Thursday 25 November 2021

Shin Annabi Muhammad (SAW) Ne Farkon Halitta?

Tura Wannan Zuwa

TAMBAYA


Assalamu alaikum Malam ina da wata tambaya wadda ta ɗaure mun kai, idan ka san amsa don Allah ka ba ni tare da gamsassun hujjoji. Tambayata shi ne, shin Allah, Annabi Muhammad ne ya fara halitta? Shin wai Allah ya ajiye shi ne sai lokacin da ya gadama sannan ya zo duniya?


SHIN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W) NE FARKON HALITTA?
Hoto: SeekPNG

AMSA


Wa'alaikumus salam, Akwai hadisin da ya zo wanda yake nuna cewa Annabi (S.A.W) shi ne farkon wanda aka fara halitta, sai dai hadisin bai inganta ba, wasu malaman hadisin, kamar Ibnu-kathir a tarihinsa da Albani a silsilatussahiha hadisi mai lamba 458, sun ce hadisin ƙarya ne.


Faɗin cewa Annabi (S.A.W) shi ne farkon wanda aka halitta ya saɓa wa Alƙur'ani, ta ɓangarori da dama ga wasu daga ciki:


1. Allah ya tabbatar da cewa Annabi Muhammad mutum ne kamar yadda hakan ya zo a ayoyi daban-daban, sannan kuma Allah ya tabbatar da cewa gaba ɗaya mutane daga Annabi Adam aka same su, kin ga idan ka ce Annabi Muhammad ﷺ shi ne farkon halitta hakan ya saɓa wa ayoyin Alkur'ani.


2. Tarihi ya zo da bayanin nasabar Annabi Muhammad (S.A.W), tun daga mahaifinsa har zuwa Annabi Ibrahim, kin ga wannan yana nuna an halicce shi ne daga maniyyin mahaifinsa, kamar yadda aka halicci ragowar mutane daga hakan.


Zance mafi inganci shi ne: farkon abin da Allah ya fara halitta shi ne Al'arshi, kamar yadda ya zo a cikin Sahihi Muslim a hadisi mai lamba 2653, cewa: "Allah ya ƙaddara abubuwa kafin ya halicci sama da kasa da shekaru dubu hamsin a lokacin Al'arshinsa yana kan ruwa".


Kin ga wannan yana nuna cewa Al'arshi ne farkon abin da aka fara halitta ba Annabi Muhammad (S.A.W).


Allah ne mafi sani.


Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user