Friday, 9 May 2025

Zabar Abokai A Tsakanin Maza Da Mata

Tura Wannan Zuwa Ga

A yau kowa kana haɗuwa da shi sai ka ce abokinka ne. Kowa yana dariya da kai sai ka ce kun yi shekara goma da sanayya. Wasu ma idan sun haɗu da mace, ba su fi sau biyu ba sai ka ji yana cewa "ai wannan matata ce nan gaba." Ashe rayuwa haka take da sauƙi kenan?


Zaɓar Abokai A Tsakanin Maza Da Mata
Hoto: Photosvit/Dreams time


Bari na faɗa maka gaskiya, domin ko ka ji daɗi ko ka ɓata rai: ba kowa ba ne abokinka, kuma ba kowacce mace ba ce ta zama taka. Kaso casa'in cikin ɗari (90%) na nasarar rayuwarka ya dogara ne da irin mutanen da ka zauna da su, wato abokai da matar aure. Sauran goma cikin ɗari kuwa addu'ar iyaye da ƙoƙarin kanka ne ke ɗauke da su.


Iyaye fa Allah ne ya zaɓa mana su. Ba mu da zabin su. Idan sun ba da shawara, to da soyayya suke, amma ba duka shawarar tasu ce ta dace da zamani ba. To amma abokai da mace kuwa, kai kanka za ka zaɓa. Kuma idan ka yi zaɓi da hangen ido kawai, ba da hangen zuciya ba, to ka shirya zaman nadama.


Mutane da yawa suna ɗaukar abokai kamar ana tara busasshen totuwar rake da daddare bayan an tashi daga dandalin wasa. Kowanne ya zo, a jefa a ɗaki. Ba duba hali, ba duba buri, ba duba irin gudunmawar da zai bayar. Idan ka tambayi wasu, me yasa suke tare da abokansu, sai su ce "ai mun saba," kalmar sabo ba za ta amfanar da kai komai ba cikin alaƙar da ke jawo ka baya kamar mai haƙan rijiya.


Aboki ya zama abokinka idan kuna ƙarfafa juna, ba idan kuna janyo juna ƙasa ba. Misali, kana da buri na kafa kamfani ko kasuwanci, abokinka kuma kullum yana zaune yana sharhi kan fim da wasan kwallon ƙafa. Kana tsammani irin wannan aboki zai taimaka maka ka cimma burinka? Sam sai dai ƙarshe ku ƙare da siyan ƙatuwar "Plasma" Ku yi ta kallon tashoshin Arewa24 kuna sharhin fina-finai.


Idan abokinka ba ya faɗa maka gaskiya, ba ya ƙarfafa ka ka fita neman ilimi ko aiki, sai fa ya zama kamar dutse ne a wuyan riga, yana hana ka motsi, amma ba ka gane ba. Aboki nagari yana tura ka gaba kamar iska ke tura kwale-kwale a cikin ruwa.


Amma ba abokai kaɗai ba, mace ma tana da rawar takawa a ginin rayuwa. Duk da cewa ana cewa kyau na da daɗi, amma ba kyau ka aura kyau kawai ba tare da hankali ba. Kallon mace kawai da kyau, ka mata tambayar: "Ta na da buri kuwa? Ta na da hangen nesa kuwa? Ta san me ake nufi da gida kuwa?" ai kai da kanka ka ɗaura kanka igiya a wuya kana ƙoƙarin rataye kanka.


Misali, ka haɗu da mace kyakkyawa tamkar hasken wata, amma kullum ba ta da wani buri sai selfie da TikTok.


Ba ta da buri sai kwaikwayon matan film da kwatanta irin rayuwarsu, burinta ta yi kwalliya kawai kowa ya dinga yaba mata.


Kana burin ya za ka gina gida ? Tana kawo maka labarin abaya 'yar 400k ta shigo kasuwa.


Kana gaya mata kana son sake buɗe shago tana sa ka rigima akan dole sai ka siya mata iPhone. Lallai kuwa a matsayinka na matashi kuma mai ƙoƙarin gina kasuwanci za ta daɗe tana jawo ka baya da wannan baƙar al'ada.


Zaman aure fa kamar haɗa tawagar ƙwallon ƙafa ne, sai kowacce lamba da kusurwa ta yi motsi kuma ta yi aikinta sosai sannan za'a yi nasara.


Rayuwa dai kamar jirgin ruwa ce, kuma abokanka da matarka su ne fasinjojin ka. Idan fasinjoji marasa amfani suka cika jirgin, jirgin zai nutse kafin ya kai bakin gaɓa. Amma idan ka tara masu ƙwazo, masu buri, masu kyau da hankali, kai tsaye za ka ratsa gaɓar arziki lafiya.


A duniyar nan, wanda bai iya zaɓar abokansa da matarsa ba, to kamar mai shuka rogo a sahara ne, ruwa babu, ƙasa busasshiya. Shuka sai a banza.


Ka buɗe idanu ka zaɓi abokai da mata masu hankali da buri. Kada ka karɓi kowa kamar ana raba ruwan sanyi a rana. Ka ɗora su a sikeli: me za su kawo maka, me za ka koya daga gare su?


Ka tuna, aboki mara amfani kamar mugun tunani yake, da ƙyar ake  iya nasarar kuɓucewa daga gare shi. Mace marar hangen nesa kuma kamar bokiti marar tsafta take, duk ruwan da ka zuba, haka zai ɓaci.


Don haka, ka yi amfani da hankalinka kafin zuciyarka ta ɓatar da kai. Rayuwa ba ta ƙyale masu saurin yarda, su ne suka fi saurin nadama.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user