Friday 28 October 2022

Kyawawan Gajerun Kalaman Soyayya Masu Ratsa Zuciya

Tura Wannan Zuwa Ga

RAYUWA


Ina son rayuwata ne saboda a cikinta na same ki. Ina son ki, saboda ke ce rayuwata.


Gajerun Kalaman Soyayya
Hoto: Medium


MarubuciAbba Muhammad Dan Hausa


SO


Sun ce sau ɗaya ake kamuwa da so, ni kuwa na ce ba gaskiya ba ne, saboda a duk lokacin da na kalli kyakkyawar fuskarki, sai na ji na ƙara kamuwa da matsanancin sonki, sau lokutan da babu iyaka. Ina son ki sarauniyata.


YANAYI


Ina fatan kin tashi lafiya cikin irin yanayin da zuciya ta fi ƙauna? Na kwana cikin mafarkanki da fatan farkawa domin ci gaba da kasancewa a tare da ke. Na farka cike da tunaninki wanda a nan na gano ke ce farin-cikin da zuciyata ta daɗe tana nema. Barkanki da safiya matata uwar 'yayana farin cikin raina.


KIMA


Kasancewa tare da ke wata martaba ce a rayuwata, kar ki nesanta da ni don Allah, domin ci gaba da kasancewa tare da kimar da duniya ke ba ni ta dalilinki. Na yi kewarki.


AZABA


Suna faɗin soyayya aba ce mai haɗari, wadda take iya azabtar da zuciya, amma ni na ɗauri aniyar kasancewa a cikinta na har abada, matukar kina tare da ni. Ina son ki masoyiyata.


MAYAƘA


A wani lokaci can baya na yi mamaki, kan irin yadda wasu suke yin faɗa akan so, amma a yanzu da na haɗu da ke, a duk lokacin da kika gifta ta cikin tunanina, sai na ji a shirye nake da tunkarar rundunar mayaƙa a kanki. Ke tawa ce, ni naki ne har abada.


Barkanmu da war haka, na san kwana biyu kun ji ni shiru wanda hakan bai yi muku daɗi ba, yanayin aiki ne, amma muna fatan kuna jin daɗin saƙonnin da muke aika muku domin faranta ran masoyanku da su a kodayaushe?


Sadaukarwa ga ɗalibaina. Mun fa dawo aji tsaf! Cikin shirin saita salon tsinkar furannin da ba su da iyakar launi.


SAKO MAI MUHIMMANCI


Kana da damar tura wa abokiyar tsinkar furenka, amma ba a amince wani ya yi amfani da shi da niyyar yaudarar wata ruhi ba. Akwai mai ganin Ka/Ki a ko'ina wato Allah. A kiyaye haƙƙin mallaka, a guje wa satar fasaha.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user