Showing posts with label Zauren Ma'aurata. Show all posts
Showing posts with label Zauren Ma'aurata. Show all posts

Tuesday, 3 December 2024

Hanyoyin Da Ma'aurata Ko Masoya Za Su Ji Daɗin Soyayyar Su

Hanyoyin Da Ma'aurata Ko Masoya Za Su Ji Daɗin Soyayyar Su

Kyautata so da ƙauna


Yana da matuƙar alfanu ga ma’aurata da su sanya wani lokaci a kullum, komai ƙanƙantar shi, wanda za su riƙa yin hirar jin daɗi da ɗebe kewa a tsakaninsu, yin haka zai yi matuƙar kyautata so da ƙaunar da suke yi wa juna, kuma zai matuƙar inganta dangantakar da ke tsakaninsu.


Hanyoyin Da Ma'aurata Ko Masoya Za Su Ji Daɗin Soyayyar Su
Hoto: Liudmyla Glashchen/Vecteezy

Marubuci:- Ridwan Khan Adam


Duk lokacin da suke irin wannan hira, ya kamata ma’aurata su kiyaye waɗannan muhimman abubuwan:


1. Ya kasance ma’aurata sun mayar da hankalinsu ɗari bisa ɗari ga junansu, wato su saurari junansu da gabaɗayan kafofin hankalinsu.


2. Kallon ido cikin ido ya zama wajibi gare su lokacin da suke hirar, da kallon fuskar juna da fahimtar saƙon da ke zayyane a fuskar wanda zai ƙara fito da ma’anar hirar da suke yi.


3. Sauraran yanayin shauƙin da ke cakuɗe cikin kowane kalami a lokacin hirar, musamman maigida ya kamata ya kiyaye da wannan, domin mata na da wani irin halin yin magana a murguɗe, wato su faɗi magana alhali a cikin zuciyarsu ba hakan suke nufi ba, ta hanyar sauraren shauƙin da ya cakuɗu da kalamin, ko yanayin zane da launin fuska, ko yanayin sarrafa jiki ne kaɗai zai sa a fahimci maganarsu ba iyakar maganarta ke nan ba.


4. Ma’aurata su kasance masu lura da yanayin yaren jikin sunansu lokacin hirar, wannan zai ƙara kusanci da jin daɗin hirar gare su.


Sarrafa yanayin jiki


Sarrafa yanayin jiki ya dace da kalaman ƙaunar da ake bayyanarwa, shi ma yana matuƙar ƙara fa’ida da tasirin kalaman bayyana soyayya tsakanin ma’aurata.


1. Kowanne kalami; kowanne karin murya, akwai irin yanayin lauya jikin da ya fi dacewa da shi.


Fuska ita ce madubin zuciya, duk abin da mutum ke ciki, za ka iya fahimtar hakan daga yanayin da fuskarsa ta alamtar; don haka sai ma’aurata su riƙa kiyaye irin saƙon da fuskarsu ke bayyanawa lokacin da suke kalaman soyayya.


2. Lokacin furta kalaman nuna so da ƙauna, sai ma’aurata su kasance fuskarsu da launukan ƙauna, ta hanyar marairaicewa da kallon juna cikin ƙwayar ido, da sa ƙwayar idon ta yi narai-narai da shauƙin so.


3. Wajen bayyanar da sha’awa shi ma sai a marairaitar da fuska cikin hayaƙin sha’awa, tare da lallauya wasu ɓangarorin jiki yadda za su fito da ma’anar cikin kalaman da ake furtawa; misali narairaitar da ido cikin ruwan sha’awa, da jujjuya ƙwayar idon, da sarrafa girar idon, da yin gatsine cikin yanayin shagwaɓa ko cikin yanayin tsiwa (amma tsiwar wasa), murguɗa baki, ɗaga gira, yanayin tafiya, yatsina na yatsun hannu ko na jiki duka, yanga, kissa da kisisina da sauran abubuwa makamantan haka.


4. Wajen nuna godiya da jin dadi, dole ma’aurata su barbaɗa garin farin ciki da jin daɗi a fuskokinsu.


5. Wajen nuna tausayawa, sai ma’aurata su jiƙe fuskarsu da jimami da shauƙin tausayi.


Da sauran ire-iren yanayin sarrafa jiki don ya dace da kalami, yanayi da kuma buƙata.


Sarrafa yanayin murya


Wata babbar ƙa'ida da take ƙara inganci da tasirin kalaman bayyana soyayya tsakanin ma’aurata ita ce yanayi da sigar da kalaman ke fita su isa kunnen mai sauraren su.


Dole sai ma’aurata sun riƙa sarrafa murya wajen bayyana shauƙin ƙaunarsu ga juna; kowanne kalami da irin sigar muryar da ta fi dacewa da shi.


1. Kalaman nuna so da ƙauna ana furta su gauraye da shauƙin bege, cikin bayyanannun kalmomi, wani lokacin ana iya furta su cikin yanayin waƙe, ko a siririntar da murya ko a nauyaya ta don ta yi daidai da lokaci da kuma yanayi.


2. Kalaman tausayawa: suna buƙatar a tausasa murya wajen furta su, a cakuɗa murya kafin a bayyana jimamin abin da ake tusayawa domin sa.


3. Kalaman ba da haƙuri: na buƙatar a nauyaya su da muryar da-na-sani, nadama da marairaicewa.


4. Kalamana godiya: na buƙatar a ƙawata furucin su da farin ciki da jin daɗin abin da ake godewa.


5. Kalaman wasa da zaurance kuwa sai a surka muryarsu da jin daɗi da nishaɗi.


6. Kalaman sha’awa: kodai a sa murya ta yi taushi yayin furucinsu, ko a sanyaya ta, ko a siririnta murya, ko a sa murya ta yi ƙasa-ƙasa, ko a riƙa fitar da kalaman cikin raɗa, ko a riƙa fitar da su ɗaiɗai cikin yanayi na jan hankali; abin nufi dai, ma’aurata su yi ƙoƙari su riƙa karya murya cikin siga mafi dacewa da lokaci da kuma yanayi.


Kalaman sha’awa ba lallai sai sun yi ma’ana ba wani lokacin, ana iya caccakuɗa wasu kalmomi a fitar da su da wani irin karin muryar sha’awa waɗanda zai sa su yi tasiri sosai.


7. Kalaman neman alfarma sai a gauraya su da muryar kwantar da kai da marairaicewa.


Da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga masu buƙatarsa kuma ya amfanar da su Amin.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu sunan adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.

Sunday, 24 November 2024

Ire-iren Mazan Da Ya Kamata A Aura

Ire-iren Mazan Da Ya Kamata A Aura

Bayan rubutun da na yi yau akan irin matar da ya kamata a aura, da yawa sun nemi na kawo ɗaya ɓangaren wato irin mijin da ya kamata a aura, domin a samu daidaito, shawarwari da ake ba wa iyaye da wakilai da mata shi ne su tantance wanda ya kamata su ba wa aure. 


Ire-iren Mazan Da Ya Kamata A Aura
Hoto: Raw pixel

MarubuciSheikh Aminu Ibrahim Daurawa


A matsayin ka na uba ko waliyyin mace ya kamata kafin ka bawa wani auran 'yarka, ka bincike shi sosai kada a yi gaggawa, abi a sannu domin 'yarka ba abar wasa ba ce, da za ka bayar da ita ga wanda ba a tabbatar da nagarta da mutuncin sa ba. 


Akwai siffofin da halaye da ake dubawa ga mutumin da za ka ba wa aure, su ne:


1. Addini, saboda hadisin "Idan wanda kuka yarda da addininsa da halayen sa ya zo neman aure ku ba shi". A wannan hadisi an bayyana muhimman siffofi guda biyu na mutumin da za a ba wa aure, su ne riƙo da addini da halaye masu kyau. 


2 Halaye masu kyau, "Idan kun yarda da halin mutum, yana da kirki da nagarta za a iya ba shi aure". Anan an bambanta hali da addini, domin wani yana kula da salla amma ba ya kula da iyali, wani kuma yana da ilimi amma ba ya aiki da shi.


3. Sana'a da aikin yi, saboda hadisin Bukhari na Faɗimatu Bnt Ƙaysi, wanda sahabbai biyu suka fito neman auran ta Mu'awiyya da Abu Jahmin, Manzon Allah (S.A.W) ya hana ta aure su, shi Abu Jahmin yana dukan mace, shi kuwa Mu'awiyya a lokacin talaka ne ba shi da hali. Wannan ya nuna wajibi ne a binciki sana'ar mutum kafin a ba shi aure, domin idan ka aurar da 'yarka ga wanda ba shi da sana'a, duk nauyin auran kanka zai dawo.


4. Asalin sa da tushen da ya fito, a bincika asalin mutum da tushen sa a lokacin da ya fito neman aure, domin rashin sanin wannan zai iya sa wa a yi rufin gida da ɓarawo.


DUBA WANNAN: Karanta Siffofin Matan Da Su Fi Cancantar A Aure Su


5. Lafiyar sa, saboda akwai cututtuka da ake ɗauka, ya kamata ko ya wajaba a je a yi bincike game da lafiyar ma'aurata duk su biyun, domin a tabbatar da lafiyar su, kafin aure.

Thursday, 14 November 2024

Hanyoyin Da Ma'aurata Za Su Gina Tsantsar Soyayya A Tsakanin Su

Hanyoyin Da Ma'aurata Za Su Gina Tsantsar Soyayya A Tsakanin Su

Saurare kafin yanke hukunci


Ya kamata ma'aurata su rayu kamar abokai ba kamar bawa da mai gidansa ba, me ya sa muke iya sauraren hirar abokan mu ko ƙawayen mu na sa'o'i biyu zuwa uku amma mu kasa sauraren abokan tarayyarmu a aure na tsawon mintuna ashirin don lalubo bakin zaren laifukan da muke tunanin abokan zaman namu na tuhumarmu da shi?


Hanyoyin da ma'aurata za su gina soyayya a tsakanin su
Hoto: Billion photos/Freepik

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Tattauna matsaloli


Wani Bature masanin ilimin zamantakewa yana cewa "A gefen kowacce mace wadda ta yi fushi akwai namiji a zaune wanda bai san laifin da ya aikata ba...........".


Hakan yana bada matsala sosai rashin bayyana matsala idan ɗaya daga cikin ma'aurata ya hango ta a zamantakewa, wannan ya fi ga mata su ne suka fi danne abu a rai su yi ta fushi da sunan kawaici.


Matsala a aure ba a zura mata ido tana buƙatar magancewa idan da hali, aure abu ne da ba a fata ya ƙare har sai ajali don haka matsalolin shi na da buƙatar tattaunawa ta kowanne hali.


Don haka ba a cewa a yi haƙuri a zauna haka ai an kusa gamawa saura kwana kaza, abu ne mara ƙarewa.


Girmama ra'ayin juna

 

Wannnan ya haɗa da girmama ra'ayin abokin tarayya, a zahiri ne mace da namiji tunaninsu da ƙudirorin da suke son cimma da abubuwan da suka saka a gaba suke son cimma ba ya taɓa zuwa ɗaya saboda bambancin hallita da Allah ya yi musu, to amma hakan ba zai sa mu ce dole sai mun bi ra'ayin juna ba, ba lallai ba ne matarka ta bi dukkan ra'ayin ka, ke ma ba lallai ba ne mijinki ya bi dukkan ra'ayinki amma idan muka girmama ra'ayin juna sai mu zauna lafiya da junanmu.


Misali


Lokacin da nake buƙatar cin Kilishi ƙila ita a lokacin naman kifi take so, dan haka ba zan mata tilas wajen cin Kilishi ba maimakon haka zan raba kuɗin siyan kilishin biyu na siya mata kifi hakan shi ne na girmama ra'ayinta.


Lokacin da nake buƙatar na yi wa gidana fenti kalar ruwan ɗorawa ƙila matata ta fi son fentin ruwan ƙasa. Don haka zan girmama ra'ayinta ko a iya ɗakunanta ne na yi mata ruwan ƙasar sauran gidan na yi wanda nake so hakan shi ma na girmama ra'ayinta ne.


Mami lokacin da kike buƙatar hira da mijinki ƙila shi lokacin yana buƙatar keɓewa shi kaɗai ne ya yi tunanin yadda zai gyara wata matsala da ta tunkaro shi ta ɓangaren kasuwancinsa saboda yawancin maza suna gyara matsalolinsu ne ta hanyar dogon tunani da kansu saɓanin mata da suke yawan neman shawara wajen gyara nasu matsalolin don haka ba laifi ba ne Mami don kin ba shi waje da lokaci ya yi tunaninsa. Wannan shi ne girmama ra'ayin.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum.

Wednesday, 13 November 2024

Sirrin Yadda Ake Neman Aure A Musulunci

Sirrin Yadda Ake Neman Aure A Musulunci

Zaɓar abokin zama a aure ya fi kowane zaɓe wahala da haɗari, domin idan mutum ya tafka kuskure, ko ya bi son zuciya, to ya shiga matsala kenan har ƙarshen rayuwar sa, shi ya sa ake buƙatar ilimi da wayewa da bi a sannu kafin yanke shawarar fitar da abokin rayuwar aure, saboda kusanci da sirrin da ke tsakanin mace da mijin ta.


Sirrin yadda ake neman aure a musulunci
Hoto: Easy peasy

MarubuciSheikh Aminu Ibrahim Daurawa


HIKIMOMIN YIN AURE DAGA LITTAFIN KIMIYYAR AURE


Alaƙa tsakanin mace da namiji alaƙa ce mai tushe, Allah ta'ala ya gaya mana matakai uku a cikin ayar farko ta suratun nisa'i, na ɗaya, ya halicci 'Yan Adam daga Annabi Adam (A.S), mataki na biyu ya halicci matar sa daga gare shi, na uku daga gare su ya samar da dukkan maza da mata, don haka soyayya da ƙauna da bege da shauƙi da ke tsakanin su na reshe ne da tushe, an ce saboda sanin asali ya sa kare ya ci alli.


Don haka mace ta na buƙatar namiji kamar yadda namiji yake buƙatar mace, kowanne yana da abinda ɗayan ba shi da shi, wanda kamalarsa da mutuntakar sa, da buƙatar sa ta jingina ga abokin tarayyar sa.


Aure abu ne mai mahimmanci a rayuwa kuma wani babban canji ne a rayuwar mutum, idan ya yi kuskure ko ganganci, ya lalatawa kansa wani ɓangare mai girma na rayuwar sa don haka a nutsu sosai a bi ƙa'ida domin kaucewa nadama.


Zuwa zance ko ganin mace domin gabatar mata da kai, a matsayin mai neman aure, shi ne abin da malamai suke kira neman aure ko kuma kiɗbah, asali ana neman auran mace a wajen waliyinta a mataki na farko domin samun iznin ganin ta da tattaunawa da ita, don samun fahimta, kamar yadda Manzon Allah (S.A.W) ya nemi auran Aisha a wajen mahaifinta Abubakar. Bukhari 5081.


Mataki na biyu, ana iya neman auran mace kai tsaye a wajen ta idan mai hankali ce, kamar yadda Annabi (S.A.W) ya nemi auran Ummu Salamata a gurin ta, har ta bayar da uzurin yawan 'ya'ya da shekaru da tsananin kishi, ya ba ta amsa da zai riƙe mata ƴaƴan, shekaru kuma shi ma yana da su, kishin kuma zai roƙi Allah ya rage mata shi, Muslim Annasa'iy.


Mataki na uku mahaifin mace ko waliyinta zai iya gabatar da ita ga mutanen kirki, domin sama mata miji, kamar yadda S. Umar ya gabatar da 'yarsa Hafsah ga S. Abubukar, sannan Usman daga baya Manzon Allah (S.A.W) ya aure ta. Bukhari 5122. Da hadisin Umma Habibah da ta nemi Manzon Allah (S.A.W) ya auri ƴar'uwarta, ya nuna mata ba ya hallata a musulunci haɗa 'yan'uwa a igiyar aure ɗaya a lokaci ɗaya. Bukhari 5107.


Mataki na huɗu ya halatta mace mai hankali ta gabatar da kanta da wani mutum nagari ko zai amince ya aure ta, kamar yadda wata mata ta gabatar da kanta ga Manzon Allah (S.A.W) ko zai amince ya aure ta, Bukhari 5120. 


Mataki na biyar wani ya na iya zama sila ko dalili wajen shige wa gaba wajen ƙulla alaƙar aure tsakanin masu neman aure kamar yadda kaulatu Bnt Hakeem ta gabatarwa da Manzon Allah (S.A.W) auran Nana Saudah bayan wafatin mijinta. 


Mataki na shida za a iya kafa wata ƙungiya mai ɗauke da amintattun mutane masu ilimi da sanin haliyyar jama'a, su ɗinka zama masu dalilin aure, duk mai neman aure mace ko namiji sai ya je gurinsu, domin tantancewa da shigewa gaba wajen haɗa aure.


Mataki na bakwai za a iya buɗe wata kafa a yanar gizo, domin wannan aiki amma yana buƙatar aiki da saka ƙaidoji domin kada a canja munufar buɗewar zuwa wani abu daban. 

Tuesday, 12 November 2024

Shin Da Gaske Ne Babu Soyayya A Rayuwar Aure?

Shin Da Gaske Ne Babu Soyayya A Rayuwar Aure?

Babu soyayya a cikin aure, soyayya a cikin zuciyoyin ma'aurata take, su ne za su ɗauko soyayyar su saka ta cikin zamantakewar auren su, lokuta da dama saurayi da budurwa sukan yi aure cike da soyayyar juna a zukatansu, amma auren ya kasa zuwa ko'ina ko ka san dalili ? Saboda soyayyar a zukatansu take ba su ɗauko ta sun sakata cikin zamantakewarsu ta aure ba.


Shin da gaske ne babu soyayya a rayuwar aure?
Hoto: Billion digital/Deposit photos

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Yawancin mutane sun yarda da wata tatsuniya akan aure cewa wai aure wani akwati ne mai kyau, mai cike da duk abubuwan da Ɗan Adam ke buƙata don zamantakewar rayuwa kamar irin su zumunci, tausayi, abota, kyautatawa, girmama juna da dai sauransu, gaskiyar magana shi ne aure a farkon shi kamar akwati ne mara komai a ciki "Empty box". 


Dole ne ma'aurata su ne za su sanya wani abu a cikin akwatin daidai da yadda suke son rayuwar auren tasu ta ɗoru akai.

Sunday, 10 November 2024

Alaƙar Ɗabi'un Mace Da Na Mahaifiyar Ta A Soyayya Ko A Aure

Alaƙar Ɗabi'un Mace Da Na Mahaifiyar Ta A Soyayya Ko A Aure

Yadda take magana


'Ya tana ɗauko yadda mahaifiyarta ke magana ne a yawancin lokuta ban ce kowacce ba amma kaso 99 na 'ya'ya mata suna magana yadda mahaifansu mata ke magana ba wai murya ba sam, ina nufin idan uwa masifaffiya ce to haka za ta taso da magana kamar ana yaƙi babu tausasawa, kuma haka za ta dinga yi maka idan kuka samu saɓani maƙwabcinku na uku ma sai ya jiyo abinda ake yi daga gidansa.


Alaƙar ɗabi'un mace da na mahaifiyarta a soyayya ko a zamantakewar aure
Hoto: Rahhal/Shutterstock

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Matuƙar da gaske kake so za ka auri mace to ka tabbatar ka san wasu da yawa daga halayyar mahaifiyarta.


Eh mahaifiyarta nake maka magana wadda ta haife ta za ka ji abun kamar izgilanci sam ba haka ba ne.


Saboda akwai halayen da 'ya mace take ɗauka wajen mahaifiyarta ko ana ha maza ha mata dole sai ta kwaso wannan halayyar matuƙar ita ta haifetan kuma ita ta tarbiyyantar da ita.


Kada soyayya ta rufe maka ido, soyayya kawai zallar ta ba ta iya riƙe aure har zuwa shekara da shekaru.


Tsara kashe kuɗi


Kaso 100 na halayyar mata suna gado mahaifansu mata ne ta ɓangaren almubazzaranci ko alkinta kuɗi. Idan surukarka almubazzara ce to matarka ma haka take kwabo da kwabo, haka idan surukarka ta iya tsumi da tanadi haka matarka za ta kasance.


Dabara da wayo da fasahar magana 


Kusan kaso 80 na mata suna kwaso dabara da wayo na mahaifansu mata ne, tun daga dabarar iya sarrafa abinci da wayon zama da miji, da fasahar magana.


Haƙuri da juriya


Kaso 90 na haƙurin mace tana kwaso shi ne daga wajen mahaifiyarta haka juriyar zaman gidan miji.


Mu'amala


Dukkan ɗabi'u na mu'amala da mutane  mace tana kwaso su ne daga wajen mahaifiyarta, idan babarta tana da mu'amala kyakykawa da mutane haka 'yar ta za ta taso.


Bari na fito maka a mutum idan surukarka ba ta da kyakyawar mu'amala da dangin mijinta wato dangin baban matarka kenan, to ina tabbatar maka ita ma matarka ba za ta gina kyakyawar mu'mala da danginka ba saboda ta taso a gida ta ga mahaifiyarta haka take. Don haka ita ma ba za ta maida hankali wajen damuwa da su ko girmama su ba.


Kula da gida


Wannan babu ja yadda surukarka take wajen tsaftace gida da kula da gida haka matarka za ta kasance a gidanka. Idan babarta ƙazama ce wajen kula da gida haka za ta zo gidanka ta yi ta ƙazantarta, idan kuma ka yi sa'a kuma surukarka mai tsaftace haka matarka za ta kasance.


Don haka idan za ka nemi aure a gida ka yi ƙoƙari ka san halayyar surukarka domin kuwa ita ce halayyar da matarka za ta kasance ciki idan ka aure ta.

Thursday, 24 October 2024

Miji Na Gari A Al'adar Hausawa

Miji Na Gari A Al'adar Hausawa

A al'adance, tun asali Bahaushe yana da sigogi da yawa na auna hankali da tunani ko mu'amular wanda ko wadda zai aura.


Miji Nagari A Al'adar Hausawa
Hoto: Getty images


Marubuci:- Hamza Dawaki

Daga ciki akwai duba yadda yake mu'amulantar mahaifiyarsa wato idan aka tarar mutum yana da kyakkyawar mu'amula da mahaifiyarsa. Ya kan zauna su yi hira ya ma taya ta wasu ayyuka da sauran abubuwa da ke kyautata dangantaka, sai a ce, lallai wannan zai kyautatawa matarsa yayin ƙuruciyarta. 


Kuma idan ta tsufa zai tausaya mata amma wanda aka ga ba ya kyautata mu'amula da mahaifiyarsa, ba ya yin wani abu na nuna mata tausayawa. To wannan sai a ce, ba zai tausaya wa matarsa yayin da ta tsufa ba. 


Kawai dai zai iya son ta da ɗoki da zumuɗin ta ne a lokutan da take kan ganiyar ƙuruciyarta.


Domin shi So da sha'awar mace dole ne, kamar yadda son mazan ya zame wa matan, saboda ɗabi'a ce da Ubangiji subhanahu wa ta'ala Ya gina kowa a kai. Don haka, kowa ma zai iya son mace amma girmama ta da ganin kima da tausaya mata kuma ɗabi'a ce da ba kowa ne ke da ita ba.

Tuesday, 24 September 2024

Karanta Sirrin Samun Soyayya Ta Har Abada Ga Masoya

Karanta Sirrin Samun Soyayya Ta Har Abada Ga Masoya

Soyayya ta kasu kashi daban-daban dangane da ɗan tsiron da ya shuka ta tun farko da kuma yadda aka ma gudanar da ita yayin da take girma da kuma irin sakamakon da ake sa ran samu daga gare ta.


Sirrin Samun Soyayya Ta Har Abada Ga Masoya
Hoto: Stock Adobe

Marubuci:- Abubakar Muh'd Adam


A jimlace, soyayyar auratayya tana da launauka guda biyu: cikakkiyar soyayya da kuma sarƙaƙƙiyar soyayya.


1. Cikakkiyar Soyayya: ita ce kammalalliyar soyayya da ya kasance komai ya ji a cikinta; ita ce soyayyar da ya kamata a ce kowanne aure a kanta yake tafiya; ita ce soyayya mai cike da so, ƙauna, rahama da tausayin juna; ita ce soyayyar da ke cike da shaƙuwa, fahimtar juna, mutunta juna da sha’awar juna; ita ce wacce ta ƙunshi dukkan mafi kyawun sinadaran soyayyar nan guda huɗu da bayaninsu ya gabata.


Daɗin dacewa da cikakkiya kuma kammalalliyar soyayya, daɗi ne da babu irinsa a zuciyar Ɗan Adam; yana daga ruhin Ɗan Adam zuwa ga ƙololuwar farin ciki; don haka babban al’amari ne da ya kamata dukkan ma’aurata su dage ga riƙe shi da kyau; ya zama samun irin soyyaya shi ne burinsu; su riƙe shi kamar wani muhimmin kasuwanci mai cike da arziki mai yawa; kar su bari jarinsu a wannan kasuwanci ya karye.


Idan ma ya karye, su yi dukkan ƙoƙarin da ya kamata don ƙara samun jarin zubawa don guje ma kasancewa cikin ƙuncin kishiyar hakan a rayuwar auren su.


Za mu ci-gaba Insha Allah.


Da fatan Allah ya horewa dukkan ma'aurata wannan kyakkyawar soyayya Amin.

Wednesday, 18 September 2024

Abubuwa 20 Da Za Ku Yi Mace Ta Makance A Soyayyar Ku Kamar Tsafi

Abubuwa 20 Da Za Ku Yi Mace Ta Makance A Soyayyar Ku Kamar Tsafi

Ya kai ɗan uwana ka sani ɗabi'ar 'ya mace kamar iska ce da take kaɗawa a hankali, idan ka furta wa 'ya mace kalma mai kyau to za ka tashi a tutocin soyayyarta. Idan kuma kai mata magana mara daɗi koda kalma ɗaya ce za su rusa soyayyarka.


Abubuwa 20 Da Za Ku Yi Mace Ta Makance A Soyayyar Ku Kamar Tsafi
Hoto: Shutterstock


MarubuciImran Musa Jahun


Lallai ne ana son namiji ka siffantu da waɗannan siffofi ashirin ɗin domin ka samu cikakkiyar soyayya da ƙauna a wurin

matarka.



1. KA MUTUNTA MATARKA: Ka nuna mata kai da ita duk abu ɗaya ne ba bambanci kana da buri ita ma tana da shi, kana da sha'awa ita ma haka, lallai ne ka mutunta ta, kamar yadda kai ma kake son ta girmamaka.


Manzon Allah (S.A.W) yana cewa "Duk wanda ya samu mace to ya girmamata.". Don haka kuskure ne da jahilci a hanawa mace 'yancin faɗar ra'ayinta ko neman shawararta, ko tattaunawa da ita a cikin wasu al'amura.


Kar a maida ita kamar kayan

wasan yara, ba a nemanta sai za a buƙaceta, duk wanda yake wa mace irin wannan ɗabi'ar tabbas zai rasa soyayyarsa a cikin zuciyar matarsa.


2. KA ZAMA ABOKIN MATARKA: Ma'ana ka yi mu'amala da ita ta kowanne ɓangare, kada ka bar wata kafa a buɗe ta yadda za ta fahimci ba ka damu da ita a wannan ɓangaren ba, lallai ne ka zama mai ɗebe mata kewa ta kowanne ɓangare, mai saka ta farin ciki da nutsuwa.


3. KAR KA ZAMO MAI CIN DUNDUNIYAR TA: Ma'ana kai a kullum burinka so kake ka ga ta yi laifi kai kuma ka buɗe mata wuta. A'a! Ka zama tamkar mai koya mata yadda

za ta yi rayuwa, inda ta kauce sai ka saitata domin a kullum ita mai raunin tunani ce idan har ta aikata mara kyau, to kada ka sakamata da mara kyau. A'a! Sai ka saitata da mafi kyau, tabbas za ka dace da soyayyarta.


4. LALLAI NE KA ZAMA MAI JURE WAUTAR 'YA MACE: Ka zama mai kyautata zamantakewarka gare ta, ka saki fuskarka

gare ta, ta yadda ba za ta rainaka ba, ma'ana kada ka yi sakacin da za ta iya raina ka.


5. KA ZAMA MAI TAIMAKONTA: Yayinda ta

shiga tsanani, kada ka yi banza da ita.


6. Ka zama mai ɗebe mata kewa yayinda

take ita kaɗai.


7. Ka zama shimfiɗar kwanciyarta yayinda

ta buƙaci bacci.


8. Kar ka nuna mata ƙosawa ko ka fara gajiya da ita.


9. Idan ta kamu da cuta kar ka share ta, ka yi iya ƙoƙarin ka wajen nema mata waraka.


10. Idan za ka shigo mata gida to ka shigo da murmushi, kuma idan za ka fita ka fita da murmushi. Hmmmmm.


11. Kar ka tozarta ta yayin da ta nemi wata

buƙata a gare ka, kuma idan har za ka yi mata alkhairi, to kada a yi mata mafi ƙaranci.


12.  Idan ta yi abu mai kyau, ka yabe ta ka gode mata.


13. Idan ta yi kuskure, ka yafe mata.


14. Kar ka yabi wata mata a gabanta.


15. Ka zama mai tsafta da kwalliya.


16. Kar ka zama mai yawan mita da dawo da kuskuren da ya wuce.


17. Ka zama mai kishin iyalinka, kar ka zama Dayyus.


18. Ka zama mai girmama 'yan uwanta,

musamman iyayenta.


19. Ka zamo mai kiyaye sirrinta, kada ka

zama mai yaɗa kuskurenta a cikin ɗaiɗaikun jama'a.


20. Kar ka zama mai son kai, wato ka girmama kanka, ita kuma ka wulaƙantata.


Da fatan za mu kiyaye.


Domin ci gaba da samun ire-iren waɗannan abubuwan, sai ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe.

Thursday, 12 September 2024

Karanta Siffofin Matan Da Su Fi Cancantar A Aure Su

Karanta Siffofin Matan Da Su Fi Cancantar A Aure Su

Kafin mutum ya yanke shawarar yin aure ya kamata ya bi matakai guda uku.


1. Ya yi istikharah wato neman zaɓi daga wajen Allah , ya yi sallah raka'a biyu, kamar yadda ya zo a hadisin Jabir ɗan Abdullahi daga riwayar Bukhari 1166, bayan ya yi sallama (wasu malamai suna ganin za a iya yin wannan addu'a kafin sallama, kamar shekhul Islam Ibn Taimiyya ) sai ya ƙaranta wannan addu'a ta neman zaɓi daga Allah.


Siffofin Matan Da Su Fi Cancantar A Aure Su
Hoto: Mother and beyond


MarubuciSheikh Aminu Ibrahim Daurawa


2. Ya nemi shawara daga masana addini da ɗabi'u da halayya, da gogayya da harkokin aure, domin su ba shi shawara bayan sun saurare shi sun ji irin tasa buƙatar, wanda yake shawara ba zai yi nadama ba. 


3. Dole mai neman aure mace ko namiji su cire son zuciya idan su na neman aure na gari, duk da shari'a ba ta yarda mutum ya auri matar da ba ya so ba, amma mafi yawan mata na gari ba su fiye kyau da yawa ba, don haka idan an sami mace mai kyau amma ba ta da tarbiyya, da mai addini da tarbiyya amma tana da ƙarancin kyau sai ka ga an raba hankalin mai neman aure.


Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Ana auran mace saboda abu huɗu, saboda kyawunta ko kuɗinta ko matsayin ta ko addininta, ka rabauta da mai addini, idan ka ƙi hannun ka ya yi turɓaya. Bukhari 5090. Daga Abu Hurairah (R.A)


Waɗannan  abubuwa guda huɗu su ne mafi yawan masu neman aure suka fi buƙata ga mace, amma ana samun wata ta haɗa dukkan waɗannan siffofin, wata kuma ta samu uku daga ciki, wata ta samu biyu wata siffa ɗaya kawai take da ita daga cikin waɗannan siffofin.


Wacce ta fi ita ce wacce ta haɗa dukkan waɗannan siffofin;


1). Mai kyau, mai kuɗi, mai matsayi, mai addini dukkan huɗun tana da shi.


2). Mai addini da kyau. 


3). Mai matsayi da kuɗi amma babu kyau babu addini. 


4).  Mai addini amma babu kuɗi.


5). Kyakkyawa amma babu tarbiyya ta addini.


6). Mace tana da siffofi guda biyu na fili kamar kyau da muni ko baƙi da fari ko tsawo da gajarta, a kwai kuma siffofi na ɓoye kamar kirki da haƙuri da tarbiyya da juriya da iya zaman aure.


Mafi yawan mutane sun fi son mace mai kyau, wannan kuwa ba laifi ba ne, amma idan mutum ya auri mace saboda kyawun ta kawai, lokacin da kyawun ya tafi, sai ka ga mace tana samun canji daga mijinta, saboda abinda ake son ta saboda shi ya tafi ko ya ƙare, kuma mace mai kyau kawai babu tarbiyya sun fi wahalar da mazan su da halakar da su, domin za su dinga yin abinda bai kamata ba. A wasu lokuta domin su faranta musu ko da hakan ya saɓawa Allah da Manzon sa.


Kowa a cikin masu neman aure daga cikin maza ko mata akwai siffofin na fili da yake sha'awa daga matar da yake so ya aura, ko daga mijin da take so ta aura, kamar fara ko baƙa ko doguwa ko gajeriya, mai ƙiba ko siririya, kyakkyawa ko mummuna, amma shi kyau da muni ya dangana ne da abin da mutum yake so, domin mummuna a wajen wani kyakkyawa ce, kuma kyakkyawa a wajen wani mummuna ce.


Ya tabbata a hadisi daga Maa'ƙalu ɗan yasar ya ce : wani mutum ya zo wajen Manzon Allah (S.A.W), sai ya ce : Na samu wata mata zan aura tana da matsayi kuma mai kyau ce, na iya auran ta? sai ya ce masa a'a, bayan lokaci sai ya dawo ya kuma yin wannan tambaya ya ƙara ce masa a'a, a karo na uku sai ya ce masa : Ku auri mai iya soyayya, mai haihuwa, domin zan yawaici al'umma da ku. Abu Dauda 2050. Nasaiy 3227. Silsila Na Albaniy. 2373.


Wannan hadisi ya zo da ƙarin siffofi guda biyu su ne soyayya da haihuwa, yaya za a yi zaman soyayya, kuma a haifi 'ya'ya a yi musu kyakkyawan reno, don haka muna iya ƙara waɗannan siffofi akan na farko su zama siffofi shida.


Akwai wani hadisi ya zo daga Abdullahi ɗan Amri, ya ce : Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Duniya wani jin daɗi ce, mafi jin daɗin duniya shi ne samun mace ta gari, Muslim ya ruwaito.


Sai aka fassara mace ta gari a wata riwayar da Tirmiziy ya ruwaito da  siffofi guda biyar, wacce idan ka kalle ta za ta faranta maka rai, idan ka ba ta umarni za ta yi maka biyayya, idan ka yi mata rantsuwa ko kashedi ba za ta saɓa maka ba, idan ba kanan ko ka yi tafiya za ta kiyaye maka dukiyar ka da mutuncin ta.


Idan muka kalli waɗannan hadisai guda uku za mu ga sun zo da siffofi  guda goma sha ɗaya kenan.

Su ne:


1). Mai Addini.

2). Mai kuɗi.

3). Mai kyau.

4). Mai matsayi.

5). Mai soyayya.

6). Mai haihuwa 

7). Mai faranta rai.

8). Mai biyayya.

9). Mai ɗaukar tsawa da kashedi.

10). Mai kiyaye dukiya.

11). Mai kiyaye mutuncin ta.


Daga waɗanan hadisai na Manzon Allah (S.A.W) muka samo waɗanan siffofin na irin matar da ya kamata mutum ya nema, amma da wuya a sami wacce ta haɗa dukkan waɗannan siffofin.


Mace mai tarbiyya dai ita ce abin nema, idan ka samu mai tarbiyya ka gama more aure.

Tuesday, 10 September 2024

Miji Nagari A Ilimance

Miji Nagari A Ilimance

Masana suna ganin duk yaron da ya taso a hannun mace mai ƙoƙari ta fannin tarbiyya da kamanta gaskiya a cikin maganganunta, da sa ido sosai wurin tabbatar da cewa ta ɗora shi a tafarki madaidaici, wadda kuma take nuna masa so, da jan sa a jiki tare kuma da kiyaye duk wani abu da bai kamata ya ji ko ya gani daga wurinta ba. To wannan yaron zai iya kasancewa mutum mai ganin kima da darajar mata, kuma zai girmama su. Don haka zai iya kasancewa miji nagari.



Miji Nagari A Ilimance
Hoto: Arab America


Marubuci:- Hamza Dawaki


Amma yayin da yaro ya taso a hannun ballagazar mace, wadda za ta iya sakin jiki ta shirga ƙaryarta a gabansa. Ta yi zage-zage da sauran maganganu na wauta da sakin layi yana ji. Kuma ta rika aibata mahaifinsa ko nuna bai isa ba a kan idonsa. Kuma ba ta ja shi a jiki ta nuna masa so ba. 


To hakika wannan yaron zai iya samun matsala a tunaninsa. Ta inda zai kasance yana kallon mata a matsayin marasa daraja da kima kuma masu tsananin butulci da rashin kamun-kai. Don haka kuma wannan yaron mawuyacin abu ne ya iya zama miji nagari ga iyalinsa.

Tuesday, 3 September 2024

Hakikanin Miji Nagari

Hakikanin Miji Nagari

Mafarkin kowacce mace nutsattsiya da ko waɗanne iyaye akilai a rayuwa, ba ya wuce MIJI NAGARI, domin shi ne mafi dacen da 'ya mace za ta yi a rayuwa.


Miji Na Gari
Hoto: Free Pixel

Marubuci:- Hamza Dawaki


Kasancewar shi miji ba wai abokin zama ne kaɗai ba. Sau da dama ya kan zama kamar malami mai tarbiyya ne ga mace.


Kodayake, abu ne da ba kasafai akan yi rubutu a kai ba, amma ina ganin kamar yadda ake yawan yin rubutu game da MACE TAGARI, haka nan ya dace a riƙa yi a kan miji na gari ko kuma ma fiye da hakan. 


Dalili a nan shi ne, macen da ta yi rashin katari ta auri mijin da ba na gari ba, ta fi shiga haɗari a kan namijin da ya auri macen da ba ta gari ba, saboda shi idan ya ji wuya zai iya yakice ta, ya huta amma ita (musamman idan ba wayayyiya ba ce sosai), ba ta da wata mafita illa dai ta ci gaba da irin zaman nan da suke cewa zaman haƙuri. Tun da ita ba ta da damar saki, kamar yadda namiji ke da ita. 


Akwai abubuwa da dama da ya kamata mu duba a tare da mutum don ƙoƙarin gano shin zai iya kasancewa miji na gari, ko kuwa dai miji gama-gari, waɗannan suffofi za mu iya dubansu ta mahangu da dama. Kamar mahangar ADDINI da AL'ADA da kuma KIMIYYAR HALAYYAR BIL'ADAMA da sauransu.


Haka nan kuma za mu kalli yanayi ko suffar mazan da ake sa ran za su iya zama maza nagarin, kafin da kuma bayan aurensu.

Zazzafar Wasikar Soyayya Zuwa Ga Miji Mai Kayatarwa

Zazzafar Wasikar Soyayya Zuwa Ga Miji Mai Kayatarwa

Dr. John Gray yana bayar da labarin farko-farkon shigarsa cikin rayuwar aure, ya ce: “Ina tuna shekararmu ta farko da matata. A lokacin bayan rubutun littafi da jagorantar tarukan bayar da bita da nake yi. Ina kuma ganawa da masu matsaloli daban-daban da suka shafi zamantakewar aure, don ba su shawarwari, a ƙalla na awanni hamsin a kowane mako. A wannan shekaran takan yawaita bayyana damuwarta game da yadda take buƙatar lokacina, da kuma irin damuwar da take shiga sakamakon rashin samun lokacin.


Zuwa ga mijina
Hoto: Wengood


Marubuci:- Hamza Dawaki


“Lokuta da dama tana bayyana damuwarta ta hanyar rubuta wasiƙa. Irin wasiƙar da muke cewa Wasiƙar Soyayya. Wadda takan ƙunshi yawancin abubuwan da suke sosa rai. Kamar damuwa da fushi da tsoro da sauransu. (Za mu tattauna sosai game da irin wannan wasiƙa: amfani da muhimmancinta nan gaba.) A irin lokacin ne ta rubuto min wannan wasiƙar soyayyar, game da yadda nake daɗewa a wurin aiki”: 


Barka Dai John,


Na rubuto maka wannan wasiƙa ne don bayyana maka abin da yake cikin raina. Ba na nufin in koya maka yadda za ka gudanar da rayuwarka. Kawai dai ina fatan ka fahimci ainihin yanayin da nake ciki ne.  


Ina cike da damuwa ƙwarai game da yadda kake cinye mafi yawan lokacinka a wurin aiki. Na damu ƙwarai da yadda kullum sai bayan ka gaji tiƙis kake nufo hanyar gida. Ga shi ni kuma ina cike da burin kasancewa tare da kai na tsawon lokaci. Na damu ƙwarai da yadda na lura cewa ka fi ba wa mutanen da suke zuwa neman fatawa wurinka muhimmanci fiye da ni.


Na fara jin tsoron kamar sam kai ba ka buƙatar kasancewa tare da ni a cikin mafi yawan lokacinka. Ina tsoron ko dai shigowata rayuwarka bai zama komai ba face ƙarin matsala gare ka! Ina kuma tsoron kar ka ce na cika naci. Sannan kuma ina tsoron ko kai ba abin da ya shalle ka da damuwata!


Amma ina neman afuwarka, idan waɗannan maganganun sun yi maka zafi, ko kuma ka ji su bambaraƙwai. Na san kana yin bakin ƙoƙarinka. Kuma ba zan gushe ba ina mai yaba maka.


Masoyiyarka, Bonnie."


Ko me zai biyo baya?


Ya ce: “Bayan kammala karanta wasiƙar tata ne na tabbata da gaske ne, ina ba wa masu zuwa neman shawarwarin wurina lokaci da cikakkiyar kulawa fiye da yadda nake ba wa matata. Sai in ba su lokaci da kuma cikakkiyar nutsuwa wurin sauraren su. Kuma kafin in zo gida na riga na gaji tiƙis. Don haka, ba ni da wani abin a zo a gani da zan iya yi wa matar tawa.”.


A baya, shi yana tunanin ya zage damtse ne yana yin aikin da zai taimake su tare, wato neman kuɗi, don ɗaukar ɗawainiya da gatata su. Sai bayan wannan karatun-ta-nutsu da ya yi wa wasiƙar tata, ya fahimci ashe akwai abu mafi muhimmanci da ya bari.


Don haka, cikin dabarar da ya yi daga wannan lokaci, sai ya rage yawan mutanen da yake gani a office. Wato maimakon ya gana da mutum takwas, sai ya mayar da su mutum bakwai. Ya kuma ƙaddara a ransa cewa, matar tasa ita ce mutum na takwas ɗin da zai gana da ita. Don haka zai dawo a ƙalla awa ɗaya kafin lokacin dawowarsa na baya. Ya kuma ƙarar da wannan awan cikin tattaunawa da ita da wani abu da ya tabbata zai burge ta.


Mafi yawan maza ba su fahimci cewa, mutum ya zauna da matarsa na awa guda, ba ya komai sai saurarenta. Su tattauna abin da ya dame ta, a taya ta jimami. Su tattauna wanda ya burge ta, a yi dariya tare. Yana ɗaya daga cikin mafiya girman kyautar soyayya da za kai mata!

Wednesday, 21 August 2024

Asalin Siffofin Miji Na Gari

Asalin Siffofin Miji Na Gari

Da yake addini shi ne mafi girman mizani da za mu iya auna komai na rayuwa da shi, za mu fara kallon nasa ma'aunin, haƙiƙa mafi dacewa abun da ya kamata a duba ga namiji don tantance ko nagari ne, shi ne, riƙon addini da kuma kyan ɗabi'arsa. Bisa la'akari da faɗin Annabi ( S.A.W ): "Idan wanda kuka yarda da addininsa da ɗabi'arsa ya zo muku (neman aure) to ku aure shi" ko "ko aurar masa".


Suffofin Miji Na Gari 
Hoto: Medium


Marubuci:- Hamza Dawaki


Yana da kyau matuƙa, mata da iyaye su lura da maganar ɗabi'ar nan sosai, domin sau da dama a kan samu mutumin da ya suffantu da addini amma ba shi da ɗabi'u masu kyau. Wannan kuma yana ɗaya daga cikin mafiya wahalar da matan da ke ƙarƙashin su.

Mutum mai kyakkyawar ɗabi'a, kamar yadda Abdullahi ibn Mubarak yake cewa: Mutum ne mai sakin fuska, mai yawaita kyawawan ayyuka, kuma wanda ya kame ga barin cutar da mutane. 

Wannan ɗabi'a tana taimaka masa ƙwarai wurin tattalin zamantakewarsa, domin shi a kullum burinsa ya yi wa mutane abin kirki. Kuma shi ba zai cutar da su ba. Sannnan yana ɗaya daga cikin manyan sinadaran soyayya da mata suke matuƙar so, wato sakin fuska.  

Mutum mai kyakkyawar ɗabi'a zai iya kasancewa mai yawan haƙuri da kau da kai da kuma yafiya. Za ka taras shi ba mai rama mugunta da mugunta ba ne. Yana da kyau mu sani cewa rama mugunta da mugunta, ko rama mummuna da mummuna yana ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suke haddasa macewar soyayya tsakanin ma'aurata.

Domin yayin da mace ta yi zargin cewa mijinta ya daina yi mata wani abu da ya saba yi mata na kyautatawa, ita ma ta janye abin da take yi masa na kyautatawa, to wannan soyayyar a saurari ranar macewarta, amma idan kuwa aka yi katari da miji na gari, sai akasin hakan ya faru, domin shi ba ya rama mummuna da mummuna. Yayin da kuwa ki ka yi wa mutum wani abu mai muni, ya kau da kai, ko ma ya rama miki da mai kyau, to lokaci guda za ki tsinci kanki cikin wani yanayi na jin kunya da nadama. Don haka duk wani yunkuri na maimaita wannan abin sai ya rasa gurbi a ranki.

Saturday, 20 July 2024

Kyakkyawar Wasiyya Zuwa Ga Sabuwar Amarya

Kyakkyawar Wasiyya Zuwa Ga Sabuwar Amarya

Ya 'yata! Za ki fuskanci wata sabuwar rayuwa wacce babu gurbin mahaifiyarki ko mahaifinki a ciki, balle wani daga cikin 'yan uwanki. Za ki zamanto abokiyar zama ga wani mutum, wanda ba ya son wani ya yi tarayya da shi a game da ke, ko da kuwa ɗan uwanki ne na jini.


Wasiyya Ga Amarya
Hoto: RBK


Marubuci:- Aminu Bala


Don haka:


Ki zamo mata ga mijinki, kuma ki mayar da shi tamkar ɗanki, wato ki ƙaunace shi kamar yadda uwa ke ƙaunar ɗanta; kuma ki sanya shi ya riƙa jin cewa shi ne komai a rayuwarki, kuma ke ce komai a duniyarsa. Don haka, ka da ki manta cewa, kowanne namiji kamar babban yaro ne, don haka 'yar ƙaramar kyakkyawar kalma kan faranta masa rai.


Kar ki yarda ki nuna masa cewa ya rabo ki da iyayenki da dangi, saboda ya aureki, domin shi ma yana jin makamancin hakan, domin shi ma ya bar gidan iyayensa, kuma ya rabu da danginsa saboda ke, sai dai bambancin da ke tsakaninku shi ne bambancin da ke tsakanin namiji da mace. Amma ba na ce ki mance iyayenki da 'yan uwanki ba ne, domin su ba su mance da ke ba har abada. Ya abar ƙauna ta! Ya zai yiwu mutum ya mance da tsokar zuciyarsa?


Amma dai ina so ki ƙaunaci mijinki, ku tsaya ku fuskanci sabuwar rayuwarku tare, ki rayu da shi, kuma ki samarwa kanki sa'ada da jin daɗi da farin ciki da shi.


ALLAH YA BA DA ZAMAN LAFIYA.

Sunday, 14 July 2024

Kyawawan Nasihohi 10 Ga Sabuwar Amarya

Kyawawan Nasihohi 10 Ga Sabuwar Amarya

Ina yi miki nasiha da wasiyyar Umamatu bint al-Hiris at-Taghlabiyyah (Rh). Yayin da Umamatu bint al-Hiris at-Taghlabiyyah za ta kai 'yarta, Ummu Iyyas bint Awf gidan mijinta, al-Harisu bin Amr, Sarkin Kindatu, sai ta yi mata wannan wasiyyar mai matukar mahimmanci.


NASIHOHI A GARE KI AMARYA
Hoto: Pinterest


Marubuci:- Aminu Bala


Ta ce da ita:


"Ya 'yata! Da a ce a na barin nasiha saboda kyawun tarbiyya ko daraja da asalin mace, da sai dai ki biya min karatu a kanta; kuma da ban dame ki da ita ba, amma nasiha faɗakarwa ce ga mai hankali, kuma tunatarwa ce ga gafalalle. Haka kuma, 'yata, da a ce mace na wadatuwa ga barin miji saboda arzikin mahaifinta, da kin fi dukkan mata wadatuwa ga barin aure, amma an halicce mu ne domin maza kamar yadda aka halicce su domin mu."


"Ya 'yata! Lalle za ki bar shingen da kika fito a cikin sa, da kuma shekar da kika yi rarrafe a cikinta, zuwa wani lungu da ba ki san shi ba, da abokin zaman da ba ki saba da shi ba. Ya zama sarki saboda mulkinki da ya yi, don haka sai ki zame masa baiwa, zai zamo miki bawa mai lura. Don haka, sai ki kiyaye halaye goma, za su zame miki taska da tanadi:


1). Ki riƙe wadatar zuci, za ki samu hutu a ranki.


2). Ki kasance mai kyakkyawan ji da bi, sai ki samu yarda Ubangiji da ta mijinki.


3). Ki kula da abin da idonsa zai gani, kar ki bari ya ga muni ko ƙazanta tare da ke.


4). Ki lazimci tsafta da ƙamshi [na turare], kar ki yarda ya ji wani wari ko kaɗan a tare da ke.


5). Ki kula da lokacin cin abincinsa, kar ki bari gobarar ciki ta tada gobara a gidanki;


6). Ki nisanci duk wata hayaniya lokacin barcinsa. Kar ki bari wannan ya fusata shi.


7). Ki kula da dukiyarsa da kayan abincinsa, don shi ke nuna kwarancewarki a rayuwa.


8). Ki kula da dangi da iyayensa, domin wannan kyakkyawar ɗabi'a ce.


9). Ki kiyaye sirrinsa, zai sa ki riƙe alƙawarin da ke tsakaninku.


10). Kar ki yarda ki saɓa umarninsa, matuƙar ba saɓon Allah ba ne, don za ki turzura shi.


Haka kuma, ki nisanci bayyana murna idan yana cikin ɓacin rai, don wannan sakarci ne; kuma ki nisanci nuna ɓacin rai idan yana cikin farin ciki da murna, don hakan zai baƙanta masa.


Ki sani gwargwadon irin girmamawar da kike yi masa da iyayensa, gwargwadon mutuntaki da zai yi.


Gwargwadon yadda kike ƙoƙarin dacewa da ra'ayinsa, gwargwadon yadda zai tausasa miki.


Kuma ki sani ba za ki iya waɗannan abubuwan da na faɗa miki ba, har sai kin fifita son ransa a kan naki, cikin abin da kike so ko kike ƙi. Da fatan Allah ya tsare min ke, Ya yi miki albarka, Ya ba ku zaman lafiya da zurriyya ta gari.

Thursday, 11 July 2024

Kyakkyawar Nasiha Ga Sabon Ango

Kyakkyawar Nasiha Ga Sabon Ango

Ya ɗan uwana, ina yi maka nasiha da ka ji tsoron Allah (S.W.T) dangane da wannan amana da ka nema, kuma aka ga cancantar ka karɓe ta; aka ba ka. Ina mai taya ka da addu'a Allah ya ba ikon riƙe wannan amana.


NASIHA A GARE KA ƊAN UWA ANGO
Hoto: Domty


Marubuci:- Aminu Bala


Ka sani cewa aure al'amari ne babba da yake kawo alkhairi duniya da lahira. 


Samun alherin duniya yana tattare da samun nutsuwa ta cikin gidan; samun alherin lahira kuma yana tare da bin dokokin Ubangiji sau da ƙafa. Don haka, ba za ka samu nutsuwa a cikin gidanka ba, har sai ka yi tanadin hakan. Ka kasance ka tsarkake niyyarka da fatan za ka zauna da ita wannan yarinya da aka aura maka har ya zuwa ƙarshen rayuwarka, ko ta ta rayuwar.


Ka sani cewa ka rabo wannan matar daga gidansu, inda ta fi sabo da shi. Amma saboda son dacewar ta da Allah (S.W.T) ta zaɓi ta ajiye wancan sabo, ta zauna da kai. Da wannan tunani ne za ka dinga bada uzuri a lokacin da ta yi ganganci, ko wauta.


Ina mai yi maka nasiha da cewa ka sani cewa kodayake wannan matar ta zaɓi ta baro gidansu ta zauna tare da kai, amma dai zuciyarta ba ta bar su ba, saboda haka ka taimaka mata a wajen dukkan abin da ya shafi iyayenta da danginta.


Ka sani cewa, yanzu dole ne ka ɗauki matsayi na gurbin waɗanda ta baro su domin ka. A nan za ka dinga cancanzawa lokaci-lokaci. A wani lokacin ana buƙatar ka ɗauki matsayi na mahaifi, ta hanyar yi mata nasiha, a wani lokaci ma a yi mata faɗa domin gyarata. A wani lokaci kuma, za ka zama kamar yayanta ko ƙaninta. Wato ana buƙatar ka ɗauke mata kewar nan da ta rasa na cewa a da tana da waɗannan 'yan uwan nata suna rayuwa da jin daɗi irin na duniya da kuma abin da ya shafi rayuwarsu ta cikin gida.


A wani lokaci kuma, ka zauna da ita tamkar ƙawarta, wadda su kan zauna su yi hira, su yi nishaɗi da barkwanci. A wani lokaci kuma, sai ka zama maigida, tsayayye wanda ba ta da wani wanda zai iya ba ta nutsuwa da kwanciyar hankali kamar ka.


Haƙiƙa bincike ya nuna cewa rashin samuwar waɗannan a cikin gidaje shi yake kawo matsaloli da ba'a iya shawo kansu.


Ina mai tunatar da kai cewa duk yayinda aka rasa wani abu kyakkyawa, to mummuna zai maye gurbinsa. Don haka, wasu daga cikin mazaje suna sakaci wajen nunawa matayensu soyayya sai wannan ya sa su samu kishiyoyi game da soyayyar matan nasu, wato su samu wasu da ke tausayawa da saurarensu tare da nuna musu ƙauna, sai su mance da mazajen nasu, sai miji ya yi ta kishi da waɗancan mutane. Wani namijin ma, da mahaifiyar matar ta sa yake kishi. 


Ya ɗan uwana, a ƙarshe ina mai maka nasiha da ka yi kishin matar da ka aura. 


Kada ka mayar da gidanka kasuwa, wato inda kowa ke da iko ya shiga babu izini. 


Annabi (S.A.W) da aka tambaye shi a kan ƙanin miji ya dinga shiga gurin matar wansa, sai ya kamanta hakan da mutuwa, ballantana abokanai maza da ba su da mahalli a cikin gidanka.


Haka kuma Annabi (S.A.W) ya bayyana cewa mutumin da ba shi da kishin matarsa ba zai shaƙi ƙamshin Aljannah ba. Allah ya tsare mu.


ALLAH YA ALBARKACI AURENKA, YA BA KU ZURIYA KYAKKYAWA; KUMA YA HORE MAKA YADDA ZA KA RIƘE IYALANKA AMIN.

Thursday, 5 January 2023

Hukunci Tare Da Muhimmancin Yin Aure Ga Musulmai A Addinin Musulunci

Hukunci Tare Da Muhimmancin Yin Aure Ga Musulmai A Addinin Musulunci

Yin aure, abu ne da ya dace da  shari'a da lafiyayyan hankali da al'ada mai kyau. Akwai hikimomi da fa'idoji masu tarin yawa wajan yin aure, ga maza da mata, Allah ta'ala ya ce: (fassara) "Su matanku tufafi ne a gareku kuma tufafi ne a gare su.". Suratul Baƙara. 


Muhimmancin Yin Aure Ga Musulmai
Hoto: About Islam


MarubuciSheikh Aminu Ibrahim Daurawa


AURE A INUWAR MUSULUNCI DAGA LITTAFIN KIMIYYAR AURE


Wannan  aya ta nuna aure ado ne kwalliya ne, sutura ne rufin asiri ne mutuncin ne da daraja, saboda yadda aka kamanta rayuwar ma'aurata da tufafi, yadda tufafi suke ga Ɗan Adam, suna da amfani da yawa don haka aka kamanta rayuwar aure da tufafi, daga ciki amfanin tufafi akwai rufe tsiraici da yin kwalliya, da sutura, kuma duk wanda zai ɗinka tufafi yana buƙatar yasan kalar yadin da zai saya, na auduga ko na kattani ko na roba, mai kauri ko mai shara-shara,  mai tsada ko mai arha ko tsaka-tsaki,  fari ko baƙi ko wata kala daban, sannan wajan ɗunki mai yalwa ko mai matsi, ko kadaran kadahan, to haka rayuwar aure take wajan zaɓin abokin zama.


HUKUNCIN YIN AURE


Kasancewar mutane sun bambanta a halitta da halaye da yanayi, yasa malamai suka kalli ayoyi da hadisai da suka yi kira akan yin aure suka ba su fassara kashi uku:


Wasu malamai suna ganin yin aure sunna ne, abin da suke nufi, idan ka yi aure za ka sami lada, amma idan ba ka yi aure ba, kuma ba ka yi fasiƙanci ba, ba ka da alhaki. Wannan shi ne ra’ayin mafi yawan malamai, Badayatul mujtahid na Ibn Rushed 2/23. Addasuƙiy 2/214. Almugniy 6/446.


Na biyu sun ce yin aure sau ɗaya a rayuwa wajibi ne ga mutum, idan ya zauna bai yi aure ba ya yi laifi, domin wajibi shi ne abin da shari'a ta nemi ayi shi dole, idan mutum ya yi yadda aka umarce shi zai sami lada, idan kuma yaƙi ya zama abin zargi, kuma ana iya yi masa uƙuba akan haka. Saboda ko ba komai aure yana cika kamalar mutum mace ko namiji. Kuma abubuwan da suke cikin aure suna da yawa na buƙatu tsakanin namiji da mace, don haka idan aka yi aure kowa zai amfana. Wata ruwaya daga Alimam Ahmad, da wasu manyan Malamai daga cikin magabata, Almuhallah na ibn Hazamin, 9/440. Fathul Bariy 9/110. Dauda azzahiriy, Ibn Hazamin.


Na uku suka ce shi aure ya kasu gwargwadon yadda mutane suka karkasu;


Na ɗaya wanda aure ya zama wajibi a kansa. (shine wanda yake da ƙarfin sha'awa kuma yana da halin da zai iya riƙe auran ko sana'a, kuma idan bai yi auran ba zai yi lalata.).


Na biyu wanda aure ya zama sunna akansa. Wanda zai iya ɗaukar nauyin iyalin kuma yana yin wata sana'a ko neman ilmi, ba shi da sha'awa mai ƙarfi).


Na uku wanda aure ya zama haramun akansa. (Wanda ba zai iya ɗaukar nauyin matar ba, kuma ba shi da buƙatar auran, ko idan ya yi zai dinga cutar matar, wajan hana ta haƙƙoƙinta, ko ba shi da lafiya wajan biyan buƙatar iyali).


Na huɗu wanda aure ya zama makruhi akan sa. (ba a so ya yi aure saboda ya shagala da wani abu mai muhimmanci, ko ibada ko wani ilimi, ko wani bincike wanda ya hana shi samun lokaci, ko kuma ba shi da sha'awa, kuma babu tsoran yin lalata tare da shi.).


Na biyar wanda aure ya zama halal a gare shi (idan ya yi babu matsala, idan bai yi ba babu matsala).


Wannan shi ne magana Malikiyya, kuma akwai irin wannan ya shahara a fatawar daga wasu cikin shafi'awa da Hanbaliya. Fathul Bariy 9/110. Alƙawaninul Fiƙhiyya Ibn Juzay. 193.

 

Wannan shi ne fassara da malamai suka bayar ga dukkan ayoyi da hadisai masu kira da yin aure.

 

Amma ba kowa ya kamata ya yi aure ba saboda wasu ba su da sha'awa wasu ba su da lafiya wasu ba su da hali wasu ba su da lokaci, wasu kuma sun shagala da wani abu da ya fi yin auran muhimmanci a wajan su a wannan lokacin, kamar yadda Shaikh Abu Gudda ya kawo tarihin wasu malamai maza da mata waɗanda har suka gama rayuwar su ba su yi aure ba, yawan ya haura talatin, a cikin littafinsa mai suna Al'ulama'ul Uzzab.


Haka kuma ba kowa zai ƙi yin aure ba, domin wasu suna da buƙatar yin auran, domin samun zuriya, wasu domin samun abokin rayuwa wasu domin kare kai da gujewa lalata, kamar zina, maɗigo da luwaɗi, wasu domin ƙara mutunci da kamala.

Friday, 4 June 2021

Hikimomin Yin Aure Guda 13

Hikimomin Yin Aure Guda 13

Komai ka gani na rayuwa yana ƙunshe da fa'ida da hikima, ko a addinance, ko a hankalce, ko a al'adance, za mu kalli aure ta waɗanan ɓangarori guda uku. Na ɗaya a addinance.


HIKIMOMIN YIN AURE


MarubuciSheikh Aminu Ibrahim Daurawa


HIKIMOMIN YIN AURE DAGA LITTAFIN KIMIYYAR AURE


1.Yin biyayya ga umarnin Allah, wanda acikin haka akwai rabon duniya da lahira.


2. Biyayya ga Annabi (S.A.W), saboda aure ya tabbata a sunna ta fuska uku, ya yi umarni a yi aure, ya yi aure, kuma ya tarar ana aure, ya tabbatar tare da yin wasu gyare-gyare.


3. A cikin yin aure akwai toshe kafar sheɗan, ta kallon abin da ya haramta ko wajan faɗawa zina ko maɗigo, ko liwaɗi ko neman dabba, ko amfani da hannu, ko sauran hanyoyi na sheɗanci


4. A cikin aure akwai biyan sha'awa ga ma'aurata da kuma samun lada


5. A cikin aure akwai rage yawan ƴanmata da zawarawa, a cikin al'umma, wanda yawan su tare da samari ba tare da aure ba, sai yana barazana gamai da ɓarkewar annoba, ta zinace - zinace, haka kuma yana kawo cututtuka da saukar fushin Allah, wanda ya hana kusantar zina.


6. A cikin yin aure akwai samun zuriya, wacce za a yi mata tarbiyya mai kyau a gaban uwa da uba da renon al'umma ta gari. 


7. A cikin aure akwai samun nutsuwa da kwanciyar hankali, da soyayya tsakanin miji da mata. 


Manzon Allah (S.A.W) yace "Babu abin da ya dace da masoya irin su yi aure.".


8. A cikin yin aure akwai samun lada mai yawa wajan ciyar da iyali da ɗaukar nauyin su da sauran hidimomin su na yau da kullum, duka yana shiga cikin sikelin lada na mutum a ranar alƙiyama.


9. A cikin aure za ka samu jari na ɗa ko ƴa ta gari wacce za su dinga yi maka addu'a ko bayan mutuwar ka, ka bar sadaƙa jariya.


10. A cikin aure akwai idan ka haifi ƴaƴa suka mutu su na ƙanana, za ka amfana da su ranar alƙiyama, kamar yadda ya tabbata a hadisi.


11. Idan mutum ya yi aure sai Allah ya ba shi ƴaƴa mata daga biyu zuwa sama, ya tsaya ya kula da tarbiyyar su, da dukkan buƙatun su na ilmi, da tarbiyya, da lafiya da sutura har suka girma ya yi musu aure, Aljanna ta tabbata a gare shi. Kamar yadda ya tabbata a hadisi. 


12. Aure yana kare addini wanda ya yi aure ya cika rabin addininsa, ya ji tsoran Allah shi ne cikon rabin. (Hadith). da rayuwa yana hana yaɗuwar cutaka masu kisa kamar HIV, da mutunci, an fi ganin mutuncin masu aure ko da kuma marasa auran su na da mutunci. da hankali domin da yawa marasa aure su na samin ciwon hauka saboda zaman kaɗaici da takaici da rashin abokin zama yake haifarwa. Da dukiya yin aure yana tsare yawan shan magunguna na ƙarya sha'awa da wahalar siyan abinci. da nasaba, domin yana tsare yaɗuwar fyaɗe da zina, a cikin al'umma da ƴaƴan shegu, duk da ba laifin su bane. 


13. A cikin littafin ihya'u ulumidden. 2/72 na Al'imam Garzali, ya kawo ƙissar wani bawan Allah, wanda ake bashi shawara ya yi aure tunda yana da halin riƙe matar sai yaƙi yi. Bayan ɗan wani lokaci sai ya kwanta bacci, yana tsakar bacci sai aka ga ya tashi a firgice yana cewa, don Allah ku aurar da ni, sai aka ce masa mai ya faru? Sai yace "Na yi mafarki a cikin wannan baccin alƙiyama ta tashi, muna tsaye cikin damuwa da baƙin ciki ga ƙishrwa mai tsanani, muna ciki sai ga wasu yara su na ɗauke da wasu fitilu masu haske, da kofuna a hannun su na zinarai da azurfa, su na shiga cikin mutane su na ba wa wasu daga ciki ruwa, su na tsallake wasu sai nace ku taimake ni da ruwa ina jin ƙishrwa mai tsanani, sai suka ce ai baka da ɗa a wannan wajan, mu muna shayar da iyayan mu ne waɗanda suka haifemu, muka mutu kafin su.". 


Ya ce wannan shi ne dalilin da yasa nace kuyi mini aure, ko Allah ya azurtani da ɗa na gari da yi mini addu'a idan na mutu, idan kuma ya riga ni mutuwa ya taimaka ni a wannan wajen.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Sunday, 2 May 2021

Hirar Nishadi Tsakanin Saurayi Da Budurwa Kafin Ya Aure Ta

Hirar Nishadi Tsakanin Saurayi Da Budurwa Kafin Ya Aure Ta

KAFIN YA AURE TA


Menene ne ya ɓata miki rai? 


Ba ki da lafiya ne naga kin yi shiru?


HIRA TSAKANIN SAURAYI DA BUDURWA KAFIN YA AURE TA


Marubuci: Salihu Muhammad Lawan


Wallahi idan na gan ki acikin ɓacin rai, ni ma raina ɓaci yake yi.


Kin san yadda nake son ki kuwa? Duk duniya babu wata 'ya mace da nake so kamar ki.


Damuwarki damuwa tace, ni fa bazan iya rayuwa ba sai da ke.


BAYAN AN YI AURE


Bayan Ya Aure Ta


Ke kaɗai ki dinga ɓata rai saboda munafurci.


Daga anyi magana ki ƙago rashin lafiyar ƙarya, aikin banza!!


Kin zo kin yi shiru, kina wani ɓata ran banza.


Ke kaɗai za ki sha damuwarki.


Idan na gan ki cikin ɓacin rai, haushi kike bani.


Ba fa ke kaɗai ce mace a duniya ba, kuma ko babu ke ba wani abu da zai ɗaga mini hankali.


Shin mai ya sa muke wulaƙanta mata bayan aure?


Mai yasa idan muka aure su duk wani kulawa da nuna damuwa muna daina nuna masu? 


Ta aminta da kai saboda yadda ka nuna mata ko babu kowa a duniya za ka riƙe ta tamkar ƙanwar ka ta jini, kuma ka biya mata duk wani buƙatun ta idan ya tashi.


Tabar gidan su saboda kai.


Tabar iyayen ta saboda kai. 


Tabar garin su saboda kai


Ta bi ka duk inda Allah ya hore maka, ku zauna ku yi rayuwa tare.


Duk wani nau'in abun jin daɗi, iyayen ta su na mata goma sha biyu, amma haka ta bari ta bi ka.


Shin mai yasa ba za ka iya kare mata haƙƙin ta? Ka biya mata buƙatun ta ba.


Daman duk kalaman da kake gaya mata ƙarya ce, da yaudara.


Ta ya ya mata ba za su dinga zagin maza jam'i ba?


Ya ku 'yan uwa na maza, wannan ba ɗabi'ar da ya dace da miji nagari bace.

 

Allah ya bamu ikon kyautatawa abokan rayuwar mu. Wanda suke tare Allah ya basu haƙurin zama da juna da kuma yin biyayya ga ko wanne ɓangare, mu kuma 'yan baya, Allah ya bamu abokan rayuwa nagari wanda za mu yi rayuwa na har abada Amin.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.