Aminci a gare ki ya sarauniya mai kyakkyawar sura da cikakkiyar nutsuwar sautin zance wanda ke fita tamkar busa irin na sarewa. Matsayin girman daraja da biyayyar da zuciyata takewa ƙaunarki ta wuce adadin busawar iska cikin adadin tafiyar kwanakin numfashina.
Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR
Ina miƙa saƙon so daga zuciyata zuwa ga zuciyar da nake neman haɗa zumunci wanda muke fatan kasantuwa har zuwa ƙarshen rayuwar numfashi.
Ya mai martaba sallama da kalaman gaisuwar aminci a gare ki tare da haɗaɗɗiyar daular murmushin fuska mai cike da nuni da isar da muhimmin saƙo zuwa gare ki.
Ki agaji zuciyata da kalaman son ki, ki yayyafawa ruhina ruwan sanyin murmushinki mai fitowa cikin tsakiyar laɓɓanki masu ɗaukar hankali.
Ina cikin tsakiyar son ki, ke ce sabuwar duniyata ta musamman mai ɗauke da kayan alatu masu faranta ruhin jikina.
Haƙiƙa hasken annurin fuskarki bai gushe ba face ya yi awon gaba da dukkan wani kuzarin da ke jikina.
Ina miƙa saƙon gaisuwa mai ɗauke da fatan amincewar ruhin zuciyarki, fatana kawai ki ce min kin karɓa.