Monday 28 October 2019

Karanta Zikirin Safiya da Maraice

Tura Wannan Zuwa Ga
{اللّهُ لاَ إِلَـهَ إِلاَّ هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ لاَ تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلاَ نَوْمٌ لَّهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ مَن ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِنْدَهُ إِلاَّ بِإِذْنِهِ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلاَ يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِّنْ عِلْمِهِ إِلاَّ بِمَا شَاء وَسِعَ كُرْسِيُّهُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ وَلاَ يَؤُودُهُ حِفْظُهُمَا وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ }

Zikirin Safiya da Maraice


Allahu la ilaha illa huwa-l-hayyu-l-qayyum. La ta'khudhuhu sinatun wa la nawm, lahu ma fi s-samawati wa ma fi-l-ard. Man dha l-ladhi yashafa'u 'indahu illa bi-idhnihi. Ya'alamu ma bayna aydihim wa ma khalfahum. Wa la yuhituna bi-shay'in min 'ilmihi illa bi-ma sha'a. was'a kursiyyuhu s-sama-wati wa-l-ard. Wa la ya uduhu hifzuhuma, wa huwal-l-aliyyu-l-azim.

Allah, babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi, Rayayye, Mai tsayuwa da komai. Gyangyadi ba ya kama Shi, wala barci. Abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin kasa nasa ne. babu mai yin ceto a wurinsa sai da izininsa. Yana sane da abin da yake gabansu (watau al'amarin duniya) da abin da yake bayansu (na al'amarin lahira). Ba sa sanin wani abu daga iliminsa, sai abin da Ya so. Kursiyyunsa (watau gadonsa) ya yalwaci sammai da kasa, kuma kiyaye su (sammai da kassai) ba ya yi masa nauyi. Shi ne kuma madaukaki, mai girma.

Ana karanta wadannan surorin (kowacce daga ciki har zuwa karshenta) bayan sallar Asuba da bayan sallar Magariba sau uku.

(قُلْ هُوَ اللهُ أَحَدٌ)

(قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ)

(قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ)

(Qulhuwallahu)

(Qul'a'uzu Birabbilfalaqi)

(Qul'a'uzu Birabbinnasi)

أَصْبَحْنَا وَأَصْبَحَ الْمُلْكُ ِللهِ، وَالْحَمْدُ ِللهِ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، رَبِّ أَسْأَلُكَ خَيْرَ مَا فِي هَذَا الْيَوْمِ وَخَيْرَ مَا بَعْدَهُ رَبِّ أَعُوذَ بِكَ مِنَ الْكَسْلِ وَسُوءِ الْكَبِرِ، رَبِّ أَعُوذُ بِكَ مِنْ عَذَابِ فِي النَّارِ وَعَذَابٍ فِي الْقَبْرِ"

Asbahna wa asbaha-l-mulku li-l-lahi, wa-l-hamdu li-l-lahi. La ilaha illa l-lahu, wahdahu la sharika lahu, lahu-l-mulku wa lahu-l-hamdu, wa huwa 'ala kulli shay'in kadir. Rabbi, as'aluka khayra ma fi hadha-l-yawmi wa khayra ma ba'dahu. Wa a udhu bika min sharri ma fi hadha-l-yawmi wa sharri ma ba'dahu. Rabbi a'udhu bika mina-l-kasali, wa su'i-l-kibari. Rabbi a'udhu bika min 'azabin azabin fi n-nar wa adhabin fi-l-kabr.

Mun wayi gari, kuma mulki ma ya wayi gari yana mai tabbata ga Allah. Dukkan yabo ya tabbata ga Allah. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, mulki ya tabbata gareShi, kuma yabo ya tabbata gareShi, kuma Shi Mai iko ne bisa komai. Ya Ubangijina! Ina rokonka alherin da ke cikin wannan rana, da alherin da ke bayanta. Kuma ina neman tsarinka daga Sharrin da ke cikin wannan rana, da sharrin da ke bayanta. Ya Ubangijina! Ina neman tsari da Kai daga lalaci, da mummunan tsufa. Ya Ubangijina! Ina neman tsari da kai daga azaba a cikin wuta, da kuma azaba a cikin kabari.

Idan kuma da maraice ne sai ya ce;

أَمْسَيْنَا وَأَمْسَى الْمُلْكُ ِللهِ...، رَبِّ أَسْأَلُكَ خَيْرَ مَا فِي هَذِهِ اللَّيْلَةِ، وَخَيْرَ مَا بَعْدَهَا، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا فِي هَذِهِ اللَّيْلَةِ وَشَرِّ مَا بَعْدَهَا.

Amsayna Wa'amsal mulku Lillahi…, Rabbi As'aluka Khayra Ma Fiy Hazihillaylati, Wakhayran Ma ba'adaha, Wa 'a'uwzu Bika Min Sharri Ma Fiy Hazihillaylati Washarri Maba'adaha…

Mun shiga maraice, kuma mulki ma ya shiga maraice yana mai tabbata ga Allah… ya Ubangijina! Ina rokonka alherin da ke cikin wannan dare da alherin da ke bayansa. Kuma ina neman tsarinka daga sharrin da ke cikin wannan dare da sharrin da ke bayansa...

اَللَّهُمَّ بِكَ أَصْبَحْنَا، وَبِكَ أَمْسَيْنَا، وَبِكَ نَحْيَا، وَبِكَ نَمُوتُ وَإِلَيْكَ الْمَصِيرُ .

Allahumma bika asbahna, wabika amsayna, wabika nahya wabika namootu wa-ilaykal-nushoor.

Ya Allah! Da ikonka ne muka shiga maraice, kuma da ikonka ne muka wayi gari, kuma da ikonka ne muke rayuwa, kuma da ikonka ne muke mutuwa, kuma izuwa gare Ka ne makoma take.

اَللَّهُمَّ أَنْتَ رَبِّي لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ، خَلَقْتَنِي وَأَنَا عَبْدُك، وَأَنَا عَلَى عَهْدِكَ وَوَعْدِكَ ما اسْتَطَعْت، أَعُوذُبِكَ مِنْ شَـرِّ مَا صَنَعْتَ، أَبُوءُ لَكَ بِنِعْمَتِكَ  عَلَيَّ وَأَبُوءُ بِذَنْبِي فَاغْفِِرْ لِي فَإِنَّهُ لاَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلاَّ أَنْتَ .

Allahumma anta rabbee la ilaha illa ant, khalaqtanee wa-ana 'abduk, wa-ana 'ala 'ahdika wawa'adika mas-tata'ata, a'oozu bika min sharri ma sana'atu, aboo-o laka bini'matika 'alay, wa-aboo-o bizanbee, faghfir lee fa-innahu la yaghfiruz-zunooba illa anta.

Ya Allah! Kai ne Ubangijina; babu abin bautawa da gaskiya sai Kai. Ka halicce ni, kuma ni bawanka ne kuma ina kan alkawarin da na yi maka (na kadaitaka da bauta) da kuma alkawarin da Ka yi mini (na shigar da wanda bai yi shira da kai ba gidan aljanna) gwargwadon ikonak ina neman tsarinka daga sharrin abin da na aikata. Ina tabbatar da ni'imarka gare ni, kuma ina tabbatar da zunubi na; Ka gafarta mini, domin ba wanda yake gafarta zunubai sai Kai.

Wanda ya karanta wannan addu'a da maraice yana mai imani da ita, idan ya mutu a cikin daren zai shiga aljanna, haka nan ma idan ya karanta ta da safe.

اَللَّهُمَّ إِنِّي أَصْبَحْتُ أَُشْهِدُكَ، وَأُشْهِدُ حَمَلَـةَ عَرْشِكَ، وَمَلائِكَتِكَ، وَجَمِيعَ خَلْقِكَ، أَنَّكَ أَنْتَ اللهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ وَحْدَكَ لاَ شَرِيكَ لَكَ، وَأَنَّ مُحَمَّداً عَبْدُكَ وَرَسُولُكَ.  أَرْبَعُ مَرَّاتٍ

Allahumma innee asbahtu oshhiduk, wa-oshhidu hamalata 'arshik, wamala-ikatak, wajamee'a khalqik, annaka antal-lahu la ilaha illa ant, wahdaka la shareeka lak, wa-anna Muhammadan 'abduka warasooluka.

Ya Allah! Ni na wayi gari ina shaidawa gare Ka, kuma ina shaidawa ga (Mala'iku) masu daukan al'arshinka, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Kai kadai, da babu abokin tarayya a gare Ka, kuma Muhammadu bawanka ne kuma Manzonka ne. (sau hudu).

Wanda ya karanta kamar yadda aka ce, Allah zai 'yanta shi daga wuta.

اَللَّهُمَّ مَا أَصْبَحَ بِي مِنْ نِعْمَةٍ أَوْ بِأَحَدٍ مِنْ خَلْقِك، فَمِنْكَ وَحْدَكَ لاَ شَرِيكَ لَكَ، فَلَكَ الْحَمْدُ وَلَكَ الشُّكْرُ.

Allahumma ma asbaha bee min ni'imatin, aw bi-ahadin min khalqik, faminka wahdaka la shareeka lak, falakal-hamdu walakash-shukr.

Ya Allah1 dukkan abin da ya wayi gari a gare ni na ni'ima, ko ga wani daga cikin halittarka, ko daga gare Ka ne, kai kadai, babu abokin tarayya a gare Ka; kuma yabo ya tabbata a gare Ka kadai, kuma godiya ta tabbata a gare Ka kadai.
Wanda ya fade ta da safe to wannan ya cika godiyar ranarsa, wanda kuma ya fada da yamma ya cika godiyar darensa.

اَللَّهُمَّ عَافِنِي فِي بَدَنِي، اَللَّهُمَّ عَافِنِي فِي سَمْعِي، اَللَّهُمَّ عَافِنِي فِي بَصَرِي، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ أَنْتَ. اَللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُبِكَ مِنَ الْكُفْرِ، وَالْفَقْرِ، وَأَعُوذُبِكَ مِنْ عَذَابِ الْقَبْرِ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ  (ثلاثاً)

Allahumma 'afinee fee badanee, allahumma 'afinee fee samAAee, allahumma 'afinee fee basaree, la ilaha illa anta. Allahumma innee a'oothu bika minal-kufr, walfaqr, wa-a'oothu bika min 'azabil-qabr, la ilaha illa ant. (3)

Ya Allah! Ka ba ni lafiya (aminci daga bala'i) a jikina. Ya Allah! Ka ba ni lafiya a jina. Ya Allah! Ka ba ni lafiya a ganina. Babu abin bautawa da gaskiya sai Kai. Ya Allah! Ina neman tsarinka daga kafirci da talauci kuma ina neman tsarinka daga azabar kabari. Babu abin bautawa da gaskiya sai Kai. (sau uku).

حَسْبِيَ اللَّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَهُوَ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ. (سبع مَرّات)

Hasbiyal-lahu la ilaha illa huwa, 'alayhi tawakkalt, wahuwa rabbul-'arshil-'azeem (7)

Allah ya ishe ni, babu abin bautawa da gaskiya sai Shi. A gare Shi kadai na dogara, shi ne Ubangijin al'arshi mai girma (sau bakwai da safe da maraice).
Wanda ya karanta ta kamar yadda aka ce, Allah zai ishe masa duk abin da ya dame shi na al'amarin duniya da na lahira.

اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْعَفْوَ وَالْعَافِيةَ فِي الدُّنْيَا وَاْلآخِرَة، اَللَّهُمَّ إِنِّي أسْأَلُكَ الْعَفْوَ وَالْعَافِيَةَ فِي دِينِي وَدُنْيَايَ وَأهْلِي وَمَالِي، اَللَّّهُمَّ اسْتُرْ عَوْرَاتِي وَآمِنْ رَوْعَاتِي، اَللَّهُمَّ احْفَظْنِي مِنْ بَيْنِ يَدَيَّ وَمِنْ خَلْفِي وَعَنْ يَمِينِي وَعَنْ شِمَالِي، وَمِنْ فَوْقِي، وَأَعُوذُ بِعَظَمَـتِكَ أَنْ أُغْتَالَ مِنْ تَحْتِي.

Allahumma innee as-alukal-'afwa wal'afiyah, fid-dunya wal-akhirah, allahumma innee as-alukal-'afwa wal'afiyah fee deenee, wadunyaya wa-ahlee, wamalee, allahummas-tur 'awratee, wa-amin raw'atee, allahummah-faznee min bayni yaday, wamin khalfee, waAAan yameenee, wa'an shimalee, wamin fawqee, wa-a'oozu bi'azamatika an oghtala min tahtee.

Zikirin Safiya da Maraice

Ya Allah! Ina rokonka afuwa da Aminci daga dukkan munana a duniya da lahira. Ya Allah! Ina rokonKa afuwa daga mummuna a addinina, da duniyata, ka kwantar da hankalina. Ya Allah ka kiyaye ni ta gabana, da ta bayana, da ta damana, data haguna, data samana, da ni kuma ina neman tsari da girmanka da kisfe kasa da ni.

اَللَّهُمَّ عَالِمَ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ فَاطِرَ السَّمَاوَاتِ وَاْلأَرْضِ رَبَّ كُلِّ شَيْءٍ وَمَلِيكَهُ، أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ نَفْسِي وَمِنْ شَـرِّ الشَّيْطَانِ وَشِرْكِهِ، وَأَنْ أَقْتَرِفَ عَلَى  نَفْسِي سُوءاً أَوْ أَجُرَّهُ إِلَى مُسْلِمٍ.

Allahumma 'alimal-ghaybi washshahadah, fatiras-samawati wal-ard, rabba kulli shayin wamaleekah, ashhadu an la ilaha illa ant, a'oothu bika min sharri nafsee wamin sharrish-shaytani washirkih, waan aqtarifa 'ala nafsee soo-an aw ajurrahu ila muslim.

Ya Allah! Masanin abin da ke fake da na sarari! Mai kagen halittar sammai da kassai! Ubangijin komai, kuma mallakinsa! Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai kai. Ina neman tsarinka daga sharrin raina, da kuma sharrin shaidan da shirkarsa, da in tsuwurwurtawa kaina wani abu mummuna, ko in jawo shi ga wani musulmi.

بِسمِ اللهِ الَّذِي لاَ يَضُرُّ مَعَ اِسْمِهِ شَيْءٌ فِي اْلأَرْضِ وَلاَ فِي السَّمَاءِ وَهُوَ السّّمِيعُ الْعَلِيمُ. (ثلاثاً)

Bismil-lahil-lathee la yadurru ma'as-mihi shay-on fil-ardi wala fis-sama-i wahuwas-samee'ul-'aleem. (3).

Da sunan Allah wanda sunansa wani abu a sama ko a kasa baya cutarwa. Shine mai Ji Masani. (sau uku).

Wanda ya fada sau uku da safe da yamma babu abin da zai cutar da shi.

رَضِيتُ بِاللهِ رَبَّاً وَبِالإِسْلاَمِ دِيناً وَبِمُحَمَّدٍ  نَبِيًّا. (ثلاثُ مراتٍ)

Radeetu billahi rabban wabil-islami deenan wabi Muhammadin  nabiyya. (3)

Na yarda da Allah Ubangiji, da Musulunci addini, da Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Annabi. (sau uku).

يَاحَيُّ يَا قَيُّومُ بِرَحْمَتِكِ أَسْتََغِيثُ، أَصْلِحْ لِي شَأْنِي كُلَّهُ، وَلاَ تَكِلْنِي إِلَى نَفْسِي طَرْفَةَ عَيْنٍ.

Ya hayyu ya kayyoom, birahmatika astagheeth, aslih lee sha'anee kullah, wala takilnee ila nafsee tarfata 'aynin.

Ya (Allah) Rayayye, Mai tsayu da komai! Da rahamarka nake neman agaji, Ka kyautata mini sha'anina dukkaninsa, kada Ka kyale ni da kaina ko da daidai da kiftawar ido ne.

أَصْبَحْنَا وَأَصْبَحْ الْمُلْكُ ِللهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ، اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَ هَذَا الْيَوْمَ،فَتْحَهُ، وَنَصْرَهُ،وَنُورَهُ وَبَرَكَتَهُ، وَهُدَاهُ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا فِيهِ وَشَرِّ مَا بَعْدَه.

Asbahna wa-asbahal-mulku lillahi rabbil-'alameen, allahumma innee as-aluka khayra hazal-yawm, fat-hahu, wanasrahu, wanoorahu, wabarakatahu, wahudahu, wa-a'oozu bika min sharri ma feehi, washarri ma ba'dahu.

Mun wayi gari, kuma mulki ma ya wayi gari yana mai tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, Ya Allah! Ina rokonka alherin wannan rana: budinta da nasararta, da hakenta, da albarkarta, da shiriyarta, da abin da ke bayanta.

Da yamma kuma sai yace:

أَمْسَبْنَا وَأَمْسَى الْمُلْكُ ِللهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ، اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَ هَذِهِ اللَّيْلَةِ، فَتْحَهَا، وَنَصْرَهَا، وَنُورَهَا وَبَرَكَتَهَا، وَهُدَاهَا، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا فِيهَا وَشَرِّ مَا بَعْدَهَا.

Amsayna wa'amsal Mulkulillahi Rabbil Alamiyna, Allahumma Inniy As'aluka khayra Hazihillaylati, Fathaha, Wanasraha, Wanuyraha Wabarakataha, wahadaha, wa'a'uwzu bika Min sharri Ma Fiyha Washarri Ma ba'adaha.

Mun shiga maraice, kuma mulki ma ya shiga yana mai tabbata ga Allah...

أَصْـبَحْنا علـى فِطْـرَةِ الإسْلام ، وَعَلـى كَلِـمَةِ الإخْـلاص، وَعلـى دينِ نَبِـيِّنا مُحَمَّدٍ  وَعَلَى مِلَّةِ أَبِينَا إِبْرَاهِيمَ حَنِيفًا مُسْلِمًا وَمَا كَانَ مِنَ الْمُشْرِكِينَ.

Asbahna 'ala fitratil-islam, wa’ala kalimatil-ikhlas, waAAala deeni nabiyyina Muhammad  wa'ala millati abeena Ibraheem, haneefan musliman wama kana minal-mushrikeen.

Mun wayi gari a kan kirar da Allah ya yi mana ta Musulunci, kuma a kan addinin Annabinmu Muhammadu, tsira da aminci  su tabbata a gare shi, kuma a kan addinin Babanmu Ibrahim, mai totar zuwa ga addinin gaskiya, Musulmi, bai kasance daga cikin mushrikai ba.

سُبْحَانَ اللهِ وَبِحَمْدِهِ. مِائَةَ مَرَّةٍ

Subhana l-lahi wa bi-hamdihi. (100)

Wanda ya karanta sau dari yayin da ya wayi gari da kuma yayin da ya shiga maraice, ranar Kiyama ba wanda zai zo da aikin da yafi abin da ya zo da shi falala sai wanda ya karanta kamar yadda ya karanta ko sama da haka.

لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَـدِيرٌ.

La ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, lahul-mulk, walahul-hamd, wahuwa AAala kulli shayin qadeer.(10)

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Mulki nasa ne shi kadai, yabo ma nasa ne shi kadai, kuma Shi mai iko ne bisa komai. (Sau goma, ko sau daya, idan ya ji kasala).

لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ.

La ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, lahul-mulk, walahul-hamd, wahuwa 'ala kulli shayin qadeer.

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Mulki naSa Ne Shi Kadai, yabo ma nasa ne Shi kadai, kuma Shi Mai iko ne bisa komai. (sau dari idan ya wayi gari).

Wanda ya fada sau dari a rana kamar ya 'yanta bayi goma ne, kuma za a rubuta masa kyakkyawan aiki dari, a shafe masa mummunan aiki dari kuma ita addu'ar za ta zamo masa tsari daga shaidan a tsawon wannan rana har ya kai maraice, kuma ba wanda zai yi aikin da yafi nasa falala sai wanda ya karanta fiye da haka.

94.

سُبْحَانَ اللهِ وَبِحَمْدِهِ عَدَدَ خَلْقِهِ، وَرِضَا نَفْسِهِ، وَزِنَةَ عَرْشِهِ، وَمِدَادَ كَلِمَاتِهِ. (ثَلاَثَ مَرَّاتٍ.

Subhanal-lahi wabihamdih, 'adada khalqihi warida nafsih, wazinata 'arshih, wamidada kalimatih.(3).

Tsarki ya tabbata ga Allah, tare da yabo gare Shi, iya adadin halittunsa, da gwargwadon yardar Kansa, da iya nauyin Al'arshinsa, da iya yawan tawwadar da za a rubuta kalmominsa. (sau uku da safe).

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Zikiri Yayin Fita Daga Gida

Karanta Addu'o'in Tashi Daga Barci

Karanta Yadda ake Yin Addu'ar Sallar Istihara Neman Zabin Allah Idan Mutum Zai Aikata Wani Abu

اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ عِلْمًا نَافِعًا،وَرِزْقًا طَيِّبًا،وَعَمَلاً مُتَقَبِّلاً.

Allahumma inni as'aluka 'ilman nafi'an, wa rizqan tayyiban wa'amalan mutaqabbalan.

Ya Allah! Ina rokan Ka ilimi mai amfani, da arziki na halal, da aiki karbabbe. (Da safe).

أَسْتَغْفِرُ اللهَ وَأَتُوبُ إِلَيْهِ.

Astaghfiru l-laha wa atubu ilayhi.
(Sau dari a rana)

أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ مِنْ شَرٍّ مَا خَلَقَ.

A'udhu bi-kalmati l-lahi t-tammati min sharri ma khalaq. (3)

Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da ya halitta (sau uku da yamma).

اَللَّهُمَّ صَلِّ وَسَلِّمْ عَلَى نَبِيِّنَا مُحَمَّدٍ.

Allahumma salli wa sallim 'ala nabiyyina Muhammad.

(sau goma)

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user