Showing posts with label Tambayoyin Musulunci. Show all posts
Showing posts with label Tambayoyin Musulunci. Show all posts

Saturday, 28 September 2024

Ma'anar Usulul-fikhi Da Ka'idar Shi

Ma'anar Usulul-fikhi Da Ka'idar Shi

Usulul-fiƙhi, usulul-fiƙhi yana nufin ƙa'idodi da dokokin da ake amfani da su wajen fitar da hukunce-hukuncen fiƙihu daga nassoshin Qur'ani da Hadisi.


Ma'anar Usulul-fikhi Da Ka'idar Shi
Hoto: Godofvecktor/Freepik

Marubuci:- Habeeb Awaisu Mmr


A taƙaice, usulul-fiƙhi shi ne tsarin da yake koyar da hanyoyin da malamai ke bi don su fahimci nassoshi da kuma fitar da hukunci daga cikinsu.


Don haka usulul-fiƙhi yana bayyana yadda ake fitar da hukunce-hukuncen ne.

Tuesday, 24 September 2024

Ma'anar Fikihu Da Abin Da Ya Kunsa

Ma'anar Fikihu Da Abin Da Ya Kunsa

Ilimin fiƙihu yana nufin tsarin ilimin da yake bayyana furu'u ko fannonin hukunci a cikin addini, wato abin da ya shafi dokoki da hukunce-hukunce da suka danganci ayyuka kamar yadda ake yin sallah, azumi, hajji, kasuwanci, aure, da sauran ayyuka na rayuwar yau da kullum.


Ma'anar Fikihu Da Abin Da Ya Kunsa
Hoto: Rb-law


Marubuci:- Habeeb Awaisu Mmr


Fiƙihu yana mayar da hankali ne kan abin da aka cimma daga nassoshi, wato shi ke ba da hukunce-hukunce.


Don haka, fiƙihu yana ba da hukunce-hukunce ne.

Friday, 20 September 2024

Shin Mece Ce Ta'aziyya Da Ma'anar Ta?

Shin Mece Ce Ta'aziyya Da Ma'anar Ta?

Ma'anar ta'aziyya shi ne yi wa wanda aka yi masa mutuwa jajen rashin ɗan uwa na jini ko na alaƙa da ya same shi, da neman shi ya yi haƙuri a kan wannan musiba da ta same shi saboda wannan mutuwar.


Ta'aziyya Da Ma'anar Ta
Hoto: Abubakar Bukola Saraki




Musulmi yana yi wa ɗan uwansa musulmi ta'aziyya, yana kuma halatta ya yi wa wanda ma ba musulmi ba ta'aziyya.

A Shari'ance da kuma Hankalce ta'aziyya ba ta nuna haɗuwa cikin addini guda, ko haɗuwa cikin wani ra'ayi, ko fahimta guda. 

Babu mai fahimtar cewa ta'aziyya, ko ziyarar ta'aziyya na nufin haɗuwa cikin wani addini guda, ko haɗuwa cikin wani ra'ayi guda sai wanda ya jahlci Addinin Musulunci, ko ya jahilci ƙa'idar zamantakewar jama'a ko ma wani irin addini ne suke bi.

Allah Ya taimake mu Ya ɗora mu a kan daidai har kullum. Amin.

Thursday, 5 September 2024

Shin Mene Ne Hukuncin Ladanci A Sallah?

Shin Mene Ne Hukuncin Ladanci A Sallah?

Tambaya

Malam Mene ne hukuncin ladanci a sallah, haram ne ko idan aka yi ba laifi?


Ladanci A Sallah
Hoto: Brecorder




Amsa

To ɗan uwa matuƙar liman yana ɗaga murya, to yin ladanci bidi'a ne kamar yadda wasu malaman suka faɗa.

Amma idan liman yana da lalura ko rashin lafiya ko kuma masallacin yana da girma ta yadda dukkan mamu ba za su ji muryarsa ba, to ya halatta, saboda a lokacin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi rashin lafiya, sayyidina Abubakar ya kasance yana ɗaga murya da kabbara saboda ba a jin na Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda Bukhari ya rawaito.

Allah ne mafi sani.

Friday, 19 April 2024

Hukunce-Hukunce 8 Na Rancen Airtime Na Layi

Hukunce-Hukunce 8 Na Rancen Airtime Na Layi

A Azumin bara (1436H) an mini tambaya game da bashin da kamfanin MTN yake ba wa masu mu’amala da shi. Ka ranci airtime na misalin N50, a ba ka na N45. A karon farko na bayar da amasar cewa, Haramun ne! Kuma zai shi ga babin ribal Qardh!.

Hukuncin Rancen Airtime Na Layi
Hoto: Tingtel



Daga baya na janye wannan fatawar saboda yadda na ƙara fahimtar mas’alar, na ba da fatawar halaccin ta, saboda dalilai kamar haka:

1. Wannan mas’ala ba bashi ne na kuɗi da kuɗi ba, ballantana batun ribal Kardh ta zo.

2. Abin da yake haƙiƙanin mas’alar shi ne, wani ne mai amfani ne da wannan kamfani na MTN ya sayi hidima ta aritime (airtime service) wadda suke sayar da ita N45, sai suka sayar masa ita a N50.

3. Kasancewar an ambaci kuɗi a ciki ba shi yake tabbatar da cewa kuɗi da kuɗi ne aka yi musanyan su ba. An yi musanyan kuɗi ne da wata hidima (airtime service) wanda masu ita suka ƙi ba shi ita a farashin da suke sayar da ita kuɗi hannu, suka ƙara masa wani abu akai. Wannan ba komai ne ba a shari’ance ba, saboda kayansu ne, suna da damar su yi maka ƙari kamar yadda suke da damar su yi maka ragi, kuma ka karɓa.

4. Abin da zai tabbatar maka da cewa, wannan abin da ka nema su ba ka ba tsurar kuɗi ne ba, hidima ce kawai, wanda aka ba shi ita a wayarsa ba za iya sayen komai da wannan ba a gurin wani ya ce yana da kuɗin biya a gurinsa, a she ka ga ba kuɗi ne ba, koda an rubuta alamar kuɗi a tare da shi.

5. Kamar yadda ya halatta katin waya na N100 a sayar wa da mai buƙata akan N110, duk da cewa ga shi a rubuce an rubuta N100. Ko a sayar masa da shi N95, wanda babu wani masani da ya taɓa cewa, wannan riba ce ko haramun ne, saboda musanyar kuɗi da kuɗi ne. Domin alal haƙiƙa wannan katin wayar mai ɗauke da N100 a kansa ba kuɗi ne ba, wata hidima ce, aka yi mata ramzi da wannan 100, shi ya sanya da zarar ka kankare ka shigar da ita cikin wayarka  za ka jefar da wannan katin tare da cewa an rubuta kuɗi a jiki, To wannn masa’al ta rance kamar haka take, don haka, duk wanda ya haramta wannan to wajibi ya haramta sana’ar sai da kati. Wanda ba na  jin akwai mai faɗar hakan.

6. Don haka ba magana ce ta an ba ni fatawa a baibai ba, magana ce ta sake nazari akan fatawar farko, wanda wannan abu ne sananne a gurin manyan malamanmu magabata da suke canza fatawoyinsu yayin da wasu dalilai suka bayyana gare su.

7. Wannan matsaya kuma shi ne matsayar wasu daga cikin abokai na ɗaliban ilimi bayan sun kalli mas’alar ta mahanga lilimi da sanin abin da ake kira riba, daga cikinsu akwai abokina Dr. Bashir Aliyu Umar kamar yadda daga baya na samu labari. 

8. Daga ƙarshe ina kira ga sauran ‘yan uwana ɗiliban ilimi mu yi kaffa-kaffa wajen sakin baki game da sha’anin halal da haram, al’amarin yana da haɗari. sanin madafar shari’a ta wanda ya karanta ta ne.

Allah ya sa mu dace. Amin. 

Wednesday, 10 April 2024

Shin Ya Dace Dukkan Mata Su Fita Sallar Idi?

Shin Ya Dace Dukkan Mata Su Fita Sallar Idi?

Sunnah ce mata su fita Sallar idi kamar yadda Hadith ya kwaɗaitar da kuma maganganun magabata da suka yi bayani akan halarcin fitar mata zuwa sallar idi.


Sallar Idi
Hoto: Britannica


Marubuciya: Faridah Bintu Salis


Ummu Aɗiyyah Nusaibah Bint Ka'ab Al-ansariyyah (RA) ta ce: Annabi (ﷺ) ya yi umurni a ranar idi mata su fita, da 'ƴan mata, da mai al'ada amma ita ta nisanci wajen sallar (tunda ba yi za ta yi ba).” [Bukhari: 981, Muslim: 890]


Abdullahi Ɗan Abbas (RA) Ya ce: “Manzon ALLAH (ﷺ) Ya kasance yana umurtar ƴaƴansa. da matansa, su fita a idi guda biyu (Babba da ƙaramar Sallah).” [Sahihul Jami'i: 3888]


Sayyidina Abubakar (RA) Ya ce: “Wajibi ce Sallar Idi ga duk wacce take da kwatankwacin malulluɓi da zai rufe ta, ta fita zuwa idoji guda biyu ƙarama da Babba.” [Ibn Abi Shaibah ya ruwaito shi a Musannaf 2/182 da sanadi ingantacce] 


Alhafiz Ibn Hajar (Rahimahullah) Ya ce: “Alƙali Iyad Bn Musa ya naƙalto wajabcin Sallar idi hatta ga mata daga Abubakar da Aliyu da Ibn Umar.” [Fat-hul Baary 2/545] 


Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albaniy (Rahimahullah) Ya ce: “Toh a sani wannan shi ne gaskiya da babu ƙoƙonto a kai na wajabcin idi hatta ga mata, saboda yawan hadisan da aka ruwaito game da haka, Hadisin Ummu Aɗiyya da ya gabata ya isar mana, ba sharʼanci kawai ya ke nunawa ba, hatta wajabcin hakan yake nunawa ga su matan, saboda umarnin da Annabi (ﷺ) ya bayar, asali kama umurni wajabci ne.” [Salatul Idaini: 15] 


Sunnah ne mata su fita zuwa Sallar Idi, don haka mata ku yi ƙoƙari ku halarci Idi, sannan a kiyaye sanya turare ko bayyanar da wani abu na ado, ku lizimci hijabi na Sharia kuma ku zamto masu natsuwa da kamun kai, sannan a yayin tafiya ku kasance masu bin gefen hanya ba tsakiya ba, kuma ku kiyaye cakuɗuwa da maza, idan kuka kasance haka sai dai ace daku: MASHAA ALLAH.

Thursday, 25 November 2021

Shin Annabi Muhammad (SAW) Ne Farkon Halitta?

Shin Annabi Muhammad (SAW) Ne Farkon Halitta?

TAMBAYA


Assalamu alaikum Malam ina da wata tambaya wadda ta ɗaure mun kai, idan ka san amsa don Allah ka ba ni tare da gamsassun hujjoji. Tambayata shi ne, shin Allah, Annabi Muhammad ne ya fara halitta? Shin wai Allah ya ajiye shi ne sai lokacin da ya gadama sannan ya zo duniya?


SHIN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W) NE FARKON HALITTA?
Hoto: SeekPNG

AMSA


Wa'alaikumus salam, Akwai hadisin da ya zo wanda yake nuna cewa Annabi (S.A.W) shi ne farkon wanda aka fara halitta, sai dai hadisin bai inganta ba, wasu malaman hadisin, kamar Ibnu-kathir a tarihinsa da Albani a silsilatussahiha hadisi mai lamba 458, sun ce hadisin ƙarya ne.


Faɗin cewa Annabi (S.A.W) shi ne farkon wanda aka halitta ya saɓa wa Alƙur'ani, ta ɓangarori da dama ga wasu daga ciki:


1. Allah ya tabbatar da cewa Annabi Muhammad mutum ne kamar yadda hakan ya zo a ayoyi daban-daban, sannan kuma Allah ya tabbatar da cewa gaba ɗaya mutane daga Annabi Adam aka same su, kin ga idan ka ce Annabi Muhammad ﷺ shi ne farkon halitta hakan ya saɓa wa ayoyin Alkur'ani.


2. Tarihi ya zo da bayanin nasabar Annabi Muhammad (S.A.W), tun daga mahaifinsa har zuwa Annabi Ibrahim, kin ga wannan yana nuna an halicce shi ne daga maniyyin mahaifinsa, kamar yadda aka halicci ragowar mutane daga hakan.


Zance mafi inganci shi ne: farkon abin da Allah ya fara halitta shi ne Al'arshi, kamar yadda ya zo a cikin Sahihi Muslim a hadisi mai lamba 2653, cewa: "Allah ya ƙaddara abubuwa kafin ya halicci sama da kasa da shekaru dubu hamsin a lokacin Al'arshinsa yana kan ruwa".


Kin ga wannan yana nuna cewa Al'arshi ne farkon abin da aka fara halitta ba Annabi Muhammad (S.A.W).


Allah ne mafi sani.


Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa

Sunday, 21 March 2021

POS: Tarihin Sa Da Hukuncin Amfani Da Shi Wajen Kasuwanci Da Fitar Da Kudade Da Tura Su A Addinin Musulunci

POS: Tarihin Sa Da Hukuncin Amfani Da Shi Wajen Kasuwanci Da Fitar Da Kudade Da Tura Su A Addinin Musulunci

Bismillahir Rahmanir Rahim Tsira da Amincin Allah su ƙara tabbata ga Annanbinmu Muhammad da Alayensa da Sahabbansa bakiɗaya.


Hukuncin Amfani Da POS Da Tarihin Sa


Marubuci: Ahmad Murtala Mansur


Bayan haka, a yau Laraba 23 Jumada Ula, 1442 H.-06 Janairu, 2021 M., na samu tambaya ta fuskoki da yawa har sai da aka rubuto cewa: “Malam ana cikin buƙatuwar yin cikakken bayani a dangane da POS. Wasu malaman sun haramta, wasu kuma sun halatta, Mun gode”. Wannan ita ce tambayar. Amma jin akwai wannan saɓani na malamai a nan ƙasar, ya sa na yi kamar ba zan bada amsa ba. Saboda ban cika son shiga irin mas’alolin da aka samu karakaina ba, ba tare da na  ji ko na karanta abin da kowane ɓangare ya faɗa ba. Sai dai tambayar ta zo daga wajen wani mutum mai kima a idona. Don haka na rubuta wannan bayani. Amma ba wai na rubuta ba ne a matsayin dole sai na gamsar da kowa da kowa ba. Wannan ba zai taɓa yiwuwa ba. Na dubi mas’alar ne da kyau gwargwadon abin da Allah ya huwace a yanzu-yanzu. Allah ya bamu sa’a da dacewa.


1-Yana da kyau a riƙa sanin tarihin wasu abubuwa da yadda suka taso da yadda suke amfani da sauran wasu abubuwan da suka shafesu. Saboda ta haka ne za a iya basu hukuncin da ya dace da su a Shar’ance. Imamu Shafi’i yana cewa, “Na ɗauki lokaci ina karanta ilimin tarihi, shekara kaza da kaza! Amma na karantashi ne kurum don na taimaka da shi wajen fahimtar ilimin Fiƙihu”.-(Al-Istiksa Li Akhabril Duwalil Magribil Aksa:1/59)
الإمام الشافعي رضي الله عنه كان يقول:"دأبت في قراءة علم التاريخ كذا وكذا سنة وما قرأته إلا لأستعين به على الفقه".


2-Akan haka, bari mu fara da ɗan tarihi kaɗan. Abin da ake nufi da POS shi ne ‘Point of Sale’ "نقاط البيع" . A wani lokacin kuma ana kiransa da sunan POP wato Point of Purchase. Duka biyun a asalinsa suna nufin tsarin ƙididdige cinikin da mai kanti ya yi a nan take ba tare da wata wahala ba. An fara ƙirƙiro tsarin POS tun a 1879 M. Da sunan ‘Cash Register’. Sunan wanda ya fara ƙirƙiro shi James Ritty. Yana da babban shago kayan masarufi. Amma sai ya fahimci ma’aikatansa suna yi masa ɗingushe. Don haka sai ya sa aka ƙirƙiro inji da sunan ‘Incorruptible Cashier’ don ya riƙa sanin adadin abin da ya shigo lalitarsa. A 1906 M. a ka fara jona wannan inji da wuta, ta yadda ya ƙara sauri wajen aikinsa. Sai kuma a shekarun 1970s aka fara haɗa wannan fasaha da na’ura mai kwakwalwa. Haka ya wanzu har shekarun 1990s a inda aka fara ƙera injina na zamani, waɗanda su da kansa kwanfiyuta ne. Shigowar shekarun 2000s a nan ne aka fara samar da irin waɗannan injin amma waɗanda za a iya ɗauka a hannu daga nan a kaisu can, suna kiransu da ‘mPOS’-wato Mobile POS

 

3-Tsarin POS ya shigo Nigeria sosai  2012 M. a lokacin da Babban Bankin Tarayya ya huwacewa ‘yan ƙasa su riƙa amfani da shi saboda rage zirga-zirga da kuɗaɗe a hannu. Kafin haka kaso 90% na cinikayya ana yinsu da kuɗaɗe a hannu tsirara! –(Challenges to the Efficient Use of Point of Sale (POS) Terminals in Nigeria na Adeoti).


4-Akwai POS kala-kala wanda kamfanoni da wuraren sayar da abinci da abin-sha da otel-otel suke amfani da su. Kowanne yana neman wanda ya dace da buƙatarsa. Amma amfani da POS a matsayin wurin da za a iya zuwa a nemi su baka wani gwargwado na kuɗi, su kuma su yi amfani da katin mutum na ATM su ɗibi wannan kuɗin su tura zuwa account ɗinsu a maimakon wanda suka bashi a nan take, wannan ya fara ne a ‘yan shekarun nan, ba da daɗewa ba.


5- Kafin mutum ya buɗe wurin harkar POS sai ya bi wasu matakai kamar haka:


i- A dokokin Ƙasa an yarda a buɗe irin waɗannan wurare kamar yadda aka faɗa a baya.


ii- Masu harkar POS suna da alaƙa da bankuna ta fuskar sai sun je sun yi rijista da wani banki tukuna. Daga cikin hikimomin yin haka shi ne don bankin zai ga ana hadahadar kuɗaɗe masu yawa akai-akai, sai ya zamo ba zai damu ba, saboda ya yarda da account ɗin da ake wannan hadahadar da shi.


iii- Akwai certificate da bankin zai bawa wanda ya yi rijista da shi a matsayinsa na “agent”-wakilinsu. Don haka zai yi rawa da bazar wannan bankin a iya ɓangaren da suka yarjewa POS ya yi hidima.


vi- Bankin da aka yi rijista da shi yana son ya ga motsin wannan POS a ƙalla sau goma a rana don ya tabbatar da yana aiki. Wannan ba tare da ya kula da yawan kuɗin da zasu shiga ko zasu fita ba ta hanyar wannan POS ɗin.


v- Zai biya kuɗin hayar shago da wutar lantarki da kuɗin data da yake amfani da ita don hawa kan intanet ko kuɗin cajin waya, da sauransu.


6- Mafi girman ayyukan da masu shagunan POS suke yi guda biyu ne:


a- Zasu bada kuɗi cash ga wanda yake so, sai su karɓi ATM card ɗinsa su ciri daidai kuɗinsu su tura cikin account ɗinsu. Misali an biyashi albashi dubu goma (10,000) sai ya zo suka bashi tsurar kuɗi dubu goma cash, sannan sai ya basu katinsa mai ɗauke da waɗannan kuɗaɗe, sai su kwashe daidai kuɗin da suka bashi daga accout ɗinsa zuwa nasu.


b- Mutum zai iya kawo kuɗi kamar dubu goma ya ce a tura masa cikin account ɗinsa ko kuma a turawa ɗansa da yake karatu a wata ƙasa ko a tura a account na mahifiyarsa ko ɗan uwansa ko zai biya kuɗin wutar lantarki, ko kuɗin makaranta, da dai sauransu.


A duk waɗannan hidimomi da masu shagon POS suka yi, zasu buƙaci a basu wani abu a matsayin ladan aikin da suka yi. A yadda al’adarsu ta gudana a yanzu akwai wani gwargwado na kuɗi mara yawa da suke karɓa bisa duk dubu ɗaya ko biyar ko goma ko ɗari ko miliyan ɗaya da suka bawa mutum ko suka tura masa. Za a iya basu daga account ɗin mutumin idan da akwai wasu kuɗin a ciki ko ya kawo ladan ya basu hannu-da-hannu daga cikin kuɗin da suka bashi.


7- Waɗannan ayyuka na POS dukansu sun halatta ta fuskoki marasa iyaka ba tare da wani dabaibayi ba. Ga kaɗan daga cikinsu:


i- Akwai abubuwa masu yawa da banki koda kuwa wanda ba na Musulunci ba ne yake yi. Kuma ba a ƙirgasu a matsayin haram. Wannan sun haɗa da tura kuɗi daga wani wuri zuwa wani “transfer” "التحويلات المصرفية. Wannan ba wani laifi a kansa. Mutum kuma zai biya banki ladan aikin da ya yi masa. Abin da masu shagunan POS suke yi a matsayinsu na wakilan banki, waɗanda ya san da zamansu a wannan sana’a, bai gaza ko kuma na ce irinsa ne kwabo-da-kwabo da wanda bankunan suke yi. Malaman zamani kuma bakiɗaya suka ce daidai nan yana da kyau a aikin banki.Wato ba haram ba ne a biya banki kuɗin aikin transfer-(Kararu Majma’ul Fikihil Islami:9/1/370; Al-Bunukul Islamiyya na Abdullahi Addayar sh/25; Al-Ma'amalatul Masrafiyya Wa Hukmuha Fil Islam sh/14-15; Al-Masariful Islamiyyah: Dirasah Li Adadin Minha na Rafik Yunus Al-Misri, sh/53-55; Al-Mu’amalat Al-Maliyyah Fil Fikihil Islami Asalah Wa Mu’asarah na Debian bn Muhammad:12/234-243)


ii- A zahiri ma shagon POS wani ƙaramin banki ne da yake gudanar da wasu daga ayyukan bankin da yake da rijista da su. A lokacin da mutum ya yi amfani da ATM ya ɗebo kuɗi daga injin da banki suka ajiye don ɗibar kuɗaɗe, zai ga bankin sun ɗebi wasu ‘yan kuɗaɗe na hidamar da suka yiwa mutum. Bankin da mutum yake da account suna ɗan yi masa ragi. Amma wani bankin daban suna ɗiba fiye da yadda nasan suka ɗiba. Don haka, shi kansa mai POS ba dalilin da zai sa ba zai karɓi wani kaso na hidimarsa ba!


iii- Masu POS cikakkun wakilai ne na karɓar kuɗin mutum daga bankinsa zuwa nasu, sannan sai su bashi daga kuɗinsu. Saboda "wakilci taimako ne" kamar yadda Ibnul Arabi Al-Maliki yake faɗa "الوكالة معونة".- (Ahkamul Kur’ani: 3/223). Malamai sun bayyana cewa ba laifi ka sa wakili sannan ka biyashi ko kuma in ya ga dama ya yi maka wakilcin Fisabilillahi, ba tare da an biya shi komai ba. Imamu Ibnu Kudama ya na cewa: “Ya halatta a yi wakilci ko don wani abu da za a bayar ko kuma haka kurum ba tare da shi ba”-(Al-Mugni na Ibnu Kudama: 5/95)              قال الإمام ابن قدامة:"يجوز التوكيل بجُعُل، وبغير جُعُل"


A zamanin yanzu ba dole ba ne sai an tura wani ya je bankin da ƙafa sannan za a ce an yi wakilci. Hatta tura kuɗin zuwa account ɗin mai POS a matsayin kamar an je an karɓo yake, irin abin da malamai suke kira da “Karbar abu a Ma’ana” "القبض الحكمي". Tunda kuɗin sun shiga lalitarsa, ba laifi don ya bayar da su ta kowace irin fuska.Wato ko ya ɗauko wannan da ya turawa kansa ya bawa mai kuɗin ko kuma ya bashi wasu da yake da su. Sannan a bashi ladansa.


iv- Masu POS suna yin amfani da ƙwarewarsu da wani ɓangare na kuɗin da suka sa a katin wayarsu ko na data ɗin da suka saya. Haka nan suna amfani da wutar lantarki da injin POS ɗin kansa da suka saya da zaman da suke yi na kuɗi a shaguna. Bugu da ƙari, sun ragewa mutane wahalar bin layin ATM ko na cikin bankuna da aka saba yi. Wannan duka a bayyane yake cewa sun yi wa mutum aiki, don haka masu POS suna da cikakken haƙƙin a biyasu kuɗin wahalarsa.


'Transfer' da kamfanin waya suka huwacewa mutane suke yi ta hanyar amfani da wasu lambobi da kowane kamfanin waya yana da irin tasa, shi ma bai gaza irin aikin da masu POS suke yi ba. Waɗannan kamfanoni suna samun wani kaso daga cikin tura kuɗaɗe da mutane suke yi. Duka ya halatta.


v- Kowace mu’amalla tana da asali guda biyu; “Halasci” da “Inganci” الإباحة والصحة. Babu wani dalili da zai haramta sana’ar POS. Sannan kuma masu yinta a halin yanzu suna gudanar da ita bisa asalin inganci. Don haka ba haram suke ci ba, ba kuma ɓatacciyar sana’a suke gudanarwa ba.


vi- Ba bu wani abu na haram ko riba a cikin mu’amalla guda biyu da ake gudanarwa ta hanyar POS. Domin riba tana shiga abubuwa guda uku ne kurum, kuma ba bu wata hanya da zasu shiga wannan mu’amalla:


a- Ciniki: Ba wata cinikayya aka ƙulla tsakanin mai POS da wanda ya zo masa don ya fito masa da kuɗi ko don ya tura masa ba. Don haka riba ba zata shiga wannan ɓangaren ba.


b- Bashi: Ba wani bashi a cikin wannan mu’amalla ta POS. Domin da ya zo shagon POS cewa ya yi yana da kuɗi (10,000) a cikin wannan ATM ɗin a kwashesu a tura wani account ɗin amma a bashi kuɗin cash. Wannan ‘transfer’ kenan ba bashi ba ce. Don haka riba ba zata shiga ba. Kada a ɗauka don ya zo ya bawa mai POS katin ATM ɗinsa, shi kuma ya tura kuɗi zuwa nasa account ɗin cewa bashi ya bashi. Kuɗin kuma da zai ba shi hannu-da-hannu biyan bashin ne. Wannan ba haka ba ne. Domin  ‘Ana ɗaukar komai da manufarsa’ "الأمور بمقاصدها" kamar yadda wata ƙa’ida ta faɗa. An gina mu’amallar ne a kan ‘transfer’, wadda daman bankuna suna yinta. Mai POS ya ɗebo kuɗin daga wani account ne ya zuba a account ɗinsa, sannan ya bada su cash.


Ko da za a ce banki su ma ajiya, ake cewa mutum, ya kai musu, amma kuma aka hana mu'amallar, saboda ta ginu ne a kan bashi. Wannna haka yake ta fuskar cewa su banki tun ranar da aka kafa tsarin bankunan da aka saba da su yau-da- gobe (Conventional Banks) ya ginu ne a kan bashi da ruwa. Sañnan har yanzu haka yake a rubuce a kan dokokinsu. Ko da mutane suna cewa sun kai ajiyar kuɗaɗe banki, shi bankin ya san ba ajiya aka kai masa ba, shi a wurinsa rance aka ba shi. Amma saɓanin wañnan mu'amalla ta POS wadda tun asali tsakanin mai kuɗi a ATM da mai shagon POS ba wanda yake da manufa ta bashi da rance, kowannensu manufarsa ita ce za a yi transfer ta kuɗi kawai. Don haka suka bambanta da tsarin da mutanen suke kira "ajiya a banki".


Wani abu mai matuƙar muhimmaci da ya kamata kowa ya daɗa ganeshi shi ne, idan har mun ƙaddara cewa alaƙar bashi da rance ce tsakanin mai POS da mai kuɗi a katinsa na ATM, to abin la'akarin shi ne shi mai kuɗin shi ne fa ya bada rance sañnan shi ne kuma ɗin dai ya bada ƙarin da sunan ladan aiki. Ba wai mai shagon POS ne ya mayar da kuɗin da aka ranta masa (in har mun ɗauka ma bashi aka bashi!), sannan ya ƙara wani abu a kai ba. Domin malamai sun faɗa cewa riba ita ce ƙudin da wanda ya karɓi rance zai mayar da kuɗin da aka bashi da wani ƙarin'. A mas'alar POS kuwa ba shi ne ya ƙara ba, shi aka ƙarawa. Wañnan yanayin kuwa ba malamin da ya kirawoshi da sunan riba!!


A yi la'akari da wañnan sosai, domin ina ganin rashin ganeshi da fayyaceshi ne, ya sa wasu suke ɗaukar akwai riba a mu'amalar POS, wanda kuma a haƙiƙa, kamar yadda aka gani, ba bu!


c- Canji: Duk da akwai burbushin cinikayya a cikin canji, sai dai a ilimi Fiƙihu ana wareshi saboda ƙarfin ma’anar da take cikinsa wadda zata iya sawa ya ci gashin-kansa. Abin nufi dai masu POS ba canji suke yi ba. Kuɗin mutum ne za a bashi irinsu. Sai dai a lokacin da ya bada Naira aka turawa ɗansa ko wakilinsa a wata jiha ko wata ƙasa, zai ɗebi daidai da canji da ƙimar wannan kuɗi a can.


Abin da hadisai suka hana na canji kamar wanda ya shafi dinare da dinare ko azurfa da azurfa ko naira da naira ko dala da dala shi ne, misalin a sami jan gwal sosai da kuma farin gwal, wanda ba mai ja sosai ba, sai a ce za a ɗauki wani abu a cikin wanda ba mai ja sosai ɗin ba. Kamar sabuwar naira da tsohuwa, sai a ce za karɓi wani abu a wurin mai tsohuwa don an bashi sabuwa. Wannan shi ne haram. Amma idan ya zamo gwal ko naira ɗin suna wani account sai aka turashi wani account ɗin daban sannan aka bawa mutum irinsa, shi kuma ya bada ladan wani kuɗi don wahalar turawa da rage masa wahalar zuwa banki da aka yi, wannan ba laifi.


Shi kuwa mai POS ya bawa mutum kuɗinsa yadda suke, sai dai yana cewa za a bashi kuɗin fito da ya yi! Ba wai mutum zuwa ya yi, a misali, ya miƙa masa ₦10,000 hannu da hannu, shi ma ya mika masa ₦9,990 a matsayin canji ba.  Ba irin wañnan aka yi ba.


Dangane da ita kuma misali naira ɗarin ta ladan fito, mai ATM zai iya bawa mai POS ita daban, ko kuma ya yarjewa mai POS ya haɗa da ita a cikin transfer ɗin da ya yi daga cikan katin, a matsayin ladan aikinsa. Masu canji kuwa cewa zai yi zan baka sababbin 'yan naira ɗari-ɗari na ₦10,000 amma zaka ɗora mini naira ɗari, to a nan sai a ce an yi riba! Domin amfanin sabuwar naira ɗari da tsohuwa duk ɗaya ne, ba bu dalilin karɓar wani abu a nan!


A cikin Mazahabin Hambaliyya, duk da cewa saɓanin Mazahabin Jumhurun Malamai ne, amma sun halatta cewa mutumin da ya sana’anta wani gwal ya zubashi a wata kama da ado na musaman a zo a sayi gwal da kuɗin da ya yi daidai da shi, sannan a ƙara wani abu a matsayin ladan sana'arsa da fasahar da ya nuna a wajen ƙera ɗankunne da sarƙa da wannan gwal ɗin. Shehul Islami Ibnu Taimiyya da Ibnul Kayyim da Ibnu Mani’, duk sun tafi a kansa haka. Sheikh Al-Mardawai ya ce, 'A kan haka fatawar malamanmu na Hambaliyya ta gudana'. Ga kuma bayanin da Ibnu Kudama ya yi. Ya ce: “Idan mutum ya ce da gursimeti  ka ƙera mini zobe azurfa, nauyinsa kamar dirhami ɗaya, zan biyaka dirhami ɗayan. Sannan zan baka wani dirhamin a matsayin ladan aikinka, wannan ba ya cikin irin abin da aka hana sayar da dirhami ɗaya da guda biyu. Malaman Mazahbinmu na Hambaliyya suka ƙara da cewa: gursimetin zai iya karɓar dirhami biyun, ɗaya a matsayin kuɗin zoben, ɗayan kuma sakamakon ladansa“-(Al-Mugni na Ibnu Kudama: 4/130-131; Al-Majmu’u na Nawawi:10/87-88; Al-Ikhtiyarat Al-Fikhiyyah na Al-Ba’ali:sh/473; Al-Fatawal Kubra na Ibnu Taimiyyah:5/391, I’lamul Muwakki’in na Ibul Kayyim: 2/159-162, Al-Furu’u na Ibnu Muflih:4/149; Al-Insaf na Ala’uddini Al-Mardawi:5/15; Azzahbu Wa Ba’adu Khasa’isihi Wa Ahkamihi na Ibnu Mani’ a Majallar Majma’ Fikhil Islami, Al-Mu’amalat Al-Maliyyah Fil Fikihil Islami Asalah Wa Mu’asarah na Debian bn Muhammad:11/273-322)
قال الإمام ابن قدامة:"فأما إن قال لصائغ: اصنع لي خاتما؛ وزنه درهم، وأعطيك مثل زنته. وأجرتك درهما. فليس ذلك بيع درهم بدرهمين. وقال أصحابنا للصائغ أخذ الدرهمين؛ أحدهما في مقابلة الخاتم. والباقي أجرة له".


8- Kulawa kada mutum ya faɗa cikin haram ko ya ci riba  yana daga cikin muhimman abubuwan da Musulmi yake ƙoƙari a kowane lokaci. Sayyadina Umar ya yi bayanin yadda mas’alolin riba suke da wahalar sha’ani wajen ganesu, sannan ya ce, “Ku  ƙauracewa riba da duk wani abu na kokwanto”.-(Sunanu Ibnu Majah, L:2276)
  قال عمر بن الخطاب- رضي الله عنه -"دعو الربا والريبة".


Duk wata mu’amalla da wani yake yi, in ya ji shi a zuciyarsa bai gamsu da ita ba, sai kurum ya ƙaurace mata. Wannan kuma bai hana waɗanda suka gamsu da ita su ci gaba da yinta ba, matuƙar akwai mafita ta Shari’a a ciki. Malamai suna faɗa a wata ƙa’ida cewa, “Abin la’akari a mu’amalla shi ne manufa da ma’anonin da suka ƙunsa, ba wai zahirin lafazi da ginin kalmomi ba”.
"العبرة في العقود بالمقاصد والمعاني، وليست بالألفاظ والمباني"


Amma saɓanin masana ko malamai a kan wata mas’ala ba shi ne yake nufin an bawa mutane damar yin zaɓi-ka-tika ta hanyar mutum ya zaɓa wani ra’ayi kurum ya darje shikenan ba! Mutum yana zaɓar maganar da tafi tsayawa a kan dalilan Kur’ani da Sunna ne kurum, ba wai ya bi yarima a sha kiɗa ba! Ko ya bi hanyar tsanantawa mara tushe! Imamu Sufyanu Assauri yana cewa, “Ilimi a wurinmu shi ne samun rangwame daga yardajjen malami. Amma matsantawa kuwa, wannan kowa zai iya yinta”.-(Jami’u Bayanil Ilimi Wa Fadlilihi na Ibnu Abdilbarri: 2/77/ 766)
قال الإمام سفيان الثوري رضي الله عنه أنه قال إنما العلم عندنا الرخصة من ثقة، فأما التشديد فيحسنه كل أحد".


Allah ya bamu tsayawa a kan neman halal da ƙauracewa haram bisa yadda Shari’a ta tsara. Ya bamu ikon tsayawa a kan tsarin addininmu da bin sahun Annabinmu – Tsira da Amincin Allah su ƙara tabbata a gareshi da Alayensa da Sahabbansa bakiɗaya Amin.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Saturday, 18 April 2020

Ya Matsayin Kudin Da Aka Tarawa Mara Lafiya Don Neman Magani Sai Ya Rasu?

Ya Matsayin Kudin Da Aka Tarawa Mara Lafiya Don Neman Magani Sai Ya Rasu?

TAMBAYA

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wa Barakatuh. malam Dan Allah a warware mana wannan matsalar.

YA MATSAYIN KUƊIN DA AKA TARA WA MARA LAFIYA DON NEMAN MAGANI SAI YA RASU...

Mutum ne ba lafiya aka nema masa taimakon kuɗi domin dashen ƙoda, ana cikin haka ba'a kai ga gamawa ba sai ya rasu to wannan kuɗin nasa ne ma'ana yazama nashi  zai shiga gadonshi ko za'a iya taimakon wani mai tsananin buƙata irin wannan larurar?? Mun gode jazakumullahu khairan.

AMSA

Wa'alaykumussalam

Dukiyar da wani ya bayar don mamaci, kafin ko a bayan rasuwar sa ne, ita ma ta na cikin dukiyar gado.

A duba : [FATA'WAL LAJNATID DA'IMA; 16/473]

Wallahu A'alam

AMSAWA: Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Sunday, 5 April 2020

WASU-WASI A CIKIN SALLAH GUDA BIYU NE

WASU-WASI A CIKIN SALLAH GUDA BIYU NE

TAMBAYA

Assalamu Alaikum, barka da warhaka.

Mallam dan Allah mene ne hukuncin mai yawan was-wasi acikin sallarsa?

MAI YAWAN WASU-WASI A CIKIN SALLARSA!!...

Kuma mene ne yafi dacewa
mutun yayi domin ya daina??

Nagode

(daga Ummie Maiwada).

AMSA

Was-wasi acikin Sallah kala biyu ne:

1. Akwai wanda yake faruwa ta dalilin sakaci da shagaltuwa da sha'anin duniya da kuma rashin damuwa da Sallar daga wajen Shi Mai Sallar.

Ta yadda zaka ga mutum yana sallah amma idonsa akan hanya, ko ta taga yana ganin masu wucewa. Ko kuma mutum yana Sallah amma ya kunna talabijin agabansa ko rediyo (ba yaso labarai su wuce shi).

Ko kuma kaga Alhaji yana Sallah a Masallaci amma zuciyarsa tana kasuwa. Harma wasu lokutan idan Liman yayi rafkanuwa a Sallar, da zarar Mamu sunyi Kabbara sai kaga Alhaji ya firgita. Azatonsa ko yaƙi aka soma.

Hukuncin irin waɗannan was-wasin, Haramun ne. idan ma basu ɓatawa Mutum Sallarsa ba, to zasu iya kaishi izuwa Rasa ladan sallar.

2. Was-wasi na biyu kuma Shine irin was-wasin da Shaiɗanun Aljanu suke haifarwa Mutum idan sun shiga jikinsa, ko kuma su na son su shiga.

Zaka ga masu fama da irin wannan larurar suna da yawan kokwanto acikin yawancin lamura. Musamman ma asha'anin Ibada.

Zaka ga idan sunzo Sallah su na yin iyakar bakin ƙokarinsu wajen kiyayewa, amma inaa! Zaka ga sun kiɗime sun rikice sun manta ko raka'a nawa sukayi.

Galibi ma tunane-tunane irin na saɓon Allah ne zasu riƙa zuwa musu acikin sallar.

Irin wannan babu laifi akan shi mai sallan.

Domin kuwa yana yin iyakar ƙokarinsa.

Wani ma har kuka zaka ga yana yi.

Kuma abin ya riga ya zamar masa cuta ko larura.

MAGANINSA SHINE:

Mutum ya dage da yawan ambaton Allah acikin dukkan motsinsa. Duk abinda zaiyi ya fara da Basmalah.

Yawaita karatun AL-KUR'ANI. Da kuma sauraron sautin AL-KUR'ANI.

Ya riƙa karanta Azkar na safe da yamma. Da na kwanciyar bacci da tashi.

Ya dena barin najasa tana daɗewa ajikinsa. Ya yawaita zama cikin tsarki da alwala.

Ya gujewa ayyukan saɓo manya da kanana.

Duk lokacin da zaiyi Sallar ya riƙa karanta Du'a'ul-Istifta­hi Afarkon Sallar.

Insha Allahu zai samu saukin abin.

Malamai sunce duk wanda irin wannan kokonton ya aureshi, yayi sujjadah ba'adi (duk sanda ya idar da Sallar).

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Source: ZAUREN FIQHU

Sunday, 29 March 2020

Shin  Ko Yana Yiwuwa Covid-19 Ta Shiga Makkah da Madinah?

Shin Ko Yana Yiwuwa Covid-19 Ta Shiga Makkah da Madinah?

Bayan hukumomin Saudiyya sun fitar da sanarwar dakatar da Umrah zuwa wani lokaci saboda Covid-19, cece-kuce ya kaure tsakanin mutane kan ko yana yiwuwa Covid-19 ta shiga Makkah da Madinah ko a'a? Masu ganin cewa cutar ba za ta iya shiga waɗannan garuruwa biyu masu alfarma ba.

Makkah

Marubuci:- Dr. Zakariyya Shu'aib Adam

Na kafa hujja ne da hadisin da Bukhari (1880) da Muslim (1379) suka rawaito cewa Annabi (SAW) yace:

 (عَلَى أَنْقَابِ الْمَدِينَةِ مَلَائِكَةٌ لَا يَدْخُلُهَا الطَّاعُونُ وَلَا الدَّجَّالُ)

 (Akwai wasu mala'iku tsaye a ƙofofin Madinah, annoba da Dujal ba za su shige ta ba)

Duba da wannan hadisi, mutum na iya cewa: annobar corona ba za ta iya shiga Makkah da Madinah ba.

A wani hannu kuma, wasu daga cikin mallamai na ganin cewa annobar corona na iya shiga garuruwan, shi yasa ma mahukuntar ƙasa mai tsarki suka dakatar da yin Umrah don gudun kada wani daga wata ƙasa ya kai cutar harami. Waɗannan mallamai na ganin cewa wancan hadisi na sama, yana nufin wata annoba ce ƙayyadadda, ba duka annoba ba.

Shi yasa mallaman suke cewa: akwai bambanci tsakanin الطاعون (Aɗɗá'ún) da kuma الوباء (Al-wabã'). A duka hadisan, Annabi (SAW) cewa yayi: الطاعون, bai ce الوباء ba.

Dalilan da ke ƙarfafa cewa corona na iya shiga Makkah da Madinah da kuma cewa akwai bambanci tsakanin الطاعون da الوباء, suna da yawa, amma ga kaɗan daga cikinsu:

1. Ahmad da Ɗabaraniy da Abu Ya'ala sun rawaito hadisi daga Aisha (RA) ta tambayi Annabi (SAW) kan ma'anar الطاعون, sai yace:

(غدة كغدة البعير يخرج في المراق والإبط)

(Kumburi ne irin na raƙuma, yana fitowa a ciki da hammata).

Dangane da ma'anar الطاعون a yaren larabci kuwa, An-Nawawiy yace a cikin sharhin Muslim:

(الطاعون: قروح تخرج في الجسد فتكون في الآباط أو المرافق أو الأيدي أو الأصابع وسائر البدن، ويكون معه ورم وألم شديد)

(Addã'ún: daji ne (cancer) dake fita a  jikin mutum. Yana kasancewa ne a hammata, gwiwar hannu ko hannu, ƴan yatsu da sauran jiki. Yana sabbaba kumburi da kuma zafi mai tsanani).

2. Shi kuwa الوباء, yana nufin annoba gamammiya dake shiga mutane da yawa kuma take aukuwa a garuruwa da yawa. Ya zo a cikin "Al-Mu'ujamul Ma'aniy" cewa:

(الوباء: كل مرض شديد العدوى، سريع الانتشار من مكان إلى مكان، يصيب الإنسان والحيوان والنَّبات، وعادةً ما يكون قاتلا)

(Al-Wabá'u: Duk wata cuta mai tsananin tashi daga wani zuwa wani (infectious), mai saurin tashi daga wani wuri zuwa wani. Tana shiga mutum, dabbobi da kuma tsirrai. Tana kisa a al'adance).

Ibnu Hajar ya hakaito maganar Iyád a cikin Fathul Bári cewa: "Duka الطاعون, to الوباء ne, amma ba duka الوباء ne الطاعون ba." Wannan itace fahimtar Ibnul Ƙayyim a Zadul Ma'ad.

3. Abinda zai ƙara fito maka da cewa corona, a matsayinta na الوباء, tana iya shiga Makkah da Madinah domin ba الطاعون bace, hadisin da Bukhari (2643) ya rawaito daga Abul Aswad:

(أَتَيْتُ الْمَدِينَةَ وَقَدْ وَقَعَ بِهَا مَرَضٌ ، وَهُمْ يَمُوتُونَ مَوْتًا ذَرِيعًا)

(Na zo Madinah (a zamanin Umar (RA)), alhalin wata cuta ta shigo garin. Mutane na mutuwa da sauri).

Wannan hadisi yana nuna cewa annoba gamammiya na iya shiga garin Madinah tun da gashi mutane da yawa suna mutuwa cikin ƙanƙanin lokaci.

Amma الطاعون ba zai iya shiga ba saboda akwai mala'iku da za su kare garin.

4. A likitance, الطاعون shine Plague. Plague epidemic ko pandemic bacterial infection ne da ke samun mutane da wasu dabbobi. Itace cuta mafi kusa da fassarar da Annabi (S.A.W) ya gayawa A'isha, wacce Imam Nawawiy ya faɗaɗa. Daga cikin alamomin plague, akwai kumburin lymph nodes, musamman na hammata (axillary lymph node) da kuma wuya.

Plague ana kamuwa da ita ne ta hanyar cizo daga infected fleas, ko kuma yayin mu'amala da dabba mai ɗauke da cutar.

Shi kuma الوباء, yana nufin mujarradin epidemic ko pandemic disease ba tare da lura da cewa Plague ne ko ba Plague ba. Ka ga Plague cuta ce da bacteria ke sabbabawa (Yersinia pestis), amma ita الوباء tana iya samuwa ta dalilin bacteria (kamar Plague, Cholera Leptospirosis) ko kuma virus (kamar Covid-19, Ebola, Influenza).

A taƙaice, wannan bayani na nuna cewa Covid-19 ba الطاعون bace, الوباء ce. Kenan tana iya shiga garuruwan Makkah da Madinah. Saboda haka, mahukuntan Saudiyya sun yi daidai da suka dakatar da Umrah har zuwa wani lokaci da Allah zai yaye cutar. Abinda zai ƙara tabbatar maka da haka shine: A yanzu haka, akwai cases 103 na Covid-19 da aka tabbatar a Saudiyya. In da ace Covid-19 itace الطاعون, to da tabbas ba za ta shiga Makkah da Madinah ba.

Allahu A'alam

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Monday, 9 March 2020

SHIN KO YA HALATTA NA AURI KIRISTA?

SHIN KO YA HALATTA NA AURI KIRISTA?

TAMBAYA

Malam musulmi zai iya auren ahlul kitab ta na addininta yana musuluncinsa?

Tambaya Mabudin Ilimi..

MarubuciDr. Jamilu Zarewa

AMSA

To Ɗan uwa Allah maɗaukaki ya halatta auren kamammu daga cikin ahlul-kitabi, wato Yahudu ko Nasara, kamar yadda ya yi bayanin hakan a cikin suratul Ma'ida a aya mai lamba ta: (5), kuma an samu wasu daga cikin sahabai, sun aure su kamar Usman ɗan Affan - halifa na uku a musulunci- ya auri Banasariya, haka Dalhatu ɗan Ubaidillah ya auri Banasariya, sannan Shi ma Huzaifa masanin sirrin Annabi ﷺ ya auri Bayahudiya, Allah ya kara musu yarda.

Duba: Ahkamu-ahlizzimah 2\794.

Saidai malaman wannan zamanin suna cewa, abin da ya fi shi ne rashin auren Ahlul-kitab a halin yanzu, saboda yadda zamani ya canza, domin da yawa idan mijinsu musulmi ya mutu yaran suna zama cirister, kai wani lokacin ko da sakinta ya yi za ta iya guduwa da yaran, sannan zai yi wuya ka samu kamammu waɗanda ba su taɓa zina ba a cikinsu.

Wasu kasashen kuma idan za ka auri Kirista daga cikinsu dole sai ka yarda da dokokin ƙasarsu, a lokuta da yawa kuma za ka samu dokokin sun saɓawa ka'idojin musulunci.

Allah ne mafi sani.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Sunday, 1 March 2020

ZAN IYA DORA RIBA IDAN AKA WAKILTA NI SAYO ABU?

ZAN IYA DORA RIBA IDAN AKA WAKILTA NI SAYO ABU?

Tambaya:

Assalamu Alaikum Mallam, dan Allah ina da tambaya, kaman misalin mutum yana baka kuɗi ka sayo mishi abu, wataran ya baka kuɗin ka sayo, wataran kuma sai ka sayo ka kai zai baka kuɗin, shin koya halasta inci riba a wanda yaban kuɗin shi in sayo mai, ko kuwa a wanda na sayo da kuɗina ne kawai zan iyacin riba, banda Wanda ya bada kuɗin shi? Nagode Allah ya ƙara basira.

Zan Iya Ɗora Riba Idan aka Wakilta Ni..


MarubuciDr. Jamilu Zarewa

Amsa:

Allah ya amsa addu'arki ƴar uwa, idan mutum ya wakilta ki, ya baki kuɗi ki sayo masa wani abu, bai halatta ki ci riba da shi ba, sai da izininsa, saboda hadisin Urwatu Al-ja'ady lokacin da Annabi (S.A.W) ya ba shi dinare (1) don ya sayo masa dabbar layya, sai ya sayo akuyoyi guda biyu, ya sayar da ɗaya akan dinare ɗaya, ya zo ma da Annabi (S.A.W) da akuya ɗaya da kuma dinaran da ya aike shi, sai Manzon Allah ya amshe ya yi masa addu'a, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 3642.

Kasancewar Annabi (S.A.W) ya tabbatar da shi akan aikinsa, sai ya nuna hakan shi ne shari'a, don haka idan wakili ya samu ragi ko ya ci riba a cinikayyar da aka wakilta shi ya wajaba ya dawo da ita zuwa wanda ya aike shi.

Idan ya wakilta bai bayar da kuɗi ba, to mutuƙar kuna kasuwanci a tsakaninku ya halatta a ɗora riba, amma in ba kwa yin kasuwanci ba za ki ɗora riba ba, za ki kawo masa abin a kuɗin da ake siyarwa a kasuwa, saidai in ya bada iznin cin riba, saboda wakili amintacce ne a shari'a, wasu malaman suna ganin za ki iya ɗora gwargwadon wahalarki, in bai bada kuɗi ba.

Don neman ƙarin bayani duba Al-mugni na Ibnu khudaamah 5\86.

Allah ne mafi sani.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.


Saturday, 22 February 2020

Mahaifinmu Ya Mutu Za Mu Iya Yin Zaman Makoki?

Mahaifinmu Ya Mutu Za Mu Iya Yin Zaman Makoki?

TAMBAYA

Malam mahaifina ya rasu, sai wani malamin islamiyyar mu ya ce min ba kyau zaman makoki, to gaskiya kaina ya ɗaure, saboda na taso na  ga ana yi, kuma idan ban yi ba za'a ce ban damu da mahifinmu ba, malam yanzu yaya zan yi? Allah ya datar da kai zuwa dukkan alkairai.

Baya Halatta ga Musulmi yin Kuka Idan Wani ya Rasu (Mutu)

MarubuciDr. Jamilu Zarewa

AMSA

To Ɗan Uwa Allah ya ba mu dacewa gaba ɗaya, tabbas malamai sun tattauna akan hukuncin zaman makoki, sai dai sun kasu kashi uku:

1. Akwai waɗanda suka tafi akan makaruhi ne, saboda hadisin Jarir R.A wanda Imamu Ahmad ya rawaito cewa: "Mun kasance muna ƙirga taruwa yayin mutuwa da kuma yin abinci ga gidan da aka yi mutuwa daga cikin rurin da Allah da ya haramta", Musnad: 6905, don haka suna cewa, sai dai a haɗu da waɗanda aka yiwa rasuwa akan hanya ko a kasuwa, ko masallaci ayi musu ta'aziyya, wannan ita ce maganar Shafi'i a cikin Umm 1\318, haka Nawawy a Majmu'u 3\306.

2. Akwai waɗanda suka tafi akan cewa bidi'a ne, kamar Ibnul-kayyim a zadul ma'ad 1\527.

3. Akwai malaman da suka tafi akan halaccin zaman makoki, saboda hadisin da nana A'isha ta rawaito cewa, lokacin da aka kashe Zaid ɗan Haritha da Ja'afar ɗan Abu-dalib Annabi ﷺ ya zauna a wani wuri, duk wanda ya gan shi zai ga alamun baƙin cikin tare da shi, sai wani mutum ya zo ya ce masa: ga matan Ja'afar can suna ta kuka, sai Annabi ﷺ ya umarce shi da ya je ya hana su, su kuma yi hakuri"
Bukhari hadisi mai lamba ta: 1299.

Waɗannan malaman suna cewa: Za'a iya fahimtar hallacin zaman makoki a wannan hadisin a wurare guda biyu:

A. Faɗin nana A'isha cewa "Ya zauna ana ganin alamun baƙin ciki tare da shi da kuma zuwan wancan mutumin". Dalili ne da yake nuna cewa: yana zaune ne a wurin da mutane suka sani kuma suke zuwa su same shi.

B. Kasancewar bai hana matan Ja'afar taruwar da suka yi ba, kawai kukan ya yi umarni da a hana su.

Wannan maganar ta hallaci an rawaitota daga Imamu Ahmad kamar yadda ya zo a Insaf 5\565 da kuma Ibnu-Abdulbarr na Malakiyya, kamar yadda ya zo a littafinsa na Alkafy 1\283, sannan wasu daga cikin Hanafiyya sun tafi akan haka kamar yadda ya zo a Binaya 3\303.

Prof. Khalid Al-mushakih (Ɗaya daga cikin manyan ɗaliban Sheik Bn Uthaimin) ya rinjayar da zance na uku, sai dai za'a guji abubuwa kamar haka a lokacin wannan zaman:

1. Yawaita yin abinci, da masu karɓar gaisuwa, zai yi kyau ya zama makusantansa ne kawai za su amshi gaisuwa.

2. Nisantar  yin laccoci a wurin, domin hakan na daga cikin bidi'o'in da ba su da hujja.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Falalar Wankan Gawa da Yadda Ake Yinsa

Daga Karshe Sunyi Kwanciyar da Babu Ranar Tashi

Hanakali Na Yana Tashi Idan Na Tuna da Wannan

3. Nisantar tsawaita zaman, a yi shi gwarwadon buƙata.

Duba maganarsa a: Fiqhunnawazil shafi na: 75.

Allah ne mafi sani.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



Wednesday, 19 February 2020

Shin ko Ya Halatta na Sayi Kare Saboda Gadi a Gidana?

Shin ko Ya Halatta na Sayi Kare Saboda Gadi a Gidana?

Tambaya

Assalamu alaikum. Dr. Mene ne hukuncin ajiye kare a gida saboda gadi? Allah muke roƙo ya kara wa Dr lafiya da basira Amin.

         SHIN KO YA HALATTA NA SAYI KARE                    SABODA GADI A GIDANA

Marubuci: Dr. Jamilu Zarewa

Amsa

Wa'alaikum assalam, Ya tabbata a hadisin Bukhari da Muslim cewa: "Mala'iku ba sa shiga gidan da yake akwai hoto ko KARE a ciki.

A wani hadisin mai lamba ta: 2974 da Muslim ya rawaito Annabi (S.A.W) yana cewa: "Duk Wanda ya riƙe KARE, in ba Karen noma ba ko farauta ko kiwo, to Allah zai tauye masa  manyan lada guda biyu a kowacce rana.

Da yawa daga cikin malamai sun yi kiyasin KAREN GADI akan waɗancan nau'ukan guda uku da suka gabata, don haka ya halatta musulmi ya riƙi Kare saboda gadi in har akwai buƙatar hakan.

Ba ya halatta a siyar da kare kowanne iri ne, saboda Annabi ﷺ ya hana cin kuɗin Kare a hadisin da Muslim ya rawaito kuma ya kira Shi da dauda.

Duk da cewa an halatta waɗancan nau'ukan guda huɗu saboda buƙata sai dai bai halatta a siyar da su ba, saboda ƙa'ida sananniya a wajan malaman Fiqhu wacce take cewa:

ما جوز للحاجة لا يجوز أخذ العوض عليه

MAKALOLI MASU ALAKA:

SHIN DAN ALLAH MALAM ME NE NE HUKUNCIN YIN SAKI UKU A CIKIN FUSHI?

MALAM NA TSINCI NAIRA ₦500 KOZAN IYA AMFANI DA ITA BATARE DA CIGIYA BA?

DAN ALLAH MALAM ME NE NE BAMBANCIN MUTANE DA MALA'IKU?

Idan mutun yana buƙatar ɗaya daga cikin waɗancan nau'uka na karnuka guda huɗu da suke halatta, kuma bai samu wanda zai ba shi kyauta ba, ya halatta ya siya, Amma zunubin sayarwar yana kan wanda ya sayar tun da shi ne bai bayar ba, kamar yadda Ibnu Hazm ya faɗa a littafinsa na Muhallah 4/793, Ƙa'ida tabbatacciya a wajan malamai tana cewa:

ما حرم سدا للذريعة يباح للحاجة أو المصلحة الراجحة

Allah ne mafi sani.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



Thursday, 23 January 2020

SHIN DAN ALLAH MALAM ME NE NE HUKUNCIN YIN SAKI UKU A CIKIN FUSHI?

SHIN DAN ALLAH MALAM ME NE NE HUKUNCIN YIN SAKI UKU A CIKIN FUSHI?

                            TAMBAYA

Assalaam Alaikum Wa Rahmatul Laah.

Mijina ya sake ni a cikin fushi kuma daga baya ya yi nadamar yin hakan, har ya nemi in koma amma na ƙi, har sai na yi wani auren. Daga baya muka yi auren sirri da wani, wanda bayan saduwa guda ya sake ni ya gudu. Iyayena kuma suka ce ba su yarda da wannan auren ba! Ni kuma ina son komawa gidan mijina wurin ’ya’yana mata guda biyar!

Haƙuri Matakin Nasara...


Don Allah wanne taimako za ku yi a kan wannan?

Marubuci: Jibrin Ahmed Baushe


                            AMSA

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

1. Taimakon da kowanne musulmi zai iya yi miki a nan sai dai ya bayyana miki hukuncin Allaah Subhaanahu Wa Ta’aala kawai a kan al’amarin idan ya sani. Sannan kuma ya umurce ki da yin haƙuri wurin yin biyayya ga dokokinsa, a matsayinki na musulma wacce ta yi imani da shi, kuma take da aƙidar sallamawa da miƙa wuya gare shi a cikin komai.

2. Malamai sun kasa sakin aure nau’i-nau’i ne: Akwai Sakin Sunnah akwai kuma Sakin Bidi’a. Saki uku yana iya shiga kowanne daga cikin nau’ukan guda biyu.

Idan Saki-uku yana nufin saki na-uku ne, watau ya sake ta saki na-uku a bayan wasu saki ɗai-ɗai har guda biyu da suka gabata, wannan ya shiga nau’in saki na Sunnah ne. Shi ne kuma wanda Nassin Alqur’ani ya tabbatar da hukuncinsa cewa:

فَإِن طَلَّقَهَا فَلَا تَحِلُّ لَهُۥ مِنۢ بَعۡدُ حَتَّىٰ تَنكِحَ زَوۡجًا غَیۡرَهُۥۗ

Ba za ta halatta gare shi ba a bayan haka, har sai ta auri wani mijin da ba shi ba.

(Surah Al-Baqarah: 230)

Idan kuma Saki Uku yana nufin saki sau uku ne a lafazi guda, kamar ya ce: ‘Ya sake ta saki uku’, ko kuma a mazauni guda, watau kamar ya ce: ‘Ya sake ta! Ya sake ta! Ya sake ta!’ A nan malamai tun daga zamanin Sahabbai har zuwa yau sun yarda cewa shi sakin bidi’a ne. Inda suka yi saɓani dai shi ne: Ko za a ɗauke shi a matsayin ukun ne, ko kuwa dai a matsayin ɗaya ne? Maganar da ta fi inganci da ƙarfi ta fuskar dalilai kamar yadda manyan malamai muhaƙƙiƙai suka tabbatar ita ce ta ƙarshen. Watau shi saki ɗaya ne wanda kuma mijin yake iya yin kome a cikinsa,kafin ta gama idda.

Wannan maganar a wurin fatawa kenan, amma a wurin hukunci dole ma’aurata su koma ga irin hukuncin da Alƙalin Musuluncin yankinsu ko garinsu ya ɗauka daga cikin ra’ayoyin guda biyu, don gudun kar a janyo hayaniya a tsakanin al’umma. Wal-Laahu A’lam.

3. Amma shi Auren sirri, watau Auren Ɓoye: Shi ne auren da namiji da mace suke ƙullawa su kaɗai a saƙo, ba tare da sanin waliyyin matar, ko kuma shaidu ba. Duk malamai sun haɗu a kan cewa: Wannan auren ɓatacce ne, ya fi kama da auren daduro wanda Alƙur’ani ya hana:

 فَٱنكِحُوهُنَّ بِإِذۡنِ أَهۡلِهِنَّ وَءَاتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ بِٱلۡمَعۡرُوفِ مُحۡصَنَـٰتٍ غَیۡرَ مُسَـٰفِحَـٰتࣲ وَلَا مُتَّخِذَ ٰ⁠تِ أَخۡدَانࣲۚ

Ku aure su da izinin waliyyansu, kuma ku ba su sadaƙoƙinsu yadda ya dace da shari’a, suna masu kamun kai ba mazinata ba, ba kuma masu yin daduro ba.

Surah An-Nisaa’i: 25.

Haka kuma Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

أَيُّمَا امْرَأَةٍ نَكَحَتْ بِغَيْرِ إِذْنِ وَلِيِّهَا، فَنِكَاحُهَا بَاطِلٌ! فَنِكَاحُهَا بَاطِلٌ!! فَنِكَاحُهَا بَاطِلٌ!!!

Duk matar da ta yi aure ba tare da izinin waliyyinta ba, to aurenta ɓatacce ne! Aurenta ɓatacce ne!! Aurenta ɓatacce ne!!!

Ahmad da Abu-Daawud da At-Tirmiziy da Ibn Maajah suka riwaito, Shaikh Albaaniy ya ce:  Sahihi ne a cikin Al-Irwaa’: 1840.

4. Daga waɗannan nassoshin ya bayyana a fili cewa:

Idan sakin da mijin ya yi miki saki uku ne a cikin kalma guda ko a wuri guda, sannan kuma ya nemi ki dawo ku Ci gaba da zama bayan ya yi nadama a kan hakan, wannan ba laifi ba ne, a maganar da malamai muhaƙiƙai suka rinjayar, kamar yadda ya gabata. In da kin amince da shi a kan haka tun a lokacin to da wataƙila a yanzu an wuce wurin, da sai dai ki riƙa bayar da labarinsa kawai.

Dogewan da kika yi cewa dole sai kin sake yin aure da wani namijin da ba shi ba, wannan shi ya kai ga faɗawa a cikin kuskure ba-biyu: Watau Auren Sirri, wanda kuma kamar yadda muka ji daga harshen Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam): Shi ɓataccen aure ne. Don haka ne ma iyayenki suka ƙi amincewa da shi. Shi ma wanda kuka yi da shi ya gudu, don yana tsoron kar asirinsa ya tonu, kamar yadda kika bayyana a farkon fatawarki.

4. Don haka, hanyar da ta rage muku ke da tsohon mijinki ita ce: Ku yi haƙuri har sai kin je kin sake yin wani aure sahihi da sanin iyaye da sadaki da shaidu da komai, kuma auren ya zama na soyayya ba na haɗin baki ba da wani mijin da ba wancan ba. Kuma idan daga baya ya sake ki a bayan sahihiyar saduwa, to a nan ne kike iya komawa ga mijinki na farko.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA HANYOYIN MAGANCE MATSALOLIN MA'AURATA CIKIN SAUKI

Shin ko Me Ne Ne Dalilin da Yasa Mata basa Son a yi Musu Kishiya?

Karanta Muhimman Abubuwa 10 da Yakamata Kowanne Miji ya Kula dasu Idan Zai Yi Magana da Matar Sa

Dalili: Saboda hadisin da Al-Imaam An-Nasaa’iy da Ahmad suka riwaito daga A’ishah Ummul-Mu’mineen (Radiyal Laahu Anhaa) cewa: An tambayi Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) game da mutumin da ya saki matarsa, kuma ta je ta auri wani mijin da ba shi ba, ya tare da ita, amma sai ya sake ta tun bai sadu da ita ba, shin ko tana halatta ga mijinta na farko? Sai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

لاَ حَتَّى يَذُوقَ الآخَرُ عُسَيْلَتَهَا وَتَذُوقَ عُسَيْلَتَهُ

A’a! Har sai ɗayan ya ɗanɗana zumanta, ita ma ta ɗanɗana zumansa!
(Sahih An-Nasaa’iy: 3407)

Wal Laahu A’lam.

Amsawa: Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode