Monday 9 July 2018

SHIN KO ME YASA MATA KE NEMAN 'YAN UWAN SU MATA DOMIN YIN MADIGO???

Tura Wannan Zuwa
Madigo wata hanya ce da Mace zata biya bukatar ta ga yar
uwarta Mace, ta hanyar sunbatar juna, shafe-shafe, rungume-
rungume, da duk wani abun da zai kwantar masu da sha’awar
su ko kuma ya gamsar da su.


Mafi yawan Matan da ke wannan
sana’ar suna afkawa wannan ibtila’in ne a sanadiyar kawance
da masu irin wannan dabi’on, wasun su kan fada ne a
sanadiyar kwadayin abin duniya, wasu rashin yin Aure da
sauran su.

Wata yar Madigo da nayi hira da ita, ta shaida min dalilin tana
afkawa wannan harkan. Ta ce “Maigidana ya kasance mutun
ne mai son kai, ba ya damu da biyan bukata ta ba, daya samu
biyan tasa bukatar”. Ta ci gaba da cewa “Mu na zaune a hakan
har zuwa lokacin da na nemi ya sake ni. Bayan mun rabo na
hadu da wata da muka kulla kawance, har ta kai ta tare a
gidana, daga nan muka fara biyawa junan mu bukata.

Da na
tambaye ta ko zata koma wa uban yayanta?

 Sai tace
“Hmmmm! Ba zaki gane ba, wallahi sam yanzu bana sha’awar
Namiji”.

ALAMOMIN MASU MADIGO

1. Zaki ga mafi yawan masu wannan dabi’ar suna saka sarka a
kafar su. Ba lallai bane duk wanda ya sa sarka a kafa ya
kasance dan madigo, wasu kan sa ne saboda suna da ra’ayin
hakan.

2. Mace ta yawaita yabon kyawon fuskar ki da na diran jikin ki.
Yar uwa ki kiyaye duk macen da takan yawaita yabon dirar jikin
ki ko kyan fuskar ki, to akwai ayar tambaya gane da ita.

3. Sanya zobe a yatsun kafa tabi’a ceta masu yin madigo, ta
hanyar wannan alama ce za su gane junan su. Akan samu
wasu matan da ke da ra’ayin sanya zoben ba tare da sanin
aibin sanyawar ba.

4. Za kiga mace tana da kawaye mata da suke yawan ziyarta ta
ko kuma ita tana yawan zuwa wurin su, ana shegewa dakin
ana shewa da tabe-tabe. Yar uwa ki guje shiga cikin irin wayan
nan kawayen.

5. Yar uwa ki guje kawar da bata jin kunyar sakin al’aurarta a
gabanki, ko kuma mai yawan kalle-kalle fina-fina na batsa ko
kuma na yan madigo.

6. Ki guje kawar da take yawan kai maki runguma, ko ta rika
kallun kirjin ki a lokacin da kika yi kuskuren sakin wani sashe
na tsiraicin ki.

Madigo yana daya daga cikin manyan laifukan da Ubangiji ya
kyamata, sai dai shari’ah bata bada ainihin wani hukuncin da
za’ayi wa masu madigo. Sai dai mafi yawan malamai suna
ganin za’ayi masu hukunci dai-dai da na yan luwadi.

ILLOLIN YIN MADIGO

1. Akan iya daukar cutukan zamani ta hanyar madigo.

2. Yin madigo yana raunana imanin mutum.

3. Yana gusar da kunya gaba daya.

4. Fushin Allah ga masu wannan aikin.

5. Gushewar mutunci a idon mutanen kirki.

6. Masu yin wannan aiki sukan samu kansu a cikin kuncin
rayuwa.

7. Rashin yin kyakkyawan karshe ga masu aikata
madigomadigo.

8. Rashin sha’awar Aure.

9. Za a kai lokacin da mace bata sha’awar namiji gaba daya.

HANYOYIN BARIN MADIGO

Wajabi ne ga duk masu irin wannan dabiar ta madigo da suji
tsoron Allah su nisantar da kan su ga barin yinsa.

Su tuna ko
wane lokaci za su iya riskar mahaliccin su bayan suna aika
wannan mummunar aikin.


'Yar uwa ga kadan daga cikin hanyar
da zaki bi ki nisanci kanki da wannan dabi’on.

1. Ki tuba da niyar ba zaki sake aikata wannan aikin ba.

2. Ki nisantar da kanki ga duk wata kawa da kuke wannan
harkan.

3. Ki yaawaita istigifari.

4. A duk lokacin da sha’awar yin hakan ya taso maki, ki yi
alwala ki karanta daga abinda ya sauwaka na daga Qur’ani.

5. Nisanta kan ki ga kallun fina-finan da hoto nan batsa.

6. Ki rika sawa ranki azabar da ke cikin yin maddigo, a duk
lokacin da sha’awar yin hakan ya ta so maki.

7. Ki yawaita yin azumin Litinin da Alhamis.

8. Ki tuna kusancin Ajalinki, kwanciyar kabari, hisabi da kuma
makomar masu irin laifin ki.

Ya Allah muna tawassali da sunayen ka kyawawa da ka kiyaye
mu da fadawa cikin wannan halin, ka shiryar da masu yi, ka
gafarta mana ka kuma anshi tuban mu.

Ina mai farin cikin samun comment dinku game da
shawarwari, illoli, da alamun da za a gane masu wannan
harkan wanda ban kawo ba.

Domin samun Labarai,Nishadi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHADANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

Source: Murja Lawal

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user