR TALAKAWA
Masana halayyar Ɗan Adam, sun daɗe da fahimtar cewa zama cikin wajen da babu damarmaki yana taimakawa sosai wajen dawwamar da mutum cikin talauci.
Sauya muhalli yana tasiri sosai wajen sauya tunani, sannan yana taimakawa wajen samun damammaki, wanda idan aka yi amfani da su sai a samu dacewa.
A cikin littafin rayuwarsa, hamshaƙin mai kuɗi Femi Otedola, ya yi ƙarin haske akan wannan, a je a karanta za’a sha labari.
5. KA NEMI ILIMI AKAN KUƊI
Akwai wani babban ganganci da mutane da yawa suke yi shi ne, suna zama ba tare da sun nemi ilimin yaya ake tara dukiya, yaya ake alkintata, yaya ake bunƙasa ta ba.
A tunanin mafi yawan mutane, arziki zuwa kawai yake yi, ba tare da mutum ya yi wani hobɓasa daga ɓangarensa ba.
A tunanin mutane masu rauni, laifi ne ka nemi ilimin yadda za ka samu kuɗi ko yadda za ka yi arziki.
Don haka da yawansu suke fama da baƙin talauci.
Bayan ka nemi ilimin karatu da rubutu, to lallai ka nemi ilimin yadda harkokin kuɗi suke, zai taimaka sosai.
6. KA YI ƘOƘARI MASU ARZIKI SU SAN DARAJARKA
Kar ka yarda ka kulle kanka a waje ɗaya, idan Allah ya ba ka ilimi, ka yi ƙoƙari ka fito da shi duniya ta sani.
Ka yi ƙoƙari duk inda ake harkar arziki kai ma a gan ka a wajen, bayan ka je wajen, ka tabbatar ka nuna baiwar da Allah ya yi maka.
Daga haka ake samu silar arziki.
Kar ka yarda da shirmen jiran 'yan siyasa, ko Auren Hajiya, ko 'yar masu kuɗi, wannan duk baragada ce.
Ka gina daraja, ka yi tsari mai kyau, ka yi addu’ar dacewa.
7. KA TABBATA KA KOYI HALAYE MASU KYAU
Kyawun hali da mu’amala mai kyau tana ba wa mutum arzikin da bai taɓa zato ba.
Kar ka zama mai kaushin hali, ko mai wahalar mu’amala da mutane, ko mara haƙuri da juriya, ko mai yawan aibanta mutane, ko mai yawan gulma da neman laifin mutane, duk wanda ka ga yana wannan munanan ɗabi’un, to ka tabbata ba inda zai je a rayuwa.
8. KA CIRE TSORO DA SON JIKI
Ka daina tsoron shiga harkar da za ta ba ka alheri in dai halal ce.
Ka daina tsoron abin da mutane za su ce, ko abin da 'yan uwanka za su ce, ko abin da matarka, budurwarka ko abokanka za su ce.
Wannan shi ne abu na farko da zai ba ka damar shiga rayuwa mai cikakken 'yanci.
Arziki ba ya zuwa da tunani ƙarami ko lissafin mai tsoro.
9. KA KULA DA LAFIYARKA
Lafiyarka ita ce babban jarinka, babu wani abu da zai tafi daidai idan lafiyarka ba ta kan saiti.
Lafiyarka tana da tsada, don haka kada ka yi wasa da abincinka, hutunka, baccinka da motsa jiki.
Kada ka yarda wani aiki, ko wani mutum ya hana ka samun waɗannan ababen.
Ni ne jagoran masu yaƙi da talauci da tunani irin na talauci.
Idan kana son samun haske da samun dabaru masu inganci akan yadda za’a samu hanyar da za ta ɓulle, to nan ce babbar tasha.
Ka ci-gaba da bi na, tare da yaɗa wannan saboda wasu ma su amfana, da haka ne za mu fatattaki talauci da 'yan koren sa.

