Monday 28 October 2019

Karanta Yadda Zaka Gane Budurwar da Ba ta Taba Saduwa da Namiji ba Kafin Kuyi Aure

Tura Wannan Zuwa Ga
Korafin samari yayi yawa cewa, 'yan matan da suke aura ba sune suka fara kwanciya dasu ba.

Ganin Jini Fa ba Shine Budurci Ba

Hujjar su anan ita ce, sunyi
saduwar Aure ta farko da matan nasu amma basu ga jini ya fito ba.

Gaskiya wannan ba hujja bace da za'a yi wa mace kallon 'yar Iska.

BUDURCI:- Wata fata ce dake cikin farjin mace matashiya, kuma fatar ba mai kwari bace sannan
tana yagewa ne da zarar ta samu takura.

Mace tana rasa budurcinta ne ta wadannan hanyoyin:

1. Saduwa da namiji
2. Daukar kaya mai nauyi
3. Guje-guje
4. Hawan keke
5. Hawan doki ko jaki
6. Mummunar faduwa
7. Sanya danyatsa a farji
8. Haihuwa

Wasu matan ko an sadu dasu
fatar budurcinsu bata yagewa
har sai sun zo wajen haihuwa anan ne zata yage.

Dan haka nake kira ga samari don Allah duk wanda ya auri mace Budurwa kar
yace lallai sai ya ga wannan jinin...

Idan har baka ga wannan jinin ba to kar ka yiwa matarka kallon 'yar iska ko mazinaciya, domin inda yar iska ce ko mazinaciya da kasani tun kafin kuyi auren, a zatona tunda sanda kayi
bincike kafin kayi auren.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA ILLOLIN ZAMA DA MATAR AURE GUDA DAYA

SHIN KO YA DACE NA ZABI BUDURWA A RANAR SALLAH?

KARANTA BABBAN KALUBALEN DAKE GABAN SAMARI

Domin ba'a zama da zargi don da zarar Zargi Yafara shiga Aure To aure zai lalace.

Allah ya kiyaye mu da kiyayewarsa, Kuma Allah yasa 'yan uwana maza su Fahimta, Allah ya bamu 'Ya'ya na gari tare da Zuriya daiyiba Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user