Da zan iya komawa shekaru 20, da na bai wa kaina waɗannan shawarwari guda 20.
Ga su kamar haka:
1. Lokaci bayan lokaci ka riƙa gwada sabbin al'amurra. Ka koyi wata sabuwar ƙwarewa, ka karanta wani littafi, ko ka yi tattaunawa mai ma'ana da wani masani, da sauran su. Manufar ita ce ka ci karo da sabbin ra'ayoyi tare da faɗaɗa tunaninka wanda hakan zai ƙara maka ƙarfin gwiwa ya zaburar da kai domin cimma burinka a rayuwa.
2. Duk wani abu da kake sha'awar yi, kada ka ji tsoron ɗaukar taku na farko. Domin taku na farko shi ne mafi muhimmanci, kuma da zaran ka ɗauke shi sauran abubuwan da kake son fahimta za su fara bayyana gare ka.
3. Ka ɗauki darasi daga nasarorin wasu mutane, wannan yana daga cikin hanyoyi mafi sauƙi domin isa ga taka nasarar. Kada ka tsaya ƙirƙirar sabuwar hanya, kawai ka bi hanyar da wasu suka bi suka kai ga abin da kake nema.
4. Abin da kake faɗa wa duniya game da kanka shi za ta gaskata. Kada ka ji tsoron bayyanar da kanka ko aikin da kake yi a duk inda ka shiga. Ka tallata kanka da kyau kuma ka ƙawata aikin da kake yi har duniya ta san ka kuma ta san sana'arka.
5. Nasara sakamako ne na aiki tuƙuru tare da jajircewa da kuma dogon yunƙuri na tsawon lokaci. Ka fara daga inda kake da kaɗan da kaɗan har ka gina gobenka domin nasara ba ta samuwa ga mutum a yini guda.
6. Ƙalubale na farko da za ka fuskanta a tafiyarka shi ne kanka. Ranar da ka iya kawar da shakku, tsoro, da munanan tunani daga zuciyarka to a ranar ka zama mutum mai 'yanci.
7. Da sannu za ka rasa wani sashi na abokai da makusanta a lokacin da ka fara aiki tuƙuru don canza rayuwar ka. Ba kowa ne zai ba ka gudunmawa ba ko ya taimake ka, amma kada ka damu domin ita rayuwa ta gaji haka.
8. Za ka yi kurakurai masu yawa a farkon tafiya, amma hakan ba laifi ba ne. Babban shaida ne akan cewa kana koyo da kana samun cigaba a cikin tafiyarka.
9. Ka girmama abokanka, da tsararrakinka, da dukkan mutanen da kake haɗuwa da su akan hanyarka domin kowane mutum da ka haɗu da shi yana da rawar da zai taka a cikin rayuwar ka.
10. Yawancin mutane sun yi nisa wurin shagaltuwa da al'amurran gabansu da ba sa iya lura da kai. Ka sani cewa babu wanda ya ke lura da kai balle ya damu da abin da kake yi don haka ka cire wannan tunanin a ranka ka aikata abin da ya dace.
11. Yi ƙoƙarin zama mai cikakken ƙwarewa a cikin sana'arka ko aikinka ko fasaharka. Koda ba ka iya kai wa ga wannan ƙwarewar ba, za ka kasance cikin waɗanda ake buga misali da su a cikin duk abin da ka sa a gaba.
12. Saɓanin yadda da yawa daga cikin mutane suke tunani, babu wata illa a ƙoƙarin karkato da hankulan mutane zuwa gare ka. Amma kuma ya danganta da burinka da manufofinka na yin hakan.
13. A gaskiyar lamari sai ka iya janyo hankulan mutane kafin su san da kasuwancin ka, da ra'ayoyinka, da kuma baiwar da kake da ita. Don haka, ka nemi hankulan mutanen da suka dace, kuma ta hanyar da ta dace.
14. Daga cikin halaye mafi muni da za su dakatar da kai daga cimma burinka shi ne jinkiri. Kada ka tsaya jiran gobe ko an jima, ka aikata duk abin da ya kamata a lokacin da ya dace.
15. Za ka samu duk irin goyon bayan da kake buƙata daga duniya idan ka kasance mai taimaka wa wasu. Ka yi farin ciki da nasarar waninka kamar yadda kake farin ciki da nasararka.
16. Babu makawa za ka fuskanci ƙalubale a rayuwarka a kowane lokaci, duk abin da ka yi kuma duk inda ka je. Babban abin da ke ƙara wa rayuwa armashi shi ne ƙoƙarin mu wajen bibiyar mafarkanmu duk da ƙalubalan da muke fuskanta.
17. Mutane halittu ne na ɗabi'a. Idan ka sare a lokacin da abubuwa suka yi wuya, zai zame maka ɗabi'a mai sauƙi ka ƙara sarewa a gaba. A gefe guda, idan ka tilasta wa kanka ka ci gaba, wannan zai taimaka maka ka gina ɗabi'a ta juriya da ƙarfin hali.
18. Abin ban sha'awa game da ƙalubale shi ne cewa a kullum akwai wani abu na darasi abin koyo a cikinsa. Amma fa sai ga masu ƙarfin gwiwar ganin hakan.
19. Rayuwa ba ta da sauƙi domin cike ta ke da gwagwarmaya da faɗi-tashi. Amma ga mutumin da yake da manufa, kowace wahala tana ƙara masa basira ne da ƙarfin hali, gogewa tare da ƙaimi wurin cimma burinsa.
20. Dukkan shafukan da kake bibiya a kafofin sada zumunta suna da babban tasiri akan tunaninka da rayuwarka. Shi ya sa wannan shafin ya maida hankali akan ilimantarwa da faɗakarwa da zaburar da ku ga manya-manyan al'amurra a rayuwa.
Ku cigaba da kasancewa tare da wannan shafin domin samun rayuwa mai inganci!
Tushe/Asali: Hausa Motivation