Friday 28 October 2022

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (47) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga

KA SHIRYA ZAMA MAI SUKUNI?


Idan ba ka shirya ba to ka shirya, shi shirin nan ba wai ka faɗi da baki kawai cewa "Na shirya" ba, a'a akwai wasu abubuwa da dole ka kiyaye.


Sukuni A Rayuwa
Hoto: Freepik


MarubuciBaban Manar AlkasimGa su kamar haka: -


1. Ka koyi faɗin a'a: Dole a rayuwa ka iya kore abin da ba zai tafi daidai da buƙatarka ba, zancen "Kar mutane su ga kamar..." Duk bai taso ba, idan lokacin barci ya yi tsayar da komai, lokacin da ba na zaman hira da abokai ba rabu da su, abin da za su yi idan ka ga bai tafi da tsarinka ba watsar kawai, fahimci cewa rayuwar da kake so ka shiga yanzu taka ce, kuɗin da kake so ka tara naka ne, kuma ba dole ba ne a ce suna da buri irin naka, ko karsashin nema, ko damar da ka samu na lokaci ko kuɗi. Don haka sami ƙwarin gwiwar da za ka iya kauce wa duk abin da wani yake so matuƙar bai yi daidai da abin da ka sa a gaba yanzu ba.


2. Janyo hankali: Yanzu dai ba ka da lokacin ɓata lokaci, siyasar farko dai kowa naka ne, wanda yake son tafiya da kai to ga abin da ake buƙata ya yi nan, ba shi damar da zai yi tunani, yi masa bayanin abin da ake so ya yi da irin mutumin da zai iya zama nan gaba, idan ya karɓa ruwansa, idan ya ƙi to ba kai ka kore shi ba, galibin abin da zai yi ta faruwa kenan a nan gaba. Kar ka ce komai sai ka yi magana a kai, ko idan wani ya cuce ka sai ka yi faɗa, a irin wannan matsayin nuna masa ka fahimci abin da ya yi amma za ka ba shi wata damar, idan har za ka iya amfana da shi kenan, idan kuwa ka ga ba alfanun da za ka samu ta wurinsa, kuma ba wata matsalar da zai iya tunkuɗe maka, sai ka sake dubawa shin idan ka rabu da shi zai cutar da kai? 


Idan ka sami cewa zai cutar to ka riƙe shi amma ka rataye shi, idan kuwa ka ga ba abin da zai iya yi maka to rabu da shi kawai ta hanyar kyautata masa yadda zai tafi cikin daɗin rai. Rabuwa da mutum cikin tashin hankali da ɓacin rai ba na me neman cin nasara ba ne, kar ka yarda mutane su riƙa faɗin munanan halinka ko wulaƙanta mutane, yi yadda ko wani ya ɓata ka, wani zai wanke ka saboda kyakkyawar ma'amallarka, sananne ne cewa idan mutum ya yi taushi za a raina shi, amma idan ya yi tsanani da yawa kuma za a guje shi, ko ana tare da shi to a idonsa ne kawai, da zai yi asara kowa Allah-ya-ƙara zai yi masa. Wannan kuwa ba abin so ba ne.


3. Rashin tsoron: - Idan ka ce kana son zama mai sukuni amma kana jin tsoron matsala gaskiya ba ka shirya ba, dole ka zama jajirtacce, kuma tsayayye, maras son kuskure, idan masu aiki da kai suka sami wata matsala kira su ka nemi dalili, sannan ka sa a gyara, komai kasawar kuskuren kuwa, wannan ya fi a ce mutum ya yi ta masifa da zage-zage gami da rashin mutunci ga mutanen dake masa aiki, don idan masifar ta yi yawa mutane za su riƙa yi maka aiki don kuɗin da kake ba su ne ba don son aikin ba, a irin wannan matsayin ci-gabanka ta hanyarsu ba dole ba ne ya yi sauri. Idan dai ka jajirce ko ka sami matsaloli za ka sake dawowa ka tsaya da ƙafafunka ka ci gaba, matsalar baya ta zama darasi kenan.


4. Kama hanya: Kuɗin ne a hannunka za ka juya ko su ɗin ma babu tsabar azabar niyya ce sai ka nemo su sannan ka fara shirye-shiryen zama mai sukunin? Ko kuwa sana'a za ka shiga? Kowanne dai kana buƙatar a ce ka hau hanyar da za ta kai ka inda kake so. Ba yadda za a yi mutumin da yake da miliyan 30 zai juya su a ce ya sayo motocin haya ya zuba a kasuwa ko keke mai ƙafa uku yana sa rai za su tara masa kuɗi barkatai, dole ka koyo sanin makaman sana'ar da farko, shin sana'ar kan tara kuɗi? Menene matsalolinta, za ka iya riƙewa duk da haka ba tare da samun matsala ba? Wasu irin motoci ne za su yi maka abin da kake so? Ya ake samun managartan direbobi? Wani irin tsari za ka yi da su yadda kowa zai sami abin da yake so a sana'ar? Su wa za su riƙa sa ido a harkar? Menene nagartar masu kula da ɓangaren motocin da masu kula da hada-hadar kuɗi tsakanin shiga da fita? Wasu irin sharaɗoɗi aka sa tsakanin jagororin kamfanin da sauran ma'aikatan? Me aka sa na kyautatawa ko ladabtarwa ga ma'aikatan? Da wannan za mu san shirinka.


Idan kuwa tun asali kuɗin ma babu sai an neme su, to lallai ka san sana'ar da za ka yi wace tabbas za ta kawo maka kuɗin. Akwai ƙananan sana'o'i waɗanda ba don samun kuɗi masu yawa ake yin su ba, misali yankar farce, sayar da gauta a bakin hanya, yawo da takalma a hannu da dai sauransu. Na san wani mutum da ya nemi sayar da kaya a wani babban kantin sauƙi ana biyansa, duk idan ya karɓi albashi sai ya rage wani ya tara, har ya sami damar buɗe wani ɗan ƙaramin kanti yana sayar da kaya idan ya dawo aiki, kayan na ƙaruwa saboda ana samun 'yar ƙaramar riba, kuma yana ƙarawa da dan abin da yake samu na albashinsa, a maganar da muke yi ya bar aikin ya dawo ya riƙe nasa, koronar da aka yi ya sami alheri sosai don shi yana buɗe shagonsa da ke jikin gidansa, yanzu dai ya tsaya da ƙafafunsa kuma yana maganar buɗe wani babban shago.


Akwai sana'o'i da ba su da alaƙa da shagunan abinci, kamar sayar da kayan keken ɗunki, kayan wuta ko na gine-gine, kayan mashin da na mota, wayoyin hannu, da sauran sana'o'in hannu kamar fawa, ƙira, kafintanci, gyaran ababan hawa, ɗunki, da wasu sana'o'i na zamani kamar fotokofi, shagon kwamfutoci, musayar kuɗi, sayar da katin waya da sauransu, duk sana'ar da mutum zai shiga ya tabbatar za ta tafi daidai da abin da yake so ya samu, idan ya shiga ido rufe, to ba za a jima ba zai bar ta ya kama wata, sai a daɗe mutum bai tsayar da sana'a guda ba, ga lokaci yana wucewa, kafin ka fara koyon sana'ar lura da inda za ka yi taka idan ka kammala koyon, shin za ka sami mabuƙata? Kuma za ta kai ka inda kake so? Idan har ba za ta yi ba to ba sana'arka ba ce gwara ma ka fita harkarta.


DUBA NA GABAKaranta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (48) Cikin Sauki


Idan kuwa kuɗinka kake so ka zuba ba laifi, amma ka yi mata karatun natsuwa, wace sana'a ce? Za ta kawo abin da ake so? Ina za a gudanar da ita? Kai za ka yi ko yi maka za a yi? Su wa za su yi? Ma'ana gwanancewarsu da amanarsu, wani tsari ka yi wanda zai ba sana'ar da kuɗin da za a samu kariya? Duk waɗannan abin lura ne, babbar matsala ga mutum ita ce ya fara sana'a don sha'awa, ko gasa, ko shawarar wasu ba tare da ya san makamarta ba, duk sana'ar da mutum zai shiga ko ba da hannunsa zai gudanar da ita ba yana da buƙatar ya san ta ciki da bai. Wannan zai taimake shi wurin ba ta kariya, musamman idan ya kasance shi ne mai ba da umurni, sabon mai kama sana'a kar ya yi nesa da ita, dole a yi komai da shi, da haka zai riƙa sa ido a komai.


Za mu ci-gaba Insha Allah.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user