Tuesday 9 April 2024

Karanta Zafafan Sababbin Kalaman Barka Da Shan Ruwa

Tura Wannan Zuwa Ga

AMFANI 


Mene ne kalmar ina son ki, idan har ba zan iya yin komai a kanki ba? Mene ne ma'anar cewa ina son ki, idan har farin cikin ki ba zai iya zamo wa nawa ba? Mene ne ma amfanin soyayyar idan har ba ta zamo silar murmushin ki ba? Ba wannan ba ma, mene ne amfani na idan har ban tura miki da saƙon Barka Da Shan Ruwa Ba? Ina fatan kin sha ruwa lafiya? Ina son ki!


Barka Da Shan Ruwa
Hoto: Photo Sune


LEMA


Da zan iya yi ko zamo wa duk abin da na so a rayuwa, da kuwa zan zamo miki laima/lema, ta yadda rana ba za ta taɓa min ke ba, na zamo miki AC ta yadda ba za ki ji zafin ranar ba, na rage miki tsayin wuni, ta yadda za ki sha ruwa kafin kowa,  haka ma na ƙawata daren ki da daddaɗan iska,  ta yadda za ki yi baccin ki cikin salama. Ina son ki. Barka Da Shan Ruwa! Fatan kin sha ruwa lafiya?


ZAFI


Da a ce kina kusa da ni, na sani wuni ba zai yi min tsawo ba, duniyar ba za ta yi min zafi ba, haka ma maƙogwarona ba zai bushe ba, da a ce kina a tare da ni, na sani ƙarfina ba zai ƙare ba, wahala ba za ta kusance ni ba, haka ma  cikina ba zai yunwa ba, kuma da a ce kina kusa da ni, na sani ba zan yi wahalar rubuto miki saƙon Barka Da Shan Ruwa Ba!  Zan faɗa miki ne kai-tsaye, fatan kin sha ruwa lafiya? Ina son ki! 


SAƘO 


Idan har farin cikina zai iya zamo wa naki, damuwarki kuma tawa, to kuwa ki saka a ranki, duk sanda azumi ya ba ki wahala, ya ba ni kwatankwacin ta. Duk sanda azumi ya ba ki wahala, zan iya ganewa, domin kuwa ni ma zan ji a jikina. Ina fatan sakona ya same ki cikin koshin lafiya, kuma ina miki fatan an sha ruwa lafiya. Barka Da Shan Ruwa.


BUƊA BAKI 


Zan so zamo wa ruwan sanyin da kike sha, yayin buɗa baki, domin na sanyaya zuciyar ki, kuma zan yi burin rikiɗewa zuwa ruwan ɗumin da kike fara saka wa cikin ki, domin samar miki da natsuwa a yayin buɗa baki. Ina ma a ce zan iya zamo wa hatta abincin da kike taunawa da ƙayatattun haƙoran ki, da kuwa farin ciki ba a magana, har abada fatana ba ya wuce zamo wa gaba-daya naki. Ina Son Ki. Barka Da Shan Ruwa.


GORO


Na kasa yarda da karin maganar Hausawa da suke cewa, "Rai dangin goro, sai da hutawa.". Domin kuwa tun da na fara son ki nake ji a raina, hutu ba nawa ba ne. Idan hannuwana ba sa aikin rubuta saƙo a gare ki. To, kuwa su na nan riƙe da waya ina magana da ke. Da baki ya ƙare nasa aikin, ido yake fara   aikin kallon hoton ki. Aikin zuciya kam, a kullum tunanin ki ne, har zuwa sanda bacci zai ɗauke ƙwaƙwalwata zuwa duniyar mafarkin ki, a dai irin waɗannan ayyukan, mutuwa ce kaɗai za ta sa na huta. Ina Son Ki. Barka Da Shan Ruwa.



HAUKA


Su na cewa "So dangin hauka.". Amma ni saɓanin haka na gani, bayan faɗawa ta ki soyayyar, a da ba ni da aikin yi, amma a yau na samu aikin tunanin ki, a da ban damu da kowa ba, a yau kuma Allah ya ban wacce nake matuƙar damuwa da ita, da ba ta kulawa. A da ban da wata manufa, amma a yau kin fuskantar da tunanina zuwa ga raya sunnar babban masoyina Annabi Muhammad (S.A.W), ai kuwa kin ceto rayuwata, kin ba wa rayuwata manufa. Ina son ki. Barka Da Shan Ruwa.



ALKAWARI


Idan kika ɓuya, zan gano ki. Idan ba kya nan zan nemo ki. Idan kuma kika tafi, zan jira ki, amma fa idan wani ya yi kuskuren raba ni da ke, to kuwa dole zan yaƙe sa, domin ke tawa ce ni kaɗai, ba zan taɓa iya raba soyayyar ki da kowa ba a duniya. Da a ce 'Yan Adam su na da iko akan komai, da kuwa na ba ki damar shiga zuciyata don ki ga hakikanin girman son da nake yi miki a zuciyata, amma tunda ba zan iya hakan ba, alƙawari ne a kaina zan ci gaba da sanar da ke yadda nake son ki a zuciya, har zuwa ranar da zuciyar ki za ta gamsu cewa soyayyata a gare ki gaskiya ce.


NI'IMA


Da a ce ni kurma ne, zan iya jin ki ne ta hanyar murmushin ki, da kuwa ni bebe ne, zan iya magana da ke ta idanuwan ki, da na kasance makaho kuma da kowacce bugawar zuciyar ki, zan san ma'anar ta. Wasu lokutan, idan na ƙura miki ido, sai na riƙa mamakin yadda wani kafin ni bai taɓa ganin abin da ni nake iya gani a tattare da ke ba, ina kasa fahimtar yadda wani bai taɓa ganin tsantsar kyawun da Allah ya ajiye a tattare da ke ba, amma kuma na kan gode wa Allah da ya sa ba wanda ya taɓa lura da hakikanin baiwar da Allah ya ajiye a tattare da ke, domin kuwa da hakan ya faru, da zuwa yanzu wasu ne akan matsayin da nake a yanzu. Na gode wa Allah da ya ni'imta ni da babbar ni'ima a rayuwata.


Sanusi Kabir ne ya gabatar da su, wakilin mu ya fitar da su a rubuce, ga wanda yake son ya saurare su a ainihin yadda suke, zai iya sauke Audio ɗin ta hanyar latsa nan.
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user