Wednesday 11 July 2018

KARANTA WASIKAR DAN WASAN KWALLON KAFA CRISTIANO RONALDO WACCE YA AIKAWA MASOYA BAYAN MADRID TA BANKWANA DA KULOB DIN - WASIKAR TA DAUKI HANKULAN DUNIYA SOSAI

Tura Wannan Zuwa Ga
A ranar Talata ne Madrid ta sayar da Ronaldo ga Juventus a kan fan miliyan 99.2 inda ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara hudu da zakarun na Italiya.Cristiano Ronaldo ya aika wasikar bankwana ga magoya bayan Real Madrid a duk fadin duniya, yana mai cewa ba zai taba mantawa da kulob din ba a rayuwarsa.

A ranar Talata ne Madrid ta sayar da Ronaldo ga Juventus a kan fan miliyan 99.2 inda ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara hudu da zakarun na Italiya.

Hakan na nufin zai zamo daya daga cikin 'yan wasa hudu da suka fi kowa tsada a duniya.

Ronaldo, mai shekara 33, ya lashe kofin zakarun Turai sau hudu da kuma kofin La Liga biyu a Madrid.

Shi ne dan wasan da ya fi kowa ci wa Madrid kwallo a tarihin kulob din, inda ya zura kwallo 451 a kaka tara.

"Lokaci ya yi da zan bude wani sabon shafi a rayuwata, a don haka na nemi kulob din ya sayar da ni", kamar yadda ya fada a wata sanarwa da aka fitar .

Shekarun da na shafe a Real Madrid da wannan birnin, kusan su ne mafiya dadi a rayuwata.


Ina matukar nuna jin dadi da godiya ga wannan kulob da magoya bayansa da kuma birnin Madrid.

Yanzu
Babu abin da zan iya yi sai dai nuna godiya ga wannan kulob, da magoya baya da kuma birnin. Ina mika godiya ta kan soyayya da kaunar da aka nuna min.

Sai dai, na yi amannar cewa lokaci ya yi da zan bude wani sabon shafi a rayuwata, a don haka na nemi kulob din ya sayar da ni.
Haka na ke ji, kuma ina neman kowa, musamman magoya bayanmu, su fahimci inda na sa gaba da kuma matakin da na dauka.

Hakika sun yi duk abin da ya kamata a shekara tara da ta gabata. Shekaru ne da babu kamarsu.

Lokaci ne na nuna dattaku da jimami, na yi dogon tunani, sai dai abu ne mai tsauri saboda Real Madrid na sahun gaba.

Sai dai na sani hakika ba zan taba mantawa da irin kwallon da na taka a nan ba, da kuma irin nasarorin da na samu.

Na zauna da abokan wasa masu kirki matuka, kuma mun yi rayuwa mai dadi.
Magoya baya sun nuna mana kauna kuma tare mun lashe kofin zakarun Turai uku a jere - biyar a shekara hudu.

Kuma na lashe lambobin yabo a karon-kaina. Na lashe kyautar Kwallon Zinare hudu da Takalmin Zinare uku. Duka a wannan gagarumin kulob.

Real Madrid ta sauya rayuwata, da ta iyali na, a don haka ne nake mika godiya ta: Ina godewa kulob din, da shugabansa, da daraktoci, da abokan wasa na, da likitoci, da jami'an lafiya da kuma ma'aikatan da suka taimaka mana.

Ina sake mika godiya ga magoya baya da jami'an kwallon kafa na Spain.
A shekaru taran da na shafe a nan, na murza-leda da gogaggun 'yan wasa. Ina martaba dukkanninsu.


Na yi doguwar shawara kafin daukar wannan mataki, zan bar Real Madrid, zan daina sanya rigarta, zan bar filin wasa na Santiago Bernabéu, amma za ta ci gaba da kasance wa a zuciyata a duk inda nake a duniya.

Ina godewa kowa-da-kowa, kamar yadda na fada a karon farko a filin wasanmu shekara tara da ta gabata: A ci gaba da gashi Madrid.

Paris St-Germain ne suka sayi 'yan wasa biyu mafiya tsada a duniya - fan miliyan 200 ga Barcelona domin sayen Neyrmar, da kuma miliyan 166 don sayen dan Faransa Kylian Mbappe a watan Yuli bayan ya shafe shekara daya a matsayin aro.

Barcelona ma ta biya Liverpool fan miliyan 142 lokacin da ta sayi Philippe Coutinho a watan Janairu.

Juventus ta wallafa zanen dan wasan a sanfurin irin murnar da yake yi idan ya ci kwalloWa zai maye gurbin Ronaldo?

Duk da cewar sun lashe kofin zakarun Turai uku a jere, ana ganin Madrid na son sauya fasalin tawagarta.

Sun kare a mataki na uku da tazarar maki 17 tsakaninsu da Barcelona a La Ligar bara.
A yanzu sun nada sabon koci, dan kasar Spain, Julen Lopetegui.

Ana hasashen za su iya neman dan wasan Paris St-Germain Neymar mai shekara 26.

Sai dai hakan zai ja hankali saboda dan kwallon ya shafe shekara hudu a abokan hamayyar Madrid wato Barcelona kafin ya koma PSG kan fan miliyan 200.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishadi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHADANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

Source: BBC HAUSA

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user