Showing posts with label Lafiya Uwar Jiki. Show all posts
Showing posts with label Lafiya Uwar Jiki. Show all posts

Saturday, 7 December 2024

Ire-iren Cututtukan Da Suke Kama Farjin Mace Da Hanyoyin Samuwar Su

Ire-iren Cututtukan Da Suke Kama Farjin Mace Da Hanyoyin Samuwar Su

1. Farjin mace (vagina) yana cikin ɓagarori na jiki da yake da matuƙar saurin kamuwa da cututtuka, kama daga bacteria, virus zuwa fungi, hakan kuwa ya samu asali ne daga yanayin halittar wannan gaɓa.


Kasancewarsa a buɗe da kuma kasancewar akwai wasu halittu waɗanda ba sa cutar da mace, amma da zarar sun haɗu da wasu ƙwayoyin cuta a waje komai kashinsu sai duk su rikiɗe su dawo ƙwayoyin cuta su fara cutar da ita.


Ire-iren Cututtukan Da Suke Kama Farjin Mace Da Hanyoyin Samuwar Su
Hoto: Be body wise

2. Akwai ruwa da mace take fitarwa daga farjinta wanda ba shi da kauri kuma launinsa mai haske ne sannan ba shi da wari kuma babu zafi ko ƙaiƙayi a farjin. 


Fitar irin wannan ruwa ba shi da matsala hasali ma hanya ce da jiki yake wanke farjin daga dukkan datti, sai dai daga lokacin da wannan ruwa ya zama yana wari ko ya canza kala zuwa mai duhu ko kuma mace ta lura da akwai ƙaiƙayi ko tana jin zafi musamman ga masu aure lokacin saduwa da mazajensu, to ta garzaya zuwa asibiti ba tare da ɓata lokaci ba. 


3. Namiji yana iya sanya wa mace infection ta hanyar saduwa. Wani abun lura kuma shi ne yanayin azzakarin namiji ya sanya shi infection ɗin ba zai nuna da wuri a jikansa ba, haka kuma ba zai fara cutar da shi da wuri ba kamar yadda zai yi wa mace, shiyasa sai ka ga namiji ya sanya wa matarsa infection, shi kuma lafiyarsa ƙalau. 


Hakan ba yana nufin namiji ba ya samun infection ba. Shi ma yana samun irin nasa, sai dai ba sosai yake kai na mace tsanani ba.


Za mu tattauna akan infection ɗin namiji nan gaba kaɗan in sha Allah. 


4. Abu ne mai tsananin hatsari mace ta ga alamomin infections ba tare da ta yi hanzarin zuwa ganin likita ba. Yana farawa ne daga yanayin rashin hatsari har zuwa lokacin da magance shi yake ƙara wahala.

 

Shi ya sa ya zama dole mace ta kula da lafiyar farjinta. A shawarce ana so mace ta riƙa zuwa asibitin mata (gynae clinic) aƙalla sau ɗaya a shekara don duba lafiyar farjinta. 


5. Tsafta yana da matuƙar muhimmanci wajen lafiyar farjin mace. Ita mace tana iya kamuwa da infection ta hanyar fitsari a waje marasa tsafta. Shi ya sa ake so mata su riƙa kiyayewa daga fitsari a bayan gida da mutane da yawa suke amfani da shi. Idan kuma ya zama dole to ta tabbatar ta samu ruwa ta zuba ko kuma ta yi flushing kafin ta yi fitsarin. 


6. A wajen wanka, yana da kyau mace ta riƙa maida hankali wajen ganin cewa ba ta bar sabulu ko kumfa ko wani datti a jikin farjinta ba komai kashinsa, saboda ya kan maƙale sai ƙwayoyin cuta su samu mafaka. 


Hakazalika sabulu mai ƙamshi da ke ɗauke da sinadarai daban-daban, amfani da shi wajen wanke farji yana kawo ƙaiƙayi da sauran matsaloli. Sai a kiyaye. 


7. Ya zama dole a riƙa kiyayewa wajen yin tsarki. Idan mace ta yi bahaya, ta  wanke hannunta tas ba tare da barin sabulu ko kumfa a hannun ba sannan ta fara da wanke farjinta ta kammala shi tas kafin ta wanke bahayan, kar ta kuskura ta taɓa farjinta da hannu bayan ya wanke bahayan saboda akwai ƙwayoyin cuta da za su iya maƙalewa a jikin hannunta, ita kuma mafitsara kamar yadda muka faɗa tana da saurin kamuwa da cuta.


Hakazalika abu ne mai matuƙar hatsari ga mace idan za ta yi tsarkin bahaya ta yi goho ta yadda ruwan wanke bahayan zai iya zuwa ya taɓa mafitsararta. Abin da ya fi dacewa shi ne a nemo toilet paper a fara gogeshi tas, sai a wankeshi ba tare da ruwa ya dawo ya taɓa mafitsara ba.


Iyaye masu 'ya'ya mata, yana da matuƙar muhimmanci ku kiyaye wannan wajen tsaftace 'ya'yanku mata bayan sun yi bahaya. 


8. Akwai mata da suke wasa da gabansu ta hanyar sanya yatsa a ciki (fingering da masturbation) wannan ma yana jawo infection ta hanyar ƙwayoyin cuta da suke yatsan mai yin wannan abu. Don haka yana da matuƙar muhimmanci a kiyaye. 


9. Ya zama dole a maida hankali wajen kiyaye saka underwear masu riƙe zafi ko kuma masu riƙe zufa da jiƙa ko ruwa, shi ma hakan yana taimaka wa ƙwayoyin cuta su rayu har da hayayyafa a farjin mace.


Tsaftar underwears da kuma tsafta jiki suna da matuƙar muhimmanci. So samu, mace ta riƙa canza panties aƙalla sau uku a rana, sannan idan an wankesu a tabbata an shanya su a rana sun bushe tas!


Hakazalika tsaftar towel da ake goge ciki yana da matuƙar muhimmanci. Yana da kyau a riƙa yawan wanke shi da kuma busar da shi a rana. 


10. Idan mace ta lura tana da irin wannan matsala, kamata ya yi ta hanzarta ta garzaya zuwa gun likita, saboda muhimmancin magance wannan ciwo akan lokaci.


Ana yin gwaje-gwaje don gano tsananin da matsalar ta yi da kuma gano maganin da zai kawar da shi ba tare da ɓata lokaci ba. Akan ɗauki sample da ake kira 'vaginal swap' don a yi gwaji a gano wacce iriyar ƙwayar cuta ce ta kama mutum da kuma irin maganin da zai kashe wannan  ƙwayar cuta kaitsaye. Ana amfani da magungunan sha da suka haɗa da Anti fungals kamar su fluconazole wadda sha 150mg a lokaci ɗaya kamar yadda WHO ta ba da shawara.


Hakazalika akan ɗaura marasa lafiya akan Doxycycline 100mg bayan kowanne awa 12 (sau biyu kenan a awanni 24) har na tsawon kwana biyar, ana iya ba da Tinidazole ko secnidazole 2g a lokaci ɗaya. Ana kuma bayar da Azithromycin 2g a lokaci ɗaya. Ana kuma iya ba da tablet da ake tura shi a cikin farjin marasa lafiya.


Ana iya sanya shi ta hanyar amfani applicator da za a tura ciki. Akwai cream da ake shafawa ta waje, hakazalika shi ma akwai wanda ake tura shi da applicator ciki. Wannan dai duk bayan an je an ga likita ne kuma an yi gwaje- gwaje. Duk mai neman ƙarin bayanai bayan taje ta ga likita.


11. Irin wannan cuta ya kan haifar da abubuwa da yawa masu muni. Na farko daga ciki shi ne yana tafiyar da ni'imar 'ya mace a wajen saduwa.


Haka zalika wannan cuta ya kan haifar da matsalar rashin haihuwa ga mace idan aka bar shi ya yi tsanani. Wannan dalili ya sa akwai buƙatar ilimantar da mata akan wannan cuta. Don kuwa indai aka kiyaye, kuma aka ɗauki matakin gaggawa da zarar an ga alamunsa to in sha Allahu ba zai kai wannan matsayi ba.


Sai a yi haƙuri yau mun taɓo ɓangaren da yake yi wa mutane da yawa nauyin tattaunawa. Mu dai burinmu al'ummarmu su samu ilimi akan lafiyarsu don magancewa da kiyayewa.


Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya Amin.


Tushe/Asali: Qaloon Health Support

Monday, 25 November 2024

Duk Ɗan Shekaru 40 Ya Dakata Anan Yanzu

Duk Ɗan Shekaru 40 Ya Dakata Anan Yanzu

WANNAN BABBAN SAƘO NE NA MUSAMMAN GA ƊAN SHEKARA 40 DA WANDA KE DAF DA CIMMA SHEKARU 40.


Assalamu alaikum warahmatullah.


Ina fatan kun tashi lafiya, Allah Ya ƙara lafiya da sutura duniya da lahira.


Bayan haka, haƙiƙa rayuwa cikin musulunci da ƙoshin lafiya ni'imomi ne masu girma da babu abin da mutum zai yi sai dai ya yi ta godiya ga Allah Ta'ala a kansu tare da nuna gazawa da ƙasƙantar da kai a gare Shi.


Duk Dan Shekaru 40 Ya Dakata Anan Yanzu
Hoto: DMP/iStock photo

Marubuci: Shehu Mansur Dala


Shekaru arba'in a duniya wani zango ne mai matuƙar muhimmanci a rayuwa wanda Allah Ta'ala ya nuna darajarsa domin a wannan lokaci ne Yake aiko manzanninsa masu girma. Kuma a wannan zango ne mutum yake zama kamili a kusan kowanne ɓangare na rayuwarsa, yake fara fahimtar haƙiƙanin rayuwa a bisa yadda take musamman idan ya samu kyakkyawar kulawa da ingantacciyar tarbiyya a baya.


Lokaci ne da tunani ya kan canja, abubuwa da yawa na salon rayuwa da jiki su sauya.


A lokacin farin gashi (furfura) yake kankama a kai da gemu, wasu ma tun kafin wannan lokacin ake ganinta.


Wani daga wannan lokaci alamun tsufa suke fara bayyana a gare shi, amma kuma a ilimance ba za a ce da ɗan shekara arba'in tsoho ba, amma yanayin rayuwa da tunani da cimaka na mutum shi ya kan sa ka ga yaro ya tafke, babba kuma ka gan shi kullum kamar yaro.


Waɗansu sukan firgice daga sun shiga shekara ta arba'in su ɗauka su tasu ta ƙare, mutuwa kawai suke jira musamman idan furfura ta yi gaggawar fesowa. Wannan kuskure ne domin idan shekaru 60 ko 70 aka yanka masa zai yi a duniya ai ka ga yana da sauran shekaru 20 ko 30 waɗanda zai iya yin abubuwa masu kyau da yawa a cikinsu.


Tsige furfura ko aske gemu don kada a ga furfurar mutum a ce ya tsufa haramun ne, ai haƙiƙanin tsoho shi ne wanda zuciyarsa da tunaninsa suka tsufa suka daskare, kuma ita furfura ado ce ga mumini kuma alama ce ta nutsuwa wacce take haifarwa da mutum kwarjini a idon mutane musamman idan an tsare mutunci.


Babu laifi a rina furfura da jar kala ko ruwan ɗorawa, amma a guji rina ta da baƙi.


CANZA SALON RAYUWA


Ya kamata ga ɗan shekara arba'in zuwa sama da ma wanda ya kusa kai wa arba'in ya canja salon rayuwarsa kamar haka:


ZUZZURFAR TUNANI


Mutum ya zaunar da kansa ya yi dogon tunani akan rayuwarsa ya gayawa kansa gaskiya ya tambayi kansa tambayoyi uku:


1 Shin me na aikata a shekaru arba'in da suka wuce? Waɗanne ire-iren nasarori na samu kuma waɗanne matsaloli na fuskanta a rayuwata?


2. Shin yanzu a wanne mataki nake na rayuwa, me nake yi?


3. Shin nan gaba me nake son yi? yaya kuma zan yi shi ?


TUNANIN ABUN DA ZA KA BARI


A yayin amsa tambaya ta uku ka yi tunani da aiki na gaske kan me za ka bari bayan mutuwarka wanda za'a riƙa tuna ka da shi ana yi maka addu'a saboda amfanarsa da mutane suke yi?


Wannan abu ne mai yiwuwa saboda mu dubi ɗimbin alkhairi da shugaban halitta ya bar mana mara yankewa wanda ya fara shi ne yana ɗan shekara arba'in. Ashe idan za mu yi koyi da shi ba za mu ce mun makara ba.


TUNANIN WA ZA KA BARI


Lallai a duk matakin da kake kai na rayuwa ka fara tattali da horon waɗanda za ka tafi ka bari domin ɗorawa daga inda ka tsaya a ayyukan alkhairi.


Idan kai Malami ne Malamai nawa za ka mutu ka bari a cikin ɗaliban ka waɗanda za su ci gaba da gwagwarmaya bayan mutuwar ka? 


Idan kai Ɗan Kasuwa ne ko wani mai sana'a ko ma'aikaci, attajirai nawa ko ƙwararru nawa za ka tafi ka bari waɗanda da an gan su za a tuna ka a yi maka addu'a?


Kai har 'ya'yanka ka yi tunani kuma ka tsara ka kuma yi aiki don ganin wanne irin samari da 'yammata da iyaye za ka tafi ka bar wa al'ummarka? Wacce irin gudummawa za su bayar wajen ci gaban zuri'arka da al'umma gaba ɗaya?


CANZA GABA-ƊAYAN SALON RAYUWAR KA


Kusan kowanne ɓangare na salon rayuwar ɗan shekara arba'in zuwa sama da wanda ya kusa kai wa arba'in yana da buƙatar sake nazari da canjin salon gudanar da shi.


Waɗannan ɓangarori sun haɗa da:


1. CAJA BATIRIN IMANI


Ya kamata a ƙara yawaita ibadu masu ƙara imani da tausasa zuciya. Idan kuma ba a yi to a fara.


Misali ƙiyamullaili, farkawa cikin dare domin yin salla da addu'a, aƙalla awa ɗaya ko rabin awa kafin sallar asuba domin a ribaci wannan lokaci mai matukar fa'ida da albarka.


Yin azumin nafila koda sau uku ne a kowanne wata.


Yawaita aikin hajji da Umara ga wanda yake a kusa da garin Makka ban da na nesa. Jaddada tuba da yawaita istigfari.


2. IDAN AN GIRMA A SAN AN GIRMA


Ya kamata wanda ya kai wannan mataki na rayuwa ya san fa yanzu ya zama babba wataƙila an fara tara 'ya'ya, kuma manya sun fara tafiya nauyi ya fara yin yawa, to ya kamata a bar hululu a yi sallama da halaye marasa kyau musamman shaye-shaye, da taɓe-taɓe, da ɗauke-ɗauke da fitintinu da 'yan uwa da maƙota da abokai, a yi sulhu da kowa, a rungumi zumunci, a tallafawa 'yan uwa da sauran mabuƙata.


3. ME KA YI WA ADDININKA?


Ya kamata kowa ya yi wa kansa tambaya wacce irin gudummawa yake bayarwa ga addininsa? Kuma mai zai tafi ya bari na ci gaban addini bayan rasuwarsa?


Wani sai ya zo duniya ya koma bai yi wa addininsa wani abun a zo a gani ba, sai dai kawai ya tara kuɗi ya sayi ƙasa ya yi abubuwa kala-kala ya tafi, shi kenan. Lallai ya kamata a sake tunani, musamman waɗanda Allah Ta'ala Ya ba su dama ta dukiya ko ilimi ko muƙami.


Za ka iya shiga kwamitin wa'azi da musuluntar da waɗanda ba musulmi ba da sauransu.


KULA DA LAFIYA


Ginshiƙan samun lafiyar jiki da ƙarkonsa su ne:


1. Cin lafiyayyen abinci: A yawaita cin ganyayyaki da kayan marmari na asali ba na gwangwani ko kwalba ba. A rage cin jan nama. A guji shan taba sigari da giya da dukkan kayan maye. A tsara lokutan cin abinci. A rinƙa yawan shan tsaftataccen ruwa.


2. Samun wadataccen hutu: A ƙalla a kullum a samu barcin awa shida ba tare da yankewa ba, a wurin da iska take gewayawa. In da hali a haɗa da barcin rana koda na mintina 15 ne.


A gujewa tara barci a ka musamman saboda kawai ana kallo ko amfani da waya.


3. Kaucewa yawan ɓacin rai: Mutum ya guji duk abin da zai jawo masa fushi da ɓacin rai. Idan kuma abin ya faru a yi haƙuri, a kai zuciya nesa. A daina riƙo da hassada da gaba. Waɗannan halaye na saurin tsufar da mutum da haifar da cututtuka musamman na damuwa da karya garkuwar jiki. Yawan murmushi da farin ciki na inganta lafiya da samun tsawon rai a duniya.


4. Motsa jiki: Lallai a kullum mutum ya tabbatar yana motsa jikinsa musamman ta hanyar tafiya a ƙasa, aƙalla tsawon mintuna 40 a kullum.


GEMU BA YA HANA KARATU


A yanzu bayan ka girma za ka iya riskar abun da ba ka samu damar riska ba a baya na karatun addini da na zamani.


Za ka iya shiga harkar koyon karatun Alkur'ani da haddace shi, da kuma majalisai ko makarantun ilimi.


Akwai manyan Malamai da sai da suka girma suka fara neman ilimi kuma suka zama bijimai hamshaƙan malamai irinsu Ibn Hazmi da Izzuddin Ibn Abdussalam da Al-Imamai Alqaffal.


Haka kuma za ka iya komawa makaranta domin kammala karatun boko da yanayi ya dakatar da shi koda kuwa ta salon karatu daga nesa ne ko kuma buɗaɗɗun jami'o'i.


Ka sani cewa ƙwaƙwalwar ka tana da buƙatar abinci lafiyayye wanda shi ne ilimi.


Yi ƙoƙari aƙalla a kullum ka ware awa guda domin karatu, ba lallai sai littattafan larabci ba, akwai littafai na Hausa masu yawa da ɗimbin fa'ida.


ƘARA INGANTA ZAMAN IYALI


Anan ma ya kamata a ƙara nazari akan yanayin zaman da ake yi, a ƙara ƙarfafa hanyoyin zaman lafiya a toshe duk wata kafa ta fitina da tashin hankali.


A ƙara kulawa sosai da tarbiyyar 'ya'ya musamman manyan cikinsu. A riƙa ba su lokaci ana zama da su ana tattaunawa da su.


Idan da buƙatar ƙara aure a yi shi cikin fahimta, a yi adalci kuma a tabbatar za a iya yi ban da rigima.


Sha'awar jinsi ita ce ƙarshen abin da yake ƙarewa ga mutum. Wani ma sai ya tsufa sai sha'awar ta dawo kamar ta matashi (balagar tsufa) ya kamata ma'aurata da iyalansu su fahimci haka kada a zalunci kowa.


Waɗannan su ne muhimman saƙonni da masana suke isarwa ga 'yan shekara arba'in zuwa sama da waɗanda suke dab da shiga arba'in domin tattalin nasarori da aka samu da ƙara haɓaka su da kaucewa matsalolin da aka gamu da su a shekaru masu zuwa da kuma samun damar kyakkyawar cikawa da barin zuri'a managarciya.


Domin samun cikakken bayani duba:


✓جدد حياتك رسالة إلى من جاوز الأربعين للدكتور محمد موسى الشريف

 

✓صحتك بعد الاربعين المعصومة علامة 

جدد حياتك لمحمد الغزالي


✓ريح النسرين فيمن بلغ الاربعين للشيخ محمد بلغوا بن عثمان بن فودي


Ina roƙon Allah Ta'ala Ya inganta rayuwar mu, Ya kyauta ƙarshenmu, Ya albarkaci zuri'armu, Ya tsare imaninmu gabaɗaya Amin.


Ku taimaka ku yaɗa wannan saƙon.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.


Maasallam.

Sunday, 3 November 2024

Dalilai 9 Da Ke Kawo Mikewar Azzakari Kaitsaye

Dalilai 9 Da Ke Kawo Mikewar Azzakari Kaitsaye

 1. Priapism shi ne miƙewar azzakari na tsawon lokaci (tsawon awa huɗu zuwa shida [4-6 hours]) ba tare da sha'awah ba ko bayan sha'awan ya tafi, wanda hakan ya kan zo da tsananin zafi ga mai wannan matsalar. Mata sukan samu priapism na clitoris (clitoral priapism, clitorism), amma ɗaiɗaiku ne. 


Dalilan Da Ke Kawo Mikewar Azzakari Kaitsaye 
Hoto: Vice

2. Priapism ya kasu kashi uku kuma waɗannan rabe-rabe sun shafi yadda jini yake zuwa azzakari ne a yayin miƙewarsa wanda za mu yi magana akansa shi ne ischemic priapism kuma shi ne wanda ya fi faruwa a cikin dukkan priapisms (19 a cikin 20). Yana faruwa ne idan jini ya tsaya a cikin azzakari ya ƙi ya koma bayan tafiyar sha'awa ko kuma ya zo ya maƙale a cikin azzakari haka kawai ba tare da sha'awa ba. 


3. Babban abinda ke jawo wannan matsalar shi ne Sickle cell disease (cutar sikila). Sannan akwai magunguna da yawan shansu ke jawo 'ischemic priapism' kamar magungunan matsalar ƙwaƙwalwa (anti-psychotic drugs) wasu magungunan depression da ake ce musu Selective Serotonin re-uptake inhibitor (SSRI misali: fluoxetine, sertraline, paroxetine da sauransu). Yawan shan cocaine da cannabis (wiwi) yana jawo wannan matsalar. Yawan shan magungunan ƙarfin maza yana kawo wannan matsalar fiye da kowane magani. 


Akwai wata kunama da ake kira da Brazilian wander spider da kuma black widow spider, cizonsu yana kawo wannan matsala. 


4. Matsalar priapism matsala ce da ake buƙata a yi hanzarin garzayawa da marasa lafiya zuwa asibiti (emergency) da zarar an ga azzakari ya tsaya a miƙe fiye da awa huɗu (4 hours) tare da tsananin jin zafi. Abu na farko da likitoci suke yi shi ne ƙoƙarin kashe zafin wannan ciwo. Sannan sai a yi ƙoƙarin zuƙo jinin daga cikin azzakarin ta hanyar amfani da syringe. Idan hakan bai yi ba, za a yi amfani da syringe a tura ruwa mai tsafta (normal saline) cikin azzakarin don ya sauƙaƙa zuƙo jinin daga cikin azzakarin. 


5. Idan zuƙo jini bai yiwu ba, za a yi allurar phenylephrine a cikin azzakarin a ƙaramin dose, sai dai phenylephrine zai iya zuwa da side effects kamar matsalolin zuciya da sauransu. Ya zama dole a maida hankali kan wannan a yayin amfani da wannan magani. Yana da kyau mu fahimci cewa idan aka ce magani yana da side effect, hakan baya nufin tabbas side effects ɗin zai faru akan duk wanda aka yiwa amfani da maganin. Ana ambatawa ne don a kiyaye kuma a tsayar da maganin idan aka ga hakan ya faru, sai dai idan matsalar da maganin zai kawo bai kai matsalar da rashin amfani da shi zai kawo ba, kuma babu wani magani da ya fi shi rashin matsala. 


Za a iya amfani da allurar diethylstilbesterol (DES) ko terbutaline ga waɗanda suke yawan samun matsalar priapism. 


6. Idan magunguna suka ƙi, za a yi surgery. Surgery ɗin ya ƙunshi buɗe wani ɓangare na azzakari tare da buɗe hanyar da jini zai bar azzakarin. Surgery ya kan zo da matsalolin da zai iya sakawa mutum ya samu matsala a mazantakarsa (erectile dysfunction, impotence) amma akan kiyaye hakan ta hanyar penile prosthesis ko penile implant a lokacin da za a yi surgery ɗin. Wannan implant ɗin yana taimakawa wajen gujewa ƙanƙancewar azzakari bayan surgery. 


7. Ana magance priapism ga masu fama da cutar sikila ta hanyoyin da muka ambata a sama. Sai dai ana farawa da ƙara wa marasa lafiya ruwa (intravenous fluids), magance zafi ta hanyar amfani da magungunan kashe zafi masu ƙarfi da kuma taimakawa marasa lafiya wajen numfashi (oxygen therapy). Ana iya ƙara jini ta hanyar canza wa maras lafiya jinin da ke jikinsa (exchange transfusion) amma ba a son yin hakan sai ya zama dole saboda matsalolin da zai iya kawowa. 


8. Ga mai cutar sikila, babban abinda ya kamata a yi wajen rage faruwar priapism shi ne bayar da muhimmanci wajen rage cutar sikila, ta hanyar shan magungunan da suka dace da kuma kiyaye abubuwan dake ɗagawa ko tsananta ciwon. Za mu samu lokaci mu yi bayani daidai gwargwado akan cutar sikila (Sickle cell Disease [SCD]) in sha Allahu. 


9. Amfanin hydroxyurea ga mai cutar sikila ba shi da alaƙa da priapism. Ana bayar da hydroxyurea ne don yana taimakawa wajen ƙara yawan jini a jikin Ɗan Adam ta hanyar samar da sinadarai masu amfani wajen samuwar red blood cells kamar su Hemoglobin F da sauransu. Hakazalika yana rage yawan ruwan red blood cells, yana rage yawan neutrophils (wasu ɓangare ne na white blood cells), yana kuma taimakawa wajen kawar da cells ɗin da suke kawo matsala wa mai cutar sikila (sicked cells). Kamar yadda muka faɗa a baya, side effects baya nufin idan ka sha magani tabbas za ka samu side effect ɗin. Ana ambata maka ne saboda da zarar ka ga wannan matsala ka tsayar da shan magani ka garzaya wajen likita. Don haka muna ƙarfafa wa marasa lafiya su sha maganin nan kamar yadda likita ya faɗa musu. 


Idan yana buƙatar ƙarin bayani kan yadda ake shan maganin da kuma abubuwan da ya kamata a riƙa kiyayewa, sai ya tuntuɓe mu.


Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya.


Tushe/Asali:  Qaloon Health Support

Tuesday, 24 September 2024

Karanta Sirrin Genotype Da Amfanin Shi Ga Al'umma

Karanta Sirrin Genotype Da Amfanin Shi Ga Al'umma

Sakamakon wani rubutu da na yi satin da ya wuce nake bada shawarar ya kamata kowa ya san genotype ɗinsa kafin soyayya ta yi nisa, don rabuwa bayan shaƙuwa babu daɗi, sai wasu da yawa suka dinga neman sanin mene ne genotype? Rubutun ya ƙayatar amma akwai jigon rubutun da ba a sani ba, wanna yasa na ce zan yi gajeren bayani akan mene ne genotype?


Sirrin Genotype Da Amfanin Shi Ga Al'umma
Hoto: Stock Adobe 

Marubuci:- Aminu Murtala Shuaibu


Mutane sun kasu kaso uku ta fuskar halittar jini da Allah ya yi musu:



1. Awai mutum mai nau'in jini AA


2. Akwai mutum mai nau'n jini AS


3. Akwai mutum mai nau'in jini SS


Shi na farko (AA) lafiyayye ne, kuma zai iya aurar mace mai kowanne irin nau'in jini ba tare da sun haifi ɗa mai matsalar amosanin jini (sikila) ba. Kai an ma fi son shi mai irin wannan nau'in jinin ya auri mara lafiya (SS) domin daƙile yawan masu wannan cuta a doron ƙasa.


Idan ya auri mai nau'in jini na uku (SS), 'ya'yan da za su haifa duka za su kasance masu lafiya a karan kansu, amma masu rabin lafiya ne a halittar su. Kenan barazanar su ɗaya ce, dangane da wanda za su aura da kuma 'ya'yan da za su haifa.


Na biyu kuma (AS) yana da rabin lafiya ne (normal but carrier). Shi a karan kansa lafiyayye ne, amma a halittar jininsa rabin lafiya gare shi. Illar tana ga abinda za su haifa ta silar macen da ya aura ko namijin da ta aura. Idan ya auri mai nau'in farko (AA), to duka 'ya'yan da za su haifa lafiyayyu ne a karen kansu, amma akwai yiwuwar su haifi masu irin nau'in jini na biyu (AS) lafiyayye a karan kansa. Amma idan ya auri mai nau'in jini na biyu (AS), to da yiwuwar (probability) ɗin su dinga haifar lafiyayyu (AA), ko masu rabin lafiya (AS) ko marasa lafiya (SS) ko kuma a dinga cakuɗa musu duka. Idan kuma ya auri mai nau'in jini na uku (SS) to wannan kam da matsala babba, domin da yiwuwar su yi ta haifar marasa lafiya (SS) ko masu rabin lafiya (AS), amma yiwuwar samun marasa lafiya ɗin shi ya fi yawa. Don haka ake bada shawarar me rukuni na biyu ya nemi ko ta nemi mai nau'in jinin rukuni na farko.


Na uku (SS), mara lafiya ne, yana fama da cutar sickled cell anaemia (sikila), don haka shi bai da buƙatar kowa wajen aure sai mai nau'in jini na farko( AA), domin ta haka ne kaɗai ba za su samu 'ya'ya masu ɗauke da cutar ba.


Duka 'ya'yan da za su haifa za su kasance masu rabin lafiya (AS), kenan a karan kansu su lafiyayyu ne, illar tana ga abin da za su haifa ta hanyar wanda suka aura.


Jan hankali;


Ya kamata kowa ya san a wanne nau'in yake (AA, AS ko SS) ta hanyar gwaji domin fuskantar abokin rayuwar da ba za su haifi ɗan da zai zamo cikin wahala da ƙuncin rayuwa ba, haka nan ku ma ba za ku kasance cikin ƙaƙanaƙayin rayuwa ba.


Masu sikila suna shan matukar wahala a rayuwa, haka nan iyayensu, sannan tsawon rayuwar su gajere ne, shi yasa da wuya ka ga mai sikila ɗan shekaru sama da 35 (ana samu amma bai fi 1 cikin 100 ba).M


Masu sikila sun kasance ababen shiga rai, ana saurin sabo da shaƙuwa da su, shi yasa duk abin da mutum ya tara to zai iya rabuwa da shi akan lafiyar wani nasa mai sikila.


Maganin bari kar a soma.


A kula:


Duk maganar da muke yi muna yi ne a kan iya namiji, amma kuma hukuncin ya shafi duka ne (maza da mata) domin taƙaita rubutun.

Monday, 17 June 2024

Muhimman Abubuwa 7 Na Amfanarwa Ga Yawan Shan Ruwa A Jiki

Muhimman Abubuwa 7 Na Amfanarwa Ga Yawan Shan Ruwa A Jiki

Yawan shan ruwa yana da matuƙar muhimmanci a jikinmu.


Muhimmancin yawan shan ruwa a jikin mutum
Hoto: Unsplash


Ga kaɗan daga ciki:


1. Wasu masana sun ce yawan shan ruwa yana taimakawa ga masu son rage ƙiba. 


Sun ce yana yin haka ne ta hanyar cika wa mutum ciki ya hana shi jin yunwa bayan ya ci abinci. Sannan kuma yana taimakawa wajen sarrafa abinci da sauran abubuwa da suke jiki. 


Masana sun ce abinda yake jawowa mutane su yi ta cin abinci fiye da kima shi ne saboda suna zaton yunwa suke ji bayan a zahiri ƙishirwa suke ji.


Hakan yana sanyawa su yi ta cin abinci maimakon shan ruwa.


Sai ya haifar da ƙiba. 


2. Yawan shan ruwa yana taimaka wa ƙoda da hanta wajen wanke abubuwan da ba su da amfani daga jikin mutum cikin abincin da muka ci. 


3. Yana taimakawa wajen magance gajiya. 


4. Yawan shan ruwa yana taimakawa wajen kare kai daga ciwon daji na mafitsara da kansan nono da kuma ciwon daji na hanji. 


5. Yawan shan ruwa yana rage ƙunci. 


6. Yana rage ciwon kai. 


7. Yana ƙara ƙarfin jiki.


Yawan shan ruwa yana ƙara kaifin ƙwaƙwalwa, yana taimakawa wajen magance basir (constipation/matsalar yin kashi/bahaya) da kidney stone. 


Akwai waɗanda suka ce shan ruwa da safe yana taimakawa wajen rage musu ciwon ulcer/gyanbom ciki.


Yawan shan ruwa yana ƙara wa fata kyau da lafiya. 


Gareku 'yan'uwa


Wane alfanu kuke samu game da shan ruwa kuma wasu matsaloli kuke fuskanta a dalilin rashin yawan shan ruwa?


Tushe/Asali: Qaloon Health Support

Tuesday, 21 May 2024

Karanta Muhimman Abubuwa 13 Da Ya Kamata A Ce Kun Sani Game da Cutar Hawan Jini Tun Yanzu

Karanta Muhimman Abubuwa 13 Da Ya Kamata A Ce Kun Sani Game da Cutar Hawan Jini Tun Yanzu

1. Hypertension ko Hawan Jini shi ne ake kira high blood pressure, wato tashin pressure na jini a jikin mutum. Mutane da yawa ba su fahimci me ake nufi da hawan jini ba. A tunaninsu jinin ne yake tashi sama daga ƙasa. Sam ba haka bane.

Gwajin lafiyar jiki
Hoto: Medical News Today


Ma'anar pressure a ilimin physics shi ne wani nauyi ko kuma ƙarfi da yake turewa ko dannewa. Ma'ana idan ka sanya ƙarfi ka tura mota ko ka ture mutum ya faɗi, ko kuma ka danne wani abu ya kasa tashi ƙarfin da ka saka shi ne ka sanya masa pressure. To idan ka fahimci pressure, sai mu ce pressure na jini shi ne ƙarfin da jini yake tafiya tare da shi daga zuciya zuwa sauran sassa na jiki a cikin wata kafa da ake cewa artery. Shi wannan artery kamar pipe din ruwa yake (amma fa ƙanana ne, suna nan a ɓangarorin jiki daban-daban). Haka jini yake wuce idan zuciya ta turashi. A lokacin da wannan pressure ya yi yawa sai ya haifar da matsaloli da yawa ga zuciya da sauran sassan jiki. 


2. Ana gane hawan jini ta hanyar gwaje-gwaje da lissafi masu yawa. Sun ƙunshi gwada yawan jinin da zuciya take turowa a wani lokaci, sannan ana auna shi ne a matsayin volume (cardiac output) da kuma ƙalubalen da hanyoyin wucewar jini suke kawowa wucewar jini (peripheral resistance). A taƙaice ana rubuta blood pressure ne ta ɓangare biyu;
 Systolic blood pressure da kuma diastolic blood pressure. 
 
a. Systolic pressure shi ne pressure da ake samu idan zuciya ta yi contraction (Wato ta takure ko ta matse).

b. Diastolic kuma idan zuciya tayi relaxing (idan ta sake ta koma yadda take daa). 

3. Joint National Committee (JNC 7) on Hypertension sun fassra hypertension da cewa shi ne tashin systolic pressure zuwa sama da 139mmHg, ko kuma diastolic ya kai sama da 90mmHg. Ana rubuta blood pressure ne a matsayin Systolic blood pressure / diastolic blood pressure. 
Kenan High blood pressure = 140/90mmHg ko sama da haka. 

4. Kashi 95 cikin ɗari na hypertension yana faruwa ne ba tare da sanin takamammen abin da yake jawoshi ba (idiopathic). Wannan shi ake kira da primary hypertension ko kuma idiopathic hypertension. Sai dai akwai wasu abubuwa da ake gani suna jawo primary hypertension kuma idan an gujesu cikin ikon Allah akan samu ƙarancin matsalar hawan jini.

Waɗannan abubuwa su ne;

a. Hypertension (hawan jini)

b. Shan sigari (cigarettes smoking)

c. Obesity (ƙiba)

d. Rashin motsa jiki (daga mota sai office zaune akan kujera, sai cikin gida a kishingiɗe, ko a zaune ko a kwace). 

e. Diabetes mellitus (ciwon sugar)

f. Dyslipidemia (shi ne lipid [fats and oil] ya yi yawa ko ya yi kaɗan a cikin jini.

e. Microalbuminuria (shi ne yawan albumin a cikin fitsari ya ƙaru kaɗan) 

f. Shekaru (sama da shekaru 55 ga maza, 65 ga mata).

g. Gado daga iyaye da kakanni ga masu ƙananan shekaru (maza ko mata da suke ƙasa da shekarun da aka ambata a sama).

h. Yawan cin gishiri.

i. Stress (tsananin rayuwa).

5. Shi kuwa secondary hypertension yana faruwa ne tare da ko bayan wani rashin lafiya mai tsanani kamar ciwon hanta da sauransu. Idan mutum ya samu waɗannan cututtuka, likitoci sukan ɗauki matakai wajen ganin cewa bai kai ga an samu hawan jini saboda shi ba ko kuma a yi ƙoƙarin sauko da jinin zuwa yadda ake so. 

6. Akwai magunguna da shan su na tsawon lokaci ke jawo hawan jini amma ba a koda yaushe ba, sannan kuma idan mutum yana shan su ana ba shi appointment ya riƙa zuwa ganin likita daga lokaci zuwa lokaci ana auna blood pressure ɗinsa. 

7. Magungunan hana haihuwa da magungunan jin daɗi irin su cocaine da wiwi da wasu magungunan gargajiya suna jawo hawan jini. 

8. Chemicals irin su Lead, mercury, thallium, lithium da sauran heavy metals suna jawo hawan jini ga mai yawan aiki da su. 

9. Wani abun lura a kan hypertension shi ne ba shi da sign ko symptoms (alamun da suke nuna mutum yana faama da hawan jini) a bisa maganar da ta fi ƙarfi. Duk da akwai waɗanda suke cewa sukan yi faama da ciwon kai, gajiya, jiri, gani duru-duru, ko wani ƙara a kunne da sauransu, amma dai magana mai ƙarfi ita ce ba a gane hypertension sai an yi gwaji. Shi yasa WHO suka kira shi "Silent Killer". WHO sun bada shawara akan mu riƙa gwada blood pressure ɗinmu daga lokaci zuwa lokaci. Aƙalla sau ɗaya a wata. Shi yasa idan ka je asibiti kafin ka ga likita, Nurses za su gwada maka BP saboda komai na iya faruwa ba tare da an sani ba. 

10. Idan hypertension ya yi tsanani yana kawo babbar matsala ko dameji ga wasu gaɓoɓi da ake kira 'target organs'. Waɗannan matsaloli sun haɗa da: 

a. Zuciya: 

Kumburin zuciya (cardiomegaly)

Mutuwar cells ɗin zuciya (myocardial infarction)

Heart failure (zuciya ta kasa aikinta na tura jini ga sauran gaɓoɓi ɗauke da sinadaran da gaɓoɓin suke buƙata don yin aiki) da sauransu.

b. Ƙwaƙwalwa

Stroke (ƙwaƙwalwa ce za ta daina aiki saboda jini ba ya zuwa mata daga zuciya; za ta ɗauke wuta sai ka ga mutum kawai ya zama kamar vegetable)  Da sauransu

c. Kidney ma ya kan samu matsalar sa idan hypertension ya yi tsanani.

d. Chronic kidney disease, 

Kidney aikinsa shi ne ya tace abubuwa marasa kyau a jikinmu ya fitar da shi ta fitsari. Idan ya samu matsala, hakan ba zai yiwu ba. 

d. Liver 

Liver kuma tace mana abinda ya shigo cikinmu take yi ta fitar da masu hatsari. Idan ta yi failing shikenan. 

10. Hanyoyin magance hypertension sun kasu kashi biyu: na farko maras lafiya zai canza tsarin rayuwarsa don magance wannan matsala ta hanyoyi kamar haka:

A. Ilimi: akwai bukatar a ilmantar da Mutane akan hypertension. Kuma a gane akwai bambanci tsakanin hypertension da mental tension, stress ko Anxiety. 

Shi hypertension ba a gane shi a fuska ko a ji shi a jiki. Sai dai idan ya yi tsanani. Mutum zai iya jinsa lafiya sumul amma yana da hypertension. Idan maras lafiya ya bi shawarwarin ma'aikatan lafiya, zai yi rayuwa mai kyau ba tare da matsala ba. 

Yana da muhimmanci maras lafiya ya gane cewa shi yake da gudummawa mafi yawa da zai bayar wajen magance wannan matsala. Sannan ya san cewa shi maganin hawan jini in aka fara shansa ba a dainawa. Sai dai a rage. 

B. Rage ƙiba da kuma exercise a kullum (regular aerobic exercise kamar jogging brisk walking [tafiya da kafa tare da dan sauri, Wato Mutum ya yi da dukkan jikinsa) da sauran su) yana da muhimmanci sosai kuma yana taimakawa matuƙa. 

C. Rage cin gishiri: Ana bada shawara ga maras lafiya ya rage cin gishiri. So samu ya daina cin gishiri da ajino moto da Manda (manguli). Maggi ma ya zama dai ƙaramin quantity da zai sa ya ji taste ne kawai a baki. 

D. Akwai abin da ake kira DASH (Dietary Approach to Stop Hypertension) Wanda ya ƙunshi cin abinci mai ɗauke da isasshen kayan marmari (fruits) da ganyayyaki (vegetables) da kuma gudun abinci masu ɗauke da fats ko dairy products (kamar su madara, nono, yoghurt, cheese da sauransu) 

E. Daina shan sigari (tobacco) da giya (alcohol). 

F. Relaxation therapy (hutu) Wanda ya ƙunshi meditation, gudun hayaniya da surutu da gujewa haske mai yawa, da yoga da sauransu! 

11. Waɗannan abubuwan da muka ambato a sama ana shawartar wanda ya san akwai masu hawan jini a danginsa da ya rinƙa yin su don kare kai. Haka kuma wanda babu a dangi ma ya kamata a riƙa yi saboda ko bai samu a dangi ba zai iya samu a shekaru ko kuma a jinsi (maza sun fi mata samun hawan jini saboda suna ɗaga mana hankali.  

12. Ɗayar hanyar magance hypertension shi ne amfani da magunguna. Suna nan da yawa. Irin su Amlodipine, Lisinopril, Losartan, Atenolol, Bendrofluorothiazide, Furosemide da sauransu. 

13. Ana ɗaura maras lafiya akan ɗaya ko biyu daga cikin magungunan nan ne bayan an yi gwaje-gwaje an tabbatar da akwai hawan jini. Likita zai dubi yanayin ciwon ya ga wanda za a ɗaura maras lafiya akan, ko fiye da guda ɗaya daga cikin magungunan.


Tushe/Asali: Qaloon Health Support

Wednesday, 1 April 2020

Maganin Covid-19 da Yardar Allah

Maganin Covid-19 da Yardar Allah

Wannan Muhadara cike take da bayani akan cutar CORONAVIRUS wacce akafi sani da Covid-19, don haka ku hanzarta sauke wannan Muhadara kuma kuyi ƙoƙarin yaɗa saƙon ga sauran al'umma.

Malamai Sunyi Sharhi Dangane da Cutar Sarƙewar Numfashi..

Babban Malamin ya gabatar da wannan Jawabi ne a Majalisin sa da ya saba gabatar da karatu a dukkan ranakun Laraba, a Masallacin Cibiyar Imamul Bukhari dake Unguwar Rijiyar Zaki a cikin birnin Kano.

Kalli Bidiyon Kai Tsaye...

Idan baku manta ba akwanakin baya mun kawo muku muhimman abubuwa 10 da yakamata ku sani dangane da cutar Covid-19 cikin nufin Ubangiji yau mun kawo muku cikakken bayani game da cutar Coronavirus da hanyoyin samun kariya daga cutar da yardar Allah.

Ku hanzarta sauke Muhadara anan ƙasa...

SAUKE AUDIO ANAN


Ya Allah ka karemu da Iyalan mu daga cututtukan zamani Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Monday, 23 March 2020

Karanta Muhimman Abubuwa 10 da Yakamata Ku Sani Dangane da Cutar Coronavirus

Karanta Muhimman Abubuwa 10 da Yakamata Ku Sani Dangane da Cutar Coronavirus

Babban Malamin addinin musuluncin nan, Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar lemo (Allah Ya kara masa lafiya da albarka) ya ja hankulan al'ummar musulmi dangane da cutar nan ta sarƙewar numfashi (Covid 19) da ta addabi duniya a halin yanzu.

Tataccen Bayani Akan Cutar Sarƙewar Numfashi (CORONAVIRUS) A Mahangar Musulunci

Babban Malamin ya gabatar da wannan Jawabi ne a Majalisin sa da ya saba gabatar da karatu a dukkan ranakun Laraba, a Masallacin Cibiyar Imamul Bukhari dake Unguwar Rijiyar Zaki a cikin birnin Kano.

Ga bayanin da Babban Malamin ya gabatar a taƙaice:

Zan yi amfani da wannan dama kafin mu fara karatu domin tunatar da 'yan uwa musulmai a kan yanayin da duniya take ciki a halin yanzu na afkowar cutar nan da ake kira da (Corona Virus).

Mu duba mu gani yadda wannan 'Yar ƙaramar ƙwayar halitta ta cuta, wacce ko da abin hangen nesa (Microscope) sai an ƙura ido sosai ake iya ganin ta, amma gashi ta mayar da kowa gida, ta tayar da hankalin duniya, har ƙasashe masu tinƙaho da ƙarfin kimiyya da karfin tattalin arziki, da cigaba, hankulansu ya tashi! Lissafinsu ya birkice, duk wani abu da suke tunƙaho dashi bai iya amfanar dasu komai ba. Wanda wannan lallai shi zai nuna maka ƙarfin Ikon Allah, zai nuna maka babu wani wanda ya isa gaba ga Allah.

Mu al'ummar musulmi ga matsayar da ya kamata mu ɗauka dangane da wannan cuta:

1. Kallon da musulmi ya kamata su yi wa wannan cuta daban yake da na kafirai, haka a cikin musulmai ɗin ma, mai karanta Alkur'ani da Sunnar Annabi (S.A.W) kallon da zai yi mata daban yake da na wanda ba ya karantasu. Mu musulmi mun yi imani da Ƙaddara, duk wani abu da ya faru to dama can Allah Ya san da shi, kuma bai faru ba sai da ganin damar Allah, saboda babu abinda ke gudana a cikin Mulkin Allah sai da izininsa sai da saninsa. (Malamin ya ambaci ayoyin Alkur'ani mai girma a kan haka).

2. Mu musulmi mun sani cewa ba wannan ne farau ba, ba yanzu aka fara samun irin wannan annoba ba, Allah Ya sha aiko da azabarsa ga al'ummomi da suka gabace mu, saboda sun kangarewa tafarkinSa, sai Allah Ya aika musu da annoba iri daban-daban, misali: mutanen Fir'auna Allah Ya aika musu da annoba iri-iri, kamar annobar ambaliyar ruwa, annobar jini, duk abinda suka buɗe sai suga ya zama jini, annobar fãra da kwarkwata. A ƙarshe kuma Allah Ya halakar dasu, haka mutanen Annabi Nuhu kafinsu, Allah Ya aiko musu ambaliya ya halakar dasu, haka mutanen Annabi Lud Allah Ya kifar dasu suka halaka baki ɗaya.

3. Duk da cewa ita wannan al'umma ta Annabi (S.A.W) Allah Yayi alƙawarin ba zai tumɓuketa Ya halakar da ita baki ɗaya ba, idan da Allah Ya so haka ɗin tabbas zai iya, irin waɗannan musibu sun isa shaida a kan haka, to amma Allah sai ya aiko da irin wannan annoba domin jan kunne da kashedi ga bayi. Yayin da annobar tazo kuma bata banbance salihi nagari da na banza, kowa haɗawa take dashi, sai dai tana zama Rahama ga Salihai, azaba kuma ga fanɗararru.

4. Daga cikin darasin da ya kamata musulmi ya lura dashi a kan sha'anin wannan cuta, mu duba mu gani, a lokacin da Ɗan Adam yake tutiya, yake tunƙaho cewa ya mallaki ilimi, ya mallaki ƙarfin tattalin arziki, wasu har suna ganin Allah ma baya yi musu komai, su sun isa, su sune!!! Kwatsam sai ga wata 'yar ƙaramar halitta daga halittun Allah, wacce ido ma baya iya ganinta saboda tsabar ƙanƙantar ta, sai gashi ta baza duniya, ta bazama manyan ƙasashe, tattalin arziki yana ta rushewa, kowa ya firgita. Lalle wannan ya isa wa'azi! Wannan ya isa shaida akan girman Allah da ƙarfin mulkinSa.

5. Mu musulmi mu sani cewa babu abinda zai yaye mana wannan annoba illa kaɗai mu koma ga Allah, mu guji dukkan abubuwanda ke janyo Allah Yayi haka ga al'umma, kamar manyan laifuka, Zinace-Zinace, Zalunci, Ɓarna a bayan ƙasa.

6. Mu sani cewa komawa ga Allah shine matakin farko domin magance wannan annoba, duk wani abu da ba wannan ba ciko ne, amma komawa ga Allah shi ne Jigo. Mu koma ga Allah da yin addu'o'i da yin istigfari.

7. Mu sani cewa lalle babu wata musiba da wuce a jarrabeka a cikin addininka, yau gashi ana ta rufe masallatai, ana hana fitowa sallar Jam'i, har sallar juma'a da yawa daga ƙasashe sun bayarda sanarwa a dakata sakamakon wannan cuta. Lalle wannan abun tsoro ne! Kamar Allah Yayi fushi da mutane ne yace: Ku fita ku bar min ɗakuna na (Masallatai) tunda ɓarnar ku a bayan ƙasa tayi yawa. Babbar musiba ce a rabaka da ɗakin Allah, a ce babu Umarah, babu Ɗawafi, babu sallar Jam'i, lalle babu musibar da tafi musiba a cikin addini. Tabbas Allah Yana fushi da mutane, Ya zama wajibi mu koma mu tuba ga Allah.

8. Musulunci ya yarda da tsarin killace marasu lafiya, da kuma tsarin kare kai daga cututtuka, musulunci shi ya fara zuwa da irin wannan tsari. (Malamin ya ambaci Hadisi a kan haka) amma kuma a musulunci munyi imani da cewa zama da mai cuta ba shi ke janyo kamuwa da cuta ba har sai idan Allah Ya hukunta haka, cuta a karan-kanta bata da ikon shiga tayi tasiri a cikin mutum sai da ganin damar Allah. ita cutar sababi ce, sababi kuwa baya aiki a karan-kansa sai idan Allah Ya ƙaddara, mu duba mu gani, wuta a al'adarta tana ƙona mutum, amma Annabi Ibrahim da aka jefa shi a wuta sai Allah Ya sa wutar taƙi ƙona shi, mu duba ruwa yana dulmiyar da mutum, amma sai Allah Ya sa Annabi Musa da mutanensa suka taka saman ruwa suka wuce ba tare da sun dulmiya ba, saboda haka ko da abu sababi ne, Allah Yana iya zare sababiyyar yaƙi yin aiki. A musulunci mun sani cewa duk abinda ya sameka ba zai kuɓuce maka ba, duk kuma abinda ya kuɓuce maka ba mai samunka bane. Kamar yadda Annabi (S.A.W) Ya faɗawa Abdullahi Ɗan Abbas.

9. Irin wannan annobar an sha yinta a baya, a lokacin Sahabbai an samu annoba da tayi sanadiyyar rasuwar wasu daga cikin Sahabbai, kamar: Mu'az bin Jabal, da Abu Ubaida bin Aljarrah da sauran su, wannan ya faru a shekara ta (18) bayan Hijra.

Haka nan akwai annobar da aka taɓayi inda tayi sanadiyyar mutuwar 'ya'yan Anas bin Malik kusan mutum saba'in (70), da Ƴaƴan sahabi Abu Bakrata kusan Mutum arba'in (40).

10. Na daga cikin abinda zai magance irin wannan annoba, gujewa aikata Zalunci, danne haƙƙin mai haƙƙi, wajibi ne shugabanni su riƙi yin adalci su guji yin zalunci, domin zalunci sababi ne afkawa irin wannan masifa.

A ƙarshe Malamin yayi addu'a mai ratsa zukata, inda Ya roƙi Allah da Ya yaye mana wannan masifa ba don halinmu ba, Allah Ya dube mu da Rahamarsa da Ludufinsa ya kawo mana agaji.

Waɗannan bayanai an tattaro su ne a taƙaice daga jawabin babban Malamin, mai buƙatar cikakken jawabin sai ya nemi karatun littafin (Alwabilussayyib) darasi na 149.

Marubuci:
Musa Muhammad Dankwano.
Secretary, Dr. Muhd Sani Umar R/lemo Academic Forum.

المنتدى العلمي للدكتور محمد الثاني عمر

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tuesday, 17 December 2019

Karanta Babban Sako Zuwa ga 'Yan Luwadi da Wadanda Suke yin Sha'awar Harkar Luwadi - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Karanta Babban Sako Zuwa ga 'Yan Luwadi da Wadanda Suke yin Sha'awar Harkar Luwadi - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Liwaɗi shine namiji yana neman ɗan uwansa namiji, kamar yadda ake neman mace.

Taɓewa tun a nan Duniya Idan ba'a tuba ba...

Marubuci: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Sheɗan ya fitowa da mutane wannan halaka,  da buƙatu da yawa,  domin tsafi, domin neman kudi,  domin neman daukaka, domin neman mulki, domin neman kwarjini da makamantansu, kuma duk karyace, babu wani abu da ake samu sai kaskanci da koma baya a duniya da lahira.

Babbar musifa babban bala'i, tashin hankali,tir, abin kaico, abin kunya abin takaici, namiji yana neman ɗan uwansa namiji, abinda ba a samu a cikin  dabbobi, amma a sami wasu matasa, wai har sun kafa kungiya ta masu neman maza, wannan kawai ya isa musifa da bala'i
da halaka.

A sami wannan laifi yana yaɗuwa a cikin matasa, mu duba yadda Allah Ta'ala ya yiwa wannan kasa, ta Annabi Ludu (A.S) , da suke liwaɗi aka ruguza su, sama ta koma ƙasa, ƙasa ta koma sama, amma ace wannan abin ya zama, a cikin al'ummar Annabi Muhammad (S.A.W) , Allah ya shiryar da masu yi da waɗanda ake yiwa.

Luwaɗi yana jawowa mai yinsa bala'i 31 kamar haka:

1. Karancin muwafaka

2. Gurɓatar ra'ayi

3. Gurɓatar zuciya

4. Toshewar basira

5. Jefa ƙiyayya da ƙyamar mai yi a zuciyar bayin Allah

6. Yana haifar da ɗimuwa

7. Rashin amsa addu'a

8. Shafe albarka

9. Taɓewa

10. Jarabta da ƙasƙanci

11. Rinjayen maƙiya

12. Kuncin ƙirji

13. Bacin zuriya

14. Mugayen abokai

15. Zama cikin tsoro da firgici

16. Kuncin rayuwa

17. Raunin jiki

18. Mugun mafarki

19. Cututtuka marasa magani

20. Kin jin dadin sauraren Alkur'ani mai girma

21. Gafala ga ambaton Allah

22. Mummunar cikawa

22. Gushewar ni'imah

23. Taɓuwar hankali

24. Zubewar mutunci

25. Ɗabi'ar daud

26. Gushewar kunya

27. Gushewar kishi

28. Kaskanci

29. Rinjayar sheɗan

30. Mala'iku zasu gujeshi

31. Hukuncin kisa ya hau kansa idan an kama shi da shedu ko kuma yayi iitirafi a gaban kotu.

Magani da Yardar Allah:

1. Tuba da Nadama

2. Hakuri daga sabon Allah

3. Canja abokai

4. Addu'a

5. Yawan Ambaton Allah

6. Yawan karatun Alkur'ani mai girma

7. Karanta tarihin magabata

8. Tunanin Wuta da Aljannah

9. Tsoran Mummmunar cikawa

10. Yin aure da wadatuwa da iyali ta inda Allah ya halatta.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA MANYAN SIFFOFIN 'YAN LUWADI DA RAYUWAR SU CIKIN SIRRI KASHI NA FARKO (1)

ME CE CE KUNYA KUMA TA YA YA AKE GANE MUTUM YANA DA KUNYA ??

KARANTA CUTUTTUKA GUDA 30 DA LUWADI YAKE HAIFARWA GA MAI YINSA

Allah ya shiryi waɗanda suka faɗa wannan bala'i ya tsare waɗanda basu faɗa ba Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode





Sunday, 8 December 2019

SHIN KANA YIN IRIN WANNNAN TUNANIN KAFIN KACI ABINCI?

SHIN KANA YIN IRIN WANNNAN TUNANIN KAFIN KACI ABINCI?

A duk lokacin daka zauna zaka ci abunci, wasu halittun ne suka sadaukar da tasu rayuwar ko aka karar musu da rayuwa, saboda kai taka rayuwar ta kara inganta.

SHIN KANA YIN IRIN WANNNAN TUNANIN KAFIN KACI ABINCI...

Marubuci: Rabi'u Biyora


MISALI DA WANNAN HOTON.....

SHINKAFA: Tana da rai amma aka kasheta domin kai kaci ka rayu.

DANKALI: Yana da rai aka kashe shi.

KARAS: Shima yana da rai.

KABEJI: Yana da rai.

SALAK: Yana tafiyar da rayuwar sa cikin jin daɗi aka kashe shi saboda kai.

TUMATIR: Rayayye ne shima aka kashe shi don kaci.

Naman da zaka ci a cikin abunci, shima dai an ciro shi ne daga jikin wata halittar dake tafiyar da rayuwa cikin 'yan uwansa da iyayensa, amma aka yanka shi saboda kai kaci namansa ka rayu.

KAIMA DAKA CINYE WADANNAN HALITTUN....

Wata rana haka zaka zama abuncin wasu halittun idan aka saka ka a kabari, koda yake akwai kalilan din mutanen dasu basa zama abuncin wasu a cikin kasa.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Amfanin Dabino a Jikin Dan Adam Cikakken Bayani da Yadda ake amfani da Shi

KARANTA MAGANIN BASIR KO WANE IRINE DA YARDAR ALLAH

KARANTA MAGANIN 'ULCER' HAR ABADA DA YARDAR ALLAH

A duk lokacin dana zauna cin abunci, bayan nayiwa Allah godiya, sai kuma nayi jinjina ta musammam ga rayukan da suka kare saboda jin dadina da karin lafiyata.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



Sunday, 10 November 2019

KARANTA MAGANIN 'ULCER' HAR ABADA DA YARDAR ALLAH

KARANTA MAGANIN 'ULCER' HAR ABADA DA YARDAR ALLAH

Kamar yadda na yi alkawarin zan kawo maganin Ulcer Alhamdulillah yau na cika alkawarin ga sau fa'idoji nan guda biyu sai a jarraba,kuma insha Allah ana rabuwa da ita ne har abada.

Maganin Ulcer Kowanne Iri


ABINDA ZA A NEMA

1. Kabeji (Cabbege)

2. Lemon tsami (Lemon)

3. Zuma.

Da farko zaka yanka kabejin naka kanana sai ka yi markada da ruwa kamar kofi daya sai ka zuba shi a kofi, sannan ka zuba lemon tsami kamar cokali daya, zuma cokali daya sai ka juya ka sha. Za ka yi haka sau biyu a rana.

HANYA TA BIYU

ABINDA ZA A NEMA.

1. Garin hulba (FENUGREEK)

2. Lemon tsami ( Lemon)

3. Zuma

YADDA ZA A HADA

Da farko zaka tafasa garin hulbar naka da ruwa kofi daya bayan ka tafasa sai ka sauke idan ya dan wuce sai ka zuba lemon tsami Chokali 1 Zuma chokali 1 ka juya kasha,shima zakai haka sau biyu a rana..

MAKOLI MASU ALAKA:




Dukkan hanyar da zaka jarraba zakayi na tsawon kwana 15, insha Allah zaka rabu da Ulcer har abada.

Abin sadaqa a yi wa Annabi Salati.
Don Allah a yada domin karuwar jama'a.

Allah yasa Mu da ce Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



Source: Magunguna A Musulunci

Thursday, 10 October 2019

KARANTA CUTUTTUKA GUDA 30 DA LUWADI YAKE HAIFARWA GA MAI YINSA

KARANTA CUTUTTUKA GUDA 30 DA LUWADI YAKE HAIFARWA GA MAI YINSA

Babbar musifa babban bala’i, tashin hankali, abin tir, abin kaico, abin kunya abin takaici, neman maza, abinda dabbobima basayi, amma an sami
wasu matasa suna yi.

CUTUTTUKA GUDA 30 DA LUWADI YAKE HAIFARWA GA MAI YINSA.


Wai har sun kafa kungiya ta masu neman maza?

Wannan kawai ya isa musifa da bala’i da halaka, asami wannan
laifi yana yaduwa a cikin matasa, muduba yadda Allah ta'ala ya yiwa wannan kasa, da suke luwadi aka ruguza su, sama ta koma kasa, kasa takoma sama, amma ace wannan abin yazama acikin al’umma.

Luwadi yana jawowa mai yinsa bala’i guda 30.

Gasu kamar haka:

1. Na daya:

karancin muwafaka.

2. Na biyu:

Gurbatar ra'ayi.

3. Na uku:

Gurbatar zuciya

4. Na hudu:

Toshewar basira.

5. Na biyar:

Jefa kiyayya da kyamar maiyi a zuciyar bayin Allah.

6. Na shida:

yana haifar da dimuwa

7. Na bakwai:

Rashin amsa addua.

8. Na takwas:

Shafe albarka

9. Na tara:

Tabewa.

10. Na goma:

jarabta da kaskanci

11. Na shadaya:

Rinjayen makiya.

12 Na shabiyu:

kuncin kirji.

13. Na sha uku:

Ɓacin zuriya

14. Na sha hudu:

Mugayen abokai.

15. Na sha biyar:

zama cikin tsoro da firgici.

16. Na sha shida:

kuncin rayuwa.

17. Na sha bakwai:

Raunin jiki

18. Na sha takwas:

mugun mafarki.

19. Na sha tara:

cututtuka marasa
magani

20. Na ashirin:

kin jin dadin sauraren Alkur’ani mai girma.

21. Na ashirin da daya:

gafala ga ambaton Allah

22. Na ashirin da biyu:

mummunar mutuwa.

23. Na ashirin da uku:

Gushewar ni’imah.

24. Na ashirin da hudu:

tabuwar hankali

25. Na ashirin da biyar:

Dabi’ar 'yan daudu.

26. Na ashrin da shida:

Gushewar kunya.

27. Na ashirin da bakwai:

kaskanci

28. Na ashirin da takwas:

Rinjayen shedan.

29. Na ashirin da tara:

Mala’iku zasu gujeshi.

30. Na talatin:

Hukuncin kisa yahau kansa.

GA SHAWARWARI GUDA GOMA.

1- Tuba dayin Nadama.

2- Hakuri daga sabon Allah.

3- Canja abokai.

4- Addua.

5- Yawan Anbaton Allah

6- yawan karatun Alkur’ani mai girma.

7- karanta tarihin magabata.

8- tunanin wuta da Aljannah.

9- tsoran Mummmunar cikawa

10 – Yin aure, da wadatuwa da iyali ta inda Allah ya halatta

MUKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA MANYAN SIFFOFIN 'YAN LUWADI DA RAYUWAR SU CIKIN SIRRI KASHI NA FARKO (1)

KARANTA YANZU KAJI: KO ME YASA MATA KE NEMAN 'YAN UWAN SU MATA DOMIN YIN MADIGO?

KARANTA KAYATACCEN LABARIN WANI MUTUM DA YAYI ZINA A JAMI'A AKWAI DARASI MAI AMFANI A CIKIN LABARIN

Karanta Masifar Da Ta Kunno Kai A Cikin Al’ummar Hausawa

Allah ya shiryi wadanda suka fada wannan bala’i Mukuma Allah ya kiyayemu afkawa ciki Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








Source: TAFARKIN TSIRA