Showing posts with label Falsafa. Show all posts
Showing posts with label Falsafa. Show all posts

Tuesday, 26 August 2025

Hanyoyi 9 Na Rabuwa Da Talauci

Hanyoyi 9 Na Rabuwa Da Talauci

Wato shi fa talauci babban maƙiyi ne, babu wata soyayya tsakaninku. Idan tsautsayi ya sa har yanzu ba ku gama raba hanya da shi ba, ga wasu dabaru da za ka iya amfani da su domin ku yi hannun riga da shi.


Hanyoyi 9 Na Rabuwa Da Talauci
Hoto: Mental health hope

Marubuci:- Abubakar Abba


Allah yake bayar da arziki, amma sai an yi aiki.


1. KAMA SANA’A MAI KAWO ARZIKI


Kowacce sana’a za ta iya bayar da arziki a wani zamanin, kuma ba lallai ba ne ta bayar a wani zamanin daban.


Yana da kyau ka tsaya ka duba wacce ce take bayar da arziki a zamanin da kake, ko kuma yaya za ka ingantata ta kawo arziki.


Arziki yana zuwa ne bayan an neme shi, ba’a yin arziki daga kwance.


2. KAMA ILIMI KAM-KAM


Duk yadda za’a zuga ka, kada ka yarda ka zauna ba ka da ilimin abin da kake yi.


Idan Leburanci kake, ka nemi ilimin inganta ta, idan kasuwanci kake, ka nemi ilimin gudanarwa, da bunƙasawa.


Babu wanda ya yi nasara tabbatacciya da jahilci.


3. KA YI NESA-NESA DA JAHILAI


Ko ka yarda ko kar ka yarda, mutanen da kake mu’amala da su yau da kullum suna da tasiri sosai wajen nasararka a rayuwa.


Jahilai har kullum lissafinsu ba na ci gaba ba ne, don ba su da masaniya akan me rayuwa take tafiya akai ba.


4. IDAN KA SAMU DAMA KA BAR UNGUWAR TALAKAWA


Masana halayyar Ɗan Adam, sun daɗe da fahimtar cewa zama cikin wajen da babu damarmaki yana taimakawa sosai wajen dawwamar da mutum cikin talauci.


Sauya muhalli yana tasiri sosai wajen sauya tunani, sannan yana taimakawa wajen samun damammaki, wanda idan aka yi amfani da su sai a samu dacewa.


A cikin littafin rayuwarsa, hamshaƙin mai kuɗi Femi Otedola, ya yi ƙarin haske akan wannan, a je a karanta za’a sha labari.


5. KA NEMI ILIMI AKAN KUƊI


Akwai wani babban ganganci da mutane da yawa suke yi shi ne, suna zama ba tare da sun nemi ilimin yaya ake tara dukiya, yaya ake alkintata, yaya ake bunƙasa ta ba.


A tunanin mafi yawan mutane, arziki zuwa kawai yake yi, ba tare da mutum ya yi wani hobɓasa daga ɓangarensa ba.


A tunanin mutane masu rauni, laifi ne ka nemi ilimin yadda za ka samu kuɗi ko yadda za ka yi arziki.


Don haka da yawansu suke fama da baƙin talauci.


Bayan ka nemi ilimin karatu da rubutu, to lallai ka nemi ilimin yadda harkokin kuɗi suke, zai taimaka sosai.


6. KA YI ƘOƘARI MASU ARZIKI SU SAN DARAJARKA


Kar ka yarda ka kulle kanka a waje ɗaya, idan Allah ya ba ka ilimi, ka yi ƙoƙari ka fito da shi duniya ta sani.


Ka yi ƙoƙari duk inda ake harkar arziki kai ma a gan ka a wajen, bayan ka je wajen, ka tabbatar ka nuna baiwar da Allah ya yi maka.


Daga haka ake samu silar arziki.


Kar ka yarda da shirmen jiran 'yan siyasa, ko Auren Hajiya, ko 'yar masu kuɗi, wannan duk baragada ce.


Ka gina daraja, ka yi tsari mai kyau, ka yi addu’ar dacewa.


7. KA TABBATA KA KOYI HALAYE MASU KYAU


Kyawun hali da mu’amala mai kyau tana ba wa mutum arzikin da bai taɓa zato ba.


Kar ka zama mai kaushin hali, ko mai wahalar mu’amala da mutane, ko mara haƙuri da juriya, ko mai yawan aibanta mutane, ko mai yawan gulma da neman laifin mutane, duk wanda ka ga yana wannan munanan ɗabi’un, to ka tabbata ba inda zai je a rayuwa.


8. KA CIRE TSORO DA SON JIKI


Ka daina tsoron shiga harkar da za ta ba ka alheri in dai halal ce.


Ka daina tsoron abin da mutane za su ce, ko abin da 'yan uwanka za su ce, ko abin da matarka, budurwarka ko abokanka za su ce.


Wannan shi ne abu na farko da zai ba ka damar shiga rayuwa mai cikakken 'yanci.


Arziki ba ya zuwa da tunani ƙarami ko lissafin mai tsoro.


9. KA KULA DA LAFIYARKA


Lafiyarka ita ce babban jarinka, babu wani abu da zai tafi daidai idan lafiyarka ba ta kan saiti.


Lafiyarka tana da tsada, don haka kada ka yi wasa da abincinka, hutunka, baccinka da motsa jiki.


Kada ka yarda wani aiki, ko wani mutum ya hana ka samun waɗannan ababen.


Ni ne jagoran masu yaƙi da talauci da tunani irin na talauci.


Idan kana son samun haske da samun dabaru masu inganci  akan yadda za’a samu hanyar da za ta ɓulle, to nan ce babbar tasha.


Ka ci-gaba da bi na, tare da yaɗa wannan saboda wasu ma su amfana, da haka ne za mu fatattaki talauci da 'yan koren sa.

Saturday, 10 May 2025

Yadda Mata Suke Rusa Arzikin Mazajen Su

Yadda Mata Suke Rusa Arzikin Mazajen Su

Da yawa daga cikin matasa masu aure, matansu ne silar lalacewar tattalin arzikinsu, kuma su ne ummul-aba’isin daƙile ci gaban mazansu a rayuwa.


Yadda Mata Duke Rusa Arzikin Mazajen Su
Hoto: LinkedIn

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Ba na cewa duka ba, amma kusan kaso casa’in cikin ɗari (90%) na mata su ne ke jawowa mazansu jarrabawa da karya musu tattalin arziki a aikace, da kuma karya musu gwiwa wajen jajircewa akan neman halal a kowanne aiki.


Na san za ka yarda da ni idan ka duba a unguwarku, ka ga yadda wasu matasa suka taso da ƙwazon nema da tattali da iya sarrafa kuɗi don rufin asiri. Amma da zarar sun yi aure, komai sai ya lalace.


Hatta ɗan gidansa wani sai ya siyar, balle kuma ɗan lifan da ya tara da wahala.


Ana ɗaura aure, sai ka ga wata tana fara fitowa da hanyoyi masu kai namiji ga lalacewa.


Wata tun daga suturarsa take fara ingizawa, tana cewa:


 "Gaskiya kamata ya yi yanzu ka dinga ɗinka shadda. Haka za mu shiga dangina ana nuna mijina, ana cewa kamar ɗan dako ba shi da suturar arziki."


Musamman idan ta ga yana ɗan sarrafa kuɗi, sai ka ji tana cewa:


 "Gaskiya ya kamata mu dinga cin miya da kaji kullum. 'Yan uwana za su tarar da ni kullum ina fama da shinkafa fara da miyar jajjage da ɗan kifi."


Haka za ta ci gaba da ingiza shi. Shi kuma yana cikin jin daɗin amarci, har ta rinka raɗa masa a kunne:


 "Wallahi, mijin maƙwabciyarmu bai kai ka samun kuɗi ba, amma har solar ya haɗa a gidansa. Dan Allah ni ma a saka min, na daina sintirin kai caji maƙwabta."


Shi kuma namiji, saboda ƙarfin hali da rashin son a ce ya gaza, sai ya ci gaba da yi wa jarinsa rubdugu, kamar wanda ya samu kuɗin gado.


Kafin ya farga, sai ka ga shagon nasa yana ramewa kamar wanda cutar ƙanjamau ta kama. A hankali, sai a cinye komai.


Daga nan kuma ta fara zuga shi da cewa:


 "Tun da babu jari, sai ka siyar da gidan, ka sayi ƙaramin gida, ragowar kuɗin ka ja jari. Tun da jama'a sun gano komai ya ƙare, kada abinci ya fara gagarar mu a ji kunya."


Ƙarshe idan bai yi hankali ba, har ƙaramin gidan zai siyar, ya koma haya. Ita kuma sai ta kai shi kotun ƴan alluna ta ƙofar Wambai, ta ce ya kasa ciyar da ita, dole a raba auren.


Ƙarshe ya shiga uku, babu:


Babu gida,


Babu jari,


Babu aure.


Ita kuwa ba ta yi asara ba. Tana fitowa, wani ya aure ta, musamman idan tana da haske.


Don haka, idan amaryarka ta fara kawo maka waɗannan jahilan shawarwarin, kai shiru ka ce:


 "Ba zan iya ba."


Idan ta matsa, ka ce:


 "A aika a kawo daga gidanku.".


Ya kai ango!! Dole ka lura kada santin amarci ya sa ka bindige jarinka kamar yadda sojojin Najeriya ke bindige ɗan ta'adda har lahira a daji.

Friday, 9 May 2025

Zabar Abokai A Tsakanin Maza Da Mata

Zabar Abokai A Tsakanin Maza Da Mata

A yau kowa kana haɗuwa da shi sai ka ce abokinka ne. Kowa yana dariya da kai sai ka ce kun yi shekara goma da sanayya. Wasu ma idan sun haɗu da mace, ba su fi sau biyu ba sai ka ji yana cewa "ai wannan matata ce nan gaba." Ashe rayuwa haka take da sauƙi kenan?


Zaɓar Abokai A Tsakanin Maza Da Mata
Hoto: Photosvit/Dreams time


Bari na faɗa maka gaskiya, domin ko ka ji daɗi ko ka ɓata rai: ba kowa ba ne abokinka, kuma ba kowacce mace ba ce ta zama taka. Kaso casa'in cikin ɗari (90%) na nasarar rayuwarka ya dogara ne da irin mutanen da ka zauna da su, wato abokai da matar aure. Sauran goma cikin ɗari kuwa addu'ar iyaye da ƙoƙarin kanka ne ke ɗauke da su.


Iyaye fa Allah ne ya zaɓa mana su. Ba mu da zabin su. Idan sun ba da shawara, to da soyayya suke, amma ba duka shawarar tasu ce ta dace da zamani ba. To amma abokai da mace kuwa, kai kanka za ka zaɓa. Kuma idan ka yi zaɓi da hangen ido kawai, ba da hangen zuciya ba, to ka shirya zaman nadama.


Mutane da yawa suna ɗaukar abokai kamar ana tara busasshen totuwar rake da daddare bayan an tashi daga dandalin wasa. Kowanne ya zo, a jefa a ɗaki. Ba duba hali, ba duba buri, ba duba irin gudunmawar da zai bayar. Idan ka tambayi wasu, me yasa suke tare da abokansu, sai su ce "ai mun saba," kalmar sabo ba za ta amfanar da kai komai ba cikin alaƙar da ke jawo ka baya kamar mai haƙan rijiya.


Aboki ya zama abokinka idan kuna ƙarfafa juna, ba idan kuna janyo juna ƙasa ba. Misali, kana da buri na kafa kamfani ko kasuwanci, abokinka kuma kullum yana zaune yana sharhi kan fim da wasan kwallon ƙafa. Kana tsammani irin wannan aboki zai taimaka maka ka cimma burinka? Sam sai dai ƙarshe ku ƙare da siyan ƙatuwar "Plasma" Ku yi ta kallon tashoshin Arewa24 kuna sharhin fina-finai.


Idan abokinka ba ya faɗa maka gaskiya, ba ya ƙarfafa ka ka fita neman ilimi ko aiki, sai fa ya zama kamar dutse ne a wuyan riga, yana hana ka motsi, amma ba ka gane ba. Aboki nagari yana tura ka gaba kamar iska ke tura kwale-kwale a cikin ruwa.


Amma ba abokai kaɗai ba, mace ma tana da rawar takawa a ginin rayuwa. Duk da cewa ana cewa kyau na da daɗi, amma ba kyau ka aura kyau kawai ba tare da hankali ba. Kallon mace kawai da kyau, ka mata tambayar: "Ta na da buri kuwa? Ta na da hangen nesa kuwa? Ta san me ake nufi da gida kuwa?" ai kai da kanka ka ɗaura kanka igiya a wuya kana ƙoƙarin rataye kanka.


Misali, ka haɗu da mace kyakkyawa tamkar hasken wata, amma kullum ba ta da wani buri sai selfie da TikTok.


Ba ta da buri sai kwaikwayon matan film da kwatanta irin rayuwarsu, burinta ta yi kwalliya kawai kowa ya dinga yaba mata.


Kana burin ya za ka gina gida ? Tana kawo maka labarin abaya 'yar 400k ta shigo kasuwa.


Kana gaya mata kana son sake buɗe shago tana sa ka rigima akan dole sai ka siya mata iPhone. Lallai kuwa a matsayinka na matashi kuma mai ƙoƙarin gina kasuwanci za ta daɗe tana jawo ka baya da wannan baƙar al'ada.


Zaman aure fa kamar haɗa tawagar ƙwallon ƙafa ne, sai kowacce lamba da kusurwa ta yi motsi kuma ta yi aikinta sosai sannan za'a yi nasara.


Rayuwa dai kamar jirgin ruwa ce, kuma abokanka da matarka su ne fasinjojin ka. Idan fasinjoji marasa amfani suka cika jirgin, jirgin zai nutse kafin ya kai bakin gaɓa. Amma idan ka tara masu ƙwazo, masu buri, masu kyau da hankali, kai tsaye za ka ratsa gaɓar arziki lafiya.


A duniyar nan, wanda bai iya zaɓar abokansa da matarsa ba, to kamar mai shuka rogo a sahara ne, ruwa babu, ƙasa busasshiya. Shuka sai a banza.


Ka buɗe idanu ka zaɓi abokai da mata masu hankali da buri. Kada ka karɓi kowa kamar ana raba ruwan sanyi a rana. Ka ɗora su a sikeli: me za su kawo maka, me za ka koya daga gare su?


Ka tuna, aboki mara amfani kamar mugun tunani yake, da ƙyar ake  iya nasarar kuɓucewa daga gare shi. Mace marar hangen nesa kuma kamar bokiti marar tsafta take, duk ruwan da ka zuba, haka zai ɓaci.


Don haka, ka yi amfani da hankalinka kafin zuciyarka ta ɓatar da kai. Rayuwa ba ta ƙyale masu saurin yarda, su ne suka fi saurin nadama.

Thursday, 8 May 2025

Shawarwari 20 Da Za Ku So Sanin Su

Shawarwari 20 Da Za Ku So Sanin Su

Da zan iya komawa shekaru 20, da na bai wa kaina waɗannan shawarwari guda 20.


Ga su kamar haka:


1. Lokaci bayan lokaci ka riƙa gwada sabbin al'amurra. Ka koyi wata sabuwar ƙwarewa, ka karanta wani littafi, ko ka yi tattaunawa mai ma'ana da wani masani, da sauran su. Manufar ita ce ka ci karo da sabbin ra'ayoyi tare da faɗaɗa tunaninka wanda hakan zai ƙara maka ƙarfin gwiwa ya zaburar da kai domin cimma burinka a rayuwa.


Shawarwari 20 Da Za Ku So Sanin Su
Hoto: Wallpaper

2. Duk wani abu da kake sha'awar yi, kada ka ji tsoron ɗaukar taku na farko. Domin taku na farko shi ne mafi muhimmanci, kuma da zaran ka ɗauke shi sauran abubuwan da kake son fahimta za su fara bayyana gare ka.


3. Ka ɗauki darasi daga nasarorin wasu mutane, wannan yana daga cikin hanyoyi mafi sauƙi domin isa ga taka nasarar. Kada ka tsaya ƙirƙirar sabuwar hanya, kawai ka bi hanyar da wasu suka bi suka kai ga abin da kake nema.


4. Abin da kake faɗa wa duniya game da kanka shi za ta gaskata. Kada ka ji tsoron bayyanar da kanka ko aikin da kake yi a duk inda ka shiga. Ka tallata kanka da kyau kuma ka ƙawata aikin da kake yi har duniya ta san ka kuma ta san sana'arka.


5. Nasara sakamako ne na aiki tuƙuru tare da jajircewa da kuma dogon yunƙuri na tsawon lokaci. Ka fara daga inda kake da kaɗan da kaɗan har ka gina gobenka domin nasara ba ta samuwa ga mutum a yini guda.


6. Ƙalubale na farko da za ka fuskanta a tafiyarka shi ne kanka. Ranar da ka iya kawar da shakku, tsoro, da munanan tunani daga zuciyarka to a ranar ka zama mutum mai 'yanci.


7. Da sannu za ka rasa wani sashi na abokai da makusanta a lokacin da ka fara aiki tuƙuru don canza rayuwar ka. Ba kowa ne zai ba ka gudunmawa ba ko ya taimake ka, amma kada ka damu domin ita rayuwa ta gaji haka.


8. Za ka yi kurakurai masu yawa a farkon tafiya, amma hakan ba laifi ba ne. Babban shaida ne akan cewa kana koyo da kana samun cigaba a cikin tafiyarka.


9. Ka girmama abokanka, da tsararrakinka, da dukkan mutanen da kake haɗuwa da su akan hanyarka domin kowane mutum da ka haɗu da shi yana da rawar da zai taka a cikin rayuwar ka.


10. Yawancin mutane sun yi nisa wurin shagaltuwa da al'amurran gabansu da ba sa iya lura da kai. Ka sani cewa babu wanda ya ke lura da kai balle ya damu da abin da kake yi don haka ka cire wannan tunanin a ranka ka aikata abin da ya dace.


11. Yi ƙoƙarin zama mai cikakken ƙwarewa a cikin sana'arka ko aikinka ko fasaharka. Koda ba ka iya kai wa ga wannan ƙwarewar ba, za ka kasance cikin waɗanda ake buga misali da su a cikin duk abin da ka sa a gaba.


12. Saɓanin yadda da yawa daga cikin mutane suke tunani, babu wata illa a ƙoƙarin karkato da hankulan mutane zuwa gare ka. Amma kuma ya danganta da burinka da manufofinka na yin hakan.


13. A gaskiyar lamari sai ka iya janyo hankulan mutane kafin su san da kasuwancin ka, da ra'ayoyinka, da kuma baiwar da kake da ita. Don haka, ka nemi hankulan mutanen da suka dace, kuma ta hanyar da ta dace.


14. Daga cikin halaye mafi muni da za su dakatar da kai daga cimma burinka shi ne jinkiri. Kada ka tsaya jiran gobe ko an jima, ka aikata duk abin da ya kamata a lokacin da ya dace.


15. Za ka samu duk irin goyon bayan da kake buƙata daga duniya idan ka kasance mai taimaka wa wasu. Ka yi farin ciki da nasarar waninka kamar yadda kake farin ciki da nasararka.


16. Babu makawa za ka fuskanci ƙalubale a rayuwarka a kowane lokaci, duk abin da ka yi kuma duk inda ka je. Babban abin da ke ƙara wa rayuwa armashi shi ne ƙoƙarin mu wajen bibiyar mafarkanmu duk da ƙalubalan da muke fuskanta.


17. Mutane halittu ne na ɗabi'a. Idan ka sare a lokacin da abubuwa suka yi wuya, zai zame maka ɗabi'a mai sauƙi ka ƙara sarewa a gaba. A gefe guda, idan ka tilasta wa kanka ka ci gaba, wannan zai taimaka maka ka gina ɗabi'a ta juriya da ƙarfin hali.


18. Abin ban sha'awa game da ƙalubale shi ne cewa a kullum akwai wani abu na darasi abin koyo a cikinsa. Amma fa sai ga masu ƙarfin gwiwar ganin hakan.


19. Rayuwa ba ta da sauƙi domin cike ta ke da gwagwarmaya da faɗi-tashi. Amma ga mutumin da yake da manufa, kowace wahala tana ƙara masa basira ne da ƙarfin hali, gogewa tare da ƙaimi wurin cimma burinsa.


20. Dukkan shafukan da kake bibiya a kafofin sada zumunta suna da babban tasiri akan tunaninka da rayuwarka. Shi ya sa wannan shafin ya maida hankali akan ilimantarwa da faɗakarwa da zaburar da ku ga manya-manyan al'amurra a rayuwa.


Ku cigaba da kasancewa tare da wannan shafin domin samun rayuwa mai inganci!


Tushe/Asali: Hausa Motivation

Monday, 5 May 2025

Darasin Da Ake So Ka Koya A Rayuwar Ka

Darasin Da Ake So Ka Koya A Rayuwar Ka

Idan wata matsala tana yawan faruwa da kai, akwai wani darasi da ka kasa koyo a cikin ta. Misali idan ana yawan cutarka a kasuwanci da ciniki, hakan yana nuna ba ka tantance abokan hulɗar ka, kuma ba ka nazari da bincike kafin ka ƙulla ciniki.


Darasin Da Ake So Ka Koya A Rayuwar Ka
Hoto: Cross walk

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


Idan kana yawan samun saɓani da iyalinka ko abokin ka, hakan yana nuna abubuwa guda biyu musamman;


Kodai akwai wata daɓi'a da kake musu cikin mu'amala kuma ba sa jin daɗin ta, kai kuma ka kasa ganewa ka daina.


Ko kuma su suna da wani hali da ka kasa fahimtar yadda za ka mu'amalance su, ko kuma ka yi haƙuri da shi.


Idan kana yawan shiga matsala da jami'an tsaro, hakan na nufin ba ka tantancewa da doka, ko kuma gane iyakokin ta.


Idan kana yawan shiga matsalar kuɗi ko bashi, hakan na nufin ka kasa tsayawa ka tantance samun ka, da kuma irin buƙatun da ya kamata ka yi, da wanda za ka haƙura har matsayin ka ya sauya, samun ka ya ƙaru.


DARASI


Da yawan lokaci mutane kan ɗauka al'amura suna faruwa ne haka kawai, ko kuma rashin sa'a ne ko ƙaddara. Amma fa da yawa akwai abubuwan da muke yi, ko muke barin su, waɗanda ke ba mu irin sakamakon da muke samu.


Don haka idan abubuwan ka suna tafiya daidai, sai ka zage damtse, ka ci-gaba da addu'a.


Idan kuma akasin haka ne, sai ka yi nazarin abubuwan da suke buƙatar sauyi, domin samun sauyin sakamako.


Allah ya sa mu dace Amin.